← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 33

Sashe 8

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watarana yay Dr yakai samiha makaranta tana da exams ya fito domin Bude mata murfin mota tafito adede lokacin su nihal sun fito domin zuwa office din Wani Malami zasu Kai masa takardu kallon da nihal ta bisu da shi ne yabawa Basma mamaki kamar de ranar ta fara ganin irin kulawa da soyayyyar da yayan yake nunawa kanwartasa basma tace "haba ke kuwa sai kace sabon abu" Basma baza ki ganeba abin nasu ne kullum gaba yake Kara yi wannan kulawar ba Yaya bane yakamata yabawa kanwa irin ta wannan kulawar irin ta masoyan da sukayi nisane matuka acikin soyayyyar su Basma tace Mai kike nufi mi kai Aiken midawo zan fadamiki,bayan sun dawo suka Sami Wani guri ta bayan ajinsu inda babu Wanda zai ju su nihal tace basma "na 'am" Ina sauraronki a gaksiya ba zan boyemiki ba zuciyata ruhina da kuma gangar jikina sun Dade da kamuwa da kaunar Yaya Dr yayan Samiha yanayin girman kansa shariyarsa na sake zurfafani cikin kogin sonsa nihal kinsan Mai kike fada kuwa Yaya Dr Wanda Baya ganin kowacce mace ya kalla Yaya Dr da mata basa gabansa shi kike cewa kina so shi Kuwa Basma Kuma "inshallah "sai na cimma nufina akansa zanfi kowa jindadi idan Hakan takasan ce 'nihal' Amman kinfi kowa sanin halin wannan bawan Allah karki damu nasan ta inda zanfara Ina Miki fatan nasara Basma tace suka tashi suka koma aji.
Komawarsu keda wiya suka Tardda Samiha na rike da littafi tana bitar karatu kafin a shiga jarabawa Wanda yakasance wanan shine halinta akodayauhse domin ta saba da karatu kullum yaya Dr sai yayi mata lesson akan exams din da zasuyi domin Baya son asami matsala ko Daya.
Kusa da ita Basma ta zauna yar gidan ya Dr ya akeciki ah! ya kuke ai na zo naga jakun kunann ku kuma naga ba kwanan nake jiran naga ta Ina zaku fito aikamde gamu mindawo ai minga lokacin da Yaya Dr ya saukeki nihal takatsesu da fadi Kuma shine kukaki zuwa migaisa da sauri Basma tace wa zai je ya masa kallon banzan da yasaba Samiha tace: Allah Kunkasa fahintar sane haka yake shi Ba shi da son hayaniya shiyasa aike Baya Miki duk girman kan nasa sai akan wasu kodan ke kanwarsace shiyasa, Samiha ta dago ta kallesu naso ace Yaya Dr Yaya nane dagaske na so ace ba wai arawa Kan mu Yan uwantakar mikayi ba na so ace mina da alaka ta jini da shi da sauri nihal ta dago ta kalleta ke Dalla bamu Gane mia kike nufi ba dagaske nake muku bamu da wata alaka da Yaya Dr Yaya abdallah da Yaya yazid Wanda ya rasu sune yayyena uwa Daya uba Daya Amman da Yaya Dr da yaya jamilu duk ba mahaifan mu Daya ba asalima ba mu da wata dangantaka ta jini da su.

Nihal !!!

lokaci daya taji juwa na diban ta saboda kar abin kunya ya afku ta fadi agun ta Sami guri ta xauna yanzude kina nufin duk wanann dangantarka da mike gani tsakanin ku ba wai yan uwa bane kwarai kuwa kawai Yaya Dr Yana matukar tausyaina Kuma ya daukeni tamakar kanwarsa nihal ce ta katse zancan da Allah yakara muku zumunci Ameen.

Tunda nihal take Bata taba shiga tashin hankali damuwa da masifa irin ta wannan ranar ba kelan tunda Yaya Dr ba jinin Samiha bane kelan soyayyya suke?,Kai babu batun soyayyya domin da soyayyya suke da zata fadimana Amma ya zamemini dole nayi bincike matuka akan wannan al'amira domin tabbas Yaya Dr yayi nisa acikin zuciyata bazan taba iya cire soyayyyar sa ba Ina masa son da bazan taba iya rabuwa da shiba ko mai zai faru sai de ya faru Amman sai na cimma nufina akansa Ina son sa,Taya zan hakura da wanann kyakkyawan saurayin irin Wanda kowacce mace ke burin fata mutum Mai aji jijji da Kai ga Kuma uwa uba dukiya Ina sonka Yaya Dr Kuma ko Hakan zai kawo karshan kawance na da Samiha tabbas na nemi soyayyyar ka Kuma Sai na Samu ......

Toupa anayin ta ana wata ga wata

Shin nihal zataje ta tunkari Yaya Dr da maganar tana sonsa?

Kuma idan ta tunkareshin shin Kuna ganin zai amince?

Mainene matsayin Samiha azuciyar Yaya Dr?

Sannan wane Hali Samiha zata shiga idan taji kawarta ta furtawa yayan nata tan sonsa?

