← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 33

Sashe 7

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zainab sai da ta nuna dan halin Dan ko kan gawar su Bata jeba duk da sai da mahaifin su Suraj ya sauke nauyi yace akirata sai ca tayi baza ta iya juran ganin gawar mijinta da kishiyar ta ba kowa kallonta yake Yana kaji Wani sabon makirci domin babu Wanda Bai San abin dake faruwa tsakanin su ba duk unguwan Bata zaman lafiya da kowa saboda suna son jummai ita Kuma mummunan halinta yasa suka tsaneta A haka aka kwashe kwana 7 ana zaman makoki Zainab ta ware kawai uzurinta take tana taka Wanda take so.

Amman abin da yabata mamaki shine Mai yasa yaran basu mutu ba sai a zaman makokin da ake taji Ashe ranar ba agidan suka kwana ba bayan ankammala zaman makoki malam liman mahaifin jummai yace zai koma garinsu sanann abashi yaran ya tafi dasu Dadyn su Yaya Dr da momy Sukayi ta rokon sa akan yataimaka yabarsu zasu kula da su kamar yadda suke kulawa da nasu yaran da kyar yayarda ya barsu Nan ya tafi Yana Mai alhinin rasa yarsa.

Zainab Takoma wajan Boka domin tunanin ta kwashe Dan abin da yake da shi da kuma tuananin ta Ina zai a fara Boka yace Kinga Yana da yaro namiji Kuma shi zai kwashe Rabin dukiyan da ace Bai da da na miji Kinga da za kifi samin dukiyan tunda Bai da Yan uwa tom yanzu Mai yakamata ayi mu batar da wanann yaron a nemeshi a rasa Kinga shikkelau Zaki kwashe Dan abin da yake da shi ki gudu Cikin murna ta dawo gida ansami nasara.

Kamar yarda Mahaifin su yaya Dr yayi alkawari ya tattara kayan su Samiha da Suraj sun koma gidan sa Yana Kuma basu kulawa Dede gwargwado Shakuwa na Kara shiga tsakanin Suraj da Samiha adede lokacin Suraj da Abdallah sunkara girma domin sun Sami admission xasu tafi Jami'a Samiha ita Kuma ta shiga js3 tana da 13 years Farinciki na karuwa a gidan sanann Suraj Yana iya bakin kokarinsa ganin ya taimakawa Samiha ta rage damuwar dake ranta damuwar suraj aduniya shine ace Samiha tana cikin damuwa,duk da yasani cewa zaiyi wiya ta cire komi Amman Yana son yaga tana fara'a kodan lafiyarta tundaga lokacin da abin yafaru shima Baya cikin walwala domin walwalar Samiha ita ce tasa farincikin ta shine nashi.Haka Kuma yake iya bakin kokarinsa wajan ganin yakara jawo abokinsa abdallah jikin sa domin ayanzu bayan Yaya jamilu Baya tunanin Yana da wasu Yan uwana da suka wuce Samiha da abdallah haka rayuwata ta cigaba da tafiyar musu makaranta daya sukeyi sai de Kuma maban banta course shi abdallah Yana medicine shi Kuma Yana karantar loor hakanne yasa basa gama lectures lokaci daya Amman duk Wanda ya riga fitowa zai jira Dan uwansa sannan sai a tafi a dakko yar auta Samiha,Samiha tana matukar ganin gata agurin yayun nata guda biyu Kuma a kullum shakuwa sake shiga tsakanin su takeyi.

Adaran ranar suna kwance Suraj Jamil,da Kuma abdallah abdallah yaji kamar ana kiransa farkawa yayi kawai ya tashi ya dinga fitowa har sai da ya zo bakin gate kofan ya bude yafita shi kansa Bai San in da yake yiba.
Asuba tayi dady ya shigo domin tashin su sallan asuba ganin abdallah Baya nan yayi tunanin sun tashi ma may be Yana bandaki tashin su yayi yace ku tashi Kuma Abdallah na fitowa kuyi sauri kuyi alwala karku makara duba da yace musu abdallah idan yafito yasa sukayi ta jira abdallah ya fito su shiga Amman shiru Hakan yasa jamilu ya mike ya Dan buga kofan bandaki Amman babu alaman za afito Dan turata yayi a hankali yaga babu kowa da sauri ya juyo yace Suraj babu kowa fa a bandaki da sauri shima ya taso sukayi ta dube dube amamn babu alamin abdallah Alwalan sukayi suka fita da kyar sukayi sallan suna jira a idar su fadiwa dady basuga abdallah ba bayan ankammala addua sunfito suka tsaya jiran dady yana gaisawa da mutane dady yana fitowa ya gansu duk sunyi wurjan wurjan lafiya Mai kuke jirane dady abdallahban ganeba Baya bandakin minduba ko Ina ba mu Gansa ba
What!!
Da sauri Yakoma gidan babu irin Neman da Bai yiwa abdallah ba Amamn shiru suna tsaka da wanann halin Samiha ta fito Ta gaidasu ta gansu gaba Daya cikin Wani yanayi dady lafiya Mai yake faruwa kowa kasa Bata ansa yayi illa Yaya Dr da ya fashe da kuka abin da yatayar mata da hankali domin ta tsani ganin hawayansa.
Tasancewa a jarumta da karfin Hali na Yaya Dr bakomi bane yake Saka shi kuka tabbas kukan nan da yakeyi ba karamin Abu bane yafaru

