← Book details Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 33

Sashe 27

Abokin Yayana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakane Samiha tom Allah yasa midace yanzu da kika karbi lambarta mai zakiya da ita?ina so nayi mata maganane akan ta manta da dukkanin wani abu da yafaru tsakanin mu ina son ta dauka aranta babu abinda yafaru a tsakaninku mu.
Ke Samiha wai kina da hankali kuwa mai kike nufi nihal xaki dawo mana da ita cikin rayuwar mu tom gaki ga ita kije kuyi rayuwanku na dau lambarta da momy na fadamiki da niyyar nayi mata magana na kuma nuna mata sakayyar da ta gani amman na fahinci ke wani abin kike tunani ma daban,tom gaki ga nihal narantse ni de bazan iya cigaba da rayuwa dake nihal tana tare dakeba,tunda na fuskanci kaman ba kanki dayaba,dan kin nu na mata tadena guduwa idan ta ganmu ba matsala bane amman mai ne amfanin wai tamanta abinda da yafaru tsakanin mu,Samiha ki sani cewa dukkanin wani makiyinka ba ka kokarin dawowa da shi gareka ni sai anjima idan gidan su ma zaki koma da zama ki koma ga gurinnan.

Basma Basma dan alllah ki tsaya ki saurareni taya kike tunanin rayuwata zata tafi dede ba tare dakeba,kinsani cewa kece duk wani farinciki na bayan yaya Dr bani da wani farinciki face ke dan Allah kada kiyi fushi dani akan wanann kiyi hakuri besty,ko juyowa batayi ta kalleta ba,hakanne yasa Samiha ta hakura ita ma tayi hanyar gida da niyyar zuwa gobe tasan ta huce sai ta tura mata message ta waya ko taje gida.

Ta koma gida tana zuwa ta iske yaya Ahamd da yaya Dr suna zaune a farfajiyan gidan suna ta shira,yanayin yadda ta gaidasu ne ya tabbatar musu tabbas akwai matsala gaba daya idanuwanta sunyi wani iri alamin tayi kuka.
Samiha zo nan inji yaya Dr mai yafaru dake naga kinshigo gidan gaba daya wani iri yanayinka babu komi yaya ki fadimin gaksiya kinsani sarai babu wanda ya kai ni saninki ki fadamin abin dake damunki kafin ranki ya baci.

Wani matsanancin kuka ta kece da shi mai matukar tsuma zuciya gaba daya hankalinsu ya tashi yaya Ahmad ne yayi saurin cewa "Dan Allah Samiha kiyi shiru da wanann kukan dan Allah "a rayuwar yaya Ahamd babu abinda ya tsana irin ganin hawayan Samiha duk da cewa yanzu babu wata kauna a tsakaninsu amman dede da minti daya bai taba jin sonta ya ragu a ransaba nan sukayi ta rarrashinta har sai da ta tsagaita kukan.

Tom yanzu fadamin mai ne yafaru yaya nihal gaba daya wata zabura sukayi suka mike tsaya Samiha nihal Kuma?ban gane nihal ba .
Ta kwashe komi ta basu labari bata rage Koda mitsitsin abuba"Innalillahi wa inna ilahee raji'un shine kawai abin da suke furtawa"sakayya tun mutum na gidan duniya tom wanann abin darasin ga wasu da ke yunkurin cutar da yan uwansu musulmai tashi ki shiga ciki Allah yasa midace.

Har ta mike ta kusa kofa ta juyo tace "Yaya sai Dr ya ansa tace Aah ba kai ba Yaya Ahamd sai ya juyo dan Allah ka kira Basma kabata hakuri"mai yafaru?naga tare Kuka fita tayi fushi ne dan na karbi number din nihal nace zanyi mata magana akan komi ya wuce tadena Jin kunyar mu murmushi yayi saboda shi tunda yake ya jima bai ga yarinya mai hankali da ta wakkali kamar Samiha ba,karki damu inshallah idan na koma gida zamiyi magana.

