← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 33

Sashe 17

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya shiga daki da minti goma ya fito ya xo ya xauna kusa da ita mamaki abin yabata tace tom lafiya acikin zuciyar ta samiha Ina son zamiyi magana Ina jinka shin dagaske kinyarda xaki auri ahmad Yaya Dr nayarda mana mai yasa kakemin wanann tambayar naga baku jima da sanin juna ba akalla yakamata ace kinsan halayyarsa tukunna Aah na fuskance shi Kuma nasan ba zai taba cutar dani ba Kuma Ina sonsa kuma daman mai ake so a aure ai soyayyya hakane Allah ya sanya alkairai tashi yayi jiki babu kwari ta koma daki yawanta yana jin gaba daya duniya tayi masa zafi yau shi Samiha take kalla take cewa tana son wani agabansa......

Cakwakiya mai ke shirin faruwa hakane☺️☺️☺️☺️

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CRETED AND WRITTEN

BY
ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 20

Yaya Ahmad saboda tsabar farinciki bai san lokacin da yakarasa ya rungume Samiha yana mata godiya ba Samiha nagode nagode inshallah na miki alkawarin baza ki taba dana sanin aurena ba zan baki kula fiye da wacca uwa take bawa yaranta xan mayar dake tamkar sarauniya mata ita keyiwa miji biyayya amman ni na miki alkawarin ni zan miki biyayya.

Maman su Basma ce tace "Samiha bansan da me xanbiyaki ba domin a yau kin cikamin burina akanki na tsawon shekara goma bani da wani buri da ya wuce ki auri Ahmad inshallah zamu kula dake kamar yadda kika mana halacci inshallah muma xamu miki"

Haka kawai Yaya dr yaji zuciyanshi bata masa dadi bai Kuma ji dadin yadda Samiha ta amince da auran Ahamd jiyake tamkar ya kashe Ahamd shikkelau babu wata dama da za a samu ta aura mata wani shi ba zai iya auranta ba sannan Kuma baya son wani ya aureta domin da ta amince da auran Ahmad ji yayi kamar ya mutu tom mai yasa shikade yake tayiwa kansa wanann tambayar mikewa yayi yayi hanyan fita dady ne ya tsayarsa yace ina zaka?dady xanje wajane yanzu zan dawo tom shine abin da dady yace masa ya juya yaci gaba da uzurinsa.

Bayan fitarsane dady yace "Tom yanzu Ina tunanin komi ya wuce idan Samiha ta gama samin sauki mika koma gida sai kuma miyi kokari a fara shirye shiryen biki"
Tom sukace mama na sake yiwa dady da momy godiya domin ji take tamkar sun bata kyautar duniya da abin dake cikin domin samin Samiha a matsayin suruka bakaramar nasara bane yarinyar ta hada duk wani abu na daraja da kima.

Nan sukayi musu sallama suka tafi Basma ma ta bisu domin takee tayi wanka ta dawo.

Bayan tafiyan su dadyn su Suraj shima tafiya yayi hakan ya bada damar barin momy da Samiha su kade momy ce tace "Samiha kinsani sarai Ina sonki Ina kuma kaunar farincikin ki keda Suraj dukkanin ku yarana nane wadan da nakejin kudin duniyatane bana son damuwar dayanku hakanne yasa dana ji abin dake faruwa nayi kokarin sanar da dadyn ku domin samin mafita Ina fatan hakan bai bata miki ba"

Hakika momy ke uwace ta gari Ina kuma alfahari dake nagode sosai da kaunarki gareni .

Kwanci tashi Samiha ta kwashe sati cur a asibiti sai de tabbas jikinta Yana matukar Kara samin sauki domin a kullum Ahmad sau uku yake zuwa gun Samiha shi yake zuwa da safe ya Kawo mata abinci ya zauna ya bata taci baya taba barinta sai yaga taci ta bata maganunuwanta dan kafin momy ta zo yagama ciyar da ita,haka yake tayi safe rana dare baya taba gajiyawa kuma idan yagama yakan zama su jima suna shira da Samiha yana matukar bata lokacinsa kuma daman Ahmad yana da matukar surutu ga wasa da dariya hakanne yasa yafara shiga ranta a dan lokacin ta dan farajin damuwar da take ciki ta ragu ba wai ta dena son Yaya Dr bane Aah sai de yanzu albarkacin addu'aoin da Yaya Ahmad ya bata da Kuma irin kulawar da yake bata tabbas tafara futa cikin damuwa Kuma ta fara dawowa cikin hayyacinta.

Kullum wanann ziryar da Ahmad keyi akan idon Yaya dr sai de idan ya taho yakan biyo shi ya leko ta window yana ganin duk irin soyayyyar da ya ke nunawa Samiha zuciyar sa na matukar Kuna da zafi yana Jin babu dadi amman idan yaji hakan sai yakoma shima yakira nihal dinsa.

