← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 33

Sashe 28

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zaune suna ta shira kawai wayan Samiha ya dau kara mamakin wacca ke kiran ne yasa ta daga, tana dagawa taji muryan nihal Samiha dan Allah dan annabi kutaimaka ku zo gidan mu yanzu keda Basma da Yaya Dr dan Allah kar kuki zuwa nihal mai yafaru?ku zo ku kawai da kyar nihal ke maganar daga ji kai kasan tana matukar cikin tashin hankali mai matukar girgiza zuciya.
Samiha daman sarkin tsoro tuni ta rikice ta fara hawaye Basma tambayar ta take mai ke faruwa amman takasa dedeta kanta balle tayi mata bayani,da kyar ta samu tace mata nihal ce dan Allah kuzo mije ke ki nutsu ki fadimin mai ke faruwa tace tana son ganin mune ke sai kace baki san makircin yarinyar nan ba har wani tace tana son ganin mu mu wani dibi kafa mu tafi sai kace bammu hankali dan Allah Basma wai ke ba kya afuwane sai kace ba musulmi

Fiyau Samiha ta fice ta bar dakin,wanann ya tabbatar wa Basma cewa Samiha fushi tayi duk abin da yasa Samiha fushi kuwa ba karami bane domin bata da saurin fushi kuma inde tayi kafin a shawo kanta ana jimawa wanann ya tsorata Basma babu shiri ta dakko mayafin ta ta fito nan ta samesu suna kokarin jan mota ganin fitowanta yaya Dr yasa ya tsaya shiga tayi ya ja suka tafi babu mai cewa uffan,lokacin da Samiha ta fito kuka kawai Yaya Dr yaga tana yi bai tambayeta mai yafaru ba tace masa su tafi gidan su nihal haka yace ta shiga yayi kokarin jan motar shine bamsa ta fito.

Suna shiga gida suka tarar momyn nihal a falo tana kallo sai hankalinsu ya kwanta Basma ta kalleta tace daman bana fadimiki rainin hankalin ta bane,Basma dan Allah ya isheki haka ya isa,nan Samiha ta Kalli momy tace Ina nihal tace tana dakinta dakin ta wuce a hankali a tashi abin da ta ganine yayi matukar tayarmata da hankali gaba daya ta rude ta kwalalala wani kara wanda shi ya jawo hankalin su, su da suke falo suka shigo a guje suna shigowa suma tashin hankaline ya mamaye su .

Momy tayi kanta nihal nihal mai ke faruwa dake Ina cikin gida bansaniba gaba daya tana cikin jini yagaja yagaja abin tausayi nan momy ta ciccibeta ita da Samiha su kansu da suka dauketa sai da suka jike da jini.
Ku tsaya ni ba burina ku kai ni asibiti ba na sani cewa mutuwa zanyi shine dalilin da yasa nace ku zoku nasani cewa bazan rayuwaba shine dalilin da yasa nace ku zo dan girman Allah ku ajjeni ku ajjeni na samu na amayar da abin dake raina kafin na koma ga ubangiji.
Nihal na kuka basama da Samiha na kuka wiwi momy kuwa ta rasa mai ke mata dadi duk dakiyar zuciyar Yaya Dr sai da ya tausayawa nihal,shi kansa hankalin sa tashi saboda yanayin yadda yaga halin da take ciki tabbas ya tausaya mata.
Suna karasawa asibiti aka shiga da ita daga baya likitoci suka zo sukace inde ba ayi mata aikiba za a iya rasata ita da abundake cikin ta nan momy ta kira dady da kyar ta iya yi masa bayani yace babu komi ta wakilcesa ta saka hannu shima gashi nan zuwa nan momy ta Saka hannu ammanfa duk sun tsorata Kuma sun fidda rai da nihal.
Nan an fito da ita za ashiga dakin tiyata tana matukar jin jiki da shan wahala amman hakan bai sa ta kasa cewa a tsayba nihal Yaya Dr Basma duk ta nuna su suka zo kusa da ita kuka gaba daya suka fashe da shi banda da Yaya Dr da yayi suman zaune yama rasa mai ke damunsa ko banza nihal tare suka taso har shi kullum tana gidan su sannan tayi abubuwan alkairai iri iri agaresu bai Kamata yabari sharrinta ya lillini alkairain ta agaresu ba,nan ta bude bakinta da kyar dan Allah ku yafemin bana son naje kabari da zunubanku duk suka bude baki dan Allah kibari nihal Inshallah zaki sami lafiya zamuci gaba da rayuwarmu kamar yadda mika saba abaya komi zai dedeta,Basma tace na miki alkawarin xan baki aminci fiye da yacca na baki a baya zan kaunaceki fiye da yacca na kaunaceki a baya nihal kidena wannan maganganun inshallah bazaki mutu ba.
Juyowa tayi tana kokarin yiwa Yaya Dr magana fuskantar hakan da yayi ya matso kusa da ita ki kwantar da hankalinki nihal duk min yafe miki inshallah komi zai tafi dede Kuma zaki sami lafiya.
Nan yayi sauri ya bar gurin da sauri domin kuwa shi kade yasan mai yakeji baya son kuka ya kubce masa a gabansu.
Momy ce ta matso kusa da ita ya fashe da wani matsanancin kuka nan tayiwa yarta addu'a ta kuma yi mata fatan nasara inshallah za ayi lafiya lau aikin da yardar ubangiji.
Anshiga aiki anbarsu kowa da tunane tunane aransa can sai ga dadyn nihal ya zo shi suka ce masa anshiga da ita shima kuwa ya tsaya jiran tsammani.
Bayan wasu yan mintuna likita ya fito ya fadi musu alhamdulillah ansami nasarar cire abin dake cikinta ansami da na miji amman ita Kuma Allah yayi mata rasuwa...............

