← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 33

Sashe 3

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun ina tsoron zama dasu har muka saba sosai, kuma ina kokarin bata abinci, sede duk sanda naje inasamu kamar taci abinci, dayake akwai rafi agaba damu, haka nasamu bokiti ina kawo masu ruwa ina aje mata, dan naga ita kezuwa tana dibar ruwan dakanta, kuma acikin wata karamar robace. Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya, har wannan yarinya tayi wayo, da kaina naje nace tadena bata nono, nadauki yarinyar nafara bata abinci, daga nan tafara cin abinci.

Aduk lokacin dana tafi daniyar fadama wani wlh malam dana dawo zan iske bata gurin, setayi kwana 2 ko 3 bata dawo ba, haka suka kara jamun kunne akan inyi hankali, tunda har aka haifi yarinyar nan agurin to nanne gurin zamansu, duk ranar dana kara kokarin fadama wani duk abinda yafaru dani ni najama kaina. Haka na hakura mukaci gaba dazama, amma harcikin raina na kudurta sena temaka masu, dan abinda suke masu ba temako bane, duk da agurinsu suna ganin kamar temakonsu sukeyi, amma abinda nagani taya za,ayi dan adam yazauna a MAKABARTA kuma ace anan ze rayu.

Ganin idan nacigaba da matsa masu zan iya rasasu kuma bansan inda zasu kaisu ba, yasa naja bakina nayi shiru, dannasan wata rana zantemakesu. Haka muka cigaba da rayuwa, munyi sabo dau sosai, diyarta tayi girma sosai, ganin yarinyar tayi girman daza,ace tafara sanin addinita yasa nace bari infara koyamata daga cikin abinda nasani, duk da nima bawani ilimi mezurfi gareni ba, amma Alhamdulillahi inada dede gwargwado. Dayake tunbayan daya kamata ace yaro yafara magana yayi, amma shiru ita yarinyar wadda Innarta tarada mata Baby, amma nikuma ina kiranta da yar Baba sbd munshaku da ita sosai, tun lokacin dana gane bata iya magana, sena lura da idan Innarta tayi mata magana tanaji, kuma nima haka, tun alokacin nagane yarinyar tanada matsalar rashin magana, wanda bansan dalilin hakan ba, dan duk kurman dana sani inde ba harshenshi ne yadatse ba, zaka sameshi bayaji, kuma baya magana, amma ita nata seyazo dasabani.

Haka muka rika maganar kurame da ita amma idan itace zatamun magana, amma idan nine zanyi mata lafiya lau zanyi tunda tanaji. Dun daga wannan lokacin muka fara karatu tundaha sarki harzuwa sallah da karatun da akeyi, sede nine kawai nake koya mata, idan bata gane ba, tanamun alamu.

Mahaifiyarta wani lokaci se inga tazauna tana ta kuka wanda idan tafara batayin shiru seta dauki lokaci, konaje zan bata hkr yar Baba zatamun alamu da in kyaleta, alokacin da girma yazo ma Yar Baba haka nazaunar da ita nakoya mata yanda zata gyara jikinta, da abinda zata bari na ibada, da kuma yanda zata tsarkake jikinta idan lokaci yazo. Wlh malam hankalin yarinyar da natsuwarta kadai ya isa yasa tashiga ranka.

Hatta da kitso wannan matar ita take yimata, sede ita matar bata bari agyarata, shiyasa idan kaganta zakaga gaba daya tafita hankalinta. Ko ciwo yasamesu nine nake samo masu magani, amma wadannan aljanu basu barin ko matar tabar cikin MAKABARTAR, iyakarta bakin rafi, shima tunda nake dauko masu ruwa tadena fita.

Akwanakin baya nayi rashin lafiya wadda ta tadamun hankali, banyi tsammanin zan tashi ba, kullum tunanina yazanyi da wadannan bayin Allah. Inacikin ciwon nasamu na tafi MAKABARTA gurinsu, haka naje nasamu Yar Baba duk tarame, kuka kawai takeyi, tana ganina ta taso da gudu tazo tana murna, alokacin nagane dalilin kukanta, harta da ita Matar marar hankali seda tayi ta murna. To malam bayan nawarke kuma nafara tunanin yanda zanyi, shine nasamu labarinka, nikuma nayi alkawarin zanzo gurinka, duk da ayanzu bansan wane mataki aljanun zasu dauka akaina ba, kuma zamuje musamesu, ko kuwa sun daukesu. Wannan shine babbar damuwar dana taho ina tunani.

