← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 33

Sashe 1

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ABOKIN YAYANA BY ZEEYNASEER PART ONE

ABOKIN YAYAYANA littafine da ya samu rubutawa da karamar marubuciyarku wato zeeynaseer
ABOKIN YAYANA littafine da ya kunshi abubuwa da dama daga ciki sun hada da soyayyya,ban tausayi tare da sanin maicece kaddara sannan kuma ubangiji shike yin abinda ya so akuma lokacin da yaso duk acikin ABOKIN YAYANA xakiga abin da ake cewa bazata ubangiji yakan yin abinda mike tunanin ba zai yiyuba kude ku biyoni cikin wanannan littafinawa domin ganewa kanku abinda nake fadimuku.

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan littafi ga mahaifina ubangiji Allah yayi masa rahama ya Kuma Kyautata makwancinsa da shi da duk wadanda suka rigamu gidan gaskiya,sannan Ina mai neman alfarama ga duk wanda yakaranta wannan littafi kar ya wuce ba tare da yayiwa abbana adduar samin rahamar ubangiji ba.

ABOKIN YAYANA😭

Amincin Allah da yardarsa sukara tabbata agareku masoyana ,yau yayi Dede da 15/8/2024,kamar yadda nace littafin mu Mai suna ABOKIN YAYANA,Zaifara zuwar muku a wannan Rana.
Acikin wanann littafi zakuga wasu maban ban ta abubuwa Misali:

Nayi amfani da yankin da nake wajan rubuta littafin zakuji garuruwan da ke ciki wasu Daga ciki ba lalle Kun San suba.

Nayi amfani da yankin da nake wajan rubutun littafina ba domin komi ba,sai Dan ganin ni yar Jigawace sanann Kuma abin zai Fi ace nayi amfani da garuruwan dake yankin mu wajan rubutun.

Nagode sosai da kasancewar ku Dani,Ina Kuma fatan zakuji dadin wannan littafi,zakuma miyi amfani da darasin dake cikinsa.

Wasu Daga cikin littafan da zasu biyo Baya,bayan min kammala wannan littafi da izinin ubangiji.

ADDININA
MARAICI
SANADIN KAWA
BAZATA
MAI NE SILA
MAHAIFIYATA

Duka wadannnan littafai Zasu bayyanane acikin wanann gida Mai albarka da yardar ubangiji,Wanda dukkanin su Rubutune na marubuciyarku
ZEEY NASEER.

ABOKIN YAYANA😭😭

Page 1

Dan Allah yayah kabari,Kabarshi haka kullum Ina ce maka mina kula saboda wasu zasu iya kamamu,Idan har kana so na dagaske wannan abubuwan basu bane abin da suka Kamata,Kana da kudi,kana da rufin Asiri,kana da komi,ka aureni shine mafita,kaga shikkelau Daga nan xamu zauna tare miyi rayuwa tare ta har abada.

Ki rufemin baki karki sake min irin wanann maganar,na fadimiki ba kya tsarin macan da Nike son aura, domin ajinki Bai Kai wacca zan aura ba,Ina rayuwa dake ne kawai saboda abin da Nike Samu Daga gareki,Kuma zamuci gaba da rayuwa a haka har karshan rayuwarki.
Dan Allah yayah idan baza ka aure niba ka bari Wani ya aureni, kabarni na kula wadan da ke so na domin na Samu nayi aure,duk da wasu mutanan sun fuskanci rayuwata yanzu ta lallace,Na sauya Daga Mai mutunci,zuwa wacca ta tanbadar da shi,Amman nasan Hakan ba zai sa na rasa Wanda zai rufamin asiri ya aureni a hakaba,Dan Allah kafita a rayuwata,In har kana nan bazan iya kula kowa ba,Ina sonka fiye da yacca nake son Kai na.
Tau ya dauketa da Mari..........😭

Yayah Dr.mari na fa kayi,yaushe zan Dena lefin da zaka dena Mari na,Mai yasa Mari ya xamo tamkar daukar Yartsanar wasan yara agurinka,Mai yasa baka tausayi na,Mai yasa duk da kana ikirarin so na baka gudun abin da zai batamin rai,Dan Allah karika tausayamin Ina jin babu dadi ace Wanda nafi so da kauna acikin mazaje shine Wanda a kullum yake zama Sanadiyyar zubar da hawayena,kaji tausayi na ko domin son da nake maka.
Kaji tausayina ko domin maraicin da Nike ciki,kada kamanta Kai ne ka zamo uba agareni alokacin da na rasa kowa nawa,Mai yasa kake so ka zubar da dukkanin wanann abin,Mai yasa kake so ka mayarni tamkar Bai wa?

