← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 33

Sashe 11

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sassanyar muryarta ta doki kunnanshi dafadin Ina kwana. Seda ya hadiyi miyau sannan ya amsa tare da lalubo lips dinta yahade danashi. Sun dade ahaka har yana neman wuce gona da iri yaji karar kofa. Dagata yayi yace kinga kinmantar dani mutane suna jiranmu, gaskiya senayi da gaske kada kirika sani jin kunya afada. Kamata yayi suka fito.

Akofar falon ya tsaya yakara gyara mata mayafinta, yace gskiya dande kada suce namasu rowa dabazaki fita kowa yakallemun ke ba. Ahaka suka shiga falon tana jikinshi, kallo ne yadawo kansu, kowa seda ya yaba da zaben Sarki, anan suka rika yimashi tsiya, itade sede murmushi, ko fuskarta kasa dagawa tayi, ahaka suka gama gaisawa, kyaututtuka da dama suka bata, daga masu kudi se zinari wasu hada kyautar mota. Tasamu zinarai dayawa da kudi, wasu kayan ma an nadesu bansan ko menene ba. Sallama sukayi mata, Sarki yace bari inmaidata daki kada tayi tuntube. Gabada sukasa dariya.

Qaseem da Waziri tare da Sarki dasauran fadawa suka taka masu hargurin motocinsu, kowa yaji dadin haduwar dasukayi haka suka tafi suna cike da farin ciki, dan sundade basuyi irin wannan haduwar ba. Bayan sungaisa dasu Waziri yawuce part dinshi dominsu karya.

Da Jakadiya yahadu tagama gyara mashi daki ankawo abinci tashirya masu, yace sannu da kokari Jakadiya, tace sannu da dawowa, Yace yauwa kije falon baki akwai kayayyakin Fulani kyautace da abokanai na sukayi mata, akwasosu ki kawomun su dakina, hannu yasa a aljihu yaciro kudi masu yawa zasu kai 100k, yabata yace yauwa gashi kibama Safeeya tukuicinta ne ayi mani godiya da irin gyaran datayi ma Fulani dazu. Amsawa tayi ta tashi tawuce.

Wani irin kululun bakin ciki ne, yarufe Jakadiya, ganin irin kudin da Sarki yabama Safeeya, aranta tace wato mutanan nan so sukeyi sucireni daga jikin Sarki, ayanzunne yakamata insamu dukiya daga gareshi ta dalilin Amaryarshi nasan akanta ze iya yima mutum kyautar mamaki, amma dan bukulu suka turo wata tazo tayi aikin da nice nakeyinshi aduk sanda Sarki yayi aure. Tabbas sena tashi tsaye akan Safeeya naga alama nan gaba Sarki ita zemaida yar gaban goshi.

Ninasan mezanyi, anfada maki sona da yakeyi haka nabarshi. Tsaki tayi tawuce falon domin kwaso kayan, mamaki da tsoro ne, suka cikata lokacin datayi arba da irin kayan da tagani afalo. Gaba daya tarikice ganin irin wannan dukiya. Aranta tace badan Sarki yaga kayan nan ba, wlh dasenayi nawa. Wata babbar jaka tajawo tasaka kayan duka aciki tadauka tanufi dakin sarki dasu. Bata samesu afalo ba, da alama abincin ma adakinta suke ci. Tsaki taja tace shikenan kuma za,a maida mana Sarki bita zai zai, yo aduk matanshi akwai wadda yataba shiga dakinta ma? Lallai Gimbiya zankai maki labarin daze tarwatsa zuciyarki, wanda zesa ki karya akidarki ta rashin zuwa gurin boka, ai wlh tunda nabace dole insamu abokan tafiya. Murmushi tayi lokacin data tuna yanda Sarkin fada yafara samun shiga gurin Medaki. Kwafa tayi tajuya tafita.

Wasu zafafan kwalla ne, suke fitowa daga idon Gimbiya Zakiyya, duk irin jiji da kanta, yau gashi agaban Jakadiya tana kuka, damma Jakadiya takori sauran Bayin. Lallashinta Jakadiya tacigaba dayi tana kara kwantar mata da hankali.

Gimbiya hakuri zakiyi, amma dole sekintashi tsaye, wlh bakiga irin makudan kudin da aka bama Fulani ba, dan sunan danaji Sarki yakirata dashi kenan. Babbar damuwata yanda taki barinshi yafito fada, abinci ma adakinta sukaci. Infada maki...... Marin da taji ya sauka akuncinta ne, yasata saurin hadiye sauran gulmar data kwaso. Cike da tsoro takara dukar da kai tana neman gafara.

