← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 33

Sashe 30

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Areef yayi yace shikenan, nina zanrika kuran Ayman da Angel. Apple din dayake kusa da Haisam yadauka ya jefeshi dashi, dasauri ya cabeshi yana dariya, Haisam yace wlh baka isa ba. Areef yace tokaima kadena fada mata beauty. Haisam yace nayarda, dannaga alama nizakafi kwara.

Dariya suka saka Areef yace dade yafi maka, amma ni inkirata. Beauty kaima haka, ai bazeyuba. Haisam yace towai kai yamaganar fitarku waje bayan aure? Areef yace wlh har yanzu banyi maganar dasu Abba ba, amma yau zanje insamesu. Idan har sukaki zan hadasu da Malam. Haisam yace insha Allah ma zasu amince, duk da nima bazanso kamun nisa ba, amma saboda cigaban Amatu kawai zan hakura, nima inaso inga tadawo kamar kowa.

Gimbiya Suhailat tana kwance ajikin Sarki Qaseem suna fira, tace Hubby, dama wata shawara ce, nace bara infada maka kafinsu Yaya su dawo se afada masu aji mezasu ce. Kara yawota yayi yace fada inajinki. Anan tafada mashi abinda takeso.

Murmushi yayi yace wlh kamar kinshiga zuciyata, na dade ina wannan tunanin, kawai ciwon Yaya ne, yahanani fada amma tabbas idan suka dawo zansamu Waziri da Yaya da maganar. Wannan abu ne me kyau. Kema Allah yabiyaki da kika kawo wannan shawarar.

Sallamar Areef ce ta katsesu, abakin kofa ya tsaya, dan dama al'adarshi ce duk inda yaje baya shiga se anbashi izini kida gidansu ne. Murmushi Sarki yayi yace Allah yayi maka albarka Yarima, hakika ina farin ciki da irin halayenka da kuma tarbiyarka, ace mutum yaje kasar waje yayi karatu amma duk da haka tarbiyarshi bata lalace ba, asalima karuwa tayi. Babu abinda zanma Alkah se godiya, domin nasani shine ya tsare bawansa.

Bayan sun gyara zamansu ya amsa Sallamar yace shigo Yarima, shigowa yayi yazauna kusa da Abbanshi tare da dora kanshi saman kafarshi yace sannunku da hutawa Abba. Shafa kanshi Gimbiya tayi tace yauwa sannu Yarima. Sarki yace zanga ranar dazaka girma Areef, ace haryanzu kana hawa cinya.

Dariya yayi yace ai babu rana Abba, yace akwai mana, nan da wata daya kam ai zaka zama megida. Kafin kaima kasamu naka dan, kaga saka barmashi ko. Gimbiya tace ai anan zasu zauna ko? Abba yace emana, ai bama son muyi nisa da juna, zamansu cikin masarautar nan zefi.

Tashi Areef yayi yana sosa kai yace Abba dama wata alfarma nazo nema, yace fadi duk wata alfarmarka, ni kuma zanyi maka. Anan yafada masu abinda yakeso. Shiru sukayi, yace dan Allah Abba.

Sarki yace bawai naki bane, ina duba yanda Yaya zeji, kasan yanada bukatar ganin Amatu akusa dashi, amma se ace ana daura aure zaku tafi. Areef yace wlh Abba koni dole ce zata sani yin nisa daku, kuma ina me tabbatar maku shekara 3 zamuyi, niba burina beautytayi zurfin karatu ba, kawai inaso tasamu karatu me kyau, dan koda tayi karatun ni bazan barta taje wata University ba, kawai tasamu karatu kodan sbd rayuwarta data yaranta.

Gimbiya tace gaskiya kayi magana me kyau, kuma nima nagoy bayanka son dazamu nuna mata kenan mubarta tasamu ilimi me kyau, kuma tunda saudiya zakuje, nasan zata samu ilimi me kyau, kaga daga kai har ita kunje kusa da gida, kafin kudawo zaku zagaya dangi.

Sarki yace shikenan, idan Yaya yadawo zamuyi maganar dashi. Areef yarungume Abbanshi yayi yana dariya. Gimbiya tace ammafa zaku rika zuwa bawai zama zakuyi harseta gama ba. Sarki yace dama ai baza,ayi haka ba.

