Sashe 17
Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ya Mukhtar ba zan iya fita da wannan rigan cikin maza ba hakan ya sabawa Addi...."
Wani wawan mari ya sauke mata har seda ta faÉ—i
"ke wai yaushe na zama sa'anki da zan faÉ—a ki faÉ—a?"
Tana dafe da kunci cikin gunjin kuka ta miƙe
"Babu biyayya a bijirewa ubangiji ya Mukhtar ba zan iya..."
Sake kifa mata mari yayi ya ja hijab É—in ya fisge ya yar kan ya janyo hannunta suka yi cikin parlorn tana tirjewa.
Chak ta tsaya tana karewa parlorn kallo, mata da maza ne daban daban cikin shiga irin ta rashin sanin darajar kai wasu na rurrungume da juna yayinda kwalaben shiha suka yi bakwai a parlor hayaƙi har ya fara cika parlorn yana maida wutan wani fari fari baki baki, ganinsu tare yasa aka hau ihu sai kallon maita mazan suke mata da sauri ta koma bayanshi ta ɓoye.
Rita wacce tsab Alaya ta gane ta ita ce ta kawo shi daren farkonsu a Buge tace
"Ga dae kyau sede babu wayewa duhun kai yayi yawa"
Shewa suka É—auka don a yadda tayi maganan har da kishi.
"Omoo kuna ganin kaya!"
Wani ya faɗa yana zuƙar shisha ɗin shi yana wani karkata kai yana kare mata kallo.
Fusge hannunta tayi da karfin tuwo ta juya da gudu tana ji suna mata ihu akan bayanta ta faÉ—a É—aki ta rufe kofar da key ta zube a wurin tare da fashewa da matsanancin kuka tana squezing zuciyarta dake zafi da hannu biyu gwanin tausayi...
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
   (heart touching story)
بسم لله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Twelve*
*Sometimes idan muna karanta labari mu kan ji kaman almara har mu kan yiwa kawunan mu tambayar cewa anya hakan na faruwa? Wannan Page is a dedication to waenda suke cikin ibtila'in auren mashayi, masu haƙuri da juriya da kaddararsu. Sadaukarwa ce ga uwar da Allah ya jarraba da haihuwar ɗa wanda jarrabawarshi ta zama shaye-shaye, Allah kana ji kana gani ya Allah ka shirya mana zuri'a, ya Allah ka kara musu haƙuri da juriya, ya Allah Alfarmar annabi da alqur'ani ka musanya musu kaddarorinsu daga baƙi zuwa fari*
(Ni kaÉ—ai na san what i went to wurin rubuta wannan Page, a painful True life story)
A wurin wani wahalallen bacci ya kwasheta ba ita ta farka ba sai da aka kira assalatu, Miƙewa tayi ta shige toilet ruwa ta fara watsawa kan ta ɗaura alwala tana jin yanda zuciyarta yayi mugun nauyi haka dae tayi sallah ta nemi magunguna ta sha kan ta kwanta, bacci ta sake yi ba ita ta fito ba sai karfe tara sanye da hijabin da tayi sallahn asuba dama da shi ta kwanta, a parlorn ta tsaya tana kallon yanda suka maida shi, kyamar parlorn gabaɗaya ya shige ta, haka dae ta daure iya dauriya ta soma tattare parlorn har ta gama ta share ta fesa air freshner kan ta nufi kitchen don neman abinda zata ci.
   Bata gama dafa indomie din ba taji motsi, da sauri ta juya tana kallon kofan kitchen ɗin a tsorace sai suka haɗa idanu, babu kaya a jikinshi daga shi sai karamin wandon jeans, daga dukkan alamu har lokacin ba wai ya dawo daidai bane daga abubuwan da ya ɗurawa kanshi.
"ke wato ma ina wasa dake ko? Ni zaki dizga? U are very stupid...don ubanki sau nawa na buga miki kofa kika barni shanye ana min dariya?"
A tsorace take matsawa ganin yana kokarin cire belt din jikinshi muryarta na rawa tace
"Kayi haƙuri, don Allah ka saurareni ya Mukhtar..."
Tun kan ta sauƙe sunan ya fara zuba mata belt ɗin, be ji tausayinta ko na minti ɗaya ba sai da yayi mata duka har da kafa kan ya juya ya fice yana cewa gobe ta kara...
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Innalillahi wainna ilaihi rajiun" abinda take ta nanatawa kenan tana kuka, da kyar ta iya lallashin kanta ta miƙe ta nufi daki bayan ta kashe gas ɗin indomien da bata ci ba kenan, tana hawaye tayi wanka idonta ɗaya yayi jajazir jini ya kwanta gefen fuskanta ga shatin belt nan har kusan uku jikinta yayi wani irin Red abin ka da farar fata.
