← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 33

Sashe 11

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kokarin kiranta yake domin yayi mata bayani yadda xata fahinta Amman bakinsa yayi masa nauyi ya rinjayesa ta yadda yakasa furta komi acikin bakinsa kalaman kasa fitowa sukayi Kuma duk Sanadiyyar fushin da yaga ta yini biyota yayi domin ko zai Sami Damar tse da ta a parlour domin yayi mata bayani Amman Kash!!!! Sai de Yana zuwa parlour ya iske dady da momy duk suna zaune can ya hango Samiha agefen momy tana zaune suna magana ji yayi kamar yaje ya kamo hannunta yayi mata bayani yadda xata fahinta Amman babu dama,abinci ta hada musu sukaci kallonta yake tayi domin su hada Ido Amman fur Samiha taki dagowa ta kallesa tabbas yau momy taga sanjin da Bata taba ganiba tsakanin Suraj da Samiha sanjin da za ace har sun fito sun fara cin abinci basu yi maganaba Hakan ya fara Saka mata zargin kode Wani abinne ya hada su Amman sai ta tuna ai yanzu ya zo ya shiga dakinta gaskiya sai de kawai maganan ne basuyi ba suka gama cin abinci sun saba tare suke tattara kayan,su mayar kitchen haka kuwa akayi suka dauki kayan domin mayarwa suna shiga Samiha Tayi kokarin juyowa domin duk ta fuskanci Mai yake nufi so yakeyi yayi mata magana ita Kuma take kokarin kufcewa wanann hanyar "Samiha " ya kira sunanta ansawa tayi ba tare da ta juyo ba magana fa nake miki shine ma dalilin da yasa ai na tsaya ki juyo ki kalleni Ina tunanin Koda ban kalleka ba zaka iya fadin abin dake bakinka tundade Baki ke magana hakane Amman zan Sami karfin gwiwar furtamiki abin dake baki nane kawai idan Ina kallon idanuwanki da ke sakamin karfin gwiwa juyawa tayi zata fuce saboda Bata da lokacin sauraran wadan nan kalaman, da sauri yasha gabanta haba samiha Mai ne Hakan wane irin hukunci kike kokarin yiwa zuciyata kinsan bazan taba jure fushinkiba ko na sakan dayane Dan Allah kiyi hakuri,Mai kamin da xaka bani hakuri na baka dama fa kayi duk abin da yakamata kisan Allah Samiha ban kula taba ban San wacece ba hasalima ban mata reply ba ai na Baki wayan kin gani na gani Amman Kai bakka da bakin da zaka yi kokarin tsayar da abin dake kokarin faruwa ko da matan da suke cewa suna sonka ni nake koya maka yadda zaka rabu da su ita wanannan Mai yasa baza kayi mata abin da kake musu ba inde da gaske ne baka San taba zan mata Samiha Daman na fadimiki ne saboda Bana son a Sami matsala , wayarsa ya dakko ya Mika mata yace ki rubuta duk abin da kika San zai sa baza ta Kara yunkurin turomin sako ba karba tayi ta shiga lambar ta rubuta sako kamar haka......

BAIWAR ALLAH KIYI HAKURI KARKICE ZAKI SHIGO CIKIN SHUKAR DA NA YIWA YABAN YA TUN SHEKARU DA DAMA,KADA KICE ZAKI ZO KI TARWATSA MIN FARINCIKIN DANA DADE INA TANA DINSA DA LALLABASA NI CE WACCA YAKE SO KUMA YAKE BURIN AURE DAN ALLAH KARKI SHIGO RAYUWAR MU KI KAWO MANA MATSALA KIYI HAKURI KIJE KIBI WADANDA SUKE SONKI DAN NA TABBATAR BAZA A RASABA.

tana kara sawa ta tura ta Mika masa wayan Aah ki rike a wajanki Dan na tabbatar watakil zata iya Baki ansa idan kungama kya kawomin to tace ta juya zata tafi hannunta ya kama ya juyo da ita yace Samiha Ina sonki Ina matukar kaunarki Bana son duk Wani Abu da zai rabani dake Dan Allah kidena fushi Dani ki Kuma Dena Saka damuwa akaina ni naki ne babu wata ya mace data isa ta shigo rayuwata bayan ke Dan Allah Samiha ki fuskance ni na fuskanceka Yaya Dr Kuma kayi hakuri akan abun da ya faru karki damu Daman ni banyi fushiba burina kawai kidena fushi Dani domin Yana Dagamin hankali......

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

ABOKIN YAYANA 😭
Created and Written
By
🤗😍 ZEEY NASEER 💗

💫💫 MOON LIGHT WRITER'S ASSOCIATION 💫💫
We shine all over the world

Page 12

Nasani nasan baka San damuwata ba kuma kasan abin da zai batamin rai amman dole naji babu dadi Yaya Dr dole saboda shigowar wata rayuwan ka na nufin tarwatsa rayuwar da mika jima mina shimfidawa ni da kai wanda ni kuma bazan so hakan ba "inshallah Samiha babu wata wacca ta isa ta tarwatsa rayuwan soyayyyar da Mika jima mina shimfidawa cikin aminci ni dake babu wata wacca ta isa ta rusa wanann abin da Mika jima mina ginawa ki kwantar da hankalinka"