Haka suka cigaba da shirye shirye, Amare suna shan gyara, dan masu gyara na musamman daga meduguri aka dauko, Fulani daki guda aka ware mata ita da ne gyaranta, tunda tashiga bata fito ba, akoda yaushe suna cikin gyara, sallah kadai da cin abinci suke tadasu.

Bakaramin kyau takarayi ba, tadawo tamakar wata yarinya, komai nata yadawo kamar da. Beauty kuwa masu gyaran har mamakin kyanta sukeyi, gashi dama tunda aka fara gyaransu su Areef suka dena ganinsu, duk ya gama shuga damuwa.

Ayaune, masarautar BUBAYERO tacika da mutane, anata gyara da shirin tarbar Sarki Hasheem. Kowa kagani cikin masarautar cikin farin ciki yake. Fulani tasha kwalliya kamar meshirin zuwa zaben sarauniyar kyau, tayi kyau harta gaji, haka suka kaita dakinta dayasha gyara har yafi ranar da aka kaita kyau.

Motoci harma da mashina ne, suka je dauko Sarki. Ana bude kofar jirgi mutane suka fara fitowa, sarki Qaseem yazuba id kawai yaga ta yanda yayanshi zefito. Waziri yafara hangowa, daga bayanshi ya hango Yayanshi cikin shiga ta alfarma yayi matukar kyau, kamar bashi bane yayi ciwo abaya ba.

Da kafafuwanshi 2 yarika saukowa daga jirgi, ai Sarki Qaseem kasa hakura yayi ya karaso, cike da murna ya isa gurinshi uka rungume juna. Kowa na gurin seda suka burgeshi. Haka suka nufi gida cike da farin ciki.

Suna zuwa Sarki Qasee yajashi zuwa part dinshi, yace Yaya kashiga kashirya kada kafito seda dare, Fulani tana daki tana jiranka, nasan kagaji dayawa. Murmshi yayi yace shikenan nagode, sena fito. Har falo yakaishi sannan yafito fuskarshi dauke da annashuwa.

Tura kofar dakin Fulani yayi, lumshe ido yayi dan wani da daddan kamshine ya bugar mashi hanci. Da sallama yashiga, ai cak ya tsaya ganin Fulaninshi, da gudu tarugo ta rungumeshi, hannuwanshi 2 yasa ya rungumeta, wani irin farin ciki sukeji dukansu.

Sun dade ahaka kafi tajashi zuwa cikin dakin, riketa yayi yana kallonta, yace anya ba masanye akamun da Fulanita dana sani ba? Murmushi tayi tace kila, jawota yayi, yace gaskiya nagodema Allah dayasa bantafi dake ba, gashinan an maidomun da mata kamar yar shekara 18. Murmushi tayi tacire jikinta daga nashi tana fadin sannu da hanya, muje kayi wanka kaci abinci.

Murmushi yayi yace nikam bazan iya cin abinci ba, tunda naganki, dariya tayi tace a,a muje de. Haka tajashi zuwa bandaki. Bayan yafito ya shirya takawo mashi abinci, da kanta tarika bashi yana jingine jikinta, kamar karamin yaro, yahanata sakat. Da haka tagama bashi abinci, yaje yayi brush yadawo yana fadin taho kimun tausa, bacci zanyi.

Murmushi tayi tanufo gurinshi, yace amma kicire wannan kayan zasu damenim tace amma naga bacci zakayi, ina ruwan kayana da kai, kanne mata ido yayi yace e sonake musami AMINULLAH. Dariya tayi yajawota shima yana dariya.

Koda Sarki Qaseem sukaje fada da dare, Sarki Hasheem befito ba, ganin haka Waziri yace abari se gobe, azauna, akwai gajiya atare dashi, Sarki yace a,a amarci kawai yakesha. Waziri yace kaima ai sekaje kasha naka. Murmushi Sarki yayi yace kaima nan da wani lokaci kaza fara shan naka. Dariya Waziri yayi yace seda safe, Sarki yace to Allah yakaimu.

Areef ze zaune afalon Jakadiya kamar zeyi kuka ya kalleta yace haba Aunty dan Allah sokukeyi inshiga wani hali, kinfi kowa sanin damuwar danake ciki, shikenan ace kullum so daya zanga beauty gaskiya bazan iya ba.