Ke wace irin dabba ce? Wlh bansan ke dakikiya bace se yau, anfada maki gidan sarauta gidan bayine? Inbanda rashin sanin darajar sarauta taya zakizo kina fadamun irin wadan nan sakarkarun maganganun irin na jahilai irinku. Ina cikin damuwa zakizo kina fadamun abinda bantambayeki ba. Bance kifadamun abinda sukayi ba, kawai na tambayeki ina Me martaba shine zaki wage sakaran bakinki wanda yasaba dashan bakar kuka da daddawa kizo kina fadamun maganarsu.

Daga yau kika kuskura kika kara fadamun abinda banice na tambayeki ba, wlh, kinji narantse maki sekinbar masarautar nan. Kara dukawa Jakadiya tayi, tana bata hakuri, tashi tayi ta tureta tashige daki, tana fadin karna kara ganin kafarki anan sena nemeki. Wasu hawayene suka zuboma Jakadiya, diyar cikinta saboda kudi da mulki yau itace take zaginta da cin mutunci har haka. Tashi tayi tana fadin yo idan har nabarki kikaci ribar zaman gidan sarauta ai ba macece ta haifeni ba.

Qaseem ya kalli Gimbiya Suhailat yace ni kaina yau ina cikin farin ciki bansan abinda yasa ba, Yayana yana cikin farin ciki dole in kasance acikin farin ciki, inama ace Rayhana itace matar Yaya ta farko, nasan har abada baze kara marmarin kara aure ba. Kamar yanda nasamu farin cikin raina banajin zan iya kara aure, shiyasa akace auren soyayya yafi komai dadi.

Murmushi tayi ta kara shigewa jikinshi tace nikaina ina farin ciki da auren yaya, inajin Rayhana kamar kanwata, insha Allahu ajikinta zamu sami babban rabo. Rungumeta yayi yace inafatan haka, inaso inga jinin Yaya agidan nan shine babban farin cikina. Fatana Allah yadoramu akan duk wasu makiyanmu, dannasan munadasu dayawa acikin gidannan, sede Allah ne kawai yasansu. Gimbiya tace babu abinda zasuyi mana domin munrigasu munce Allah. Jawota yayi yace yakamata fa kiyima Areef kanwa dan kinsan ina son mace. Murmushi tayi tace nima haka ina addu,ar Allah yabani mace, yace to tashi muje daki ai ba,a samun mace abaki. Dariya tayi yadagata suka nufi daki.

Afalon Medaki Jakadiya tasamu Sarkin Fada suna zaune yanashan kayan marmari, medaki tana kusa dashi har jikinsu yana gogar na juna, kofar da aka turoce tasasu saurin matasawa, dan Medaki takori duk bayin. Murmushin jin dadi jakadiya tayi ganinsu ahaka, aranta tace kema kinshigo hannu.

Medaki duk kunya takamata, Jakadiya tace rankiyadade ashe mutumin yana nan? Shiru tayi, Jakadiya tace uhm kisaki jikinki kinganni nan nimafa haryanzu ina dan taba duniyancin nan ai mace fitila ce bata aiki dole seda batir. Dariya Sarkin Fada yayi yace da gaskiyarki Jakadiya, ainafada mata nidake da ita munzama aminan juna, akwai amana atsakaninmu, dan haka bakinmu adinke yake muci tare mu tashi tare babu wanda zeji kanmu.

Medaki tace amma gaskiya nagode, tunda nasan yanzu munzama saniyar ware aidole musami abokin fira. Anan Jakadiya tafada masu rashin mutuncin da Gimbiya Zakiyya tayi mata. Sarkin fada yace kirabu da ita, wlh kotana so ko bata so seta aikata babban laifin daze jamata kisa ko dauri acikin gidan nan, ita da anyi magana seta nuna mana sarauta da mulki, zamu gwada mata bakomai sarauta take bama mutum ba. Kibarta mucigaba da binta wata rana zata dawo garemu, kuma kada ki kara zuwa gurinta, da kanta zata nemeki. Ai ba ita takawoki gidanba, karewa ma kinfita matsayi agurin Sarki, kawai agurin shinfida zata gwada maki. Dariya suka sa gaba daya.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, babu ruwan wani da wani, Jakadiya tadena zuwa gurin gimbiya Zakiyya, ko aikenta sarki yayi dataje zata fadama Babbar Baiwarta tajuyowarta. Sunhade kai da Medaki, Sarkin fada tuni yasamu shiga agurinta, wata rana har kwana yakeyi agurinta, kasancewarshi babban mutum me karfi hakan yasa Medaki takejin dadin mu,amala dashi. Baruwanta da daga hankalinta, sede idan ranar girkinta yayi taje tayi kwana 2 tadawo.

