← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 33

Sashe 23

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar an hankadota ta sake matsowa kusa da inda yaya Dr yake dan shi wayan shine a hannunsa bai masan mai akeyiba bakinsa ta kama ta fara sakarmasa wata kyakkyawan sunbata wacca ta saka ba shi da akeyiwa ba harta nihal da kawarta Atika sai da suka fara fita a hayyacinsa saboda yacca Samiha ke abin cikin salo da matukar birgewa babu shiri suka bar gurin.

Suna matsawa Nihal tace lalle yarinyar na ta rainamin wayo agabana takeyiwa yaya dr wannan abin Atika akwai matsala Ina matukar son yaya Dr wai ba yacca za ayi asake wani abin ya so ni sai de mu sake gwada wani malamin amman de kinji abin da wancan malamin yace tomshikkelau inde akwai wanin mijemana akwai su sosai makuwa kuma wadanda suka fishi mugunta da iya aiki aiko zamuje tom sai kishirya gobe mije.

Samiha da yaya da kyar suka samu sukayi control din kansu yace mata ta shi mije ina xamije Samiha kelan kede ki tashi .
Daman bai shiga da motarsa gida ba nan ya dauki kayanta ya sanya mata cikin mota sanann yaja nan bayan layinsu kadan yaje yayi parking akofar wani hadaddan gida juyowa Samiha tayi ta kallesa zatayi magana ya rufe mata baki.

Bayan sun tsaya ya dauki kayanta ya shiga da shi ciki ita ma ta shiga babu fargaba ko tsoro.

"Samiha anan zaki zauna har karshan rayuwanki domin da kanki kika bada xanan gidan nan kikace ayi da kanki kika bada duk wani fasali na wanann gida a matsayin gidan da zamu zauna idan minyi aure tom yanzu zaki zauna anan kafin inshallah nan da wani lokacin zan san yadda za ayi zan fadiwa dady sai a daura mana aure"

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo acikin idanuwan Samiha ta matso kusa da yaya Dr ya durkusa bansan mai zance da kai bansan Kalmar da zanyi amfani da ita wajan gode maka ba,ka zamo tamkar uba agareni ka sharemin duk wani kuka na inde ka ganni cikin damuwa kafin nayi magana akan abin dake da muna kake karantar halin da Nike cike kasmaarmin da shi hakika samin masoyi kamar ka a wanann lokacin yana da matukar wahala Ina kaunar ka yaya Dr Ina maka fatan nasara cikin rayuwan ka yadda baka da buri sai na kulawa da ni Ina fatan ubangiji yaci gaba da tabbatar da farincikin ka ya sake buda maka.

Durkusawa yayi ya dagota ya rungume ta akirjinsa karki damu Samiha inde Ina tare da ke inshallah bazan taba bari ki wulakanta ba goge hawayan ko so kike nima kisa na fara Aah yaya tom goge ta goge hawayan tana murmushi kama mata kayan ta yayi sukaje aka ajje a dakin gado da yaake babu wani abu da Yaya Dr bai saka acikin gidan ba jitayi zuciyarta ta fara samin nutuswa da sukuni amman ta Ina zata fara rayuwa ita kade ba tare da momy ba wadda tayi sabawar da ita sabawar da batayi da mahaifiyarta ba hawaye taji na kokarin zubo mata sai tayi kokarin tsaidasa da yakinin inshallah momy zata hakura ta barta ta koma gida.

Samiha na'am yaya zanje na samomiki dan kayan abincin da zakina dafawa sai Kuma na siyo Meiki ko dan karamin gas ne tom yaya nagode sosai ke ni kidena wannan godiyar kin manta cewa ke masoyi yata ce idan ban miki abububa wa zanyiwa idan ba kyautawa wadan da mike so ba wa zami kyautatawa hakane yaya tom sai na dawo ki kuka da kanki, inshallah Yaya.

Bayan yafita Samiha ta xauna take ta tunanin yacca rayuwarta ke sauya da turgudewa da yardar Allah ke kawo mata mafita "Alhamdulillah"shine abin da kawai take furtawa.

Ba jimawa kadan ya dawo ya kawo mata uban kaya sai kace wanda zata shekara Yaya wanann kayan abincin ai yayi yawa,kin manta ba ke kade bace ni da wane keda yaya Dr mana ko kina tunanin zan na cin abinci a wani gurinne bazan iyaba na saba da daddadan girkinki murmushi tayi tace Yaya Dr dina ni kade nan suka kwashe kayan suka Kai kitchen bayan sun fito sun zauna yace rintse idon ki ta rufe idon ta ya dora mata abu akan tafin hannunta yace bude tana budewa taga waya wani wawan tsalle tayi ta rike Yaya Dr tana ta murna wani farinciki yayi ganin Samiha cikin wanan farinciki domin ya kwan biyu bai ga hakan daga gareta ba nan fa tace "Nagode sosai da sosai yaya Dr ubangiji Allah yaci gaba da dafa maka albarkacin annabi ya sake buda maka kofofin samu Yaya ka zamomin uba kana min komi kana bani komi ka bani farinciki kaciremin duk wata damuwa ta kabani duk abin bukata Yaya Ina matukar kaunar ka.

