← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 36

Sashe 35

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗakin Mukhtar ta nufa, a natse ta sanya hannu zata tura kofan ta ji yayi magana da ɗan ƙarfi
"Dr. Ahmad Don Allah ka kyaleni ba zan yi ba! Ba zan yi ba nace! Me ya saura? Kar ka sake min barazana da sanar da iyalina saboda a yanzu bana buƙatar tashin hankalinsu, don Allah ka rabu dani da zancen nan..."

"Mukhtar ka yiwa Allah ka bari a gwada, sai fa an gwada ake samun dacewa, zamu dace don Allah ko É—an uwanka mu sanar wa in ya so ko ba anan ba sai ayi, its getting late please don't let it be worse than this u really are sufferring"

Mukhtar zai yi magana kawai suka ganta a kansu?
"Me za'ayi? Menene ba'a so mu sani? Me kake ɓoyewa ya mukhy?"

*****

Zaune take cikin tantsamemen parlorn nasu, iyayenta na kan dining suna cin abinci, a yanzu ta san babu wacce ta kai mommy jin daaɗi saboda hankalin Abbanta da ta kawar kan Waenchan banzayen, yanzu burinsu ya cika suna rayuwa cikin jin daaɗi su ukun su babu wata matsala, hankalinta ya rabu gida biyu tana jin hiran irin kayen da Abban su Mukhtar ya sha saboda abinda Mukhtar ya aikata Dukda daga baya an gane ba sa hannunsa sai dae baƙin alƙalami ya riga da ya bushe.

Mommy tace
"ko dae farar kafafun waennan sadaka yallar da ya kwasa ba, ai sun ban mamaki daga shi har matar tashi da basu san menene ma'anar arziki ba ai arziki shine a ci a sha a nunawa talaka wutsiyar rakumi tayi nesa da ƙasa"
Abban Meelah yace
"nayi mamaki daga baya wai akan mutanen nan Alhj Hammad Abdulhameed yake gayamin magana hmm gashinan nan wadda be ji bari ba ya ji hoho"

Wani irin Miƙewa da Meelah tayi tare da buga salati tana wani zazzare idanu shi ya firgita su suka yi kan tilon er ta su a rikice suna tambayar me ya faru? Ta kasa magana sai kawai ta sake fasa ihu

"Jameelah menene? Menene a wayan?"
Abba ya ƙarasa ya ɗauko sai ya ga rubutu ne kawai ta riƙe Mommyn tana ta zare idanu chan da kyar ta fusgo maganan
"Mommy....Captain cold.. Captain cold!"
"Na gane Captain cold naki, wadda kike matukar so amma baki gama bincike a kansa ba me ya same shi? Ya rasu ne?"
"A'a mommy be rasu ba! Mommy sai dae kila na rasa shi, mommy Captain cold complete name ɗin shi Umar Hammad Abdulhameed chanji... Ƙanin mijin Wannan shegiyar.. Mommy Meyasa kuka bari kuka ɓata da babanshi? Abba ka yi mishi magana don Allah ku shirya ina son Umar ba zan taɓa aure ba in ba shi na aura ba"

Duk ta rikice ta rikita iyayen nata,
"Wai kina nufin É—an Alhj hammad chanji shine Captain din naki? Meyasa baki faÉ—a da wuri ba?".
Abba ya ce yana riƙo ta.
"Abba personal information É—in shi are very very confidential saboda yanayin aikinshi, na shafe sama da shekara ina nema na kashe kudade masu yawa don kawai ko full name nashi na samo. Wayyooo na shiga uku!"

"Baki shiga uku ba! Zaki aure shi Jameelah na miki alƙawari!"

