← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 33

Sashe 30

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da safe sun tashi suna cin abincin safe yazeed babban yayan Yaya dr yakira dady a waya bayan sun gaisa yake sanar dasu cewa inshallah rabb nan da sati uku zai dawo "alhamdulillah"gaskiya nayi farinciki sosai ai ni nayi tunanin sai nan da wata uku zaka dawo Aah dady sun rage mana semester dinne okay Allah yakawo mana Kai lafiya, Allah yayi baka nan za ayi bikin yan uwan naka su wa kelan dady?auran Samiha da Suraj da Kuma Abdallah da Basma kawar Samiha duk da ma de shi banje na tambayo ba tukunna amman Inshallah Ina saran zasu bamu.
Abdallah Kuma Dady yaushe aka gansa? nan ya labarta masa duk abin da yafaru yayi matukar farinciki sosai,amman dady Ina neman wata alfarma Ina ganin bai kamata ace anyi auran nan babu ni ba dan Allah dady kabari na dawo tukunna sai ayi,nariga da nasaka ranar aure sati biyu ansami matsaltsalu sosai a baya akan maganar auran nan bana son na sake dagawa,dan Allah dady kataimaka ni kadene fa yayan su guda daya da suke da shi dukan mu dan Allah dady kabari na dawo shikkelau naji na amince zanjira kadawo amman da sharadin kana dawowa kai ma za a hada da naka nikuma dady "eh"idan bakka wacca kake so ni zan samo maka kan kadawo "Aah dady Ina da ita akwai wata yarinya akalla min shekara uku mina tare Ina matukar sonta ita nake so na aura amman dady ni ban shirya aure yanzuba Ina son sai nan da shekara biyu"tom inde zanjira kadawo sai de na hada auran su da naka shikkelau dady kawai ba sai an jirani ba ayi,tom na tambayeka shin wane irin shirine na aure da ake bukata wanda baka dashi mina da kudi mina da komi dan mai zakace baza kayi aureba,nan dady yayi ta masa nasiha har ya sami nasarar amincewarsa ya fadi masa yarinyar da yake so dakuma yar gidan waye,mahaifin yarinyar shima hamshakin mai kudine nan dady yayi alkwarin shima zai je yana.

Ya nema masa aure amman duk wata daya auran zai kasance kelan yana dawowa gida Nigeria da sati daya za ayi auran,dady yayi murna sosai xai aurar da yaransa duka alokaci guda alhamdulillah nan yayi maza ya tashi ya nufi gidan su Basma.
Yaya zuwa ya sa akayi masa sallama da mahaifinta yana zuwa yaga shine yayi masa iso ya shigo cikin falo,nan babu nata lokaci ya fada masa duk wani abu da yake tafe da shi hakika mahaifin Basma yayi matukar farinciki domin kuwa babu wanda zai ki kai yar sa gidan mutunci irin wanann,ba karamin abun alfahari bane mahaifin su Yaya Dr ya zo nema wa dansa auran yarka.
Nan yanuna masa jindadin da yayi amman yace masa "Yanzu zamani ne ba ayiwa yara auran dole saboda haka zan fadiwa yarinya kasa yaronka anjima da yamma ya zo yaganta idan ya so Idan taji ya kwanta mata mashallah shikkelau sai ayi"yayi farinciki sosia yace inshallah zai fadawa Ahmad akan ya zo yaganta.
Yana tafiya ya koma
ya fada musu duk yadda sukayi sanann yayiwa Ahamd umarnin da yamma yaje yaganta suga juna.
Sanann yayi musu gargadi da kar Yaya Dr ko Samiha wani yabisa domin baya bukatar a takuramata ganinsu Kuma zai sa taji kunyar kin amincewa.
Shima ciki ya shiga ya sami mahaifiyar Samiha yayi mata bayanin komi sanann yace tafadamata anjima inshallah zai zo.

Maman Basma taji dadi sosai saboda ita tana matukar son ta hada jini da Samiha tunda Allah yayi danta Ahamd bai auri Samiha ba,tana fata Allah yasa Basma ta amince da auran Abdallah,ta kira basma tayi mata bayanin komi duk da batasan Abdallah ba lokacin suna yarinta amamn tana iya tunano kirkinsa da sanyin halinsa lokaci daya taji tana son anjima tayi domin ta gansa takuma ga ko zata iya amincewa.
Kamar yadda dady ya umarci Abdallah da yamma ya shirya yaje gidan su Basma bayan yaje ne maigadi ya bude ma gate ya shiga da motarsa sannan yaje ya isarwa da Basma cewa tayi bako nan ta nemi alfarmar da ya shiga da shi dakin baki,ya bude masa ya shiga wani sanyi mai ratsa zuciyane ya shiga cikin jikinsa daga can Kuma hancinsa ya jiyo masa kanshin wani dadddan turare da aka saka acikin dakin, Abdallah mutum ne mai matukar san tsafta nan kawai yaji Basma ta shiga ransa domin ya tabbata duk gyaran nan tayi domin shine.
Nan ya samu gu ya xauna bayan wasu yan mintuna hankalin sa na kan wayarsa sai yafara Jin sabon canji akan turaran da yaji wani turaran yaji wanda ya keta wancan kanshi,dagowa kansa ke da wiya sukayi Ido hudu da ita da yake labulan dakin a dage yake suna hada Ido gaba daya sukaji bugun zuciyar su ya sauya,nan fa basma tayi saurin sun kuyar da kanta dakin tashigo bakin ta dauke da sallama da yar siririyar muryarta.
Tsugunnawa tayi agabansa ta ajjja farantin da ke hannunta ta xauna akan kujera ta rusna ta gaidasa ya ansa fuskarsa dauke da murmushi.
Nan ta sakko ta zuba masa lemo ta mika masa da hannu bibbiyu,gaba daya salon yarinyar ya gama kashe masa jiki yama rasa mai zai ce mata nan bayan yasha lemon sun dauki mintuna a haka babu wanda yace komi.
Yayi karfin hali yace mata "Na zo ne daman domin miyi magana akan tsare tsaren da zamiyi abikin mu,kinga yakamata ace min tsara komi yadda yakamata"
Mamaki abin yabata kelan de shima Abdallah ya amince yana sonta tundade yake wanann maganar amman mai yasa bai fara tambayar ta tana sonsa ko ba ta sonsa ba yafara yi mata maganar biki"
Kan ta na sunkuye tace "Aah yaya Abdallah ai naji ance bikin tare za hada duka da na Samiha tom duk tsare tsaren da mikayi zata fadamaka"