Ita ma kukan ta fashe dashi suka kafa yi acikin dakin Dady kansa yaji babu dadi Hakan yasa ya dakatar dasu Banda abin ka Kai da zaka rarrasheta tunkan tasan abin dake faruwa har kasaka ta kuka inshallah za aga abdallah babu Wani Abu da zai faru dashi da shi Zan Nemo sa duk in da ya shiga ku kwantar da hankalinku hayaniyar da suke ce ta fargar da momy Daga baccin da takeyi ta fito Ta Sami bakin labari Nan ta bada shawarar ya tashi ya Kai sanarwa gidan radio Dana television watakil a adace.
Tashi yayi ya futa cikin tashin hankali kana ganinsa kasan Yana cikin matsananciyar damuwa Mai yawa Babu nutuswa a attare da shi ko wanka Bai ba haka yaje ya sanar agidan radio ya biya kudi domin Neman abdallah yawo yayi tayi Yana raba photon abdallah guri guri Yana son yaran saboda yaran suna da matukar shiga Rai ga biyayya duk Wanda suka zauna da shi sai sun shiga ransa sai Kuma kayi farinciki da kasancewar su da Kai Haka ya yini Yana yawo tukun ya dawo gida ko ruwa Bai Saka acikinsaba Ya shigo gida momy ta hada masa ruwa yayi wankaDa kyar ta lallabasa yaci abinci.
Tambayar ta yake Ina su Samiha tana can ita da yayanta Yana ta rarrashi kasan Baya son damuwar Samiha Hajiya bansan halin da Suraj zai shigaba idan akace babu Samiha Sunyi matukar shakuwar da ni Kai na Ina mamkinta Inshallah Alhaji babu Wani Abu da Zai faru.

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

ZEEY NASEER

ABOKIN YAYANA😭

Page 5

Shekaru sun shude an nemi Zainab sama da kasa an rasa har sun hakura sunce taje tayiwa kanta,su Samiha kuwa kullum sake zama cikakkiyar budurwa akeyi domin dukkanin Wani alamu na girma yafara bayyana a tattare da ita,a yanzu tacika shekara goma sha Shida cif-cif aduniya kyawunta ya sake fitowa farinta ya sake fitowa haka kuwa manya manyan idanuwanta masu rikita duk Wani Mai kalla sun sake fitowa,kirjinta ya Kara girma yafara zama na cikakkiyar budurwa haka Kuma shape dinta yafara zama irin na coca cola ta ko Ina ta fara zama cikakkiyar mace girma yafara bayyana ajikin Samiha,idan ka Kalli fuskanta Sau Daya sai ka kara juyowa ka sake kalla domin irin halittar da Allah ya ajjiye acikin fuskar ga dogon hanci ga ma dai daita labbanta duk Wanda ya Kalli Samiha Daga sama har kasa sai yakara juyo ya kalleta.
Ta ko Ina ta hadu ta Kuma ansa sunanta na mace

Adede wanann lokacin tana ss3 suna kokarin fara zana jarabawar fita wanann abin yasa Yaya Dr Dede da kofar gida ya Hana Samiha fita duk in da zataje shi yake Kai ta domin yatsani Wani yaganta ya tabbatar duk Wanda yaganta sai Ya yaba Kuma sai antaya Yana tsoron Wani ya shigo rayuwar su ya tarwatsa musu farincikinsu ko kawayanta Basma da nihal ne suka zo Baya taba bari ta rakasu iyakar ta da su bakin gate.
Chapter 7 · 0% Book details