← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 33

Sashe 33

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mu tafi tare suka mike dede lokacin da suka karasa dady yana magana da yazid yana cewa"Babu abin da zai hana auran nan inshallah ana kai gawarsa za adawo a daura aurannan kai yazeed kaga daman kai ne yayansa uwa daya uba daya, saboda haka kai yakamata ka auri Samiha yanzu za adaura auran ka da mata biyu kelan".
Aah dady da wane Ido zan kalli Zainab nace mata su biyu na aura,Kuma duk da abin da Samiha ta aikata na badala da fasikanci ace ni na aureta,tom uban waye ya lalatata ba dan uwanka bane gaskiya dady kayi hakuri amman bazan iya auran Samiha ba,momy ce ta dago kai tace"Yazid tunda mike da kai baka taba maana musuba amman yau da mu kake musu".
Kyaleshi hajiya na tabbata kyakkyawan zuciyar samiha da irin kaddarar da take gani a rayuwarta zata iya saka ta sami mutum na gari.
Kamar daga sama sukaji Ahmad yace "a karo na biyu inde dady ka amince Ina son abani auran Samiha na yi muku alkawarin bata farinciki da jure duk wani wulakancin da zatamin har ta dawo dede daga radadin mutuwar Suraj".
Allah yayi maka albarka Ahamd mingode.
Nan aka sanar da mutanan jana'iza aka fita akayiwa yaya Dr sallah aka kaishi gidansa na gaskiya bayan andawo aka daura auran.
AHMAD DA SAMIHA
ABDALLAH DA BASMA
YAZID DA ZAINAB.
ita kaddarar bawa arubuce take babu wanda ya isa ya dau kadararar wani kuma babu wanda ya isa ya sauya kaddararsa kamar yadda matar mutum kabarinsa babu wanda ya isa ya auari matar wani.

