← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 33

Sashe 2

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tundaga nesa yahango fadawan sarki suna zuwa, murmushi yayi, cikin hausarshi wadda bata gogeba, yace aikin kenan, kullum azo adameni da kira, kuma haryanzu ankasa samo mani Diyata, da abinda ke cikinta. Kwallar data zubo mashi ce yasa hannu yagoge. Da sallama suka karaso gurinshi, ahankali ya amsa masu. Daya daga cikin fadawan yace Barka da hutawa Baba, yace yauwa sannunku, yauma wani kiran neko?

Murmushi Bafaden yayi yace a,a Baba, dama Sarki ne, yace muzo mukawo maka kayan abinci. Murmushi yayi yace to madalla, nagode, yajikin me martaba? Bafaden yace to Baba dasauki zamuce, kasan sauki sede agurin Allah, fatanmu de Allah yanuna mana inda Gimbiya take ko zamu samu Hankalin kowa ya kwanta. Baba yace addu,a kam kullum munayinta, sede haryanzu acikin raina nakasa yarda cewa Rayhana itace tabar gidan Sarki da kanta, kuma nakasa yarda cewa bata raye, inaji ajikina wata rana zamu gana da ita, fatana de Allah yasa kome tahaifa ace yana raye. Sukace amin Baba, bara mushigar maka da abincin ciki, yace tonagode, dama gashi bayin dasuke dafamun abincin sungama aikinsu suntafi, kushigarmun dashi ciki.

Jakadiya ce take tafaman Sallama abangaren Gimbiyar Babban Gida, daga ciki akace shigo mana Jakadiya, tace Gafaranku de, ai nadauka ko bacci kikeyi, Allah yatemakeki Babbar Gimbiyar Sarki, Allah yakaramaki lafiya da tsawon kwana, Allah yabaki muma musamu awajenki, ke kadaice Babbar mata agurin Sarki, duk wanda yazo sede yabiyo bayanki. Daga gefe Gimbiya me Daki tarika wurga mata harara jin irin kirarin datakeyi ma Kishiyarta.

Murmushi Gimbiyar Babban Gida tayi tamata nuni data zauna, guri tasamu tazauna sannan takalli Gimbiya medaki tace Ina gaisuwa ranki yadade. Murmushi tayi tace sannu Jakadiya, daga ganin bakinki akwai magana, meke tafe dake?

Babban labari ne yake tafe dani kuwa Gimbiya. Dazu nazo wucewa tagefen Dakin memartaba Sarki Qaseem, senaji yana magana kamar yana fada, dajin haka nayi saurin daukar tsintsiya nayi kamar ina shara, sede na boye fuskata, gudun kada aganni tunda ansan ba,a bangarensu nake aiki ba, asalima nice mebada umarnin ayi aikin........ nan takwashe duk abinda taji sunfada ta fada masu.

Tashi zaune Gimbiyar Babban Gida tayi, tace gaskiya naji dadin wannan labari naki Jakadiya, dan haka kina da kyauta me tsoka. Washe baki Jakadiya tayi tace godiya nake Gimbiya, Allah yakara girma. Amma Me daki wace irin shawara kike ganin yakamata mubi don mu samu muyi amfani da wannan dama?.

Gyara zama tayi tace, inaganin tunda har Sarki ya furta Bayason Yarima ya kawo mashi bare, meze hana kisamo daya daga cikin matan gidan sarautarku kimaidota gidan nan. Murmushi Gimbiya tayi tace Medaki kenan, kina tunanin Gimbiya Shuwa zata bari Yarima yaso wata data fito daga bangare na? Kinfi kowa sanin bama ga maciji da ita, dan haka wannan shawara taki bata karbu ba. Jakadiya kawo mana mafita.

Kara hade rai Medaki tayi jin ba,a karbi shawararta ba, sede yata iya, tunda bata da karfi agidan, dole tabi asannu kodan tasamu fada. Jakadiya tace Gimbiya inaganin tabayan gida yakamata mubiyo masu, tunda bazasu taba karbar abinda yafito daga gurinki ba,kamar yanda mukayi da farko yanzuma hakan yakamata ayi. Kayataccen murmushi Gimbiya tayi tace haka nake sonki Jakadiya. Allah yakaimu.