Cikin uniform ta shirya don ta yankewa zuciyarta duk wuya zata yi karatu ko don nan gaba ta iya tsayuwa da kafafunta idan Mukhtar be yi sanadin ta ba, ji take kaman zata mutu kwana kusa a yanda take jin kirjinta da ciwonshi da ya dawo sabo fiye ma da na baya, tafin hannunta ta ware ta É—an zubawa idanu kan ta gimtse tana sake ajiyar zuciya me nauyi na tsantsar damuwa a haka ta tafi makarantar, dayake bata kula kowa babu wanda ya damu ya tambayi me ya sameta ko ya akayi ta ji rauni har aka tashi bata iya ta ci komai ba.
Bayan ta dawo ta haÉ—a custard ta sha ta sake shan magunguna kan ta janyo wayanta don jin lafiyar mahaifiyarta.
Wani irin sabon baabin wahalar rayuwa ne ya buɗe mata, Mukhtar bashi da tausayi ko imani ko na miskala zarratin, ga zafin zuciya matukar ya sakata yin abinda ya saɓawa addininta in ta ƙi haka yake mata dukan mutuwa, marin shi a gareta ya zama kaman man shafawa da da matukar wuya a wayi gari a yini be kai hannunshi jikinta ba, ga bautar yi masa girki da abokansa wanda ba kadan ba idan suka tashi zuwa, a kullum se sun nemi ganinta ita kuma bata fasa ƙin fita ba ta kulle kofan ta gam shi kuma da safe ya mata dukan mutuwa, ko yaushe in yana bukatarta haka ze je mata walau yana hayyacinshi walau yana cikin maye, duk wani alwashi da ta ci a farko akan Mukhtar bata iya ta soma tabuka komai ba don gani take har Abada Mukhtar baze chanza ba, bata da lafiya sossai don zuciyarta ya sake rauni kan rauni sede babu wanda ta faɗawa haka take lallaɓawa kuma take karatu.
   Yau suke gama waec ta yi jamb tun sati biyu da suka wuce, Alhamdulillah sun gama lafiya da Fatan jiran sakamako me kyau, a koyaushe tana jinjinawa Maami da irin jajircewarta a kanta Dukda wani sa'in idan muktar ya mata wani abin sai wata zuciyar ta raya mata dole ne ai Maami ta so ta don ta san zama da ɗan ta sai wanda iyayenshi suka sallama, da sauri kuma sai ta yi a'uziyya ta kawar da tunanin don ta san Maami da zuciya ɗaya take mata hidima kuma take tausayinta, babu wanda ze ganta ya shedata sbd wani irin rama da tayi a watannin da ta durfafi yi gidan muktar, tayi wani irin haske har kana ganin kalar green green a jikinta in kana kallonta, idanunta sun kara girma da haske haka hancinta ya sake fita zirrr, bata wani ado bare kwallaya in tayi wanka ta shafa mai ta sa kaya shikenan.
Yanzu da ta gama Waec zaman gidan ya zame mata kaman wacce take rufe a prison na karkashin ƙasa, Rita a gidan take rayuwa daga parlor zuwa kitchen duk nata ne yayinda Alaya ke ɗaki a koyaushe abinda ke fitar da ita yunwa sai kuma idan shine ya zo ya sakata girki amma bata yi ta ajiye kam don ba lallai ma wasu ranakun yana kwana a gidan ba, kaman yau, gabaɗaya yinin tayi shi ne ba daaɗi sbd hayaniyarsu da suka yini yi bidiri kala kala a gidan, kaman wani kwarya kwaryar lifaya ne suke yi a gidan, daga inda take a ɗakinta babu irin warin ababen Mayen da bata ji, tana dukunkune kan gado, tana bukatar shan sassanyar iska marar surki irin wannan, ji take kaman zata mutu ne sbd wari da tashin zuciya.
Kofan ta da ta kulle ne yinin ranar gabaÉ—aya don ko abinci bata iya fita ta nema ba taji ana bugawa da karfi, chan ta jiyo dakakkiyar muryarshi yana kiran ta da sunan da shine ya raÉ—a mata wato
"ke! Ke!!"
Gabanta ya faɗi, zuciyarta ya hau tseren bugu me zata mishi a wannan yanayi da yake ciki? Kallon jikinta tayi idan tana son lafiyan jikinta kuma abu me sauƙi shine ta bude kofan taji me yake tafe dashi sede tsoro kaman ta narke ta ɓacewa gani da sauraranshi ya lullubeta, jin kaman ze ɓalla kofan ne yasa ta sanya kafafunta ƙasa kaman wacce kwai ya fashewa a ciki ta nufi kofan hannunta ɗaya na kan zuciyarta da bugawarshi har ya shafi numfashinta, hannunta na kakkarwa ta miƙa ta buɗe, banko kofan yayi sai gata gabanshi ya fisgo ta riƙo na mugunta yayi mata
"yarinya in ba zaki bi abinda nake so ba kina cikin wahala, buɗe bakinki ki karɓa"