← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 33

Sashe 2

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani Abu dake Bata mamaki,duk irin kalar musgunawar da yake mata,Baya taba barinta cikin matsala ta Wani Abu na rayuwa,tun iyayanta suna raye yake dawainiya da ita,Yanzuma haka Kuma Bai Dena ba,Gidan taf yake da kayan abinci Wanda ya zama duk watane sai ya kawo Mata
abin da take bukata ,Baya taba barin ta rasa ko maggi,komi ya tanadar mata,Baya son ta zauna da yunwa,tom Mai Hakan ke nufi,Yana Sonta harynzu ko yaya?tambayar da take Tayi acikin zuciyanta kelan Amman ta kasa samin ansarta,kawai sai ta tsinci kanta da yin murmushi,tare da Bude ledan da yakawo mata,take a way ne yayo mata,jallof din shin kafane aciki wadda taji kayan Hadi matuka,sai Daya ledan gashashiyar kazace Mai Rai da lpy,Sai kuma drinks guda biyu da ya sako mata da su,Yaya Dr kelan,ko yamanta jiya ya kawomin drinks dina na wata suna nan jibge a fridge,dariya abin ya Bata,tabbas Haryanzu Yana son ta,tom Amman Mai yasa yake mata abin da yake mata?..........
Amsar na cikin wanann littafin na ABOKIN YAYANA,Kuci gaba da kasancewa damu ngd.

Bayan ta kammala cin abincinta ta tashi taje domin yin alwalar sallan Ishan,ta idar da sallah tayi shafa'i da wutri,taje Kan gadonta domin ta kwanta,photonsa shine abin dake haskaka wallpaper din wayanta,shine Kuma abu na karshe a kullum da take kalla idan zata kwanta bacci, Murmushi tayi mai hade da ciwo tare da fadin yaya Dr.mai yasa,Mai yasa Kai da ka zamo farinciki na a baya a yanzu ka zamo damuwata,Dan Allah yaya Dr.kataimaka,Ka dawo tamkar da,muci gaba da rayuwa cikin farinciki,miyi aure miyi irin Kala rayuwan da Mika tsara lokacin mina yara.
Tana wannan tunanin bacci ya dauketa misalim karfe uku na dare ta farka,Samiha duk da shedan cinta da irin Kalan rayuwan da sike da Yaya Dr.hakan Bai sa ta zubar da addinim da take da shi a bayaba,illa iyaka karuwa da yayi domin a kullum tana ganin tana bukatar Neman yafiyan ubangiji domin lefin da take tafkawa,Bata wasa da sallah,Bata wasa da ibada,ba Kuma ta wasa da addua,to Amman mai yasa duk da irin wanann abubuwan da take aikatawa ta kasa kufcewa tarkon sa,ita kanta a kullum tana yiwa kanta wanann tambakar Amman ta kasa saminta,Amman karku damu alkalamina zai sanar muku da ita.

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

ABOKIN YAYANA😭
Zamina posting na wanann littafi abokin Yayana Sau uku a duk sati,Sannan adadin reacting posting dina da kuke shine zai karamin karfin gwiwa wajan tabbas kunajin dadin karanta wanann littafi,Amman muddin zanyi posting babu reacting a lokacin da kuka karanta,zanga tamkar ba karantawa kukayiba sannan bazan na samin karfin gwiwar posting ba,sannan Koda posting din Bai yi muku dadi ba,akwai alama da zaku danna wacca zanga Hakan at least de ace in de kukaga posting kuka karanta,kuyi liking wajan nuna alama,Wanann zai karamin karfin gwiwa,Sannan Kuma zan ware Rana Daya a sati wacca zan Bude group domin comments Daga baku nan ku,Nagode sosai da kasancewar ku cikin wanann group,Allah yabani ikon kawo muku abin da zuciyarku zatayi dadi.