Salati malam yafarayi, da tasbihi jin wannan al,amari. Gyaran murya yayi yace tabbas Baba kazo da magana me ban al,ajabi, kuma kaima kayi kokari sosai, wanda bakowane ze iya abinda kayi ba, lallai duniya babu gsky, tsoron Allah yayi karanci aduniyarmu da zukatan mutane, yanzu dan Allah ina wanda yakeda alhakin haukatar da wannan mata zesa dumbin zunuban daya dauka nata ita da yarta har na tsawon shekaru 18?.

Innalillahi Wainnailaihirraji'un. Yanzu Baba abinda nakeso da kai, ka kwantar da hankalinka, insha Allahu babu abinda ze sameka, kuma zamuje musamesu a inda kabarsu, addu,a zata temakemu akan wadan nan aljanu, kuma zanyi magana dasu, dan suma basuda niyar cutar dasu, asalima suna temakonsu ne. Bara inkira sauran dalibaina su shirya muje musamesu, amma ai bazamu bar bayin Allah acikin daji ba, kuma a MAKABARTA. Kodan lafiyar ita yarinyar.

Tashi yayi yakira yaranshi yafada masu su shirya zasuje wani guri, koda yadawo, yasamu Baba yana jiranshi, haka suka dauki mota yasa aka kira Jakadiya da matarshi suka shiga, dan sutemaka masu gurin daukosu. Baba addu,a kawai yakeyi Allah yasa su samesu, agurin.

Nima nace amin Baba.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]

Season 15⚜20

Hankali tashe Baba yafito daga motar yanufi inda rumfarsu take, amma abun mamaki babu ita babu dalilinta, idan ba wanda yasan da ita ba, babu wanda zece mutane sun taba zama agurin. Wasu irin zafafan hawayene suka fara zarya afuskarshi yan fadin Innalillahi wainna ilaihirraji,un. Zama yayi adede inda rumfar take yana kuka.

Malam ne, yakaraso gurin yadafashi yace Baba ba kuka yakamata kayi ba. Insha Allahu nizan dawo dasu duk inda sukaje, dama munsaba da aljanu, masu taurin kaima ina gogawa dasu, har kafiran cikinsu muna fama dasu, bare kuma wadannan da alama musulmai ne. Baba yace wlh malam, da,a ace sun dauke su Yar Baba bansan inda suke ba, gara ace banfada maka ba, muyita zama dasu anan har mutuwa tazo tasamemu. Tsautsayi ne, da kuma tausayi yasani karya dokar dasuka saka mun.

Shiru malam yayi, can ya kalli daya daga cikin yaranshi yace daukomun shinfida acikin mota kataho mun da gorar ruwa, bayan yakawo mashi ya amsa yafara alwala, shikuma ya shinfida mashi abin sallah. Kallonshi yayi yace kacemasu Jakadiya sukoma mota suzauna harsenace sufito.

Sallah yafara yi, kowa yana kallonshi, seda yayi raka,a 4 sannan yazauna yafara karatu, da yayi seya tsaya yayi adduo,i sannan yacigaba. Seda yadauki tsawon minti talatin, sannan wata kura ta taso kafin wani lokaci sega rumfar su Yar Baba ta bayyana agurin datake. Hamdala malam da Baba sukayi, dasauri Yar Baba ta iso kusa dashi tana dariya. Daya daga cikin yaran malam, wani yace Tsarki ya tabbata ga mahaliccin dayake tsara halittun bayinshi. Anya wannan yarinya mutum ce? Aini tunda nake bantaba ganin yarinya me kyanta ba, damma wai tana cikin rashin galihu, wannan da,a birni take gidan masu kudi ai se anrika boyeta.

