← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 33

Sashe 29

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan tashin momy sabon jimami suka kafa tabbas nihal na matukar son yaya Dr Samiha ta juyo tace "Basma mai yasa nihal bata zo ta sameni ba tace na barmata soyayyyar saba,mai yasa bata zo ta rokeniba"Bamsa watakil tana tunanin baza ki iya sadaukar da soyayyyar ki bane kai innalillahi wa inna ilahee raji'un.
Har akayi aka gama zaman makoki babu wanda ya dawo dede cukinsu .
Ranar sun koma gida Samiha take fadawa yaya abin da yafaru ta juyoo tace "Yaya Dr nayi da na sani a rayuwata Yaya Dr na so ace nihal tabi ta hanya mai sauki wallahi da bar mata kai zanyi amman sai tabi ta hanyar da ta cutar damu wallahi tabbas nihal ba karamin so take maka ba,Allah yayi miki rahana nihal,haka Samiha tayi ta fama kamar mai sun batu Yaya dr kuwa yarasa mai zai ce mata Ida nuwansa sun kada sunyi jajir kai kana gani kasan yana cikin matukar tashin hankali.Mikewa yayi Ina zakaje yaya Dr zan kwanta Samiha bana jin dadi tom sai da safe .

Samiha ita ma ta tashi ta shiga daki bacci kaurace mata yayi ta kasa tana ta tunanin nihal saboda ita gani take kamar ita ce ta jefa nihal cikin halin da ta shiga da sauya rayuwar ta da tayi.Da taga baccin ba xuwa zai yiba ta tashi taje tayi alwala ta zo tayi sallah....

A bangaran yaya Dr kuwa bai san lokacin da hawaye ya fara zubo masa ba,saboda tabbbas idan yace bai taba son nihal ba yayi karya sai de soyayyyar da yakeyiwa Samiha ita ce abin da ta rufe masa Ido daga soyayyyar kowa,tabbas nihal yarinyar kirkice Kuma shine sanadin da yasa ta fara zuwa gun boka tunda da lokacin da ta fara turo masa sako a waya ya kirata sunyi magana ta fahintar juna bai wulakantataba tabbas ya tabbatar da cewa da haka bata faruba,shima yayi kuskure girman kansa bai amfana masa komi ba,Allah yayi miki rahama nihal.
Washegari da safe momy din nihal taje tana gyra dakin tana daga filo taga takarda ta dakko ta fara karantawa duk wani abu da yafaru tsakanin ta da su Basma da Samiha sai da tabawa momy labarin sannan ta fada mata tunda take bata taba aikata zina ba,sai da ta fara zuwa gurin boka ya nemi dole sai ya kwanta da ita tukunna aikin su zai yi,anan ta sanar da su cewa wanannan dan na wannan bokan ne sanann maganar da ta fada musu a baya karyane ta fada musu ne kawai dan kar ta fada musu waye ne hakikanin uban da..........
Kuka momy takeyi mara iyaka yanzu daman Sanadiyyar soyayyya kika jefa rayuwanki ciki matsala nan tagama kuke kukenta ta dau takardar da boye.....

Taku a kullum ZEEY NASEER.
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

CREATED AND WRITTEN

BY

ZEEY NASEER

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 35

Rayuwa tafara tafiya amman kowanannan su kullum cikin tunane tunane yakeyi,momy ta fuskanci haka hakanne yasa ta kirasu ta xaunar da su tayi musu nasiha ta Kuma nuna musu cewa duk abinda Allah ya tsara shiyasan dalili sannan sudena tada hankalinsu wajan tunani akan abinda suka aikatawa nihal duk abin da suka aikata ai ita ta jawowa kanta.

Nan momy ta kwakkwantar musu da hankali suka sami nutuswa,suna tsaka da wanannan shirane sukaji anyi sallama dagowa kai sukayi suna kallon mai fuskar kamar sun santa amman sun kasa gane waye kallon kallo akayi tayiwa juna.
Momy ce ta mike tace "Abdallah ashe kana rayebaka mutu ba duk tsawon wanann lokacin".
Alhamdulillah Allah mingode maka kai ne mai bayarwa kuma mai hanawa yau kadawo mana da Abdallah garemu ,Yaya Dr ne ya mike aguje yakarasa ya rungume Ahmad da tuni alokacin yarintarsu ta fara dawomasa ya tunano irin tsananin kaunar dake tsakanin su,nan sukayi ta kuka shi da shi da kyar momy ta rarrashesu suka zo suka xauna,ku rika abu sai kace ba maza ba ku baku iya daurewa ne.
Bayan sun xauna Samiha ta dago kai ta kallesa kasa magana tayi saboda ta rasa mai zatace ashe da rabon xataga jininta wanda suka fito duniya tare uwa daya uba daya,kallonsa kawai takeyi kawai sai ta fashe da kuka sakkowa yayi ya dawo kusa da ita Samiha mai yasa kike kuka ba kya farinciki da dawowar yayanki, rungume shi ta sake sakin wani azababban kuka haba yaya kai kade nefe ka ragemin kai ma ka tafi ka barni a lokacin da nafi bukatar ka mai yasa bazanyi farincikin ganinkaba na rasa da wacce kalma zanyi amfani wajan nuna farincikinane hakika yaya nayi kewar rashinka dan Allah karka sake nisa dani "inshallah"Samiha na zo kelan babu wani abu da zai sake sakawa na barki.
Nan momy tace suraj ku tashi ku shiga daki Abdallah yayi wanka ya zo yaci abinci ya huta sanann sai yabamu labarin mai yafaru da shi duk da naga babu alamin gajiya a tattare da shi tom momy sika mike suna murmushi.
Bayan sun shiga daki Yaya Dr yake cewa"Hakika Abdallah minyi matukar kewanka minyi matukar rashinka rayuwa sauya mana tayi na rasa yacca zanyi da ka tafi kai kadene abokina wanda na yarda da shi nake son sa nake son rayuwa da shi tun bayan tafiyar ka bansa ke abokiba har nagama karatu sai kwa nan nan da nayi wani abokina Ahamd"
Allah sarki Suraj tom gashi yanzu na dawo inshallah kuma bazan sake nisa dakuba albarkacin annabi.