Page 2

Soyayyya ta zamo min Karfan kafa,ta zamo matsala ta,Bantaba tunanin soyayyyar Yaya Dr.Zata zamo matsala a rayuwata ba,Dan Allah yaya Dr.Ka dawo tamkar da,ka tausayawa Maraicina,a yanzu Kai kadene farinciki na da Kuma fatana karka bari rayuwata ta kare a haka,Kuma takeyi wiwi,ta rasa Mai ke mata dadi

Tana cikin wanann tunanin ta mike domin Ta shiga tayi alwala,ta fito Ta dauki abin sallah,Ta idar da sallah tajira tayi sallan asuba,ta dauki kur'ani ta karanta yadda ta saba,duk da ba Wani nisa tayiba,Amman tasan surori da yawa,Wanann shine al'adarta Koda kuwa tana period Bata taba bari dare ya wuceta,ta kan raye daran ta wajan bautawa ubangiji da adduar Allah yakara shiryar da ita,Bayan ta kammala ta koma Kan gado domin taci gaba da bacci,Wanan shine al'adar ta akowane dare,Bata komawa bacci sai tagama duk wasu ibadu,kama Daga karatun alkur'ani da Kuma azkar sanann idan Takoma bacci da wiya kaga ta shi sai wajan azahar,ko Kuma idan yayan Nata yakirata wannan ita ce rayuwarta a kullum Bata da Wani buri ba Kuma ta da Wani fata,A yanzu Bata san Ina rayuwarta ta do saba.

Samiha wacca ada take da buri na zama shahararriyar Likita,tamkar yayan nata ita ce wacca yanzu ta zamo Bata da Wani fata illla na zaman gida,har fargabar fita take saboda sa idon Jama'a,Gaba Daya rayuwar ta ta zama cikin kunci da damuwa,yah rabbi Ka kawomin agaji.

A Dede lokacin tana tsakiyan bacci ne tayi mafarki da mahaifiyar ta,tana ce mata Samiha ki tashi tsaye ki gyara rayuwarki,hakika akwai dalilin faruwan duk wanann abubuwan dake faruwa dake karki bari rayuwanki ya lallace a aikin banza,kiyi yaki domin dawo da rayuwanki kamar da,kici gaba da addua,kici gaba da Neman agurin ubangiji inshallah zai shiryeki,Fitik ta mike sharaf da gumi jikinta,tana Kiran sunan Allah hade da zazafan hawaye a fuskarta,sallamar da ta Jine ya sa mata karfin gwiwar mikewa domin ta San wace Mai sallamar ita kadece wacce ke shigowa in da take tun bayan rasuwan mahaifanta,ita kadece wacce take shigowa ta Bata shawarwari wadan da ke mata dadi,ita kadece wacca ke jurar zama da ita,ita kadece wacce Bata kyamatar ta a halin da ta tsinci kanta,wanan dalilin yasa take matukar kaunar ta,yanzu a duniyar Samiha bayan Yaya Dr,babu Wanda take so irinta,Babu abin da Samiha baza ta iya yi mata ba in de tana da shi,domin ta gama mata komi a rayuwarta,Bata kya mace taba,bata nuna mata komi ba,Kamar yadda mutanan anguwan ke kyamatar ta,babu Wanda ke kulata ta Kai ta kawo manyan unguwar kansu ba kowa ke ansa gaisuwar taba,Hakan yasa ma ta hakura ta Dena gaida kowa,ita kanta da take zuwa gurinta,mahaifanta Basa so.

Tayi kokarin ganar da su da kyar mahaifiyar ta ta fahinta ta bar ta taci gaba da mu'amala da Samiha,shima Dan anace ciwon ya mace na ya macane,Wanann yasa mahiafiyarta ta fuskance ta ta Kuma barta ta cigaba da mu'amala da ita,tare da fatan Allah ya sa yarta ce Sanadiyyar shiryiwar Samiha,Amman har yau duk da tsawon shekarun da suka shude kwata kwata mahaifinta yakasa fahintarta,Hakan yasa Bata samin Damar shigowa gurin Samiha sai bayanan.

Wacece ita
Wane matsayi ne da ita a gareta agurin Samiha
Mai yasa take son zuwa gurin Samiha ?

Mai yasa Kuma ta kasa rabuwa da Samiha?

