← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 33

Sashe 14

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare dasu Qaseem da waziri suka taho, Waziri yace lafiya rankaidade naga tundazu kamar kana da damuwa? Kallonshi yayi, yace wlh wani mummunan mafarki nayi kuma da Fulani nayi mafarkin, shine nashiga dakinta da asuba sede naga dakin ahargitse, kuma Fulani bata yima daki haka, sede karar ruwan danaji abandaki yasa hankalina ya kwanta, amma kuma haryanzu gabana yana faduwa.

Waziri yace to kayi mata magana abandakin kaji ta amsa? Yace a,a Qaseem yace Yaya mudeje ka kara dubawa ko? Waziri yace haka yakamata.
Part din suka wuce, sede afalo suka tsaya shi kuma yawuce dakin. Karar dasukaji ce tasasu saurin shiga dakin, Sarki suka gani kwance kasa da alama faduwa yayi, hawaye suna zuba a idonshi, dasauri Qaseem yamatsa kusa dashi yana fadin yaya lafiya?

Da hannunshi yayi masu nuni dawani guri, jini suka gani agurin, ga kofar bandaki abude ruwa na zuba a famfo, babu alamun mutum aciki. Da kyar Sarki yake fadin babu ita wlh bata nan, Waziri yafita waje dasauri, haka yarika bin masu gadin gidan sede babu wanda yace yaga wani abu yafaru cikin dare, abu kamar wasa har rana tafito babu Fulani.

Gaba daya gidan antaru ankira hukuma ansanar da ita sede haryanzu babu wanda yakira yace ansamu wani labari akanta. Sarki kuwa tun faduwar dayayi haryanzu akwance yake tun maganar dayayi da farko bekara cewa komai ba. Gimbiya Suhailat da Safeeya se kuka sukeyi, Baban Rayhana kuwa zaune kawai yake, idonshi harsun kumbura sbd kuka, yakasa cewa komai.

Abu kamar wasa har dare yayi babu Fulani, yan sanda harsungaji da nema, hankalin kowa atashe yake, banda munafukai, sede Jakadaiya tana zaune kusa da Sarki, idonta itama ya kumbura dan kuka, mutane se hakuri suke bata. Waziri yakira malam yayi mashi bayanin halin da,akeciki, shima ya jajanta masu. Yace sujirashi zuwa washe gari.

Washe gari tunda asuba. Malam yakira waziri yace mashi agaskiya Fulani tana cikin mawuyacin hali, sede besan inda take ba, amma kuma tana raye, za,a cigaba da addu,a. Anan yafada mashi halin da Sarki yake ciki, anan malam yace bakomai nan da kwana 2 zezo se asan abinda za,ayi.

Jikin sarki babu sauki, ko abinci bayaci se dakyar suke matsa mashi yaci kadan, Ranar da Malam yazo ne, suka shiga suka tattauna da mayan fada, kuma suka yanke hukuncin nada Qaseem amatsayin Sarkin masarautar Bubayero. Lokacin da Qaseem yaji kin amincewa yayi.

Da kyar suka shawo kanshi, washe gari aka nadashi Sarki. Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba, se fada take tana fadin wannan ai shine kai kai koma kan mashekiya, wato munyi abu kuma yadawo kaina, kai bazeyuwu ba yanzu shikenan natashi daga matar Sarki? Wlh dasake. Jakadiya tace haba Gimbiya najifa ance rikon kwarya ne aka bashi, da sarki yasamu lfy zemaida mashi mulkinshi.

Haka sukayita bata baki, da kyar ta hakura, abu daya ne yasata kara yarda mulki zedawo hannunsu dataji ance Qaseem yace baze dawo gidan Sarki ba.

Bayan anyi nadi malam yakoma Darazo, haka akacigaba da nema ma Sarki magani da adduo'i, ankaishi asibitoci dayawa amma jikinshi babu sauki, matsalar shanyewar barin jiki ne tasameshi, hakan yasa aka fara yimashi gashin kashi, sede babu yanda basuyi ba akan afitar dashi waje, amma sarki yaki yarda koda suka fadama malam, seyace su kyaleshi, babban abinda zesa yadawo dede to ganin Fulani ne, hakan yasa suka kyaleshi aka cigaba da yimashi maganin gida.

