← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 33

Sashe 25

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina godiya agareku masoya da jimirin bibiyata.

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN
BY

ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 29

Sun tattara kayan Samiha gaba daya sunkoma gida,BASMA kuwa tarasa yadda zata kwatanta farincikin da take ciki tabbas babu abun da yafi karfin ubangiji duk wanda zai mika lamarinsa ga ubangiji ya isarmasa zai sami duk wani biyan bukata,bayan sun karasa gida suka isa dakin samiha tsaf yake saboda momy kullum sai ta shiga ta gyarsa cike da kewar Samiha.

Nan suka saka kayan suka fito bayan sun zauna momy tayi ta musu nasiha akan sukara dankon amintarsu sananan Kuma suna yaki da zuciyar su adullokacin da sukaji shedan yaraya musu su cutar da juna,Samiha basma kawace ta gari duk runtsi duk wiya karki yarda kirasata ki Kara riketa hannu bibbuyi inshallah momy.

Samiha ce ta sakko kasa tace "Momy Ina mai neman afuwanki akan dukkanin abinda na miki kiyi hakuri ki yafemin inshallah zanyi iya bakin kokarina wajan kiyaye aikata ba dede ba,nagode sosai da sosai da irin rikon da kulamin ubangiji Allah yabiyaku"

Momy ce ta kama hannun Samiha ta tasheta haba samiha bakiyimin komi ba dukkanin abin da yafaru ai ba lefin ki bane saboda haka ki kwnatar da hankalinki ubangiji Allah ya yafe mana baki daya.

Nan sukayi Shira ta dan lokac kadan Basma ta tashi tace zata tafi gida nan sukayi mata godiya matuka,kamar yadda Samiha ta saba ta tashi tayi musu abincin dare kai abin ya baka mamaki matuka sai taga kaman ba itaba,tana tsakiyan aiki Yaya Dr ya shigo motsinta da yaji a kitchen ya sa ya shiga nan yakama mata aikin kamar yadda suka saba a baya ya tayata suna shira sun farinciki.

Rayuwa ta cigaba da tafiya musu cikin farinciki da nishadi sunkuma sake rike addu'a da karatun allura hannu bibbiyu domin cigaba da kaucewa shedanu irin su nihal.

Yadda suka saba ba wanda zai ci abinci ba tare da dan uwansaba Kuma yanzu da yake yagama makarantar masa shine ke tayata komi,duk da yana business amman business yafi ta allaka da online zai yi order din kaya za akawo za a zuba su a shago tom yaransa ke zama ba shiba,shi iya Kaci yana tallata kayansa ta wayane Kuma alhamdulillah yana samin matukar samu saboda kasuwar tasa ba karama bace, alhamdulillah komi yana tafiya dede.

Ranar dady ya xaunar dasu yace "Kaga yanzu kagama karatunka na likitanci wanda shine burinka Ina ganin yakamata ayi wani abu wanda zai taimaka maka wajan taimakon al'umma da ilimin da ka samu,na yanke shawarar bude maka asibitin ka na ka nakanka sai ka dauki duk ma'aikatan da kake bukata amman ya ka gani"

Nagode sosai da sosia dady na dade Ina wannan tunanin araina amman kaga zantafi bautar kasa, ta Ina abin zai tafi yanzu idan ka tafi bautar kasar ka kafin kadawo komi ya kammala ya dedeta kana dawowa sai de shirye shiryen diban ma'aikata hakane dady ,nagode sosai da sosai ubangiji yakara budi.

Ke Kuma Samiha ga matsalan da aka samu akan jarabawarki na yanke shawarar zan siya miki wata,Aah dady kabari zanyi jarabawa da kai na shekarar kaman yanzune zatayi na fi so ace da Kai na na rubuta jarabawata tomshikkelau Allah ya nuna mana da rai ubangiji Allah yayi muku albarka ameen dady .

