← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 33

Sashe 24

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman su ce tace "Basma karki damu inshallah komi yayi farko zaiyi karshe zan taimakawa Samiha kamar yarda idan kece a irin halin ta tsinci kanta nasan Kinga dole zanyi fafutuka wajan ganin kinsami maslaha tom da yardar Allah itama zanyi mata haka, domin kuwa na dauki Samiha a amtsayin diyata wacca na haifa"
Tom mama nagode sosai da sosai ubangiji Allah yasaka da alkairai,a wanann rana de Samiha batayi wani baccin kirki ba gaba daya hankalinta da tunanin ta yana kan Masoyiyarta Samiha,haka Ahmad gaba daya bacci yakaurace masa ya hau kan sallah yana kuka yana rokon ubangiji akan Allah yakawowa Samiha mafita,shi kansa yayi mamakin irin kalar kukan da yayi domin bai san lokacin da yakeyin saba.
A bangaran Samiha kuwa wayar da yaya Dr ya siya mata ita ta Kunna ita ce ke dan debe mata kewar wasu abubuwan,da magrib yayi ta tashi ta dora girki ta kirashi awaya akan zai zo yace mata eh zai zo nan ta dora musu abincin tare.
Kwnaci tashi Samiha ta shafe watannni a wanann gida amman har yau momy bata san tana nan ba,yadda kasan a rufe wa mutane baki akan sanar da ita,sai de babu abinda mutane basu saniba tunda Samiha sukan fitowa ita da Yaya Dr suje siyayya ko kuma idan zai kaita gyaran kai,duk mutanan yankin babu wanda yake mu'amala da ita dan harta gaisuwar ta babu mai ansa shiyasa itama ta hakura tadena gaida kowa.
Watarana sai abubuwa suka fara sauyawa duk da yaya Dr yana abin da yaga dama da ita amman yana yin komi ne cikin shauki da soyayyya,tom amman yanzu ta sauya zani kullum cikin cin mutuncin ta yake yadena nuna mata kauna kwata kwata,kuma kullum cikin zuwa yayi abin da yaga dama da ita yakeyi.

Samiha ta shiga wani sabon tashin hankali wanda yakusa sakata zaucewa nikam na shiga uku mai ke shirin sake faruwane "Innalillahi wa inna ilahiee raji'un".Haka taci gaba da kasancewa cikin wanann halin cikin Wanann yanayin bata fadiwa kowa ba sai ranar da Basma ta zo ta gani da idonta.

CIGABAN LABARI

Basma ta ci gaba da kasancewa da Samiha takuma yi alkawarin babu wani abu da zai rabata da ita saboda tana son Samiha tsakani da Allah baza ta taba iya kaurace mata ba Koda ace Samiha ita ta sakawa kanta abin da take aikatawa baxata gujetaba,ballantana kaddarace wacca babu wanda yafi karfin ta.

Ranar mama na zaune ita da Basma tace mata "Yaushe zakije wajan Samiha ga maganunuwa nan na tsawon wata guda na hadosu idan ya so in zakije sai ki tafi mata da su kowanne akwai yadda zatayi amfani da shi ajiki Kuma inshallah inde ta bisu yadda suke a ka'ida duk wani abu da nihal tayi zai war ware".

Tom mama nagode sosai da ubangiji yasaka miki da alkairai,nima Samiha diyata ce ya zama dole na kula da ita.

Basma ta shirya tsaf cikin farinciki da murna taje gidan Samiha tana zuwa ta tarar da yaya Dr yasaka ta gaba sai jibga yakeyi kamar ya sami jaka zama tayi tana kallonsu har yagama dukanta sanann ya wuce ya ficewarsa,bayan yafita ta matso kusa da ita ta share mata hawayanta ki kwnatar da hankalinki besty inshallah komi ya zo karshe ta dakko ledan maganunuwan nan tamika mata su,sanann anan suka bude kowanne da yadda za ayi amfani da su ciki har da wanda zata zubawa Yaya Dr a abinci da wanda zata zuba masa ya tsallaka,tayi tayiwa Basma godiya matuka nan kowannann su yakasance cikin farinciki saboda kawai gani suke tamkar komi ya zo karshe.