Yarima Areef ne kwance adakinshi, shida abokinshi Haisam, suna fira, Haisam yace Yarima yanaga kamar wani abu yana damunka? Yamutsa fuska Areef yayi yace kawai kabari Man, wlh jiya Abba da Momy suka kusa samun hawan jini. Dariya Haisam yayi yace uhmm nasan wasa kakeyi, yanda Abba Da Momy suke sonka, harzasu iya bata maka rai, kaifa agurinsu haryanzu yaro ne, dan haryanzu baka girma da hawa cinya ba. Areef yace banason sharri, idan wasu sukaji kace hawan cinya ai sesu dauka rungumeni akeyi.

Dariya suka saka, Areef yace wlh Man ba maganar wasa ba, aide kasan irin burina akan matar danakeso na aura ko? Yace E, yauwa to jiya daga nafada masu kalar matar danakeso shikenan, suka rufeni da fada, kasan ai ra,ayin momy da Abba duk daya ne, kuma nasan wannan magana dasuka fada harcikin ransu. Haisam yace kada kadamu, kaida ko matar ma baka samuba, meye naka na damuwa?.

Areef yace kaide ai dole nadamu, kasan me kwarmin ido dawuri yake fara kuka. Haisam yace abinda nakeso dakai, addu,a zaka cigaba dayi domin itace mafita, nikaina bana maka sha,awar auren macen gidan sarauta, kasan mata da sarauta, basu iyata ba, nafison kaje waje ka auri wata daban, hakan zebaka kwanciyar hankali sosai. Areef yace nima ai jinsu nakeyi, dan bansamu wadda nakeso bane, shiyasa nayi shiru, amma duk lokacin dana samu, agskiya sede kowa yayi hkr, dan bazan iya biyayya anan gurinba. Haisam yace muje mugaida Baban Umma fulani kwana 2 bamuje ba, tashi Areef yayi yana fadin wlh nima yana raina, dan bakaramin tausayi yake bani ba, ace mutum yazo gari da iyalinshi amma yanzu beda kowa, matar ta mutu diyar kuma babu wanda yasan halin datake. Muje mudawo, dan dazu waziri yake fadamun gobe zamuje darazo wai Abba ze aikemu. Haisam yace kai gsky zanje, nima inason zuwa Darazo, fita sukayi suna dariya.

Washe gari tunda safe suka dauki hanyar bauchi, daga can suka wuce darazo, tare suke da Jakadiyar Gimbiya Shuwa, dan itama garinsune shiyasa tabiyosu tanason tayi kwana 2. gidan wani babban malami sukaje, kuma dama shine malamin dayake masu addu,a akan batan matar Sarki Fulani. Bayan sungama gaisawa, suka fadi sakon Sarki, malam yace haryanzu muna nan muna addu,a sede kuma babu abinda ya nuna mana bata raye, akullum muna ganin tana raye, kuma akusa damu, danni abinda nake gani tafi kusa dani akan inda kuke, to Allah shine masanin gaibu, shikadai yafimu sanin gsky. Zamu cigaba da addu,a har Allah yasa mudace.

Ruwan addu,a yabada akaima Tsohon Sarki, godiya sukayi mashi, Waziri yasa fadawa suka shigo da kayan dasukazo dasu. Waziri yace to muzamu koma. Malam yace tonagode, kallon Jakadiya yayi yace ammade Jakadiya ke anan za,a barki kidan mana kwana 2 ko? Tace E Malam, dama cewa nayi inzo inganku. Yace to ai yayi dede kishiga daga ciki. Tashi tayi tace to Yarima Allah ya kiyaye. Yace amin sekin dawo.

Bayan suntafi wani tsoho yazo yace yanason ganin malam, malam yace ashigo dashi, bayan sungaisa Malam yace Baba meke tafe da kai? Tsohon yace wlh wata magana ce take tafe dani, nadade inaso inzo insameka amatsayinka na babban malami agarin nan, duk da ba,a cikin gari nake ba, amma inada labarinka, nine megadin MAKABARTAR datake wajen gari. Akwai wani abun mamaki dayake damuna, wanda yadade yana faruwa, sama da shekara 18, akan wata mata da diyarta. Malam yace Baba inajinka bani labarin abinda kasani.