Basma tayiwa su Yaya Ahamd bayanin duk abin da yafaru saboda tsabar farinciki Yaya Ahamd har azumi yayi na kwana uku na godiya ga Allah da ya kawowa Samihan sa mafita,abin har mamaki yake bawa mamansu tabbas Ahamd na son Samiha amman babu yacca zai yi dole yayi hakuri.

Ranar Samiha na zaune ita da Yaya Dr sukace Yakamata su shirya suje gidan su Basma domin yiwa mama godiya akan taimakon ta agaresu,bayan sun shirya suka biya wani gurin siyayya sukayi mata siyayya matuka leshine,atamfa shijabbai dan kunnaye,haka de suka hada mata ka yayyaki,Samiha tace "Yaya Dr mai yasa kace mu tsaya miyi mata siyayya"?domin a duniyar nan babu abin da ya kai kyautatawa dadi,aduniyar babu abin da yakai inde kana da shi ka kyautatawa mutanan da ke so ka domin Allah,duk kudin su duk mulkin su inde ka kyautata musu xasu ji farincikin abun aransu zakuma suji dadi, shiyasa kikaga inde Ina da shi bana kyashin kyatatawa kowa domin kyautatawa tana Kara soyayyya tana kuma tafiyar da makiya,hakane Yaya Dr Ina fatan ubangiji Allah yabani ikon koyi da halayanka na gari ameen Samiha ta.

Haka sukayi ta shira har suka karasa suna zuwa suka tarar da yaya Ahmad zai fita gurin aiki, ya tsaya ya karasa gurin su suka gaisa sosai cikin faran faran yace "Allah yayi ma xamu gaisa fita xanyi amman alhamdulillah naji dadi da Allah yasa kuka sameni"
Ayyah babu komi Ahmad ai anriga anxama daya inji Yaya Dr,dan made kai ka zubar da zumunci baka dan lekawa gida.
Abubuwane yanzu duk sunmin yawa baba ya ajje komi na company nike yi shiyasa amman inshallah zan na kokartawa Ina zuwa tom Allah yayi mana jagoranci ameen ameen.

Nan bayan sun gama Samiha tace "Yaya Ahamd Ina kwana fatan kana Lafiya"alhamdulillah Samiha yagida lafiya lau mashallah ya juya yace tom na tafi okay Allah ya tsare sukace masa a tare.
Suka shiga gidan shi Kuma ya shiga motarsa yafita.
Basma na zaune a parlour sukayi sallama murna kamar ta kasheta nan ta tarbesu ta kawo musu ruwa da abinci,sukace mata sunzo gurin mama ne ta kira musu ita ,mama ta zo hakika taji matukar farincikin ganin su a haka rayuwan su tayi kyau alhamdulillah.
Nan sukayi mata godiya matuka,ita Kuma ta sake yi musu nasiha da kokarin tsare kansu daga mugun nufin duk wani mugu.
Suka tashi suka koma gida wal wala da farinciki cikin fuskansu,yau kimanin wata uku kelan da dai daituwar al'amiran su shine ya Kai kimanin wata biyar da barin nihal daga cikin garinnan.

