← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 33

Sashe 20

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai gadi ta kira ya taimaka suka saka shi cikin mota mai gadin momy ta saka ya tuka su ya kai su asibitin lokaci daya akan basu taimakon gagggawa sai da aka shiga da shi momy ta sami nutsuwar Kiran dady ta fadi masa yace gashi nan zuwa "inshallah"haka sukayi ta gewaye gewaye cikin asibitin nan har tsawon minti talatain tukun likita ya fito tambayar sa sukayi mai ke faruwa yace ina mahaifin sa akace masa yana nan zuwa yace Idan ya zo ace yana son ganin sa "To sukace masa"
Sannan yace musu kar wanda ya shiga dakin da yake yanzu dan yana bukatar hutu haka sukayi ta faman kewaye kewaye har dady ya sami isowa yana zuwa momy ta fadi masa sakon likita hakanne yasa ya tafi momy ta busa juyowa yayi yace mata "Kibari najeni tunda ni yace Yana bukatar gani"Aah alhaji Suraj de danane sannan duk abin da yake damunsa babu bukatar aboyemin babu yacca daddy zai yi haka yabari momy ta bisa Samiha ji tayi gurin yayi mata fadi baza ta taba iya jurar sai sundawo taji mai ke damun Yaya Dr ba tasan kuma bai kamata ace ta bisu ba amamn tabbas binsu zatayi baza ta taba iya jurewa sai sun dawowa ba.

Tana isar kofar office likitan ta tarar ta abude momy da ta shiga daga karshe bata sami nutuswar rufewa ba hakanne ya bawa Samiha daman juyowa zancan da suke yi sai taga babu bukatar ta shiga ciki tunda tana ji.

Likitane yace "Alhaji kai kade nake son gani"Karka damu Dr ni mahaifiyarsa ce wacca na haifesa duk wata damuwa ta sa yàkamata ace na sani ka fadi duk wani abu dake damuna suraj babu wanda yafi kaddarar ubangiji dole mutum ya zama cikin shiri wajan karbarta.

Gyaran murya yayi badan ya so ba yace "Kamar yarda kika fadi kowane bawa yana da kalar tasa kaddarar kamar yarda kika fada yanzu tom a gaksiya bazan boye muku ba danku Suraj ya kamau da matsananciyar cuta wadda da kyar zai iya sake wata guda daya acikin duniya"

Cikin sauru momy da dady suka dago kai suka kallesa likita bamu gane mai kake nufi ba daman akwai wanda yasan lokacin da bawa zai mutu?babu alhaji amman yanayin jikin Suraj ba karamin kwana bane zai ta sheshi Suraj ya kamu da matsanancin ciwon zuciya zuciyar shi gaba daya ta lallace damuwata tayi masa yawa nayi iya bakin kokarina naga Koda wani aiki da zan iya masa amman Ina babu damuwar da yake ciki ita ta haddasa komi tabbas yanayin jikin Suraj sai de ubangiji.

Samiha dake waje ne tayi wani uban Kara wanda gaba daya yasa hankalin su ya tashi zuwa sukayi suka tararta a sume babu inda ke motsi ajikinta "Innalillahi wa inna ilahiee raji'un allahumma ajirni min musibatin wa'aklifni Khairan Minha"Shine abinda momy da dady suke ta furtawa........

😭

Barkan mu da ranar juma'a miyi hakuri da wanan..... inshallah next post zamiyi typing Mai yawa.

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 24

Tashin hankali ba asaka masa rana a yau a halin gidan sun tsinci kansu cikin tashin hankali mara lissafi irin tashin hankalin da rabon da su shiga irin sa tun mutuwar mahaifan Samiha (Rayuwa ba karabuwa da kalubalai da jarrabawa iri-iri matukar kaga kadena ganin jarrabawan rayuwa a tattare da kai sai de idan ka debe kayanka da ga gaban ubangiji,jarrabawa alama ce ta Imani da Kuma bauta ga ubangiji,ga dukkanin wani bawa hakuri da juriya shine abin da yake bukata dede yadda ka riki kaddaran da Allah yabaka dede cigaban da zaka gani a rayuwan ka, ubangiji Allah kabamu ikon cinye duk wata jarabawa da zamu fuskanta acikin rayuwanmu)Yanayi yayi tsamari damuwa tayi yawa tashin hankali ya bunkasa addu'a ita ce kawai abun da suke furtawa acikin baku nan su bayan wasu a wanni Allah yasa Samiha ta farfado daga dogon suman da tayi farinciki kamar ya kashe su suka rasa inda zasu tsoma ransu saboda momy gani take tamkar Samiha mutuwa tayi sai da ta farfado tukun hankalin ta ya dawo jikinta.

