← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 33

Sashe 9

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Baba yasa aka kira mashi Rayhana tana zuwa suka fara kuka, Waziri yace suje fada Sarki yanason ganinsu. Bayan Sungama gaisawa Sarki yakara yimasu ta'aziya. Anan waziri yafada ma Sarki sunyi magana da Baba yace ya hkra zasu zauna, sede yafiso yakoma gidan daya kama yazauna aciki.

Qaseem yace Baba dan Allah kayi hkr kazauna tare damu kaga Rayhana zatafi jin dadin zama anan saboda akwai mutane, amma acan daga kai se ita, kuma daka fita zata zauna ita kadai, kaga kadaici zeyi mata yawa. Baba yace shikenan naji zanbarta anan amma nikam nafiso nazauna acan. Waziri yace shikenan Baba munyarda, amma zakayi hkr kadawo kusa damu, kaga can yayi nisa kuma zakayi nisa da 'yarka, akwai wani gida nesa kadan da masarautar nan za'a gyara makashi se asaka maka wadan da zasu rika yimaka hidima seka zauna, kaga koba komai kana kusa damu. Baba yace to nagode sosai, Allah yakara budi.

Kallon Rayhana yayi wadda tayi lamo ajikinshi, cikin larabci yayi mata bayanin komai, shiru tayi tana kuka, kai tashiga girgizawa tace ita bata yarda ba, da kyar yasamu yashawo kanta. Haka yayi masu bayani ta amince, bakaramin dadi Sarki yaji ba, tagefen ido Qaseem yakalleshi shima yayi murmushi ganin farin ciki kwance afuskar Yayanshi.

Haka aka gyarama Baba gidan aka zuba komai, yakoma ciki, Qaseem da kanshi yazabi bayi maza da mata dazasu rika yimashi aiki. Rayhana kuwa ankawo mata kayanta, kuma Gimbiya Suhailat da Qaseem sunce agurinsu zata zauna.

Gimbiya Zakiyya da Gimbiya me daki bakaramun jin haushin abinda akayi sukai ba, baram ma Gimbiyar Babbar Gida, gani take kamar anmaidata saniyar ware,Jakadiya wadda itace take kawo masu duk wani labari daga fada. Kallon Jakadiya Gimbiya tayi tace agskiya jikina bebani zaman wannan balarabiyar agidan nan akwai alkhairi ba. Kawai ni tunkafin inganta wlh naji na tsaneta, tsana ma ta sosai, dan haka dole musan wane irin kulli zamuyi mata tabar gidan nan.

Jakadiya tace Gimbiya da ace Gimbiya suhailat tana daukar zuga kuma tana bani fuskar shiga gurinta danaje mata dawani kaidi wanda na tabbata setayi sanadiyar fitar wannan yarinyar agidan dan sena nuna mata mijinta akwai dalilin dayasa yakawota gidanshi tazauna.

Gimbiya medaki tace kai amma Jakadiya kinkawo shawara me kyau, kuma dole sekin san yanda zakiyi kisamu kishiga jikinta. Gimbiya Zakiyya tace ni nasan me za'ayi, ina Sarkin Fada, ai mutuminta ne, dan haka tagurinshi zamu samu damar aikata abinda mukeso. Jakadiya tace angama ranki yadade. Murmushin farin ciki tayi takoma ta kwanta tana fadin seyanzu nafara jindadin aiki dake, dan kinfara kawo shawara irin tamasu tunani, wato yan gidan sarauta. Kallon Gimbiya medaki Jakadiya tayi, suka hada ido, su duka sunji zafin maganar data fada masu, amma haka nan suka hadiye bacin ransu.

Kwance Gimbiya Suhailat take ajikin Qaseem yana wasa da gashinta, Gimbiya tace Hubbi kasan mene? Yace sekin fada, wlh naji dadin zuwan Rayhana gidan nan, naji dadi sosai daka kawomun ita part dina, inajinta ajikina sosai. Qaseem yace nasan zakisota, shiyasa nakawo maki ita, kinsan nasan duk wani abu daya dace dake. Kinma san menene? Tace a,a inaso kikara kula da ita sosai, dan inaji ajikina Yaya kikema kiwo. Dariya suka saka tace kai Hubbi da gske? Yace sosai ma, kodazu munyi maganar da waziri, shima ashe yagane abinda Yaya yake ciki. Kai amma naji dadi, aikuwa zankoya ma Rayhana yanda zata kwace Yaya daga gurin wadan can matan nashi.