Kamar wasa Basma da Yaya Ahamd sunfita zasuje unguwa ranar ma gidan su Samiha zasuje kawai sunzo wucewa sukaga wata mai ciki cikin nata ya tsufa da alama takusa haihuwa domin yadda cikin ya zama katoto sosai Basma ta tausaya mata yadda take tafiya da kyar son tsallaka kwalbati take amman takasa cikin sauri Yaya Ahmad yace Basma je ki taimaka mata,da sauri ta karasa sannu baiwar Allah nan ta kamata suka tsallaka wannnan kwalbatin nagode sosai baiwar Allah tunda nake son tsallaka wanann guri amman ya gagara nagode sosai,gaban bamsa ne ya fadi saboda muryar da taji tamkar ta san muryar juyowa tayi da sauri domin tabbbatar wa idanuwan ta abin da take zargi aiko abin da take zargi shine ya tabbata wannan matar ba kowa bace illa nihal,Basma ce ta kama sunan ta nihal da sauri ta waigo taga ashe Basma ce matar da ta taimaka mata cikin sauri take ta sauri domin bata son ta sake furta wani abu nihal ki tsaya mana miyi magana Yaushe kuka dawo yaushe kikayi aure Ina ai nihal ta manta da cikin dake jikinta saboda tantarayyar tashin hankali gudu tafara mai isarta ...
Ikon Allah!!! ta koma gun Yaya Ahmad kasan wacece waccan Aah,nihal cefa wai Allah!!!! daman tayi aure ne?shine tambayar da nake tayiwa kai na Kuma kaga da ta ga ni ce sai taki tsayawa ta gudu, koma de mai nene ita ta sani ki kyaleta ita ce a wahale hakane Yaya,haka sukayi ta shirarsu har suka karasa gidan su Samiha suka shiga a parlour suka iske su baki daya nan suka gaida momy Ahmad ya koma kusa da Yaya Dr domin yanzu sun zama amine kullum suna cikin Kiran juna ko zuwa gurin juna,haka suka zauna akayi ta shira har da momy dady Kam Yana gurin aiki.

Can Basma takasa jurewa tace wai kunsn mai Aah,yanzu fa nihal na gani a hanyar tahowar mu gidan nan.....

Tashin hankali ba
asaka masa rana shi Kuma alhaki ai abiye yake da kai duk abin da ka shuka shi xaka girba kuci gaba da kasancewa dani acikin littafin ABOKIN YAYANA......

Taku a kullum

ZEEY NASEER.

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 30

Da sauri Samiha ta dago kai tace nihal Kuma Basma,yaushe ta dawo ko ta zo yin wani abune gaba daya Samiha ta tsorata lokaci guda jikin ta yayi sharaf da gumi kana gani kasan tana cikin matsanancin tashin hankali da damuwa,ke miye hakanne ki kwnatar da hankalinki bafa ca nayi miki lokacin mutuwarki yayi ba kiga yadda kika bi kika daga hankalinki miye ne hakan Kuma,baza ki ganeba Basma bana son duk wani abu da zai sake jefani irin kalar halin da na shiga abaya kar ki damu da can ma ba ita taje faki ba,Allah ya riga ya kaddara hakan na rubuce acikin littafin kaddararki nihal Kuma ita ta zamo sanadi saboda haka ki kwnatar da hankalinki.
Yaya Ahmad da yaya Dr sosia suke tayi mata dariya saboda yanayin yadda ta tsorata yayi matukar basu mamaki,matsoraciya kawai Yaya Ahmad yace,Yaya Dr kuwa ya ma kasa tsagaitaqa da dariyar saboda yana iya tuna duk abin da yafaru ya tabbata shine abin da yasa tayi wanannan tsoratar.

Kuka Samiha ke kokarin kufcewa da shi momy ta daka musu tsawa ku miye ne hakan manyan banza zaku sakata agaba Kuna mata dariya saboda rashin mutunci lokaci daya sukayi shiru kowa yace shikkelau kiyi hakuri yar momy.

Momy tace "Dariya ba ita bace abin da yaka maceku Kamata yayi ku fara bincike akan abin da yasa nihal ta dawo garinnan,duk da cewa daman kunce min da yiyuwar zasu dawo domin babansu yafi son xaman nan,sanann ku binciko ya akayi take da ciki ko aure tayi".Amman momy duk mu ina ruwan mu da wanann yaya Dr ne ke fadin haka ,idan Kai babu ruwanka da shi mu ai muna da ruwa da shi inji Samiha.
Inshallah xamu binciko momy Yoh kodan mu tsuyeta mi dan dana mata irin kalar madacin da ta dan dana mana ai ma yi bincike akayi.
Chapter 25 · 0% Book details