Dariya nakusa dashi yayi yace kaima kenan dakake iya magana. Baba se shafa kan Yar Baba yakeyi yana murmushi, ita ko tashige jikinshi don da alama tsoron mutanen gurin take, dan atsawon rayuwarta bata taba ganin kowa aduniya ba, daga Mamanta se Baba. Mamanta kuwa kasa fitowa daga runfar tayi, se kuka takeyi.

Malam yace Alhamdulillahi, Allah mungode maka, kallon gefenshi yayi yace bayin Allah, meyasa bakuso atemaki wadannan mutanen? Kowa yafara kallon inda malam yake magana, sede babu alamun kowa agurin, maganar mutum daya tafara tashi me cike da alamun ladabi.

Allah yagafarta malam, mundauki tsawon shekaru 18 muna tare da wadannan bayin Allah, mune muka temaki wannan mata, alokacin da takusa halaka, wanda babu wani dan adam daze iya temakonta, semu, kuma ga dukkanin alamu munga kamar hadari ne, ya jefota gurin datake, sede koda muka bincika bamuga alamun mota tayi hadari ba, asalima mugunta akaso ayima wannan mata. Shiyasa muka temaketa, sede haryanzu Allah bebamu ikon gano dalilin daya kawota nan ba, kuma babu wani asiri ajikinta, wannan lalurar datake tare da ita da alama kode ajikinta take, ko kuma buguwar datayi ne yakawo mata ita. Malam yace naji, amma me kuka sani game da ita? Tsawon shekaru 18 dasuka wuce wata rana da dare muna zaune afadarmu.

Se kawai mukaji fadowar wani abu akusa damu, sede abun mamaki, muna dubawa semukaga mace ce da tsohon ciki, kuma cikin ikon Allah babu abinda yasamu cikin, anan muka kara dubawa semukaga tabbas bil adamace, anan nasa yarana dasu dubamun ko hadari ne akayi, dayake akasan wani rami muke, hakan yasa nayi zaton ko hadari ne, dan wani lokacin idan akayi hadari mutane suna fadowa nan. Bayan yadawo yace mun babu wata mota datayi hadari, kafin mu ankara semukaji wannan mata tana nishi da karfi, nan take nagane haihuwa zatayi, anan nasa akayima me dakina magana.

Allah gafarta malam, ita dasauran wasu jinsinmu suka temaka mata harta haihu, sede koda ta haihu bata cikin hayyacinta, haka suka gyarata ita da diyarta, aka samo kaya aka samata, anan nace su kwantar da ita kusa da mahaifiyrta. Dayake safiya takusa, haka muka tashi mukabarta agurin ita da yarinyarta, anufina idan gari yakara haske kila wasu suganta sutemaketa.

Bayan dare yakarayi muka sake dawowa fadarmu, abun mamaki kuma bamuga wannan mata ba, senayi tunanin wasu sun daukesu, muna nan zaune sega daya daga cikin yarana yazo yacemun ahanyarshi tazuwa nan yaga anyi wata runfa agefen wata MAKABARTA sede yar karama ce akayi, daya kara matsawa seyaga wata jaririyace kwance acikin rumfar, saman hakukuwa anshinfida mata zani tana bacci, daga waje kuma wata mata ce kwance agaban rumfar, dan tayi masu kadan bazasu iya shiga su 2 ba, asalima rumfar yara ce, abinda yabashi tsoro yaga wata halitta daga cikin jinsinmu sede basa cikin zuri,armu wato musulmai, yaganta tana kokarin daukar yarinyar.

Shine yaje gurin dasauri, to dayake sunsan kowaye kuma suna tsorona, yana ganinshi yayi saurin bacewa. Shine yazo yana fadimun, koda nasa adauko munsu senaga wannan matar ce tajiya, nan take tausayinta yakamani, anan nayi alkawarin kareta ita da yarta kuma babban dalilin dayasa nabarsu aMAKABARTA, sbd bazeyiwu nakaisu cikin jinsina ba, haka kuma nagane bil adama basuda tausayi harsuka iya barin wannan mata ita da yarta acikin daji babu metemakonsu, shiyasa nasa yarana suka yimata rumfa babba wadda zata isheta ita da yarta, kuma nasaka yarana suzama masu gadinsu.
Chapter 3 · 0% Book details