Sanann ita kanta Samiha wane matsayi ta bawa yaya Dr acikin zuciyarta?
Duk wanann alkalamin Zeey Naseer ne kawai zai iya bayyana muku kuci gaba da bibiyar mu ngd👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽

Ubangiji Allah yaci gaba da shiga lamiran mu yaci gaba da dafa mana ya rabamu da kunci da matsaloli na rayuwa, ubangiji yasa mucika da Imani yakara mana tausayi Imani da Kuma gaskiya acikin zukatanmu 🤲🏼🤲🏼🤲🏼🤲🏼🤲🏼🤲🏼🤲🏼

Kuyi sharing saboda Allah

Haka Kuma Zaku iya adana tambayoyinku Tare da comments zuwa anjima inshallah zan Bude group domin tattaunawa.
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

ZEEY NASEER

ABOKIN YAYANA😭😭😭😭

Page 6

Nihal ta yanke shawarar tsagaitawa ta fara fuskantar Mai ne tsakanin Samiha da yaya Dr shin kanwan ya dauketa ko Kuma da akwai soyayyya tsakaninku su,tana fatan Allah yasa iya kanwa kawai ya dauketa domin hakanne zai taimaka mata matuka wajan samin soyayyyar ta cikin sauki,tom Amman idan son Samiha yakeyi fa?,Ta Ina zata fara shima Hakan bazai zamo matsala ba domin zata iya ruguza alakar dake tsakaninta da Samiha akan Yaya Dr , tabbas zata Sami cikar burinta agun Yaya Dr Ta tsagaita komi har zuwa sukarasa jarabawa tare da fahintar ai nahin abin dake faruwa a tsakaninsu shine abinda yakamata nayi inji nihal.
Abubuwa sunci gaba da tafiyawa Samiha da Yaya Dr Dede.

Watarana ranar da Samiha baza ta taba mantawa da ita ba ranar da ta zamowa samiha ranar samin duk wata ansa da Zuciyarta ke ta mata Amman ta kasa saminta,a wannan ranar ne ta San matsyainta ta Kuma San ma wacece ita,kamar yadda Yaya Dr ya saba futa da ita yawan shakatawa duk karshan mako ya saya mata abubuwa ranar ma sunfita sunje Wani gurin Shan ice cream suna zaune yaya Dr yake mata Wani kallo Wanda tunda take da shi Bai taba yi mata irin saba kallon da yasa jijiyar ta da tsikar jikinta fara tashi ba tare da ta shiryaba gaba Daya jinta tayi Wani barkwakwai ba tare da tasan dalili ba,kasa jurewa tayi tace: yaya mai ke faruwane wannan wane irin kallo ne?,sai kace baka taba gani naba Wani kayataccan murmushi ya saki Wanda Bai yaba yi mata irinsaba Samiha yakira sunan ta "na'am" Yayana Samiha tunda Nike a rayuwata bantaba tunanin zan so wata maceba Wanda son zai hanani nutsuwa ya sakani tashin hankali na fara fita a hayyacina ba min taso tare tun mina yara komi namu tare na dauki Hakan a matsayin yan uwantaka a kullum mina girma wanann soyayyyar da shakuwar na sake shiga tsakanin mu wanann ne yasa nake tayiwa Kai na tambaya Anya wanann iya soyayyyar Yan uwantakane tun muna yara abdallah yasha fadimin cewa wanannan soyayyyar ba yan uwanta kabace yasha cemin sonki nake amamn Ina yi masa musu da cewa ni kawai na daukeki ne amatsayin yar uwata,a kullum damuwa dake karuwa yake acikin zuciyata nayi tuanani Mai zurfi na Gane cewa tabbas sonki nakeyi kaunarki ta mamaye zuciyata Bana tunanin zan iya rayuwa da wata mace bayan ke,kece farinciki na dake natsara duk wata rayuwar aurena dake natsara komi na rayuwata Ina sonki Ina kaunarki hakika kece farinciki na,na tsara na furtamiki abin dake Rai na ayaune saboda tsoron karwani ya shigo rayuwanki alokacin da banyi tsammani ba ni Kuma Ina ta boye abin da yake Rai na,Samiha Dan Allah karkice ba kyaso na domin bazan taba iya jurewaba,zan iya bada rayuwata domin taki zan iya komi domin ki.......
Wani kuka Mai cike da tausayi tare da farinciki Mai kunshe da tambayoyi iri_iri acikinsa Samiha ta saki kallon Yaya Dr takeyi tarasa wane irin kalma zata fadamasa wacca zata sanyashi irin cikin farincikin da yasakata tunda take a rayuwarta Bata taba tsintar kanta cikin farincikin irin na yau ba,ta rasa Taya zata nuna wanann farincikin murmushin da yaga tanayine ya tabbatar masa da tabbas soyayyyar sa ce ta kawo haka "alhamdulillah " Samiha Koda bakice komi ba fuskarki ta fadimin nagodewa Allah da zuwan wanann Rana hakika tunda Nike bantaba shiga farinciki irin na yau ba yau ta zamo babbar Rana Mai cike da tarihi Wanda bazan taba mantawa da shi ba.

Tashi sukayi suka tafi gida har sukaje gida Samiha Bata iya dagowa ta kallesaba saboda Wani mugun kunyarsa taji ta Kamata tare da narkakkiyar kaunar sa da take kara shigarta,Bayan yayi parking zasu fita ya kira sunan ta Samiha: "na'am" ki dago Kai ki kalleni ko nasami nutsuwar ruhi da farinciki ki dago Kai ki kalleni ko zuciyata ta Sami nutuswa kyawawan idanuwanta masu kyan kallo ta juyo ta dubesa tace:
Yaya Dr Ina sonka Ina matukar kaunar ka Ina maka irin kaunar da ake iya bada Rai da rayuwa Kai ne farinciki na bazan taba iya rayuwa babu Kai ba,haka Kuma bazan taba iya bawa Wani na miji gurbi acikin zuciyata ba, murmushi yayi Wanda ya sake bayyana asalin kyawun sa Nagode kanwa gaba dayansu murmushi suka sakeyi suka fito kowa fuskarsa dauke da farinciki da walwala...........💗

MAFARIN al'amira Yaya Dr ya bayyana soyayyyar sa ga Samiha tom ya nihal Kuma zatayi?

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

ABOKIN YAYANA

ZEEY NASEER

Page 7
Chapter 8 · 0% Book details