Kingama wanann shine abin da taji anfurta Daga ban garansa,Sanin kanki ne Samiha kin sani cewa Ina sonki,Ina Kuma kaunarki,Taya Zaki fadimin maganar wai na barki kije ki auri Wani,Taya kike tunanin zan zuba Ido,Ina kallonki kina rayuwa agidan Wani a matsayin matarsa,sanin kanki ne kin San cewa Wanann abin ba Mai yiyu wa bane,Ni kade ne Wanda zan rayu dake domin ke akayi ni,babu Wani na miji da zai rayu dake bayanni tabbas dullokacin da kikayi yin kurin shigo da Wani cikin rayuwarki,Wallahi sai na Kasheki na kashe sa,na Kuma kashe Kai ma,bazan taba jurar Ina tare da ke Wani na miji ya kasance da keba,Wanann ya zama lokaci na karshe da Zaki sake yimin zance Wani namiji,in ba hakaba zan Miki hukuncin da ban taba yi Miki irin saba.

Kasa motsi tayi saboda Zafafam kalaman da taji ya furta,kelan haryanzu soyayyyarta na cikin zuciyarsa,ammam Mai yasa yake wulakantata,Mai yasa ya Dena Bata kulawa,kullum kalar rayuwar Tasu tana Bata mamaki,Bata taba ganin wadan da ke soyayyya hakaba,Bata taba ganin masoya irin su ba akullum masoya burin su su ririta juna,Kulawa cike da shauki

Amman shi a kullum Bai da buri sai muzgu na mata,Bai da buri sai wulakantata,tana mamakin yacca kwata kwata Baya tausayinta,tana mamakin yacca kwata kwata Baya son faranta mata,Amman duk da wanann musgunawar da take fuskan ta agurinsa Hakan Bai sa ta sare ko Kuma Tara sa yacca zatayi ba,a kullum son sa da kaunarsa sake shiga cikin zuciyarta suke,ita kanta tana mamakin yadda takejin sa,domin babu Wani Abu na kyautatawa da yake mata da zai sa ace yayi sandin sace zuciyarta da shi,wanna wane irin musibace,Bata iya yi mas musu a dullokacin da ya Bukaci Yana son su hadu,Bata iya mas musu a dullokacin Daya Bukaci yake be da ita,ya mayar da ita tamkar matarsa,yakan yi abin da yaga dama da ita,a Kuma lokacin da yaga dama,Wanda Kuma da ba haka suke ba,duk tsawon shekarun da suke abaya,Dede da hannunta Baya taba yunkurin kamawa ballantana har yaketa iyakar ubangiji,Amman lokaci daya ya saya,sauyin da haryanzu ta kasa gano dalilin sa,tom Amman Mai a dullokacin da Samiha ta koma gida,da na Sani mara adadi ke tun kararta,da na Sanin da take tunanin Mai yasa tasan zatayi shi Amma ta biyewa Yaya Dr.,suke aikata abin da suke aikatawa ita kanta bata Sami wanann ansar ba haryanzu

Amman kullum cikin addua take ubangiji Allah ya Bata ikon Dena rayuwar da sukeyi, Ubangiji Yabata ikon gyarawa,Sai kace bani bace Samiha Mai addini da mutunci,Mai kulawa da karatunta,mai ya Sami rayuwata hakane,Mai yasa rayuwata ta lallace,Duk wani muradina yanzu ya tashi a banxa na kasa cika burina,Kuma burin mahaifana, ubangiji yayi muku rahama,ya Kuma bani ikon shiryuwa nadena abin da nikeyi,Kai Kuma yaya abdallah Allah ya dawomin da Kai,domin tsantsar Zalinci ne yasa aka bari kayi nisa Dani😭😭, rayuwata Bata da wani amfani a yanzu,Kiran sallan magri bane ya tsayar da ita Daga tunanin da take,tashi tayi ta shiga ban daki domin ta tsarkake jikinta,Ta fito ta shirya sannan ta dakko Abin sallah,bayan ta idar da sallah tayi addu akan Allah ya shiryar da ita,yakuma bata ikon Dena abin da takeyi,da adduar ubangiji Allah ya bawa yaya Dr.dinta masoyi daya da batta da tamkarsa Damar dena wulakantata,ya dawo yaya Dr.dinta na Baya mai sonta da Kuma kulawa da ita,Baya son bacin ranta a baya,Amma a yanzu ya sauya kullum cikin mu zantata yake,Mai yasa Mai ya sauyasa akan abinda yake mata......

