← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 33

Sashe 23

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Seda yakawoshi kusa da su Waziri sannan ya sake shi, shide kallonsu kawai yakeyi, Jakadiya Safeeya takamo hannun Fulani wadda take boye abayanta, tafito, adede lokacin dasuka hada ido da Sarki Hasheem Fulani taji kanta yayi wani irin sarawa.

Shi kam Sarki Hasheem besan lokacin daya mike tsaye ba bakinshi yana motsi yana nuna Fulani da hannu ba, itakam nan take ta kwala wani irin ihu tafadi kasa, shima jikinshi ne, yafara rawa yazube kasa idanunshi suna fitar da kwallah.

Dasauri suka isa gurinshi, Jakadiya Safeeya kam gurin Fulani ta nufa, sede tana tabata taji babu alamun numfashi atare da ita, Waziri yakama Sarki Hasheem yadora kan cinyarshi jikin sarki se rawa yakeyi yana kara nuna Fulani da yatsa, da karfi yace Fulani.

Jakadiya Safeeya takalli su Waziri tana kuka tace bata numfashi fa. Sarki Qaseem wanda duk yagama rudewa, yama rasa ina zeje, ya kalli Waziri yace yazamuyi ne? Waziri yace kawai muwuce dasu duka asibiti ina ganin zefi sauki.

Sarki Qaseem yace ma Jakadiya taje takira Suhailat tazo sutafi tare, anan Waziri yakira wasu fadawa suka kama Sarki aka kaishi mota, Sarki Qaseem kuwa da kanshi yadauki Fulani ya kaita mota. Waziri yatara manyan fadawa kusan guda 20 yace nabaku umarnin bayan fitarmu kada wani ko wata yakara fita koya shigo masarautar nan, harse mundawo idan nabada umarni.

Jakadiya Safeeya kam tana zuwa part din Gimbiya Suhailat, jikinta yafara rawa, dan batasan dawane ido zata kalleta ba, ganin zata bata masu lokaci yasa kawai tashiga, alokacin Gimbiya tana zaune falo tabuga tagumi. Saurin tashi tayi tana kallon Jakadiya cike da fargaba tace.

Dan Allah kada kicemun narasa Yarima dan Allah, sunkuyar da kai tayi tace baki rasa shiba, sede memartaba ne yace infada maki kifito mutafi asibiti. Ai dasauri taje tadauko hijabinta tafito suka nufi mota, tana zuwa suka shiga wata mota ita da Jakadiya, su kuma suka shiga dayar Wazirri jasu zuwa asibiti.

Azaune, Areef yake bisa gadon beauty ya rike hannunta idanunshi suna fitar da hawaye, kara kallonta yayi yace dan Allah beauty kitashi haka nan, wlh zan iya samun matsala idan har baki farka ba. Haisam ne ya matso kusa dashi yadafa shi, yace kayi hakuri abokina zata samu lafiya, bagashi kana kallo numfashinta yna tafiya dede ba. Addu,a zaka yimata zata tashi.

Suna zuwa aka nufi emergency dasu, sede shi Sarki wani daki aka kaishi tunda dama likitan yasan cesa dinshi, akan Fulani likitoci suka taru suna bata temakon gaggawa.

Gimbiya Suhailat da tambayoyi suka cika cikinta, gashi tana son ta tambayi Jakadiya Safeeya amma kunya ta hanata, ganin haka yasa Jakadiya tace Gimbiya muje kiga jikin Yariman mana, kamar jira takeyi ta tashi cike da kunya tace muje de infara ganin jikin surikar tawa ko?.

Bakaramin dadi Jakadiya taji ba, dajin furucin Gimbiya, tace to muje, Gimbiya tace dan Allah kiyi hakuri da abinda namaki, wlh idona ne yarufe, har na furta maki wadan nan maganganun, amma kiyafe mun, kuma Hubby yayi mun bayanin komai nagane.

Tabbas soyayya baruwanta dawani mulki ko sarauta, kudi ko talauci, wlh nayarda da zabin Yarima dari bisa dari, ada kam nayi kuskuren cewa dole dan sarauta seya auri jinin sarauta, segashi tun ba aje ko inaba Allah ya nunamun ishara, kuma nayarda da abinda nagani.

