← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 33

Sashe 4

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar bata da hankali yasa abubuwa da dama mune muke temakonta dasu, tundaga abinci dakuma ruwa, na hana yarana subarta tafita daga MAKABARATAR, sbd ina gudun kaidin bil adama, ko gawa aka kawo babu wanda yake iya ganinsu, nina zaba masu suyi rayuwarsu ahaka. Aranar da megadi yazo lokacin yarana suna sallah, basuyi tunanin wani zezo ba, hakan yasa shima yayi sa,ar ganinsu.

Danaga shima yanada zuciyar imani hakan yasa na kyaleshi yacigaba dazama dasu, sede banyarda yafadama kowa ba, dan nasan zuciyar kowa daban take, kuma yayimun alkawarin baze fada ba, mune muke daukesu aduk lokacin dayayi niyar fadama wani. Koyanzu yaci sa,a kaine yafada mawa, amma daba kai bane, yanda muka daukesu nayi niyar bazan ajesu anan kasar ba gaba daya, gara nakaisu wata kasa inda babu wanda yasansu, nasan zasu temakesu. To malam wannan addu,ar dakayi ita kadai tadawo damu. Kuma nayima Baba hakuri tunda naga alkhairi yakeson su dashi, yanzu Malam kome kayanke zamubi umarninka, amma kasani duk inda zaka kaisu kada karabasu dan yarinyar nan bazata iya zama awani guriba batare dasu ba. Kaima Baba kasan yanda kuka shaku.

Malam yace naji dukkan bayaninka, kuma naji dadi sosai daya kasance kaine katsinci wadannan bayin Allah, nasan irin halin temako dakake dashi bazaka taba barin wani abun cutarwa yasamesu ba. Allah yabiyaka kaida yaranka, hakika zakaran da Allah yanufa da cara, to ko ana muzuru ana shaho seyayi. Tabbas wannan yarinya Allah kadai yasan irin alkhairin data debo kuma shine yaraya abunshi. Yanzu abinda nakeso infada maka, gaskiya zaman yan adam agurin nan beyi ba, saboda rayuwar gaba, kaga wannan yarinya tagirma, yakamata ace tashiga cikin mutane, dan kada wata rana tafi haka girma ace zata koma cikin mutane abun ya gagara, kalli yanda take cike da firgici sbd ta ganmu wanda banga laifinta ba, nasan bata taba ganin kowa ba, se mutum 2.

Dan haka nayi maka alkawarin zandaukesu zamuje mu sama ma wannan mata magani, duk da kace ciwonta babu asiri ajiki, zamukaita asibiti aduba lafiyarta, kuma nizan rikesu tamkar jinina. Nagode sosai daka fahimcemu. Godiya sosai Malam yayima wannan shugaban aljanu sannan yabace.

Malam yace to Baba kajide yanda mukayi dashi, yanzu yakake ganin za'ayi? Baba yace naji dadin abinda kayi, kuma dama abinda nake fata kenan arayuwata inga ranar dasu Yar Baba zasu bar gurin nan, shiru yayi yana goge kwallan idonshi. Malam yace yanzu kutashi muje gida semusan abinyi. Jakadiya da matarshi yasa sukamo maman Yar Baba, tana ganin zasu dauketa tafara kuka sosai, da kyar suka kamata, shima seda Baba yaje yakamota yarike hannunta dana Yar Baba sannan ta bisu, gurin shiga mota kuka Yar Baba tasa masu, tsayawa tayi takishiga motar, duk tarike Baba, dakyar yasamu tashiga, haka suka nufi cikin gari.

Zaune suke afadar Sarki Qaseem, Waziri yamika gaisuwa tare dafadin Allah yatemakeka, munje kuma mun isar da sakonka, malam yace afada maka sunanan suna addu,a insha Allahu za,a dace, kuma yace afada maku Fulani tana nan araye, sede haryanzu Allah be gwada mashi inda take ba. Ga wannan ruwan addu,a ne yace akawo na me martaba.