Ita kaddarar mutum a rubuce take kuma abiye take da shi.
Bayan daura aure Kuma anci gaba da zaman makoki kamar yacca yake a al'ada na tsawon sati guda
Bayan an kammala zaman makoki an kai amae gidajen su amman fa har lokacin Samiha bara farfado daga suman da tayiba.
An dawo da ita gida ancigaba da bata dukkanin wata kulawa Ahamd kodayaushe yana zirya cikin gidan sai da tayi wata guda sanann ta samu bude idanu a ranar kowa yana cikin farinciki,harta Basma da Abdallah ranar agidan suka yini saboda Samiha ta bude ido,bayan kwana biyu Kuma gangar jikinta ta fara motsawa alhamdulillah ranar Samiha ta farfado amman sai de banda hawaye babu abin da yake zuba daga cikin idanuwanta fuskarta ta kumbura tsabar hawaye sai da tayi kwana biyu tukunna tafara magana,Basma ta dawo gidan gaba daya da zama kullum ita take kara kwnatar mata da hankalinta da yi mata nasiha tare da sakata yin addu'aoi da salloli a haka aka Kara shafe wata guda tukun ta dan dawo cikin hayyacinta ta nutsu tana cin abinci dede gwargwado amman fa fara'a babu ita a fuskarta kwata kwata.
Har lokacin babu wanda ya sanar da ita andauramata aure.
Ranar dady yasaka taro ciki har da Ahamd anan aka sanar da ita komi, wani kukane yakare yanke mata yanzu da wani zatayi rayuwar auranta ba yaya Dr ba yanzu duk wani abu na farinciki da ta tsara zata basa shikkelau babu dama wani ne zai mallaketa a amtsayin mata,nan dady yayi mata nasiha mai ratsa zuciya sannan yace "A daran yau za a kaita gidanta".
Sabon tashin hankali bata taba tunanin zai ce hakaba haka tayi ta kuka kamar momy tace kar akaita yau sai de gwammah akaita saboda cigaba da xamanta agidan xai cigaba da tuna mata Yaya Dr da rayuwar da sukayi.
Nan fa ta mike ta shige dakin Yaya Dr take ta kuka ko Ina ta kalla gani take kamar zata gansa,daga filonsa tayi ta ga wata farar ta karda.
SAMIHA NASANI KINA SONA KINA KAUNATA AMMAN BABU WANDA YA ISA YA KAUDA KADDARAR UBANGIJIN SA SAMIHA INDE DA GASKE KINA SONA KINA KAUNATA KIYI BIYAYYA MATUKA GA DUK WANDA YA ZAMA MIJINI, KARKI YARDA KI KAI KANKI WUTA SANADIYYAR KAUNATA KARKI YARDA KI KAI KANKI WUTA SANADIYYAR SONA,NI TAWA TA RIGA TA KARE NASAN ZAKI KARANTA TAKARADR NAN ALOKACIN DA BANA RAYE,NA RUBUTATANE LOKACIN DA CIWON CIKI YA MATSAN TAMIN.INA SONKI SAMIHA NA RAYUWA DA SONKI KE KADE KUMA NA MUTU DA SHI NA KI A KULLUM YAYA DR DINKI KUMA FARINCIN KI.
Wani kuka ta sake kecewa da shi da kyar suka zo suka fitar da a dakin aka shiryata aka kaita gidanta.
Adaran daman Yaya Ahamd bai yi yunkuri n shigowa inda takeba saboda yana matukar tausaya mata dole ta shiga wani yanayi duba da irin kaunar dake tsakanin su.
Da safe bayan ya tashi ya dafa abinci yaje ajjemata adaki yasan ba bacci yeakeyiba kawai baya son ya takura mata ne.
Haka sukayi tayi har tsawon wata guda.Wata rana ya zo yace mata "Samiha Ina son na baki hakuri kidena kokarin ja da hukuncin ubangiji,yayi mata nasiha mai matukar rastsa zuciya,kuka ta fara mai tsuma zuciya nan ya ja ta ya rungume ta ya rarasheta ta bashi hakuri akan yayi hakuri ta kasa dedeta zuciyarta ne"
Karki damu inshallah zaki dawo dede Samiha,rayuwa ta fara sauya ta fara tashi tayi masa girki da komi,sannu a hankali har yafara shiga dakinta watarana mai afkuwa ta afku tsakaninsa abunda ya bashi mamaki shine,ance Yaya Dr ya lalata rayuwar Samiha amman ya akayi ya sameta cikakkiyar budurwa ya kasa jurewa hakane yasa ya tambayeta.
"Yaya Ahamd tunda nike da yaya Dr bai taba saduwa daniba na sha bukatar hakan amman yaki duk da asiri na yawo acikin jikin Yaya Dr amman hakan bai sa yaketa iyaka ba,kullum idan yazo yayi abubuwnasa dani yakan ja gefe yayi ta hawaye yana dana sani amman asirin dake jikin baya hana gobe ya dawo ya Kara sabawa ubangiji ".
Dukkanin yabo da godiya yakara tabbata ga Allah nan yaja Samiha ya rungume yana godiya ga Allah.

Samiha ta haihu ta haifi Yan biyu maza da mata Ahmad yaa saka sunan yaya dr Suraj,macan Kuma aka Saka mata Samiha.

Suraj suna Kiran sa da da Yaya Dr.

Amman har abada tunanin Yaya Dr ba zai taba barin Samiha ba duk yanzu tana kaunar mijin ta amman soyayyyar Yaya Dr ta dabance.
Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah ina godiya ga Allah subhanahu wata'atala da yabani ikon kammala wannan littafi,abin da na fada dede ubangiji Allah yakai ladan kabarin mahaifina, wanda nayi ba dedeba ubangiji Allah ya yafemin albarkacin annabi.
Na sadaukar ga wannan littafi ga mahaifina malam Nasir amarous ubangiji Allah yayi masa rahama ya Kuma kyautata makwancinsa yasa yana aljanna da shi da dukkanin musulmai baki daya.

Na tabbata makaranta yau basu ji dadin wanannan posting din ba,amman Ina son na tunatar damu wani abu bakomi bawa yake nema ya samu a rayuwaba,haka kuma wasu abubuwan da mike so ba alkairai bane a arayuwar mu,duk yacca Mika kai ga son Abu ubangiji yafi mu sanin abin da ya dace damu .

Ina godiya agareku masoyana

Mu hadu a littafi na gaba wato (ADDININA).
Chapter 33 · 0% Book details