Innalillahi wa inna ilahiee raji'un tashin hankali ba a saka maka rana ita Kuma mutuwa ba a sanin lokacin da zata wakana shikkelau fa rayuwa kelan ubangiji Allah yasa mucika da imani yasa muyi kyakkyawan karshe.

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 34

Ba tare da sun luraba kawai kara sukaji suna wai gawa sukaga ashe momy ce ta fadi da gudu dady yayi kanta su kuwa duk cikin su babu mai karfin da xai iya daga kafarsa daga gurin dukkanin su babu wanda ya iya ansar dan da kyar yaya Dr yayi karfin hali ya karbesa,ya rone fari tas da shi kyakkyawa.

Samiha da Basma kuwa sun rugeme juna banda kuka babu abinda sukeyi domin kuwa na daya daga cikin ranar da baza su taba mantawa da ita a rayuwar suba nihal Masoyiyarsu da suka ta so tare ta mutu ta bar duniya.
Nan aka dauki momy aka wuce da ita emergency dady yayiwa Yaya Dr umarnin da ya bawa su Basma yaron ya mika masa mukullin mota yace yaje ya kirashi xai je ya anso gawar sai su tafi.

Kamar de yadda yace masan hakan yayi,andakko gawar nihal alokacin ne hankalin su ya sake gigita suka dimau ce sukamanta cewa a asibiti suke,a yunkuri dady da ca zaiyi su zauna anan saboda momy amman ina ya fuskanci gwammah a tafi gidan dasu nan ya saka su agaba yace su tafi mota.
Ya daga waya ya kira kanwar momy yace ta zo asibiti yanzu yakuma yi mata kwatancan dakin da xata shiga idan ta zo,nan ya wuce tunda ya sami wacca zata kula da momy.
Kafin suje yakira yan uwa da abokan arziki abin ka da mutum mai ahali kofar gidan har yayi dankam da mutane,nan aka shiga da nihal aka shiryata aka saka mata tufafinta na gaskiya tufafin da shine dukkanin managarcin tufafi duk kudinka duk mulkin ka,bayan ankammala shiryata akace mahaifinta ya zo ,ya shiga ya ganta yayi mata adduoi daman ita kadece yar su balla ace za a kira kannnenta.
Ana haka sai ga momy da kanwarta sun shigo da mamaki dady yace "Ya akayi kuka baro asibiti"ta farakane tace "Dole sai ta zo taga gawar nihal kafin akaita".
Nan ta shiga dakin ta tsugunna akan gawar nihal tace "Hakika nihal ke yarinya ce mai hankali da tarbiyya ke yarinyace mai gudun duniya,amman sai gashi lokacin da rayuwanki ta zo karshe kika lalace ki ruka aikata abin da ba dede ba,bansan dalilin hakan ba,amman Ina godiya ga Allah da sai da kika shiriya kika tuba tunkan mutuwa ta zo miki kuma nayi miki alkawarin zan so danki fiye da yadda na soki,zan kula dake fiye da yadda kika kula dake,Allah yayi miki rahama nihal".
Bayan ta kammala ta fito tacewa dady "Ina ganin yakamata abar Basma da Samiha suga gawar nihal domin tabbas sudin tamkar yan uwane agunta"
Hakane saka ayi musu magana nan akace suje suganta "Suna shiga ganin nihal cikin likkafani a daddare kowanannan su kukansa ya dawo sabo ji kake jigib jigib gaba dayan su sun fadi kasa babu mai motsi cikin su.

"Innalillahi wa inna ilahiee raji'un"nan akadaukesu akayi dakin momy dasu aka dauke gawar nihal domin kaita gidan ta na gaskiya na hakika.
Bayan antafi momy ta zo ta watsa musu ruwa duk suka farfado.
Nan ta xauna kusa da su tace "Nasani cewa Kun shaku da nihal amman hakan ba zai sa nace kuyi hakuri ku fawwalawa Allah ba,bata da wani gata agurinku illa kuyi mata addu'a ubangiji Allah yasa ta huta".
Nan momy tayi ta musu wa'azi,fitowa tsakargida sukayi Samiha ta gano momy ashe da ita akayi sutura,can ita ma Basma ta gano mamanta duk sun zo su ashe.

Da daddare lokacin Jama'a sun ragu wadan da suka zo daga wasu garuruwa kuwa sun sami makwanci sun kwanta,nan momy dady yana daki taje ta samesa ta mika masa takard gashi wanann likitane ya bani bayan na farfado yace nihal ce ta bashi bayan ta haihu da yake sai bayan anceto abin dake cikin ta ta rasu.
Karba dady yayi yana budewa ya fara karantawa "Bani da karfin da xanyi dogon rubutu amman dady momy dan Allah kutaimakamin kusakawa yaron da na haifa sunan yaya Dr yayan Samiha "
Mamaki ne ya cika su gaba daya tom mai yasa zatace asaka masa sunan sa,kodan bakomi bane watakil girman zumunci da amincin dake tsakaninsu.
Ranar da akayi uku ranar akayiwa yaron huduba da (SURAJ).
Bayan su Samiha sunzo momy take ce musu ansakawa yaro suna Suraja kallon kallo suka fara tom ko suna da wani dan uwa Suraj,nan momy ta basu labarin duk abin da yafaru da wasikar da nihal ta bada har dakko musu ita tayi.
Chapter 28 · 0% Book details