Wacece Samiha
Wayene yaya Dr....????
Kuma Mai ke faruwa tsakanin su,kuci gaba da kasancewa damu,domin ganin ansar Wannan tambayoyi .

Bayan ta kammala addua ne ta zauna akan gefen gado tana tunanin yacca rayuwa ta sauya mata tana tunanin yacca komi yayi mata zafi,Tana jin Ina ma ita ma ta mutu tabar duniya kamar yacca iyayanta suka mutu,Ina ma ita ma ta koma ga mahaliccinta sai yafi mata sauki akan halin da take ciki,karan da wayarta ta yini ya tsaidata Daga Dan lukutin yanayin da take ciki na tunanina,Dammul jisim shine abin da ya bayyana a fuskar wayan,Duk Wani hali da take ciki idan ta Gansa takanji ta Sami nutuswa,Idan yakirata a waya kuwa ji take tamkar anbata kyautar duniya,duk da cewa shine sila da Kuma sanadin damuwarta,shine sila na shigar ta duk wata musiba,Amman takanji farinciki idan ta Gansa,abin dake saka mata rashin kwarin gwaiwa kuwa shine irin yadda yake treating dinta,Hannunta na karkarwa ta dauki wayar ta Daga tana Mai farinciki,Amman abin mamaki yacca ta saba jinsa babu fara'a haka ta jisa,ki fito ina kofar gida shine abin da taji anfada kiyat ya kashe wayan bin wayan tayi da kallo idan da sabo ta saba da irin wannan yanayin,Amman a shekarun da suka shude irin shaukin da Yaya Dr. Yakeyi adullokacin da yakirata ya linka Wanda takeyi,Mai yafaru,Mai ya shiga tsakaninta da masoyinta?,Wani wahalallan hawayene Wanda take son futar
Dashi tun dazu shine ya zubo Mata, murmushi tayi Wanda iyakar fuskartane,tashi tayi ta shafe jikinta da turare ta fita,cikin fara'a tana zuwa taga fuskansa yadda ta saba ganinsa babu Wani sauyi.

Sallama tayi da muryarta Mai dadi tare da taushi,Yaya Dr.ina yini,Wannan ita ne sallamar da kike min Daman,yanzu rainin har ya zama ki zo kimin irin wannan gaisuwar,Abin ya Bata mamaki duk da ba yau ya saba yi mata hakaba,tom Taya zata Sami karfin gwiwar tunkararsa,ba ya nuna mata Wani shauki ko farinciki da zai sa ta so kasancewa kusa da shi.

Kara sowa tayi jiki duk babu kwari,tayi hugging dinsa yacca suka saba,A Dede lokacin ruwan hawayanta ya zuba akan gadon bayansa,shi kansa sai da yaji zuciyar sa,tayi masa Wani irin zafi Yana son ya rarrasheta،amman ba shi da kwarin gwiwar Hakan,a dullokacin da yayi yunkurin yin Hakan ya kanji ya kasa,Zuciyarsa tayi ta masa sake sake iri daban daban ,tabbas yaji Yana son rarrashinta domin aduniya babu Wani Abu da ya tsana irin ganin hawayanta,Wanda yasan shine sila,Amman ba shi da wata dama ko ikon Hana su zubowa,a hankali ya zareta Daga jikin sa,domin radadin da yakeji da zafi aransa na damuwar da take ciki,murfin motarsa ya bude ya dakko katuwan Leda,gashi abinci na kawo Miki,naga Baki baro gurina da wuri ba,baza ki Sami lokacin daura abinci ba,karba tayi tana godiya ya juya ya shige motarsa.
Chapter 1 · 0% Book details