Nagode sosai yaya ta wuce da dan fara'a a fuskarta domin duk wani abu da zai jawo mata nisa da Basma bata so, tana son Basma tana kaunar Basma dan duk son da takeyiwa yaya Dr bata ki ace su auresa su biyu ba saboda Basma kawace ta kirki wacca samin irinta a yanzu na da matukar wahala.
Tana shiga taga momy bata parlour sai tayi farinciki sosai saboda bata son momy ta fuskanci halin da take ciki,nan tana shiga dakinta tayi wanka ta gabatar da sallan azahar ta xauna tana ta tunanin rayuwa da yadda ada abotar su take su uku,komi tare sukeyi babu wanda ke son damuwar dan uwansa.
Nihal duk abin da dadyn ta ya kawo gida bata taba ci sai ta taho musu da shi makaranta sunci tare rayuwarsu na birge kowa,wani hawaye taji ya zubo mata amman yanzu duk sanadin namiji wanann abotar ta rushe(Mai muka dauki soyayyya minzabi mu rabu da kowa da komi na mu akanta bazan ce soyayyya ba gaskiya bace amman duk wani abu dake cikinta yafi kama da almara,duk wanda ya biya sharrin soyayyya da son zuciyar sa tabbas zai aikata abinda har ya mutu ba xai dena da na saniba,domin wani lokacin ba wai karfin soyayyyar da mikewa wadan da mike tare da su bane yasa mike aikata wani abin,tsantar rura mana wutar son su da shedan keyi shine ke jawo komi, adullokacin d a mika fada tarkon soyayyya yakamata mu nutsu mu Kuma san mai mikeyi saboda gudun aikin da na sani).

Haka tayi ta tunani kuka kuwa yaka sa tsayawa tana jin Ina ma tana da damar dawowa da rayuwansu tamkar da,Ina ma tana da damar da xata sauya komi da yafaru nihal Allah ya sani Ina sonki domin Allah.
Nan ta jawo wayarta ta lalubi lambar nihal ta shiga ta Whatsapp ta fara rubuta mata sako kamar haka.
ASSALAMUALAIKUM NIHAL FATAN KINA NAN LAFIYA,INA MAI NEMAN WATA ALFARMA AGURINKI WADDA NASAN TABBAS NAFI KARFIN TA AGUNKI,NIHAL INA ROKONKI DA ALLAH DA ANNABI KI MANTA DUK WANI ABU DA YAFARU A TSAKANIN MU KISA A RANKI BABU ABINDA YA TABA SHIGA TSAKANIN MU,NIHAL KODA BAKI AIKATA ABINDA KIKA AIKATA BA DOLE SAI WATA TA AIKATA DOMIN ALLAH YA RUGA DA YA RUBUTA HAKAN SAI TA KASANCE ACIKIN RAYUWA TA,KUMA BAN ISA NA KAUCE KADDARAR DA UBANGIJI YA RUBUTAMIN BA,DAN ALLAH NIHAL KI MAIDA KOMI BAKOMI BA,SANANN KI DAUKI KADDARAR DA ALLAH YA SAUKARMIKI HANNU BIBBIYU KI NEMI YAFIYAN UBANGIJI DONIN DAN SHI KIKE RAYUWA BA DOMIN MUTANE BA,DAGA KARSHE INA MAI SANAR DAKE CEWA NA YAFEMIKI DUK WANI ABU DA YAFARU TSAKANIN MU UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI DAYA,SAMIHA......
Bayan ta kammala rubuta wanann sako ta tura ta Kuma fita domin aiki,kamar wasa nihal na zaune a daki tana ta kuka dan tun bayan tafiyar su Samiha ta kasa fitowa kawai tana tunano irin abubuwan da ta aikatane a baya da yadda suke zumuncin su abaya,ita kanta a yanzu kyamatar kanta takeyi ta tabbata abinda tayi bata kyauta ba kwata kwata,kamar ance ta kunna data dinta tana kunnawa taga bakuwar lamba ta tura mata sako,tana budewa ta fara karantawa tunda ta fara karantawa har ta gama tana zubar da hawaye matuka zuciyarta ta sake karaye addu'a kawai take Ina ma ta mutu sai yafi mata sauki da wanann halin da take ciki,tana fara katantawa jikinta yabata Samiha ce sai gashi a karshan rubutun taga ansaka Samiha ,wani matsiyacin kuka ta fashe da shi take ta rai rashi wanda bata san ranar tsayuwar saba,haka tayi ta fama har tayi mai isarta.