Ina gyaran nan danni akeyishi? To nide abarmun ita haka banaso. Dariya Jakadiya tayi tace yi hakuri bara inturo maka ita karkamun kuka, fita tayi sega beauty tafito. Tsayawa yayi yana kallonta, tana zuwa tazauna kusa dashi tana murmushi, yakamo hannunta yace haba beauty nan shikenan sekirika guduna.

Kema bakison ganina ko? Girgiza mashi kai tayi, yace yauwa kokefa beauty na, hannunta yasaki, yace jeki dauko mani abinci yunwa nakeji, tashi tayi tadauko mashi, akasa tadameshi, nan tazauna tazuba mashi. Atare suka fara cin abinci, yana bata tana bashi, har suka gama sannan suka zauna yana mata fira.

Washe gari se bayan azahar sannan aka taru afada, atare Sarki Hasheem da Fulani suka fito, daka gansu kasan suna cikin farin ciki. Bayan angama gaisawa, aka bude taro da addu'a.

Sarki Qaseem yace Alhamdulillahi, munama Allah godiya daya kawomu wannan rana Yaya yasamu lafiya, komai na masarautar nan yazama dede, ina rokon Allah daya kara tsaremu damu da yaranmu baki daya. Dan haka inaganin zanmika ma Yaya kujerarshi, dama amatsayin rikon kwarya na amsa.

Sarki Hasheem yayi murmushi yace, a,a ai kuma nida mulki har abada, wanda nayi abaya ya isa, kaine zaka cigaba da mulkarmu, kafin Yarima yakawo karfi se abashi, amma wannan maganar ma kabarta.

Waziri yace wannan magana haka take, munriga da munyanke zaka cigaba da zama Sarkin Gombe, har Allah yakaimu lokacin dazaka sauka. Allah yatayaka riko.

Waziri yace magana ta 2 akan maganar bikinsu Yarima ne, munsami labarin mahaifin Haisam zezo gobe da jama'arshi neman auren Ayman, dan haka nan da sati 2 za'ayi bikinsu in Allah yakaimu.

Kallon Baffan beauty yayi yace akwai wata magana da Yarima yazo mana da ita, jiya Sarki Qaseem yake fadamun. Anan yafada masu alfarmar da Yarima yake nema. Shiru Baffan beauty yayi bece komai ba. Can yadago kai yace ai hakanma yana da kyau, Se ayi magana acan kasar asama mashi aikinyi kafin itama tagama karatun nata. Allah yasa aje asa'a akuma samu abinda akeso.

Sarki Qaseem yace kuma akwai dayar maganar, aure danakeso inyi, dama akan Waziri ne da Jakadiya Safeeya, ina ganin insha Allah nan da sati 2 tare danasu Yarima za,a daura. Dago kai Waziri yayi yasaki baki yana kallon Sarki Qaseem. Baffan beauty yayi murmushi yace lallai kamar kashiga zuciyata.

Dan Allah Waziri kada kace komai, kawai kayi fatan alkhairi, kasan baza zaba maka abinda zakayi dana sani ba. Sunkuyar da kai Waziri yayi yana murmushi. Sarki Qaseem yace ai ya amince, Allah yakaimu musha biki.

Shirye shirye ya kankama agidan su Yarima, iyayen Haisam sunzo anyi magana, kuma har can misra an fada masu, kuma sunce zasuzo. Baba Fulani ma yakira yan uwanshi yafada masu, wasu daga cikinsu sunce zasuzo. Duk wani shirin tafiyarsu Areef angamashi, anyi masu visa, da takardar shedar zama akasar, kuma an sama ma Areef aiki acan har gudan dazasu zauna ansamu. Dayake abun namasu sarauta ne. Babu wani bidi'a dazasuyi abikin, hakan yasa aka kira me wa'azi yazo yayi masu.

Ayau ne dubban jama,a suka halarci daurin auren mutane, 3 nagidan sarautar BUBAYERO. Daurin aure ne daya tara mutane dayawa, daga garuruwa daban daban, harma daga kashashe. Bayan daurin aure akayi babbar walima, anci ansha, kowa seda ya yaba da irin auren wannan Masarauta. Gashide auren yaransu, abin sonsu akeyi amma kuma babu wata bidi'a da akayi. Mutane dayawa abin ya burgesu.
Chapter 30 · 0% Book details