Murmushi Jakadiya tayi tace haba ai babu komai, nice yakamata innemi yafiyarki, dan na rufe maki abubuwa da yawa wanda ba laifina bane, amma muje kiga jikin nasu, daga baya zakiji komai.

Hannun beauty dake cikin na Areef ne yafara motsi, saurin kallonta yayi yana fadin Haisam wlh beauty motsi takeyi, kara matsawa kusa da ita sukayi, Ayman tace aiko Yaya ga idonta nan yana juyawa, Areef yace beauty bude idonki nine akusa dake, babu wanda ze rabamu, dan Allah kitashi Abba ma yana dubaki kuma shima ya amince. Kallon Ayman yayi hawaye suna zuba a idonshi yace dan Allah kuce ta tashi.

Adede lokacin da su Gimbiya suka turo dakin babu wanda ya kula dasu dan hankalinsu yana gurin beauty, tsaye Gimbiya tayi tana kallonsu, gaba daya tausayinsu yakamata, gani takeyi duk itace tasasu awannan halin, matsawa Jakadiya tayi kusa dasu.

Adede lokacin beauty tabude idonta, bata sauke su akan kowa ba se akan Gimbiya Suhailat, ai kawai gani saukai ta tashi cikin tsorata ta kwala kara daga karshe tace Mama............ gaba daya dakin seda suka firgita dajin abinda beauty tayi, saurin shigewa jikin Areef tayi jikinta yana rawa, kara rungumeta yayi yana shafa bayanta.

Se alokacin ya juya yaga Momynshi ce ashe beauty tagani, saurin daure fuska yayi yace Momy dan Allah kifita, kina ganin yanda beauty ta tsorata daga ganinki, tunda beauty take bata taba magana ba, amma ayau ta dalilin tsoranki datakeyi gashi magana tafito abakinta.

Dan Allah kifita tunkafin takara ganinki tarasa ranta, wlh nima mutuwa zanyi. Cike da tashin hankali Gimbiya tajuya tayi hanyar waje tana kuka, Jakadiya tayi saurin kamota tana fadin kada kifita kidawo zanyi mata magana, kai kuma Yarima ka nutsu kasan dawa kake magana.

Jawota tayi suka matso kusa da gadon beauty wadda take kwance ajikin Areef, ahnkl Jakadiya ta dafa kafadarta tace tashi kiji wani abu Yar Baba kinsan de bazan cutar dake ba ko? To idan har kinyarda da hakan inaso kitashi kuma kada kiji tsoron komai, Gimbiya tazo dan tadubaki kuma tafada maku tayarda zakuyi aure keda Yarima.

Ai dajin haka beauty ta tashi sede bata rabu da jikin Areef ba, shikam murmushi kawai yakeyi, yana kallon Momynshi. Kusa da beauty Gimbiya ta matso takama hannunta, tace diyata kiyi hakuri kinji wasa nakeyi maku, babu wanda ze rabaku, nima inasonki, jawota tayi ai kamar jira takeyi tashige jikin Gimbiya, ai gabavdaya dakin aka sa dariya.

Da wani irin ihu Fulani ta farka tana fadin wayyo nashiga 3 zasu kasheni, haka tayi ta ihu, ganin taki natsuwa likitocin suka leka suka kirawo su waziri, addu,a Waziri yayi ta tofa mata shida Sarki Qaseem, cikin lokaci kankani ta nutsu, sede gaba daya afirgice take.

Wani likita yace da alama tunaninta yadawo, sede agskiya atsorace take, kila mutanen dasukayi mata sanadiyar shigarta wannan halin sun tsoratata sosai, dan haka shawarar dazan baku idan har akwai malami, to ku kaita yayi mata addu,a insha Allahu zata dawo dede.

Waziri yace mun gode sosai, amma kana ganin za,a iya sallamarta ayau? Likita yace kwarai ma kuwa, ai babu sauran wani abu dayake damunta, dan ta dade tana shan magani, duk da ba mune muka bata ba, amma mungane ana bata magunguna masu kyau. Sarki yace mungode bari muduba jikin Yaya.