Shikkelau Yaya ya wuce "Inshallah" zan kiyaye" kusa da ita ya karaso ya manna mata Dan karamin sun Bata a goshinta ya fice nan ya barta cikin Wani tunani Mai zurfi da shauki Wanda kullum idan tana tare da Yaya Dr take cikinsa,taya wata zatayi kokarin shiga rayuwarsu ta Ina zan fara kokarin ganin wannan abin Bai faruba bani da Wani farinciki da ya wuce Yaya Dr shine abin dake raina Kuma nike fatan kasancewa da shi akowane lokaci bazan taba bari wata ta shigo rayuwan saba in de Ina nunfashi zanyi iya bakin kokarina wajan ganin Hakan Bai faruba da izin Allah,fitowa tayi ta koma dakinta domin tagama dukkanin aiki.
Zama tayi tana Kara duba sakon da yarinyar ta turo abin Kuma na sake Bata mamaki,Daga bangaran Nihal kuwa tana tashi da safe ta duba taga babu Wani Sako jiki babu kwari ta mike Amman da fata da tunanin baza ta gajiyaba saboda ta tabbata dole zai iyi Bata ansan sakonta tana zaune tana cin abinci kamar Daga sama taji Karan wayarta cikin sauri ta dauka ta Bude ganin layin Yaya Dr yasa ta saki wani murmushi Wanda batasan ma tayi saba cikin sauri da hanzari tayi kokarin budewa domin tana tunanin tunda har Yaya Dr ya biyata ya Bata ansar sakonta koda zagi yaturo mata tabbas da alamin nasara,abinda ta ganine yayi matukar tayar mata da hankali yabata mata rai wanda da kyar ta Samu tayi saisaita kanta lalle ma yaraina mata hankali yanzu Samiha yabawa wayan ta rubuta mata ansa kelan yakasance Da gaske basa boyewa juna komi tabbas dole ta sauya taku wannan hanyar baza ta bulle mata ba zata tafi Abu nagaba babu ruwanta da cutar da su da zaiyi ita de inde zata Sami nasara akan Yaya Dr tom Bata da wata matsala akan haka,cikin sauri ta shirya ta dauki mayafinta ta nufi gidan su kawarta shigarta ke da wiya ah!!! Nihal kece agidan namu"Kede bari atika ya zama dole me mije de mi zauna na Baki labari".

Zuwa sukayi suka zauna nan nihal ta debe labarin komi ta fadi mata atika dariya tayi Mai isarta sannan tace "Keda in ba Koda human ci ba kina Dani Zaki tsaya kina Bata lokacinka kinsan Allah da kinzo tun bayan ba da tuni mingama da wanann babin",wai Allah kawata Yoh ba sai ki zauna anan ba yanzu abin da xakiyi shine kije ki tattaro kudadde gobe zamu shirya zanfara kaiki gun Boka na kan tudu na tabbata cikin kalilan din Lokaci za'asami nasara,"Kinsani sarai cewa kudi ba matsala ta bane kawai ni biyan bukata Nike so"angama kuwa dan bakki da matsala gobe xamije da la'asar yau ma Dan zanyi bakone amman da yau din xamije babu komi Allah ya kaimu goben Ameen
Atika tace "Kede kawai ki kwantar da hankalinki in de kikaga Baki aure yaya Dr ba tom tabbas ba mije gurin wanann bokan ba" murmushi tayi wallahi sai yanzu na Sami nutuswa Amman bazan iyi kayyade Miki kalan tashin hankalin da nike ciki ba nagode sosai kawata bara na tafi sai goben.

Cikin farinciki nihal aka koma gida domin gani take ai bukatarta ta gama biya.....

Shin Mai zai faru?
Nihal zata Sami nasarar raba wanann soyayyya?

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN

BY

ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 13

Washegari kamar yadda Atika tace mata haka suka shirya suka nufi wajan wanann boka,suna zuwa boka yace "Ba sai sun fadi abin dake tafe dasu ba ya xayyana duk abin da ya kawota tace masa"Eh"hakane yace tom yanzu mai take so ayi musu,bana Son ayi musu wani sbu da zai cutar da su saboda Samiha kawace tagari tana matukar girmamani Kuma nima haka wanann yasa ni kawai Yaya Dr nake so na kwace ita kuma bana son komi ya tabata iya bakincikin rabata da shima ya isheta,ba yadda zanyi bazan iya hakura da shi ba Ina sonsa matukar so, tomshikkelau yanzu zan baki magani ki tabbatar kin zuba masa a abinci yaci, kallo ta bishi da shi mutumin da kallon banza ke hada su da shi shi za a Bata ta zubawa magani a abinci,Atika ta fahinci haka hakanne yasa tunkan ta kwafsa tace wani abin ta bawa boka ansa da zasuyi hakan nan ya dakko maganin yabata yakuma sake tabbatar mata da cewa inde ta zuba masa yaci a abinci ko da Sau dayane tabbas ya zama nata,na so na duba nayi miki aikin daga nan tom amman ta ko Ina nakasa saminsa Yaya Dr mutum ne Mai matukar Shiri yana da ibada haka Kuma yana da yawan karatun alkur'ani kafin na same shi za ayi matukar Bata lokaci zakuma asha wahala,shiyasa na Baki kibashi abin da zai ci za afi saminsa cikin sauki.
Chapter 11 · 0% Book details