Ashe akwai mutanan kirki irin haka haryanzu a rayuwa tabbas Samiha ke kawar kirkice bantaba tunanin zaki yafemin abinda na miki a dan karamin lokacin nan ba,tabbas Samiha nagode sosai da irin abin da kikamin abinda take furtawa kelan a ranta tana Jin Ina ma xata iya rubuta masa sakon kamar haka amman takasa kunya da nauyi gaba daya ya hanata yanzu Kuma bata da burin da ya wuce su hadu da Samiha domin tana son sukara ganawa su kalli junan su a matsayin abokai tana ta wanann tunanin momy ta shigo ta tararta a daki kuka taga tanayi nihal lafiya mai ya sameki? jitayi kamar tabawa momy labarin duk abin da yafaru amman sai ta kasa saboda bata son ta saka tsanar kanta azuciyar mahaifiyar ta kawai sai ta cigaba da kuka nihal kiyi hakuri ki sakawa zuciyarki ruwan sanyi babu wanda yafi karfin kaddara aduniyar nan Kuma babu wanda yafi karfin ubangiji ya jarrabashi a lokacin da yaga dama,duk da wani lokacin akwai sakacin mu amman komade mai ne abinda yaka mace mu idan abu ya samemu shine mu guji gaba domin duk abinda yafaru ya riga da yafaru hakane momy,tom Ina son ki rage wanann koke koken saboda bana jin dadi sa sannan Kuma ba a son mai ciki tafiya shiga cikin damuwa domin matsalane, inshallah momy zan rage.

Bangaran Samiha kuwa tana ta jira xataga nihal tayi mata reply amman shiru bakomi tundade ta karanta aishikkelau.Hankalinta Kuma da tunaninta yakoma kan Basma tafara tunanin ta kirata sai de tasan yar mai shegiyar zuciyace ba sauraranta zatayi ba murmushi kawai tayi tace "Basma baza ta taba iya samin farinciki ba inde babu ni,nima Kuma haka na tabbata xuwa gobe zata huce"tayi murmushi abin ta taci gaba da aikinta......

Ubangiji rabbi marasa lafiya na gida da asibiti Allah kabasu lafiya,iyayan mu da suka rasu Allah kasa sun huta,iyayan mu dake raye Kuma ubangiji Allah ka karawa rayuwar su albarka,ka kuma sake rufamusu asiri🤲🏼🤲🏼.

https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf

CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~

Page 33

Abubuwa sun cigaba soyayyya da shakuwa kullum na kara shiga tsakanin wadannan mutane biyu bada ban kan nayi karya ba da nace yanzu sunfi kaunar junanan su fiye da da,saboda yacca suke kaffa kaffa da dukkanin wani abu da zai shiga tskanainsu. Hakika Yaya Dr na matukar kaunar samiha haka Kuma Samiha.
Washegarin faruwar lamarin Samiha da Basma da safe Basma ta shirya Yaya Dr ya dauketa ya kaita har gidan su Basma,ta bata hakuri da mamaki sai taga Basma na kuka besty mai ne ya sakaki kuka tunanin yadda rayuwan mu ta sauya baki daya a baya bani da wadata kawar da ta wuce nihal karki manta ni ce Sanadiyyar haduwarki da ita,wallahi Samiha ina matukar jin bakincikin halin da nihal ke ciki Ina matuakar tausaya mata sai de zuciyata ta kasa aminta da ta yafe mata.
Kiyi hakuri Basma babu wanda ya isa ya wuce kaddararsa yanzu da Allah ya so akanki ko akaina zai faru muyi hakuri miyi yafiya ga juna rayuwan ma gaba dayanta takaitacciya ce babu wani abu da zai dawwama.

Hakane Samiha na yafewa nihal inshallah komi ya wuce kiyi hakuri kinji babu komi Basma kinsani cewa daman bana taba iya rikeki ko na kwana da fushinki.
Chapter 27 · 0% Book details