Abu dayane ya tayar musu da hankali yanda Samiha ta farka gaba daya agigice tanayin wasu abubuwa tamkar mai aljanu ko wata zaucacciya gaba daya ta rikice magan ganun takeyi marsa kan gado sannan masu gigita lissafin wanda ke sauraro "Yaya Dr dan Allah karka tafi kabarni kada kayi nisa da rayuwata bazan taba iya rayuwa babu Kai ba na fadimaka duk abinda na fadamaka ne saboda bansan ta ina zan karya alkawarin auran Yaya Ahmad ba bazan taba iya watsa masa kasa a ido ba kai kai ne wanda ya rayu dani tun Ina yarinya yabani farinciki,sannan alokacin da ka gujeni shine wanda ya zo yabani farinciki alokacin da nike tunanin narasa duk wani jindadi hakika duk cikin ku babu wanda yakamata na juyawa baya saboda duk kaunata kuke domin Allah,ni bansan ya xanyiba Allah ubangiji kabani mafita kuka takeyi tunkarfi cike da damuwa tashin hankali mara lissafi ita kanta bata san tanayi ba,wani kuka ne ya kubcewa momy wanda bata san lokacin da ta fara ba dady ne yace "Kiyi hakuri hajiya inshallah Allah zai kawomana mafita"Haba alhaji kagafa duk yarannan neman zaucewa sukeyi Kuma duk dan sanadin soyayyya damuwa tayi musu yawa suna rayuwar su cikin farinciki amman wanann tsinanniyar nihal din ta zo ta tarwatsa musu farinciki wallahi da nasan zata zama matsala acikin gidana bazan taba bari suyi mu'amala da Samiha ba kukan da momy takeyi yana matukar taba zuciyar dady saboda sai ka rantse karamar yarinyace ke wanann kukan"
Rarrashin ta dady yafara duk da cewa shima juriya yakeyi duk wani karfin gwaiwar sa yakare yama rasa ya zeyi hajiya ko da nihal bata shigo rayuwan Samiha ba tunda Allah ya tsara haka zai faru da su tom sai yafaru sanadin wata duk abin da Allah ya tsara babu wanda ya isa ya kaucewa wannan kaddarrar rarrashinta dady yayi tayi da kyar ya samu ta tsagaita kukan da takeyi,Samiha sukaji maganganun da takeyi sunyi yawa gaba daya ta koma mahaukaciya futuk Kai idan ka ganta sai ka tausaya mata,kan ta sukayi suna ta kama sunanta amman ina bata san sunayiba dady ne yayi sauri yaje yakira likita shikansa likita sai da ya tausayawa Samiha alluran bacci yayi mata saboda ita kadece mafita bashi da wani abu da zai iyayi.

Nan ta samu bacci ya dauketa nan likita yace "A dauke Yaya Dr a akawo shi dakin da Samiha take yana ganin hakan zai taimaka wajan bashi farinciki a dullokacin da ya farfado "

Haka kuwa akayi da yake asibitin kudine na masu kudi kowa shi kadene a dakinsa aka dakko sa aka sanya gadonsa kusa da na Samiha.

Haka suka kwana a wanann asibitin ba tare da sun run tsaba har asuba kuma duk cikin su biyun babu wanda ya farfado bayan dady ya dawo daga sallan asuba yacewa momy taje gida ta kintsa ta hado break fast "Fuskarta car da hawaye tace alhaji bazan iya ba idan na hadoma waye zai ci daga ni har Kai babu mai iya ci"Tom ai ko saboda su Idan suka farka suma ko sunfarka ba iya ci zasuyi ba kawai kaje ka hado musu wani abun a restaurant saboda kar su farka ba wani abin ko yaya nasan zasu taba tom hajiya.

Kirane ya shigo wayan dady ya dagawa yayi dafa gefen da ake Kiran aka gaisar da shi akace Basma ce kawar Samiha ayyah!!Basma yakike alhamdulillah dady tunjiya nake kiran wayan momy amman bata shiga shine nace bara na kiraka sai kahadani da ita mikawa momy wayan yayi yace mata Basma ce.

yana mikawa momy wayan ta fashe da wani sabon kuka abin da ya gigita zuciyan Basma momy lafiya mai yake faruwa tunjiya nida Yaya Ahmad mike ta Kiran wayar ki amman shiru yanzuma shiyasakani a gaba na kira wayan dady na tambayar ma sa ko lafiya da kyar momy ta iya cewa Basma Samiha da Suraj momy ta sake fashewa da matsanancin kuka mai bada tausyayi momy dan Allah ki fadimin mai yake faruwa dasu momy ki fadimin dady ne ya ansa wayan a hannunta saboda ta kasa magana sautin kukan tane kawai ke futa dady ne yace "Basma mina asibiti nan ya fadimata address din asibitin ya kashe wayan".

Gaba daya hantar Basma jitayi tana Kadawa tom mai ya samesu Kuma de ai Samiha ce batta lafiya ita za a iya cewa ko jinyar ce ta sake tashi aka kai ta asibiti tom amamn Yaya Dr fa? "Innalillahi wa inna ilahiee raji'un shine abinda take ta furtawa"Yaya Ahmad ne yace "Duk wanan abun ba zai kai mu ba ki tashi mu shirya mu tafi asibitin"Yaya da wanann asubar haka zakice taya kike tunanin tunjiya bansan halin da matar da zan aura ke cikiba hankalina zai kwanta taya kike tunanin nutuswa zata sameni bayan mai samar min nutuswar tana can bansan halin da takeciki ba haba Basma Samiha fa ita ce rayuwata Ina son ta Ina matukar kaunarta wallahi Ina Jin tamkar idan nasarasata bazan iya rayuwaba.

Haba yaya duk mai yakawo fadin wanann inshallah babu abin da zai sa karasa Samiha kana tare da ita har karshan rayuwanka Allah yasa ta shi kije ki shirya wane shiryawa yaya shijab dina kawai zan zurmiki maitafi bana cikin nutuswan da zan iya wani shiri nan suka fita ba tare da maman su da abban su sun saniba,mai gadi suka barwa sallahun idan sun tashi ya fadi musu sunje unguwa nan suka tafi asibitin Ahamd jiyake kamar ya tashi sama saboda babban burinsa yaje yaga mai yake faruwa da Samiha.
Sun isa asibiti lafiya suna shiga dakin abun da ya ganine ya sake fadar masa da gaba ga gadon Samiha ga na Yaya Dr hakan na nufin tare aka kawo su kelan gaba daya tsorata yayi tashin hankali ya ziryaci zuciyan sa Yana matukar tsoron rasa Samiha a rayuwan sa yana wanann tsoron.
Chapter 20 · 0% Book details