Jinjina ta musamman gareku masoyana. Nagode sosai, sekunjini a next page😘
.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]

Season 45 ⚜50

Sarkin Fada ne zaune afalon Gimbiya Suhailat, Areef yana bisa cinyarshi yanata wasa yanacin biscuit, Murmushi Gimbiya tayi tace Sarkin Fada kaida mutumin naka ne? Washe baki yayi yace barka da fitowa ranki yadade uwargidan Yallabai.

Zama tayi, bayan sungaisa Areef ya mika hannu alamun tadaukeshi, murmushi tayi tace a,a nibazan dauke ka ba, ai nadauka kamanta dani, kara wangale baki yayi kamar yaji abinda tafada. Hannu tamika mashi segashi yataho.

Lafiya de Sarkin fada naganka awannan lokacin? Kanshi yadan sosa ahankali yace lafiya lau, dama wani dan labarine naji awaje shine nace bari inzo inji daga uwar dakina ko haka zancen yake, dan abun yashafeki, nikuma aduniya babu abinda zanji dangane dake ace nabarshi.

Inajinka, E to, to dama de akan wannan bakuwar balarabiyar ne datake zaune agurinki, shine naji mutane suna cewa wai yallabai Qaseem ne yakawota, koshima zebi sahun Memartaba ne yabi Sunnah. Kuma da alama itace ze aura ko? Wani murmushi Gimbiya tayi takara kallon Sarkin Fada, gaba daya babu natsuwa atare dashi, kozama yakasayi.

Kara murmushi tayi tace tonagode, amma nibani da labari, sede kazauna inaji yakusa shigowa semuji daga gareshi, zaro ido yayi yace haba Gimbiya rufamun asiri, ina ni ina zama inyi irin maganar nan da Yallabai, nifa dama ban tabbatar ba, kawai kinsan bazanso arika maganarki ina guri ba, shiyasa nace gara inzo inji da kunnena. Murmushi tayi tace gaskiya kam ka kyauta, to bahaka maganar take ba. To harnaji dadi, aini bazanso ayima uwar dakina abokiyar zama ba. Tonizan koma, ahuta lafiya. Mikama Areef hannu yayi nan yataho suka fita.

Murmushi tayi ta girgiza kai, kallon wata baiwa tayi tace takira mata Safeeya. Bayan tazauna ta fada mata abinda Sarkin Fada yace mata. Shiru Safeeya tayi nadan lokaci, sannan tace nifa Gimbiya dama nafada maki banyarda dashi ba, ina yawan ganinsu tare da Jakadiya, amma kikace kinyarda dashi. Gimbiya tace bakomai Safeeya ki kyaleshi ni haryanzu ina mashi kallon mutumin kirki, kila da gaske yaji maganar, kinsan gidan nan akwaisu da gulma, bare sunga ankawo yarinya mekyau dole surika tsegumi. Safeeya tace amma duk da haka kirika kula sosai Gimbiya, ba'a saurin yarda da mutum, nasan kuma wannan halin kine, amma naga kinyarda dashi. Tace shikenan Allah yashige mana gaba, tace amin.

Haka suka cigaba da rayuwa, su Gimbiya Zakiyya duk yanda sukaso su hada tuggu akori Rayhana sunkasa. Sarki kuwa Son Rayhana yayi girma azuciyarshi, gashi baya ganinta dan bata fitowa sede idan zataje gaida Babanta ita da Safeeya, ganin abun zedameshi ya yanke shawarar fadamasu Qaseem.

Waziri ne da Qaseem Zaune afalon Sarki, su dukansu cike suke da murnar abinda Sarki yafada masu, dama kuma abinda suke jira suji yafada kenan, dan Waziri yace ma Qaseem yabari shida kanshi yayi masu maganar.

Waziri cike da murna yace agskiya naji dadin wannan labari, nima tunda naga yarinyar kawai naji ta kwanta mun arai, duk da bata fito daga gidan sarauta ba, amma inaganin aurenku akwai alkhairi aciki. Amma mekace Qaseem? Murmushi yayi yace aini nakasa magana sbd farin ciki.