Medaki kuwa cin duniyarsu sukeyi da tsinke, ita da Sarkin fada. Duk wani munafunci yadawo daga Jakadiya se Sarkin Fada. Gimbiya suhailat da Safeeya haryanzu sunajin kadaicin rashin Fulani, Babanta kuwa tundaga ranar yadena zuwa ko ina kullum yana kofar gida, sede masu aiki suzo suyi mashi aiki sutafi.

Wannan shine asalin labarin Masarautar Bubayero. Zamucigaba da cigaban labarin anext page. Nagode

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]

Season 65 ⚜70

Tafiya sukeyi amota, Jakadiya Safeeya, kallon Wannan mahaukaciyar kawai takeyi, tana kara tuno maganganun da malam yafada mata ana gobe zasu taho, waigawa tayi takara kallon Yar Baba wadda tayi lamo ajikin Baba tana ta bacci.

Aranta tace tabbas suna kama sosai ma, sede kawai wahalar duniya zatasa baza,a iya gane kamar suba. Dole nayi yanda malam yace idan har muna son musami abinda muke so. Tunawa tayi da abinda malam yafada mata akan Waziri, aranta tace tabbas da ace kowane Sarki zesamu mutum me amana kamar Waziri dayaji dadi, addu,a tayi akan Allah yate makesu akan mutanen masarautarsu.

Alokacin dasuka isa Masarautar Bubayero Jakadiya Safeeya tayima Waziri waya akan sun iso, alokacin gurin karfe 12 , Waziri yace togani nan zuwa. Yana zuwa yabada umarnin abude masu gate, direct gurin part din Sarki Qaseem suka nufa, dayake ranar asabara ce, kuma azahar batayi ba, babu kowa awaje se bayin dasuke kai da kawowa.

Suna fitowa Jakadiya Safeeya takama matar, shi kuma Baba yakama Yar Baba Waziri yayi masu jagora zuwa bangaren Jakadiya Safeeya, dayake, dakuna ne, guda 2 se falo da kitchen, kuma kowane daki akwai bandaki aciki, idan kaga yanda Gimbiya Suhailat tasa aka gyara ma Jakadiya Safeeya part dinta zaka dauka nawata mekudice, babu abinda ba,a zuba ba na kyale kyale afalon, dakunan ma haka, gidan yayi kyau sosai. Duk da abangaren Gimbiya takecin abinci amma a kitchen dinta ma akwai kayan girki da kayan abinci.

Bayan sun shiga Waziri yakalli Baba yace sannunku da hanya, Baba yace yauwa munsameku lafiya? Yace lafiya lau, Waziri yace Alhamdulillahi Baba gashi kazo masarautar mu, kuma insha Allahu zakaji dadin zama damu, sede akwai abubuwan danakeso ka kiyaye kuma ka kula dasu, na farko de nasan malam yafada maka yanayin yanda gidan sarauta yake, dan haka abu daya zan fada maka shine akwai Wani mutum Sarkin Fada, inaso duk yanda zeso yashiga jikinka kada kabari wata magana wadda tashafeka tahadaku, zan kaika gurin Sarki amatsayin wanda malam yaturo domin kazauna tare damu, ka kula dashi sosai dasauran mutane, idan muka fita zan kaika gurin Baban Gimbiya Fulani, mutum ne, nagari kuma shima dattijo ne, nasan zakaji dadin zama dashi, koba komai daka zauna kana fira da mutanen gidan nan gara karika zuwa gurinshi kuna fira.

Baba yace nagode sosai, kuma insha Allah zaka sameni merike alkawari, fatanmu de Allah yabama wannan baiwa tashi lafiya, suka ce amin. Waziri yace muje ingwada maka masaukinka kafin Sarki yafito, kallon Jakadiya Safeeya yayi yace nasan akwai abubuwa da dama dasuke bukata, anjima kamar da yamma zankawo maki kudi, sekije kasuwa kisiyo masu kayan amfani, game da sutura ma, duk kisiyo masu, idan yaso seki hado da dogayen riguna surika sawa kafin tela ya gama dinkawa. Kallon Yar Baba yayi yace daga cikin gidan nan kada kifita ko ina kinji? Ta daga mashi kai, yace yauwa, dakin fita akwai mutanen dazasu kamaki, saurin boyewa tayi bayan Jakadiya safeeya jin abinda Waziri yafada. Murmushi yayi yace tsoro kamar farar kura.

