← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 33

Sashe 13

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya falon yayi shiru jin irin kazaman kalaman da Gimbiya Zakiyya take fadi akan talakawa, kallonsu tayi taga gaba daya fuskarsu tacanza, se alokacin ta tuna baram baramar datayi, cikin sauri tace shiyasa nake godema Allah daya hadani da mutanen kirki irinku, daban kuke agurina, kunfi kowa matsayi azuciyata acikin gidan nan.

Murmushin yake Jakadiya da Sarkin Fada sukayi, can Sarkin Fada yace bakomai Gimbiya muma muna tare dake, kuma dasannu zamu nuna maki muma muna cikin masoyanki, kinsan bawa akwaishi da amana. Murmushi tayi tace yayi kyau.

Shima murmushin mugunta yayi ya kalli Jakadiya da Medaki yakanne masu ido. Medaki tace yanzu yazakayi kasanfa dole aikin yakasance ranar da Sarki baya dakinta. Gimbiya tace kabari seyadawo gurina dan nasan Medaki bawani sanin yanda zata dauke mashi hankali tayi ba, kasan jinin sarauta ako ina daban yake, dan haka kabari nan da jibi. Yace angama ranki yadade.

Fita sukayi shida Jakadiya, acikin Lambun gidan suka sami guri suka zauna, Jakadiya wadda acike take da bacin rai ta kalli Sarkin Fada cike da bacin rai, tace yanzu haka zamu cigaba da zama tare da Wannan matar, diyar cikinmu tana mana cin kashi akullum? Wlh dole mugwada mata talaka ma, yanada yanci, kuma zata gane bakomai bane jinin sarauta suka sani, mune acikin gidan nan, dan haka zamu gwada mata munfita sanin gidan nan.

Dariya Sarkin fada yayi yace dadina dake saurin hawa, kalli nan, aljihunshi yayi mata nuni dashi, sede banga komenene aciki ba, lekawa tayi, tace meye amfanin hakan? Dariya yayi yace kisa ido kawai malama, zakiga yanda akeyin duniyanci, kinganni nan bana yarda da jinin sarauta, duk yanda ka kai dayi masu hidima wata rana dole sumaka butulci.

Shiyasa acikin aikina bana barin sahu, ko kuma baya da kura, dan haka kizuba ido kigani wata rana dole Gimbiya tanemi juya mana baya, alokacin zan nuna mata asalin kalata. Dariya Jakadiya tayi tace amma naji dadi, ai nadauka duk zagin datayi mana zetashi abanza? Yace tama isa, haba Sarkin Fada fa nake, kinsan yanda akayi nasamu wannan matsayin kuwa, nikaina ina tsoron kaina, bari infada maki abinda babu wanda yasani agidan nan seni kadai, sekuma marigayi ya matata, itama dalilin sanin abinda na aikata yasa nakara mata iska, wanda haryanzu babu wanda yasan da mutuwarta, kowa yadauka yanda nace guduwa tayi sbd bata haihuwa nikuma nace zanyi aure shine tagudu.

Har yanzu maganar ahaka take, alokacin Sarki dakanshi yarika bani hakuri, Waziri da Qaseem kuwa cewa sukayi kada insake inje bikonta, dama ba'a garin nan take ba, nace masu ai tama tafi garinsu.

Murmushin jindadi Jakadiya tayi tace inajinka bani labari insha, kara gyara zama yayi yace alakocin da za'a nada sarautar Sarkin Fada, mu 3 aka tsaida, sede yanda mutane suka zabi sauran biyun suka barni hakan yayi mani ciwo, shiyasa nashiga damuwa saboda nasa rai akan sarautar, bayan an kara kuri'a aka tsaida mutum daya acikin su biyun.

Hmmm kinsan menayi? Tace seka fada, cikin dare nashiga dakin Mati wanda shine za'a nada washe gari, dama kuma tare suke kwana da abokin takararshi, inazuwa na saka wuka nakashe Mati, Kallah yana baccinshi besan abinda yake faruwa ba, haka na debi jinin Mati duk nashafa ma Kallah ajiki harda fuska, kuma nadauki wukar nasaka mashi ahannu, haka najuya nafita.

Inazuwa gida nayi saurin dibar ruwa domin nima jikina duk yabaci da jini, hanyar bandaki na nufa kawai senaji maganar matata ta faramun salati, tana fadin inakaje da wannan daren, dama muna kwance naga sanda kadauki wuka ka boye awondonka kafita, kuma gashi yanzu kadawo jikinka duk jini. Anya megida ba wani abun kaje ka aikataba?.