Samiha ya isa haka sai de zan fadamiki wani abu gashi nan da sim card aciki Allah duk ranar da naga wani na miji ya kiraki zan kwace Kuma bazan sake baki wayaba hakama baza ta faru ba Yaya.

Nan yace mata zai tashi ya tafi anjima zai dawo okay sir nagode yafita kowannen su fuskar sa cike da farinciki da walwala.

Rayuwan ta fara tafiyawa su Samiha cikin farinciki sai de fa suna nan kullum cikin aikata alfashan su amman suna cikin farinciki.

A can kuwa momy na tunanin ko ina Samiha ta tafi abin na damun ta amman Kuma zuciyarta na fada mata abin da ta aikata shine dede Yaya Dr yayiwa Samiha matukar gargadi akan kartayar da tafito domin kar Jama'a su gane anan take kar aje a fadiwa su momy sai de su Jama'a duk yacca ka Kai ga boye abu sai sun tonoshi yanzu sunfara gane rayuwan da Samiha da Yaya Dr sukeyi acikin wanann gida sun Kuma gani tare suke sun Kuma san ba aure garesu ba domin duk unguwa dayane da unguwan su babu nisa.

Watarana tace yaya Dr Ina son ganin Basma mai Zaki mata dan Allah nasan bata san inda nakeba na tabbata ita ma tana can tana nemana kataimaka min kaje ka dakko, ta har gida yaje yayi sallama da ita yakuma fadamata abin da yakawo shi tayi murna sosai domin tana cikin matuakar tashin hankali da taje gida momy ta mata rashin mutunci takuma fada mata Samiha ta koreta,ta zo ta fadawa Yaya Ahmad kullum Samiha da yaya Ahmad suna yawo ko Allah zai sa adace su san inda take amman Allah bai ba,ta shiga ta fadiwa maman su suna tare da yaya Ahmad ta fadi musu cew yaya Dr ne ya zo zai dauketa Samiha na son ganinta yaya Ahmad mikewa yayi cikin murna yace "Alhamdulillah tun ranar da Samiha ba a san inda takoma ba nake cikin tashin hankali sai yanzu na sami nutuswa"
Yanzu a Ina take ina xakuje ban saniba ya de cemin Idan minje na gani tomshikkelau sai kindawo yaya Ahmad yace "Dan Allah kice Ina gaidata inshallah Yaya zan fadamata".

Nan ta futa fuskarta cike da walwala da farinciki ya kaita gidan da samiha take farinciki kamar ya kashe su sunga juna nan suka zauna Samiha tabata labarin abin da yafaru tundaga farko da dalilin da yasa momy ta koreta.

Basma abin dake bani mamaki da Yaya Dr shine kinsan Allah ada ki tafi hannuna bai taba dora hannunsa ba saboda matuakar taka tsantsan din da yakeyi akan bazai aikata ba dede ba dani Yaya Dr yana da matukar tsoron Allah ammam lokaci guda ya sauya Basma a kullum yaya Dr sai yazo ya aikata abin da zai aikata dani ya jagwalwalni ya mayarni tamkar kayan wanki,abin Yana damuna.
Tabass Samiha akwai matsala tom mai yasa ba za ki hana saba idan ya zo zai aikata bazan iya ba Basma bazan iyaba.

Amman Ina da wata tantama Anya ba nihal bace ta sake aikata wanann abin akan Yaya Dr haba de basma mai yasa nihal zatayi haka Ina tunanin baza ta tabamin abin da zai lalatamin rayuwa ba karki manta irin amincin da ke tsakanin mu wancan ma da tayi tayine saboda sonsa.Amman nihal nasan bazatayi abin da zai wargaxamin rayuwaba.

Ke Samiha dadina dake yarda shi wancan din da tayi kinsan zata aikatane har kike wani yabonta akan baza ta aikataba king ni nagama sawa araina ita ta aikata Kuma inshallah nihal sai tayi da na sanin abunda ta aikata ki kwnatar da hankalinki inshallah xan kawo karshan komi.
Ta Yaya Basma?idan tayarda da boka mukuma minyarda da ayar alkur'ani tare da addu'a babu wani abu da baza su iya magancewa ba inshallah duk wanann abubuwan da tayi sai sun koma kanta,akwai wani limami a unguwan bayan layin mu Allah yabashi ilimin matuka akan wanann abin yana karya asiri sosai xanje na masa bayanin komi inshallah albarkacin darajar annabi sai nihal tazo ta durkusa agabanki ta nemi yafiyarki kici gaba da Hakuri Samiha inshallah duk tsanani Ina tare dake.....

Barkan mu da ranar juma'a ubangiji ya hadamu da dukkanin alkairain dake cikin ta yakuma rabamu da dukkanin wani sharrinta Albarkacin darajar fiyayyan halitta annabi muhammadu (SAW).
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN
BY

ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 28

Basma tashi tayi ta koma gida ta tsinci kanta da bawa mamansu duk labarin abin da yake faruwa dede lokacin Ahmad zai shigo yaji tana bada labarin sanin watakil idan ya shigo zata iya dakatawa yasaka ya tsaya sai da yagama Jin komi kuka wiwi yakeyi saboda tunani iri-iri da ya sarkafe masa zuciya tausayin samihane yai matukar kama shi ya rasa mai yake masa dadi fasa shigowa gidan yayi kawai ya juya ya tafi.
Chapter 23 · 0% Book details