Duk da inada ra'ayin kin auren wadda bata fito daga gidan sarauta ba, amma nikam nayima Yaya sha'awar auren Rayhana, sbd mune muke tare da ita nasan halinta mekyau gashi babu ruwanta, tana da addini, Allah ya tabbatar da alkhairi.

Sosai Sarki yaji dadin maganarsu, kallon Waziri yayi seyayi shiru. Waziri yace to ai ba tsayawa zamuyi ba, zanyi magana da Malam domin yayi mana addu'a akan al'amarin, kome yafada semuyi magana da Baba. Qaseem yace wannan yayi dede, Allah yate maka. Waziri yace amma inaso abar maganar anan, harse komai ya tabbata, kasan halin mutane. Sarki yace wannan yayi dede.

Bayan kwana 2, malam yakira Waziri suka yi magana akan istaharan dayayi. Waziri yaji dadin abinda malam yace, sundade suna kara tattaunawa akan masarautar, sannan sukayi sallama. Qaseem yakira yafada mashi komai, sannan suka fadama Sarki. Sosai yaji dadi, waziri yace zasuje suga Baba.

Gimbiya Suhailat da Safeeya sunji dadin maganar, sede Rayhana batasan abinda akeyi ba. Da dare Gimbiya Suhailat takirata, bayan tazo Gimbiya ta sheda mata dalilin kiranta. Sunkuyar da kai tayi tana murmushi bata ce komai ba, Safeeya tace Rayhana kiyi magana mana kin amince? Da gudu ta tashi tana dariya tashige daki. Dariya Gimbiya tayi tace Allah mungode maka, gaskiya naji dadi sosai. Allah yashige mana gaba. Safeeya tace amin, amma ina tausaya mata gata karama babu ruwanta zata shiga cikin matan Sarki.

Gimbiya tace kinsan yanda Yaya yake sonta kuwa? Betaba auren Soyayya ba seyanzu zeyi, kinsan baze bari wani ya wulakanta taba, kuma akusa dashi za'a ajeta, bakiga ana kara gyara part dinshi ba? Nasan de kawai su Gimbiya Zakiyya zasu sha kayan haushi sede suyi hakuri. Nikam yanzu zan kara koyama Rayhana zama dasu, kuma dole ayi mata gyara na musamman, nasan dawuri za'ayi bikinta amma duk da haka daga gobe zata fara amsar gyara.

Bayan su Waziri sunje gurin Baba sukayi mashi bayanin daya kawosu, sosai Baba yaji dadin maganar, nan take ya amince, masu suka bada kudin neman aure dubu dari biyar. Anan aka yanke rana sati 2. Godiya sukayi mashi kuma suka fada mashi basu bukatar komai.

Zaune Jakadiya take afalon Sarki, Bayan sungama gaisawa yakalleta cike da girmamawa, danshi yana matukar girmamata, dan sunyi sabo sosai, komatanshi bayajinsu kamar yanda yake jinta, sun share shekaru tare tun farkon zuwanta gidan, take mashi hidima, shiyasa yabata amana sosai. Kallonta yayi yace dama nakiraki ne dan inbaki sako kifada ma su Gimbiya Zakiyya da Nafeesa maganar aurena nan da sati 2.

Akwai Yarinyar da take zaune gurin Suhailat wadda mukazo da mahaifiyarta nan akayi mata sutura wadda driver na ya kade harta rasu. To itace nakeso na aura. Washe baki tayi tace amma naji dadi sosai, kallonshi tayi tace Rankai dade da alama naga kana son Rayhana sosai, bantaba ganinka cikin wannan farin cikin ba alokacin da zakayi aure ba, se wannan karon. Ko aurenka na farko banga wannan farin cikin atare da kaiba. Murmushi yayi ya sosa kai, dan yanajin Jakadiya kamar mahaifiyarshi dan tagirmeshi, yace wlh Jakadiya ina mata son daban taba yima wata mace ba. Dariya tayi tace Allah ya shige mana gaba, kuma anan danaga ana gyara za'a ajeta ko? Yace haka ne.
Chapter 9 · 0% Book details