Aje bokitin nayi najata zuwa daki, anan itama na shaketa, nan take ta mutu, haka na hada duka kayanta na kullesu adan kwali, naje cikin bayan lambun nan na haka rami sannan naje nadaukota ita da kayanta narufesu aciki, namaida kasa sosai, yanda babu wanda zesan anrufe wani abu nazuba, dama kuma gurin ba'a shigarshi sosai ai kingani.

Washe gari da safe naji ana kururuwa, ina fita naga mutane sunzagaye Kallah yanata kuka jikinshi duk jini ga wuka ahannunshi, yana fadin wallahi banine na kashe shiba. Haka aka jashi zuwa fada, bayan anyi bincike aka gane sahun hannunshi ajikin wukar, nan take shima aka yanke mashi hukuncin kisa. Sede babban abin ban haushi wannan shegen Wazirin wanda yakeda dogon hangen nesa, da zurfin tunani, shine yaja Sarki daki, bansan mesuka ceba, Sarki yazo yace hukuncin kisan daurin rai da rai agidan yari za,ayi mashi, bahaka naso ba, amma sanin kowa yaji hukuncin nasan baze taba fita ba hakan yasa hankalina ya kwanta.

Bayan kwana 2 kawai naji ance niza,a bama sarautar. Dadi sosai naji, sede ban gwada afuskata ba, Sarki yake cemun meyake damuna haka, anan nafada masu karyar kwanana 4 banga medakina ba, dama mundade muna rigima, shine kawai natashi naga takwashe kayanta tacemun garinsu zata tafi. Nace masu nayi neman harnagaji banganta ba. Anan kowa yatausayamun sukayita lallashina, dahaka washe gari akamun sarauta. Kuma daga ranar babu wanda yakara tamabayar medakina, asalima Waziri cewa yayi kawai inkara aure, nikuma nace tunda bana haihuwa bazanyi aure ba, shiyasa suka kyaleni.

Tokinji babban sirrina, kuma nafada makine, saboda nasan bazakici amanata ba. Wani irin murmushi Jakadiya tayi nikaina bangane kona menene ba, tace haba aini taka ce, cikinmu daya. Sarkin Fada yace kisamomin maganin saka mutum bacci, amma na fesawa, tace angama.

Fulani ce zaune afalo ita da Babanta sunata fira, tundazu yazo sundade suna fira, yakasa tashi yatafi, itama bataso yatafi, kallonta yayi yace Rayhana inaso bayan kin haihu idan abinda kika samu yayi kwari, zamuje gida domin mugansu, kuma suga abinda kika haifa, kinga zasuji dadi. Tace nima Baba inason zuwa gida, insha Allahu dana haihu kamar da wata 7 semutafi ko? Yace hakan yayi, amma kibari sekin haihu sekima mijin naki maganar.

Hannu yasa a ajjihunshi yaciro wani zobe mekyau, yamika mata, sakashi tayi ahannunta, ta kalli Babanta tace wannan fa? Kwallan idonshi yagoge sannan yace zoben mariganyi yane, nima jiya ina duba kayanta, kinsan tunda tarasu bandaga kayanta ba, to acikin wata jakarta naganshi shine nace bari inkawo maki kisaka ahannunki. Itama kwallan ta goge tace nagode Baba, yace bakomai bari intafi yamma tayi, tace Baba kabari se anjima mana, yace a,a ai na dade, gara intafi sena kara dawowa. Har bakin kofa tarakashi idanunta sunkasa dena zubar hawaye, shikanshi kwallace tacika mashi ido. Sun jima abakin kofa yana lallashinta kafin yatafi.

Gimbiya Suhailat ce da Safeeya sukazo duba Fulani takawo mata farfesun yan ciki, zaune suke tanaci sunata fira, Gimbiya tace kinde kusa haihuwa kihuta, nasan insha Allah nan da kwana 7 zaki cika wata 9 dede, nasan kozaki kara kwanaki bazaki kara dayawa ba. Fulani tace nima nagaji nakosa in haihu, sede bansan abinda yasa ba, yan kwanakin nan se intaji yawan faduwar gaba.