Amman Samiha wani hanzara ba guduba malam ladan yace a afadimiki duk wadannan maganunuwa baza suyi amfani ba ko baza suyi aiki ba har sai kin sake nutuswa kincigaba da tsaida sallah akaan lokaci sannan kici gaba da dawwama wajan karatun alkur'ani wannan shine babban abin da zai sa aikin yayi cikin hanzari da sauki inshallah Basma zanyi nagode sosai.
Nan suka ci abinci tunda daman ta dafa abinci tare suka yini suna shira agidan sai da magariba da yaya Dr ya zo ya mayar da ita gida.
Tun a adaran ranar ta fara amfani da wannan magani anfadimata Koda taci abincin da ta sakawa maganin babu wani problem anan ta zuba wanann maganin da taje dakko musu abinci sukagama yayi mata sai da safe ya tafi gida.
Tsawon sati guda Samiha tayi tana amfani da wanann maganunuwa kullum tana fata da adduar Allah yasa komi ya dedeta,acikin satinne Basma ta zo take fadimata ai nihal sun tashi babanta ya sami sanjin gurin aiki amman taji labarin ba lalle su jima ba zai yi kokari ya sami canji ya dawo murna kamar ta kashesu Kinga wanann na daya daga cikin nasarar da mika samu alhamdulillah alhamdulillah,abubuwa shikkelau sukacigaba da tafiya takuma cigaba da amfani da maganunuwanta yadda yakamata ita kanta ta fara ganin sauyi domin yanzu Yaya Dr yadena hantarar ta da zaginta yadena dukanta haka kuma sai yayi kwana uku bai bukaci yayi wani abin da ita ba,ba karamin murna takeyi ba da hakan domin kuwa tabbas ta sami saukin zuciyata Kuma tanaji ajikinta komi ya kusa dawowa dede da izinin ubangiji.
Basma ta Samiha yanzu kusan kullum tare suke yini domin dadyn Basma ya tafi america wani project hakanne yasa maman su ta kara karfafawa Basma baya akan taci gaba da mai da hankali wajan ganin rayuwan Samiha tayi dede.

Bayan wata daya da sati biyu da fara amfani da wannan maganunuwan Basma da Samiha na zaune suna shira sai ga Yaya Dr ya shigo gaba daya hankalinsa a tashe a firgice baya cikin hayyacinsa,Samiha tace yaya lafiya mai ke faruwa mai aka maka?.

Kasa cewa komi yayi yace mata zo ciki Ina son zanyi magana dake abin yabawa kowanann su mamaki toupa yau Yaya Dr ne ke son privacy su kebe batare da kowa yaji mai zasu tattauna ba babu komi yaya Basma ce babu abin da bata sani ba a arayuwan mu,kayi maganar ka kawai.

Wani azababbbe wahalalallan kuka ya saki wanda gaba dayan su suma ya saka su zubar da hawaye ba tare da sun shiryaba duk rahsin tausayinka kaga yadda Yaya Dr ya xage yana wanannan kuka sai ka tausayamasa domin gaba daya ya gigice sai kace wani mahaukaci, kukan kawai yakeyi ya kasa furta komi....
Samiha ce tayi karfin halin cewa yaya dan Allah ka fadimin mai ke faruwa tunkafun hakurina yakare bazan iya jurar ganin damuwarka ba Yaya Dr bazan iya jurara ganin tashin hankalin kaba,bana son duk wani abu da zai zame maka matsala bana son duk wani abu da zai zamemaka damuwa dan Allah ka fadimin abin da yake damunka.

Samiha "Nasan na cutar dake na bata miki suna kowa yana miiki kallon mazinaciya mara tarbiyya Samiha Ina zan Kai wanann hakkin Samiha taya zanyiwa ubangiji bayani akan wadan nan abubuwan da nayi miki Samiha dan Allah Kiyi hakuri kiyafemin Samiha kiyi hakuri nasan tabbas kafin ki yafemin za ajima amman dan Allah ko bayan raina kisani nayi da nasanin abin da nayi miki Kuma Ina sonki fiye da yadda nake son Kai na.