Samiha zan aura ko Basma ke da kanki zaki kirani ki fadamin tsare tsaren da kukayi aike zan aura ba itaba.

Tomshikkelau Yaya Abdallah inshallah, bani wayanki na saka miki number ta ta mika masa bayan yasaka ya kirayi layin sa nan shima number dinta ta bayyana akan screen din wayarsa.

Ya mike sai ya dakko wani abu a gefansa acikin wata Leda haka mai dan girma ya mika mata,Aah yaya kabarshi ban gane na barshi ba,rokata kikayi Kuma idan rokata kikayi ma aikin kai ki rokenine idan ni da nake sonki bakii tambayeni na miki abuba wa zaki tamabya.

Ki dauka na bakine domin kyautatawa kuma daga yau ki dauka duk wani Abu da kike bukata kofa abude take zaki iya tambayata, idan ban kwatan ta kulawa dake ala yiba taya zaki sami karfin gwiwar zan kula dake idan mikayi aure.
Tom yaya nagode sosai da sosai ubangiji yasaka maka da alkairai yakarawa nemanka albarka ya rabaka da dukkanin sharri yakaremin Kai aduk inda ka shiga.

Adduarta tayi matukar yi masa dadi ya sami ansar abin da yake bukata batare da ya tambayeta tana son sa ko Aah ba,nan ya tafi ya barta.
Basma tunda take wani na miji bai taba rikitata da salon saba ya tafi ya barta da tunaninsa,tana shiga gida daki ta wuce ta kwanta kan gado tana tunano wanan fitinann kallon da yayi mata Lokacin da ta zo shigowa dakin,ai Basma gaba daya lokaci daya ta tsunduma kogin son Yaya Abdallah bata tunanin zata ki amincewa da auran,ita Kam alhamdulillah ta sami miji irin wanda ya dace,ranar nan de haka Basma ta yini cikin tunanin waannn dan bawan Allah yaya Abdallah..

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 38&39

Yaya Abdallah yana tafiya cikin nutsuwa ya sanya sautin karatun alkur'ani yana saurara a motarsa, tunano abubuwan da suka faru tsakanin sa da Basma yayi shi kade yake murmushi tabbas ya kamu da soyayyyar yarinyar nan domin daga kallon farko ya fuskanci tabbas ta tattara duk wani abu da ake bukata agun mace daman Samiha tagama fadi masa halayyan Basma Kuma ya ruga yayi na'am dasu amman yanzu da yazo idanuwan sa sun Kara tabbatar masa da wacece Basma sannan zuciyarsa ta gansu matuka da ita,yanayin takunta yanayin kallonta da Kuma yanayin yadda ta iya sarrafa harshanta wajan furta kalamai cikin nutsuwa,shi kade cikin mota yake ta sumbatu Ina sonki Basma kawai yaci gaba da tukinsa .

Yakarasa gida yana shiga gida ya tarar da dady, momy, Samiha,Suraj ,duk sunyi zugum a falo suna jiran dawowan sa domin suji mai yafaru yana sallama yanayin da sukaga ya shiga da shi cikin gidan shine ya tabbatar musu tabbas akwai nasara zama yayi ya gaidar da su dady.
Sai Kuma ya kona gefen yaya Dr ya zauna ya kalle dady yace "Kamar yadda dady ka umarce ni da naje naga Basma naje Kuma alhamdulillah da dukkanin abinda na fuskanta daga gareta ta amince dani"alhamdulillah shine abinda dukkanin su suka furta dady yace "Shikkelau komi yazo karshe shima yazeed naje gidan su yarinyar mahaifanta sun amince yanzude dukkanin ku na saka auranku wata daya inshallah"

Washe gari da safe weekend ne kamar yadda Yaya Dr da Samiha suka saba fita yawan shakatawa haka kuwa akayi sukacewa yaya Abdallah shima ya shirya su fita tare,tom ammam Abdallah mai zai hana kakira Basma ka fadamata zaka zo ku fita yanzu ta shirya,haba kai kuwa Suraj kawai daga fara zuwa gurin yarinya sai nakirata nace mata zamu fita, haba karka bani kunya mana wannan fitar zata Kara sakawa ku shaku da juna hakane Kuma bara na gwada ,yawwa zaka iya fadamata ma tare zamu fita duka okay.
Chapter 30 · 0% Book details