Bayan ansallamesu daga asibiti Ahmad shi ya daukesu ita da momy ya mayarsu gida sanann yakara mata wasu darrussan na rayuwa akan yin hakuri akan dukkanin wani abu da bawa yarasa (Samiha nasani haraynzu kina cikin damuwa baza ta fita lokaci dayaba ammann Ina son kisani cewa duk wani abu da bawa zai rasa tom tabbas daga Allah ne Ina son ki Kara sakawa aranki akwai wani abu da ubangiji ya tsara shiaysa yarabaki da Suraj ubangiji yafi son mu fiye da kowa Kuma yafi mu sanin abin da yafi zama alkairai agaremu, ubangiji da kansa yace mikan son abu amman ba alkairai bane agarin mu sanann mukan kin abu Kuma shine Alkairi agaremu ,tom kinga Abdullokacin da Allah ya jarabce mu da wata kaddara Kamata yayi mu daga hannu mu gode masa matuka nuna damuwa akan abin da Allah ya jarabcemu tamkar mina nuna masa cewa minji haushi ba miyi Imani da shi ba)

Ni zantafi sai na zo na daddare Allah yakara sauki matata ta gobe inshallah,juyawa yayi da sauri Samiha tace yaya Ahmad wai gowa yayi saboda yanayin yadda tayi maganar tayitane cikin wani salo na Jan hankali"Ina sonka Ina kaunarka a karon farko zuciayata ta sake fadawa tarkon wani na mijin karasowa kusa da shi tayi tace dan Allah karka cutar dani Kai ma karkasa na wahala"
Da sauri Ahmad ya tasar da Samiha haba samiha kidena mini magiya inshallah bazan taba barinki ba nagode Yaya Ahmad nine da godiya da yau kika furta kina so na nagode juyawa yayi karaf yaga Yaya dr a tsaye ashe duk abin da sukayi akan idon sa Yana tsaye yana kallonsu matsawa Ahmad yayi yamika masa hannu suka gaisa ba yabo ba fallasa Suraj ya ansa masa.

Ciki yaya Dr yayiyo shikuma Yaya Ahmad yafita tagansa sarai yana karasowa tace masa Yaya Dr barka da gida Ina yini lafiya lau alhamdulillah Samiha ya jikinnaki da sauki sosai tom ki kula fa sosai inshallah sai ya wuce daki tayi mamaki matuka da yanayin da yayi mata magana irin yanayin da tayi kewa lokacin suna soyayyya Kai Aah ba hakabane kawai de tausayina yakeji.

Bayan ya shiga daki da minti goma ya fito ya xo ya xauna kusa da ita mamaki abin yabata tace tom lafiya acikin zuciyar ta samiha Ina son zamiyi magana Ina jinka shin dagaske kinyarda xaki auri ahmad Yaya Dr nayarda mana mai yasa kakemin wanann tambayar naga baku jima da sanin juna ba akalla yakamata ace kinsan halayyarsa tukunna Aah na fuskance shi Kuma nasan ba zai taba cutar dani ba Kuma Ina sonsa kuma daman mai ake so a aure ai soyayyya hakane Allah ya sanya alkairai tashi yayi jiki babu kwari ta koma daki yawanta yana jin gaba daya duniya tayi masa zafi yau shi Samiha take kalla take cewa tana son wani agabansa......

Cakwakiya mai ke shirin faruwa hakane☺️☺️☺️☺️

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN

BY
ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 21

"Innalillahi wa inna ilahiee raji'un"ita ce Kalmar da yake ta furtawa yarasa mai yake yi masa dadi yarasa Ina zai sa kansa haka kawai yaji hankalinsa ya tashi bai Kuma gamsu da abinda yake shirin faruwa ba anya zai iya zuba Ido yana gani Ahmad ya auri Samiha tom ya zaiyi idan Kuma yace "Aah"sai de fa shi ya hakura da auran nihal anya ta Ina zai iya hakura da soyayyyar nihal ba zai taba iya rayuwa babu ita ba ta xama jinin jikinsa wai mai ke shirin faruwa da nine haka yayi ta tunani ba tare da ya san ansan abin da yake faruwa ba.

Falo kuwa momy da Samiha ne ke zaune suna ta shira domin alhamdulillah jikin Samiha yayi sauki momy na sake yi mata wa'azi da na nasiha akan ta karbi kaddarrar da Allah ya rubuta mata momy tace "Samiha Ina da tabbacin cewa Suraj ba acikin hayyacin sa yakeba saboda abubuwan da yake sun fice hankali Ina ganin Ina Kuma zargin kamar anyi masa wani abu wanda ya jawo faruwar wannan abun amman koma mai nene inshallah zai yi sauki kiyi hakuri ki karbi kaddarar da Allah ya doramiki na tabbata auran Ahmad zai zama alkairai agareki da izinin ubangiji.

"Inshallah momy na karbi komi Kuma na yafewa Yaya Dr na tabbata nima ba a son rashin yakeba akwai wani abin amman bana son zargin kowa fatana de Allah yayi mana zabi mafi alkairi ".
Ameen umma tace sallamar da sukaji ita ta katse su daga zanacan da sukeyi Ahmad ne da Basma da niki_nikin leda a hannun su gaida momy sukayi suka tambayeta ya mai jiki ta fadi musu da sauki sosai nan Ahmad yayiwa Samiha sannu ta fadi masa jikin yayi sauki sosai nan momy ta tashi ta basu guri Basma ma ma tace bara na biyoki momy na barsu Aah Samiha tace "Dan Allah ki zauna yau ina bukatar mi zauna miyi Shira dukan"

Nan Basma ta dawo zama sukayi suna ta shira cikin farinciki tare da walwala alhamdulillah shine abin da Samiha ke furtawa cikin zuciyarta bata taba tunanin zata sami sauki acikin zuciyar ta na soyayyyar Yaya Dr cikin sauki ba,bata taba tunanin zata cigaba da rayuwa bayan babu shiba sai de gashi cikin karamin lokaci kulawa tare da addu'aoin da Yaya Ahmad ya bata tafara jin sauki matuka acikin ranta.
Chapter 17 · 0% Book details