Cikin farinciki ta tsallako Daga Kan gado ta nufo falo da saurinta ta zo ta rungumeta ai nasani sarai Daman kina nan kina baccin asarar nan taki,ke bakki da aiki sai bacci,ke kullum baza ki Samu Wani Abu da zakiyi ba sai bacci.

Dan Allah Samiha ki Samu ki koma makaranta,Koda baza ki koma Boko ba,ki koma islamiyya Hakan zai taimaka Miki wajan sake sanin abin da yake Dede sanann ya sa kisake rage abubuwan da kikeyi sanin kanki ne Bana son wanannan rayuwar da kike,Ina jin babu dadi idan naji yadda mutane ke xaginki acikin gari,Ina jin ciwo idan naji yadda ake muzantaki,Samiha Dan Allah ki gyra halinki,Besty shine sunan da Samiha takira da wadda ke mata maganar,sanin kanki ne kinsan ba haka nake ba,narasa Mai ya sauyani,narasa mia yasa na daukawa Kai na wanann rayuwan,Mai yasa haka ke faruwa Dani,a kullum addua ta Allah ya shiryeni ya Kuma gyaramin rayuwata,Kuma inshallah na tabbata albarkacin Imani da nayi da shi da Kuma addua da nake dare ba Rana,na tabbata xai shiryeni,zai Kuma dawo Dani Dede da izinin ubangiji,Nasani besty daga Daya bangaran matar tace da Samiha,Amman kisani kullum sake girma muke idan mune yau bamu bane gobe,Dan Allah ki gyara inshallah Samiha tace.
Tom yanzu Zaki koma islamiyyar Dan Bata Rai tayi,tace kinsan sarai yadda mike karkewa da dalibai da Kuma Malaman makarantar,kwata kwata basa son ganina kowa kyamatata yake,sauran malan Kuma wasu Daga ciki suna wulakantamu saboda naki karbar soyayyyar su,nayarda na aure su,na rabu da Yaya Dr.ke kinsani duk Wani Abu da zai Nisan tani da shi Bana so Bana Kuma kaunar sa,na gwammatah na rayuwa da shi,shi kade cikin duniya Koda kuwa kullum zamu rayu cikin bani madaci da rayuwar axaba da yake yanzu.

Nunfashi ta ja,Samiha wanann wane irin rayuwane mara karshe,Basma,sunan da naji ta kirane yasa na wai waya ita wacca aka kira da besty dazu Ashe sunan ta Basma,Sun ta so tun suna yara su uku acikin unguwar su,duk da cewa dukan yaran talakawane Amman suna da rufin asiri Dede gwargwado Sannan suna rayuwa cikin farinciki da aminci,Samiha,Basma,nihal,Su uku suka tashi a unguwar su,babu Mai jin kansu kullum suna tare makaranta Daya sukayi, Islamiyya da Kuma Boko,Kafin Kuma Samiha ta sauya halayyarta da Kuma dabi'arta,saboda tsabar amincin dake tsakanin su,Har suna suka hadawa junansu """Bashal""an dauki kalma dai dai cikin sunan kowa,Tom Amman yanzu Ina nihal,Ko ita ma ta guji sami hane?,ni kai na ban saniba Amman bincike zai tabbatar man da Ina take.

Basma karki damu ajikina nakejin inshallah zamu rayuwa da Yaya Dr.zai aureni zakuma miyi rayuwa cikin farinciki,Amman Samiha Taya kike tunanin kunyi rayuwa irin wanann sanann Kuma kike tunanin zai aureki,tom idan ya aureki Mai zai Samu, soyayyya ta da Yaya Dr.ba soyayyya bace domin jikina ko Wani abin, soyayyya ce Daga ruhi zuwa gangar jikin mu,Amman Kuma kuke irin wannan rayuwar?,Basma baza ki Gane komi ba, kede kici gaba da tayani da addua, ubangiji ya kawomin komi cikin sauki alfarmar annabi, tomshikkelau Samiha inshallah da yardar ubangiji,Kuma nima Ina jin komi zai yi dede inshallah ngd sosai kawata Allah yasaka Miki da alkairai ngd sosai kawata.
Chapter 2 · 0% Book details