*Kar dae ku manta book 1 na gab da karewa wadda be wuci shafi biyu bane suka saura in ma na samu lokaci a goben zan gama su, ku yi hanzarin yin payment don karatu na gaba, in shaa Allah ba zaku yi dana sani ba.
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shaidar biya ta nan
09039206763
500 Naira kacal*

🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)

Adabi Writers Association

Book 1
*Last Page of book 1*

Ba zata ce ga yadda aka yi aka gama duk wani formalities na karɓar gawa ba, ba zata iya fasalta halin da take ciki ba har aka gama komai da ya kamata a yi, idanu kawai take bin taron mutanen da kaman yayyafinsu ake, a take ilahirin gidan Maami ya cika maƙil wasu na Adu'a wasu na zub da hawaye, lallai duk wadda ya san Mukhtar a watanni bakwai zuwa takwas da yayi bayan shiryuwar shi ya san ya rabauta, gabaɗaya alkhairanshi na kwanakin ake tunawa, da kyar take fidda numfashi bata sanin duk abinda mutanen da suke zagaye da ita ke cewa, ita dae gata nan ne ga yanayinta.

"Ina matarshi? Ta zo suyi sallama"
Wani ɗan uwan Abba ya leƙo bayan sun ƙira Maami ta jima a chan, Aunty ruqayya ce ta kama ta ta miƙar tsaye sai taji kaman kafafunta ba zasu iya daukar ta ba, abin mamaki kuma sai ta ganta tana tafiya ɗin kaman a iska har zuwa gaban gawan Mukhtar, a kan gwiwowinta ta zube, da kyar tayi kokarin fusgo kalmar
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun shikenan ko? Shikenan kai kuma ka tafi ka bar mu da wannan ruÉ—aÉ—É—iyar duniyar, ya Mukhtar Meyasa yanzu?.." Tayi saurin yanke maganan tace
"Astagfirullah na san baka yi sauri ba, muma bamu yi jinkiri ba kowa lokacin shi yake jira da yayi babu me karfin ikon hanaka tafiya, Allah ya gafarta maka Ya Mukhtar, Annabi rahama ya san da zuwanka lallai ayar Allah tayi aiki akan ka..."
Su baba ta kalla tace
"Ashe ba'a yankewa bawa tsammani? Ashe babu mahalukin da ya isa shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa? Alhamdulillah in shaa Allahu naka yayi kyau, Ba zan maka kuka ba kaman yadda na yi maka alƙawari, ba zan yi ba.."
Tana maganan ne a rarrabe hawaye na bin fuskanta da tsananin gudu, gabaɗaya ta ɗimauce, babu wadda ya hanata kowa yayi ƙasa da kai yana zub da hawayen tausayinta.

Adu'o'i ta cigaba da jera mishi ana amsawa, saida taji bata iya jan numfashi kan ta dakata, babu wadda ya tsaida ta saida ta gama da kanta ta kai zaune tare da ɗaura hannunta akan gawan ta saki sanyayyiyar kuka da ya kara ɗaga hankalin mutanen wurin, Maami ce da itama hawaye take ta zo ta ɗaga ta, haƙiƙa mutuwa akwai ɗaci kuma akwai zafi sannan aya ce me girma a garemu ga duk wadda ya san labarin Mukhtar zai gasgata faɗin Allah na ɗayanku zai kasance yana aikata sharri har sai gab da zai mutu sai ya aikata alkhairi ya shiga aljanna, haka idan babu rabo ɗayanku zai kasance yana aikin alkhairi dab zai mutu sai ya aikata sharri ya shiga wuta. Allah ka sa muna da rabo a aljanna.

Suna ji suna gani dumbin al'umman musulmi suka sallaci Mukhtar bayan an idar da sallahn juma'a aka tafi da shi gidan gaskiya, gidan da kowa zai je shi, a jikin Maami numfashin Alayah ya É—auke rushing É—inta aka yi zuwa hospital sanin condition É—inta.