Safeeya tace kada kidamu kirika fadin Innalillahi Wainnailai Hirraji'un, insha Allah zaki samu sauki, kuma koma wani abune zesameki zezo maki dasauki. Tace shikenan nagode, Gimbiya suhailat tace bari mutafi nasan yanzu Yaya zeshigo, Fulani tace ai banan yakeba. E duk dahaka aidole yazo yaganki kafin ya kwanta. Fulani tace Allah banaso kutafi, to kibar Aunty Safeeya ta kwana anan tunda nikadai zan kwana. Dariya Gimbiya tayi tace a,a kibari kawai mutafi.

Kamar zatayi kuka tace dan Allah Aunty. Safeeya tace to bari inje idan yatafi seki kirani sena taho, murmushi tayi tace yauwa nagode, haka suka yimata sallama suka tafi.

Suna fita tashiga daki ta kwanta, ba dadewa Sarki yashigo dakin, kusa da ita yaje yakwanta ta bayanta yarungumota yana me tusa kanshi cikin wuyanta, murmushi tayi tace sannu da shigowa, yace yauwa, inacen sunrikeni afada, nikuma duk nakosa inzo kada kiyi bacci bamuyi sallama ba, tace kaima kasan bazan iya bacci bankarbi sakon seda safe daga gareka ba.

Kara rungumeta yayi, yace aide jibi kamar yanzu muna tare, tace sosai ma, kallonta yayi yace kinyi kyau sosai Ummin AMATULLAH. Dariya tayi takara shigewa jikinshi tace wato harma kasan mace zan haifa, kuma kasa mata suna? Yace sosai ma, tace ai nadauka sunan Ummanku zakasa? Yace naso insaka sunanta, sede yanda na dade ban haihu ba, kuma Allah yabani yanzu shiyasa naga yadace insaka wannan sunan kinsan idan akace Amatullah ana nufin amintattar Allah, idan kuma namiji ne, tozansa AMINULLAH. Shima fassarar duk daya ce.

Murmushi tayi tace kayi gaskiya, idan Allah yakara bamu wasu se asaka, yace hakane, zatayi magana yahade bakinsu guri guda, sundauki lokaci me tsawo ahaka, ganin yafara fita hayyacinshi yasata saurin sakinshi ta matsa. Runtse ido yayi yana maida numfashi.

Ahankali cikin mutuwar jiki tace nasan Gimbiya Yaya tana jiranka adakinka, yakamata katafi, bude idonshi yayi sede idon yayi ja sosai, maidawa yayi yarufe, sega kwalla sirara suna saukowa, dasuri tamatsa kusa dashi tace meyafaru? Saurin rungumeta yayi yana fadin dan Allah kada kibarni kinji, wlh kece farin cikina, duk ranar da babuke akusa dani rayuwata bata da amfani.

Saurin rufe mashi baki tayi tana fadain wai meyafaru kake wannan maganar? Murmushi yayi yace bakomai, kawaide ina fada maki ne, tun safe yau nakejin faduwar gaba, addu,ar danakeyi ce tasa nakejin sauki.

Tace babu abinda zefaru se alkairi, katashi katafi kada tayi fushi, yace wlh da ace Medaki ce, nasan zata iya saidamun kwananta, amma Zakiyya ko duniya zan bata bazata yarda ba. Tace a,a nima banaso nafison kwanana yazo da kanshi.

Murmushi yayi yace bazaki gane yanda nakeji bane shiyasa, tashi yayi yace muje kirakani to, tace to kuma idan katafi waze sani bacci? Yace kai namanta, jawota yayi yakwantar da ita akusa dashi, tausa yafara yimata ahankali yanayi yana mata fira medadi, tun tana bashi amsa haryaji shiru.

Zama yayi yana kallonta yadauki kusan minti 30 yana kallonta, daga karshe ya sumbaci goshinta, wuyanta da bakinta sannan yatashi yafita jikinshi asanyaye.

Washe gari tunda asuba, Sarki yatashi dawani irin firgici, sakamakon mafarkin dayayi, Gimbiya Zakiyya tace lafiya naga kana zufa? Tashi yayi bece mata komai ba,yanufi part din Fulani. Turus ya tsaya ganin bata cikin dakin, kuma dakin duk ahargitse, karar ruwan dayaji ne, abandaki yasa yaji hankalinshi yadan kwanta, juyawa yayi yaje yayi wanka ya nufi masallaci.
Chapter 13 · 0% Book details