Nan Abdallah yagama komi ya shirya tsaf suka fito yaci abinci duk da cewa kana ganinsa kasan baya jin yunwa.

Ana haka sai ga dady ya zo ba karamin farinciki yayi ba ganin dawowan Abdallah ashe zasu kara saka sa a idon su ashe bai mutuba.

Bayan ya kammala cin abinci yafara basu labari kamar haka "Alokacin da na farka da asuba na fita agida a guje batare da nasan Ina nakeba na tsinci Kai na cikin wani daji wanda da kafata na kai kai na wanann dajin batare da na saniba,Ina zaune naji abin da yafaru yana dawomin Ina jin kamar na dawo gida,amman gaba daya sai naji natsani gidan bazan iya rayuwa acikin gidan ba a haka na shafe kwana uku acikin wannan daji,watarana wani makiyayi ya zo wucewa ya ganni yamin tambayoyi sai na fadimasa cewa ni marayane.
Nan ya tafi dani cikin gari yacemin mije shima shanun maigidan sane wannan yake kiwo muje idan Allah yasa ya daukeni aiki nima nake samin na abinci,haka na bishi mika tafi gidan da mikaje ne yabani mamaki wani kantameman gidane kana ganin gidan kaga gidan attajiri.
Mina shiga yagabatarwa mutumin ni nan alhajin yace nafadi masa wayene ni ban boye masa komi cikin labarina ba na fada masa komi da komi yace na shirya ya mai doni gida nace masa ni bazan koma gida ba,yace tomshikkelau yayi alkawarin rikeni har lokacin da xanje Ina son na koma gida,ya tambayeni nayi karatu nace eh yamin magana da turanci yaga Ina mayar masa nan fa yace tabbas wannan makaranta yakamata na sakaka ataikace de ya turanci kasar waje tare da yaronsa guda daya na miji da Allah ya bashi ,naje na karanci aikin tukin jirgi a yanzu haka ni matukin jirgin samane bayan mundawo kowannen mu ya bamu jari mai matukar yawa,yanzu haka zan iya ce muku ni kai na bansan iya adadin dukiyar da nake da ita ba,domin dana fara kasuwanci Allah ya sakawa kasuwancina albaraka.

Lokaci daya Ina zaune naji Kun fadomin Ina Kuma son na zo na ganku,naje na sameshi na fadamasa Ina fadamasa yace "alhamdulillah "daman yaje ance masa asiri akamin ya dage da addua inshallah watarana zai karye shine yamin izini da na shirya na zo shima gobe zai xo yau yana da taro a office.

Murna sukayi ta taya sa da kuma murant dawowa cikinsu .

Anan dady yace yana da wadda yake so yace Aah ,yace tom na zaba maka Basma kawar Samiha a matsayin matar da xaka aura inafatan baza ka bijire ba dady siko batamin ba dan farincikin ka xan karbeta, bana son ka karbeta dan farincikina Ina son ka karbeta domin kana so dady na karba,zanje na sami mahaifanta naji idan basu mata mijiba sai a fadamata idan ta amince kaga shikkelau sai na saka ranar auran tare da naka da na su Samiha.

Nan yace Samiha da Suraj suka dago kai inshallah sati biyu masu zuwa za'a daura muku aure ya juyo ya Kalli momy yace "Sai ki fara shirya yarinyar ki dan da man Ina son na yi muku bazatane"saura kwana goma sha hudu daurin auransu..

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN
BY

ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 36&37

Murna kamar ta kashe Samiha da Yaya Dr shikkelau yanzu zasu mallaki juna a gaban dady ma sun kasa boye murnar su.

Nan suka mike sukayi dakin samiha da Yaya Dr da Abdallah dukansu,suna shiga Abdallah ya Kalli Samiha yace "Oh ni Abdallah wai yanzu Samiha ce ta isa aure na so ace su baba suna nan suga wanann rana sai de Allah bai so hakaba ubangiji yayi musu rahama"Ameen suka ansa masa.Nan Yaya Dr yace "Tom kai ma gashi zaka angonce"hmm kamanta sai anje nemomin matar yanzu idan akaje tace bata so nafa kaga ni nasanta shiyasa na amince tunda lokacin da na bar gidama ai sun dantasa amman ita fa ba lalle ta ganeniba.
Samiha ta dago Kai tace "Ina da yakinin Basma baza ta taba watsa maka kasa a ido ba Ina da yakinin tabbas zata amince da auranka da izinin ubangiji haka sukayi ta fira abinsu kamar kar su rabu sai da dare yayi sosai tukunna suka bar dakin samiha suka koma dakinsu.
Chapter 29 · 0% Book details