****

A hankali take buɗe idanunta da suka yi mata nauyi ainun, dishi dishi take gani hakan ya sa ta ɓata lokaci sossai idanun nata zube a ceiling kan ta fahimci asibiti take, daki-daki haka hoton rayuwarta daga farko zuwa yanzu ke dawo mata kaman wacce aka kunnawa magiji(television) har zuwa kan fitar da Mukhtar da aka yi wadda shine ƙarshen abinda zata iya tunawa, idanun ta maida ta lumshe hawaye na bin gefe da gefen kuncin ta, hannu taji ana share mata a hankali ta waiga sai idanunta suka faɗa cikin na Meelah.

Bata san ina ta samo ƙarfin tashi zaune ba tsabar mamaki da ya so kasheta daga kwance.
"Jameelah?"
Ta maimaita a kan lips É—inta
Da sauri Aunty ruqayya dake zaune kan sallaya ta miƙe
"Alayah? Kin farka? Sannu ya jikin?"
Kallonta tayi ta sake kallon jameelar dake ta zabga mata murmushin da ya fi kama da na mugunta ko na makirci a hankali tace
"da sauƙi Aunty"
Ficewa Aunty ruqayya tayi da niyyar kiran Dr yayinda Jameelah tace
"Sannu Sis, sai kawai kika ganni, mun samu labarin rasuwar mijinki ne yasa nace bari na zo na miki gaisuwa sai kuma muka tarar kema ba lafiya gashi har yau kwananki goma sai dae ki farka ba cikin hayyaci ba a sake miki allura ki koma, sannu Allah ya gafarta masa"
Ta ƙarashe da fuskan damuwa.

Dukda abin da take ji ya tokare mata zuciya hakan be hana ta yin murmushin dake bayyana zallar takaici ba, wannan kuma wani sabon salon wasan kwaikwayon ne? Baya ta matsa ta jinginu da gini a hankali kan ta furta
"Ameen"
A kan labbanta bata sake magana ba har likitan ya shigo, ko duniya zata naɗe bazata taɓa yardar wa kanta saboda Allah ne Jameelah take zaune a wurin ba, ta riga ta san su farin sani son zuciyarsu kawai ke kaisu gangar wadda suka ɗauka makiyi, kuma ita bata ga dalilin sake shigowa rayuwarsu da take kokarin yi a karo na biyu ba ka guji soyayyar maƙiyi don da matukar wuya ya kai zuci.

Sossai Dr Philips ya dubata kan ya cire mata karin ruwan yace ta watsa ruwa ta ci wani abu sai a mayar, Jamila ta miƙe don taimaka mata tayi saurin ɗaga mata hannu, a ranta ta saka zata nunawa jameelar yanzu da da akwai bambanci komin ƙanƙantarshi kuwa, duban Aunty ruqayya tayi tace
"Ayyah Aunty ruqayya É—an taimakeni zuwa bayin"
"Ok Binty"
Kusan haka bakinsu ya riƙe sbd yadda Maami ke yawan kiranta da hakan, da taimakonta ta shiga bayi tayi wanka da ruwa mai zafi, ko da ta fito ta samu Maami a ɗakin da Mukhtar Junior da kuma Tabawa, sannu duk suka mata har ta zauna sai a lokacin Jamila ta musu sallama ta fice, da kallo duk suka bita kan Alayah ta kalli Maami
"Maami ko me ya kawo ta?"
Maami tace
"yadda kika gansu haka na gansu Alayah, Abbanku ma har mamakin ganin Alhj Alhassan ya zo gaisuwa yayi itama matar tashi tana zuwa gida, bamu dae ce musu komai ba kuma ina so ki kiyaye don bamu san da wani sharrin suke tafe ba"
A hankali Alayah tace
"In shaa Allahu Maami"
Daga nan ta shirya aka ɗaura mata Mukhtar Junior kan kafafunta ta soma bashi abincinshi ya ƙarba kuwa da gudu bawan Allah, haka ta zubawa fuskanshi idanu ranta na kunar tuna Mukhtar sai dae tayi alkawari bazata sake mishi kuka ba don haka bata yin ba sai Adu'a da tayi ta mishi a ranta.
Chapter 35 · 0% Book details