Shima Sarki Hasheem jikinshi yayi sauki, dan soyake abarshi yaje yadubo Fulaninshi, amma likitan yahana, turo kofar dakin sukayi tare da sallama, aibyana ganinsu Sarki yace ina Fulani ya jikinta? Gaba daya seda sukayi mamakin maganar data fito daga bakin Sarki, dan yau shekaru 18 da watanni beyi magana ba. Da sauri Srki Qaseem yaje gurinshi yana murmushi ya rungumeshi yana fadin Yaya wlh itama ta warke ayau ma zamu koma gida.

Cike da fara,a Sarki Hasheem yace da gaske? Waziri yace sosai ma, runtse ido yayi wasu hawaye suka zubo mashi yace Allah nagode maka daka dawomun da Fulanita, ya Allah katona asirin duk wanda yayi ma Fulani hakan ni kuma nayi alkawarin wlh bazan barshi ba.

Likita yayi gayran murya yace Alhmdull, dama nace maku yawancin irin wannan matsalar idan har mutum yahadu da ita ta dalilin rasa wani abunda yakeso, to aduk lokacin daya ga wannan abun alokacin da beyi tsammanin ganinshi ba, to inhar Allah yaso ze iya samun sauki.

To hakane yafaru da memartaba, jikinshi yasamu lfiya, nan da wani lokaci zefara tafiya kamar kowa, amma kada yayi garaje, gurin fara tafiya, yanzu haka zamu bashi sanda wadda zata temaka mashi gurin tafiya. Kuma zaku iya tafiya ayau, sede dole seyasha magungunan dazamu bashi, suna zasu temaka mashi jikinshi yayai kwari.

Sarki Qaseem yace yanzu kam tunda farin cikinshi tadawo ai ba magani ba, komai zesha. Dariya suka sa gaba daya, Sarki Hasheem yace yanzu de ku kaini inga Matata ko kuma intafi da rarrafe, dariya sukayi likita yace a,a ga kujera nan kuturashi yaga farin cikinshi.

Kwance take idanunta akulle, amma ba bacci takeyi ba, tanaso tayi tunanin,sede data fara setaji kanta yana sarawa, da sallama suka shigo, lokaci guda ta bude idonta, bata sauke su ako ina ba, se akan mijinta, jan jiki tayi ta tashi zaune, fuskarta dauke da murmushi, turashi sukayi har kusa da gadonta, sannan Waziri yakamo hannun Sarki Qaseem sukayi waje.

Hannunshi yasa yakamo nata, fuskarshi dauke da murmushi, saukowa tayi daga bisa gadon ta durkusa kusa dashi ta shige jikinshi tana kuka, kara rungumeta yayi yana shafa bayanta.

Dakin beauty suka nufa, azaune suka samesu se fira sukeyi, suna dariya, beauty kuwa tana jiin Gimbiya, se dariya takeyi, sede haryanzu tun maganar datayi tafarko bata kara cewa komai ba, Areef ma kasa matsawa yayi yana manne da ita, wani irin farin cike ne yaratsa zuciyar Sarki Qaseem ganin yanda yasamesu.

Sarki yace waini ina Areef marar lafiya ne, munje dakinshi mabu ganshi ba? Dariya suka saka, Areef yace Abba ai nawarke, Gimbiya tace ba dole ya warke ba, tunda yasamu abinda yakeso, dariya sukayi. Waziri yace ai seku tashi mufara shirin tafiya gida tunda kun warke dare yayi sosai. Sarki yace gaskiya kam, yaude asibitin tazama ta masoya.

Haka likita yabasu sallama tare da magungunan Sarki Hasheem dana Fulani, suka kama hanya zuwa gida, sede haryanzu Sarki Hasheem bega beauty ba, dan seda suka fara shiga mota sannan suma suka fito. Lokacin dasuka isa gida kuma dare yayi sosai, hakan yasa Gimbiya taja Ayman da beauty tace ma Jakadiya kema kitaho mukwana anan kisan de Yaya baze baki Matarshi ku kwana tare ba. Dariya tayi tace hakane, muje kawai. Kallon su Areef tayi tace Haisam kaima kafada ma su hajiya anan zaka kwana gurin budurwarka kada suji shiru.
Chapter 23 · 0% Book details