Tashi sukayi shida Baba, yace Sena dawo anjiman, tace to mungode, nima abinci zan dafa masu kafin inshiga gurin Gimbiya. Yar Baba tashi tayi ta matsa kusa da mamanta wadda take zaune akasa tayi shiru tana ta wasa da kafet din falon, kwanciya tayi bisa cinyarta, tana mata murmushi, dankwalin kanta mamar tacire, tafara yimata wasa da gashin kanta, ita kuma se lumshe ido takeyi. Jakadiya Safeeya tana kallonsu tace ikon Allah, Uwa da Diya se Allah, gaba daya sungama burgeta, murmushi tayi tace Allah yasaka maki, akan duk wanda yayi maki wannan abun. Tashi tayi tanufi kitchen.

Waziri ne, zaune afadar Sarki, bayan sungama gaisawa yafada mashi Jakadiya Safeeya ta dawo, tare da wani tsoho, malam yace sutaho tare, yazauna anan, amma nabashi masauki abangarena, shine nace bari infada maka. Murmushi Sarki Qaseem yayi yace, Waziri ai duk abinda kayi dede ne, babu laifi, kazaba mashi duk aikin daze iya mesauki kasan abinda zaka rika biyanshi ai? Yace hakane, godiya muke.

Sarki Qaseem yace Waziri akwai maganar danakeso muyi akan Yarima, kasan yagama karatunshi kuma yacemun shi aikin gwamnati yakeson yayi, to munyi magana da abokina harma an daukeshi , ranar litinin zefara zuwa, anan gidan gamnati, sun bashi assistant director. Kuma nasan saboda abokinshi ne yanace yanason yayi aiki acan, dan shima acan yake aiki.

Kasan wani magana dayazo mani da ita? Munyi mashi maganar aure, Momynshi tanaso tayi mashi maganar diyar yayarta datake can kasarsu, amma seta fara tambayarshi koyana da wadda yakeso, budar bakinshi se cewa yayi yafison yasamu wadda bata fito daga gidan sarauta ba. Haba Waziri yama zece haka, ko Yaya daya auri mata 2 ba yan sarauta ba, ai matarshi tafarko daga gidan sarauta tafito, shine mukace bamu yarda ba, amma zaka iya kiranshi ka karaji daga bakinshi, kasan banason bacin ranshi, inaso kanuna mashi nayarda yafara auren yar sarauta daga baya se ya auri zabinshi.

Waziri yace wannan ba wata matsala bace daza'a bata rai, kabarni dashi zanji tabakinshi tunda beriga yasamu wadda yakeso ba, ai dasauki, kuma zanga abokinshi Haisam nasan shima zeyimashi magana. Murmushin jin dadi Sarki Qaseem yayi yace. Hakan yayi kyau, muje muga jikin Yaya.

Jakadiya Safeeya ce zaune afalon Gimbiya Suhailat, Gimbiya tace bakiji yanda naji ba, yan kwanakin nan dabaki nan, idan Sarki yafita sede inta zama nikadai, dariya Jakadiya Safeeya tayi tace nima duk banji dadi ba, ya Sarki da jikin? Gimbiya tace jiki kam dasauki, da ranar dasu Waziri suka kawo mashi magani, dakuma maganar da malam yayi akan Fulani ranar har murmushi seda yayi, kuma nantake yashanye maganin, inasha Allahu zesamu lafiya. Jakadiya tace Allah yabashi lafiya, ina dana Yarima?.

Hmmm Yarima rigima, kinsan abinda yazo mana dashi kuwa? Tace a,a. Nan tafada mata yanda sukayi dashi, tace kuma nibazan amince mashi ya auri kowa ba, se jinin sarauta, Jakadiya tace kiyi hakuri, ita harka ta aure ba,aso ana tsanantawa acikinta, addu,a yakamata kiyi mashi amatsayinki na mahaifiyarshi se Allah yayi mashi zabi nagari.
Chapter 14 · 0% Book details