Kubiyoni zakuji yanda komai yake. Nagode da kaunarku.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]

Season 10⚜15
Malam yace inajinka Baba, dama Allah gafarta malam, tsawon shekaru 18 dasuka wuce nakasance ina gadi a MAKABARTAR bayan, gari, akwai ranar danayi rashin lafiya har kimanin tsawon sati guda banje gurin gadi ba, arana ta 8 danaje, inadan zagaya MAKABARATAR. Can daga nesa da ita naga wata rumfar kara, wadda daga gani kasan bata dade dayi ba, kuma gsky malam rumfar bawata rumfar arziki bace, dan ansha yin ruwan sama tana yacewa, sede abun mamaki da gari yawaye zan iske anmayar da ita.

Ganin wannan rumfa danayi bakaramin tsoro naji ba, dan tunda nake gadi rumfata ce kadai agurin, matsawa nayi abin mamaki malam senaji kukan jariri aciki. Bayan nayi addu,a sena karasa gurin. Inazuwa daga ciki nahango wata babbar mata me alamun tabin hankali tana rike da yarinya ahannunta.

Da sallama nashiga gurin, saurin dagowa matar tayi tana kallo na, guri nasamu nazauna, nace baiwar Allah mekikeyi acikin MAKABARTA kuma hada yarinya jaririya? Kawai senaga tanamun dariya, malam abinda na lura wannan yarinyar diyarta ce, dan agabana naga tafiddo nono tana bata.

Ganin wannan mata bazatayi mani magana ba, kawai sena fita , cikin rumfata naje nadauko abincin danaje dashi nakoma nakai mata. Inazuwa na iske yarinyar hartayi bacci, matar namika ma abinci, segashi ta amsa tana dariya, zama nayi harta gama namika mata ruwa tasha, kallonta nayi nace baiwar Allah kozaki bini gidana inkaiki keda jaririyarki? Saurin kallona tayi tana girgiza kai, nace ba cutarki zanyi ba, amma akwai hadari azamanki gurin nan.

Kuka naga tafara tana kara rike diyarta, haka nayita lallashinta hartayi shiru, ganin idan nakara mata magana zatayi kuka yasa nafita nabarta. Ganin har magriba tayi duhu yakarayi se tausayinsu yakamani, komawa nayi nasameta rike da diyarta, sun kwanta. Maganar dazu nakara yimata. Amma abun mamaki seta samun kuka, kamar daga sama naji wata murya tafara magana.

Yakai wannan bawan Allah me tausayi, kasani kamar yanda kayi niyar temakon wannan mata da diyarta, muma haka muke temakonta, kuma kaci sa,a dakazo da niyar temako, dan munyi alkawarin duk wanda zezo da niyar cutar dasu bazamu kyaleshi ba. Wannan mata haka Allah ya kaddaro mata rayuwarta agurin nan, kuma tunda ba,a sonta mu muna sonta, dan haka babu wanda zamu bari yadauketa agurin nan. Kabarta, Allah yana tare da ita, kuma muma muna tare da ita, amma tunda kaima mazaunin gurin nan ne, zaka iya temaka mata. Bakasan komai game da ita ba, mune muka sani, dan haka munaso kabarta kamar yanda ka ganta, shiyasa aduk lokacin daza,a kawo wata gawa babu wanda yake cin sa,ar ganinta.

Malam tunda naji wannan magana na tabbatar ma kaina lallai ba Bil,adama bane suke magana aljanune, hakan yasa na kyale matar nan, dan sunce basu san na matsa mata da tambaya, haka muka cigaba dazama a MAKABARTA tare dasu, yanda suka umarceni kada infadama kowa, haka nayi shiru ko medakina ban fadamawa ba, sede yan kayan diyana mata harma dana medakina idan naga sun tsufa nakan dauka ince mata wasu zan kaimawa.
Chapter 2 · 0% Book details