Sarki yana kokarin yin adalci atsakaninsu, sede Fulani daban take agurinshi, duk ranar girkinta kowa seyasan ita keda girki dan ko fada baya son zama sosai. Gimbiya Zakiyya kuwa kissar datake mashi ce take dan kara sanyata aranshi. Medaki kuwa hakanan yake zama da ita dan bewani gamsuwa da ita, shiyasa wani lokacin idan kwananta ne ba kullum yake kusantar taba.

Bayan shekara daya, aka saka Areef makaranta dan alokacin yana da shekara 3, har lokacin Fulani bata samu ciki ba, duk da Sarki yafara damuwa amma sbd son dayake mata, ko maganar betaba yimata ba, akullum yana addu,ar idan har haihuwa alkhairi ce agareshi to Allah yabashi me amfani, idan kuma babu alkhairi Allah yasa mashi dangana.

Jakadiya tazo shiga part din Gimbiya suhailata taji suna maganar cikinta har yakai wata 5. Bakaramin tashin hankali tashiga ba, cikin sauri tajuya tanufi gurin Medaki da Sarkin fada. Suma hankalinsu yatashi dajin labarin, anan Sarkin Fada yace yakike ganin za,ayi? Jakadiya tana huci, tace na rantse da Allah baza ahaifi cikin nan agidan nan ba, ai nafada babu wanda zekara haihuwa agidan nan, dan haka gobe zanyi tafiya, kafin indawo ina me tabbatar maku cikin zezube. Dariya sukayi Medaki tace kinyi dede Jakadiya, Allah yabada sa,a. Bari indauko maki tawa gudunmuwar.

Safeeya ce tafito da gudu tana neman dauki, karo sukaci da Waziri zeje fada. Lafiya Safeeya naganki haka? Wlh Gimbiyace bata lafiya se zubar da jini takeyi, naga alamar ma kamar barine tayi, cikin sauri yadaga waya yakira Qaseem, sannan ya aika wani bafade yakira driver.

Likitane, yafito daga wani daki yace su sameshi office. Bayan sunzauna yakalli Sarki da sauran mutanen, sannan yace Rankaidade agaskiya sede kuyi hakuri domin abinda ke cikinta yafita. Sede munyi bincike bamu gano dalilin fitar saba, sede muce daga Allah ne. Qaseem yace likita yajikin nata? Yace dasauki babu wata damuwa anjima kadan za,a sallameta. Sarki yace innalillahi wa inna illaihirraji,un. Waziri yace se hakuri, Allah yamaida mafi alkhairi.

Bayan kwana 2 jikin Gimbiya yayi sauki sosai, sede haryanzu tanajin zafin barin datayi, kallon Safeeya tayi tace wlh ina mamakin abinda nagani acikin baccina, wanda shine yayi sanadiyar yin bari na. Kinsan jiya nace maki nagaji bacci kawai nakeji, harkikacemun inje inyi alwala kafin inkwanta nace maki nide nagaji zanyi addu,a kawai, to wlh ina kwanciya bacci yadaukeni, banyi addu,ar ba, kawai cikin bacci naga wasu irin mugayen halittu marassa kyan gani masu ban tsoro sunbiyoni ina gudu kawai nafadi, suka zagayeni, daya gada cikinsu yataka cikina, shine kikaji wannan karar daniyi kawai senatashi naga jini yana zuba.

Safeeya tace tabbas Gimbiya rashin addu,ar dabakiyi bane yasa wannan al,amari yafaru dake, kinsan addu,a tana da matukar mahimmanci arayuwa, kuma alwala kafin mutum yakwanta bacci tana da matukar tasiri ajikinshi. Kodazu munyi magana da waziri shima seda yayi mamakin al,amarin. Kuma yafadama malam, yace ajirashi nan da kwna 2. Gimbiya tace koma menene Allah yamana tsari dashi.
Chapter 11 · 0% Book details