Kuka wiwi Samiha takeyi idanuwan ta sun kunbura sunyi sintim murna fal cikin xukatansu ita da Basma komi ya dedeta,Samiha tace "Yaya Dr babu wani abu da zakamin aduniyar nan da bazan iya yafe maka ba Ina sonka irin kaunar da take hana sukuni irin kaunar da ake bada rai da rayuwa dominta bazan taba iya rayuwa babu Kai ba,bazan taba iya bari na zama Sanadiyyar salwantar farincikin kaba Yaya Dr kayi hakuri kai ma,Kuma na yafe maka duk abin da kamin Ina Kuma Neman alfarmar da karaksake tuna kayimin wani abu acikin zuciyarka komi ya wuce mufara shinfida sabuwar rayuwa "

Matsowa yayi ya rungume ta suka cigaba da azzaba kukansu da kyar Samiha ta samu ta nutsu ta dedeta tunaninta ta rarrashi yaya Dr da kyar yayi shiru ya zama tamkar karamin yaro zuciyar sa gaba daya ta narke,nan de duka suka nutsu Basma ta sake yi musu nasiha matuka,tare sukaci abinci cikin farinciki da walwala,suna zaune suna shira sukaji sallama dukkanin su sai da suka tsorata amman banda Basma saboda daman tasan da faruwar abin.

Daga kan da sukayi sukaga momy da dady wani faduwar gabane yasake ratsa Samiha na shiga uku shikkelau bazan taba samin farinciki a rayuwata ba a lokacin da nike tunanin na fita daga wata matsala a alokacin wata matsakan ke sake tun karoni Innalillahi wa inna ilahiee raji'un abinda tayi ta fadi kelan cikin zuciyar ta.
Shima kanshi yaya dr yayi matukar tsorata ya shiga sake-sake iri iri akan mai yakawo su gidan sanann Kuma waya fadimusu anan suke,nan momy da dady suka zauna .
Momy ce tace " ya naga gaba Dayea Kun firgita kamar kunga wasu aljanu".
Samiha zo nan ki zo ki xauna kusa dani nayi matukar kewarki mikewa tayi cikin tsoro da fargaba da takarasa,dady ne yace nasan duk kunyi mamakin ganin mu babu bukatar dogon bayani,Basma taje ta samemu ta Kuma fadamana duk abin da yafaru miyi da na sanin abin da mika aikata miki Samiha duk da Ina da tabbacin yadda kukayi tayin abu ba cikin hayyacin kuba itama momyn ki abin da tayi ba aikin hayyacinta tayi ba Ina fatan Zaki yafemana sanann ki tashi ka hado kayanki mu tafi gida.
Wani sabon kukan farinciki ne ya kwacewa Samiha alhamdulillah alhamdulillah shine abin da take furtawa,momy tace
"Samiha dan Allah ki yafemin inshallah haka baza ta sake faruwa ba"
Dan Allah momy kidena ke mahaifiyata ce damab ban kullace ki da komi ba Ina fatan kema xaki yacemin duk wani abu da na miki "
Nan suka shiga daki aka hada kayan Samiha suka koma gida.

Wanann kelan ...............

(DUK ABIN DA YAYI FARKO A RAYUWA DOLE ZAIYI KARSHE BABU WANI ABU DA YAKE DAWWAMAMME DUK WANI WANDA YAYI HAKURI TABBAS KARSHAN HAKURINSA NASARACE BABBA).

yanzu aka fara wasan kuci gaba da bibiyar mu acikin wannan littafina mu mai suna ABOKIN YAYANA.
Ubangiji ya datar damu ya sake rufamana asiri duniya da lahira ya zaba mana dukkanin abin da yake alkairai a rayuwanmu kar yabar mu da zabin zuciyoyin mu, ubangiji Allah ya rabamu da mummunar kaddara🤲🏼🤲🏼🤲🏼.

Taku a kullum ZAINAB NASEER (ZEEY NASEER).
Chapter 24 · 0% Book details