Areef ne ya amshi addu,ar ya ajeta agefen Sarki. Gyaran murya Sarki yayi yace to Alhmdullh, inaganin muma semucigaba da addu,a nasan wata rana Allah ze bayyana mana Fulani da kuma abinda tahaifa, addu,ar mu Allah yasa kome ta haifa ace shima yana raye. Waziri yace maganar gashin jikin memartaba, meze hana a maidashi yazamana duk bayan kwana 2 sbd inaganin hakan zefi temaka mashi. Sarki yace hakan ma yana da kyau, muje abashi maganin. Areef yatashi yadauki maganin suka nufi gurinshi.

Gimbiyar Babbar Gida suka samu agurinshi tana bashi kayan marmari, sallama Waziri yayi, daya daga cikin fadawan yaje ya sanar da ita zuwan me martaba. Komawa yayi yamasu iso sannan suka shiga, bayan sungaisa yatambayeta mejiki tace dasauki, tashi tayi tafita, jakadiya ta mara mata baya.

Duka sauran bayin suka fita, se Babban Hadiminshi ne, kuma wanda sarki ya aminta dashi ne kadai yarage, karbar robar Sarki yayi yazauna kusa da Yayanshi, yace sannu yaya, Malam yace yana gaisheka, kuma yace abinciken dayayi yagano Fulani tana raye bata mutu ba, insha Allahu zecigaba da addu,a za,a ganta. Kokarin dago kanshi yafarayi jin anyi maganar Fulaninshi, cike da farin ciki Sarki da Waziri suka temaka mashi yajingina, wani murmushin farin ciki ne, ya bayyana afuskarshi. Shima Sarki dasauran mutanen dakin kowa farin ciki ne, yacika fuskarshi.

Sarki yace hakane Yaya bata mutu ba, ga wannan maganin yace abaka kasha, dan Allah kada kaki karba, kaga yau shekara nawa ana kawo magani baka sha, ayau naga farin cikin dana dade bangani afuskarka ba, inaso kasha maganin nan, kaga kaima zaka samu karfin yimata addu,a.

Babu bata lokaci yabude baki, Sarki dakanshi yabude robar yayi bismillah yafara bashi maganin, tas yashanye, aka dauko dayar robar Sarki yace wannan ajiki za,a shafa maka, kallon Waziri yayi, babu bata lokaci yakama keken yaturashi suka nufi daki. Cike da farin ciki Areef yafita yanufi bangaren Momynshi. Dede zewuce alambu yahadu da sarkin Fada, kara hade fuska yayi, sarkin fada yamatso dasauri yana washe baki yace Allah yatemaki mejiran gado. Hannu kawai Areef yadaga mashi yawuce, da harara Sarkin Fada yabi bayanshi, kwafa yayi sannan yayi gaba.

Bayan sunje gida dakyar Yar Baba tasaki Baba Jakadiya takamata ita kuma Ladidi matar Malam takama Maman yar Baba suka shiga ciki, haka yaran gidan suka rika sakin baki suna kallon Yar Baba, itam seboyewa take ajikin Jakadiya. Daki takaita tazaunar da ita, haka suka kama Mamanta suka nufi bandaki da ita, da kyar sukayi mata wanka, sun sabata yafi so 5, haka suka fito da ita se kuka takeyi.

Dakin Ladidi suka kaita, sannan Jakadiya tariko Yar Baba takaita bandaki, kintsayawa tayi, dan bata taba ganin irin shiba, seda Jakadiya ta tsaya takoya mata yanda zata wanke jikinta da soso haka tasata tayi wanka tawanke mata kanta, sannan suka fito, kallo daya zakayima yar Baba kagane tsanin kyan datake dashi, dan kamatake da larabawa.

Bayan sungama shiryasu suka basu abinci anan maman Yar Baba takwanta se bacci, yar Baba kuwa tanajikin Jakadiya takwanta tayi shiru, ita kuma tana gyara mata gashinta, wanda yaji mai se kyalli yakeyi, daga haka itama tayi bacci. Malam ne yaleko yace idan sungama sufito suji abinda ya yanke akan su Yar Baba.

Ur's

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]

Season 20⚜25

Malam yayi gyaran murya ya kalli Baba yace nataraku anan dan infada maku abinda nayi tunani akan wadannan bayin Allah, da farko de dakai zanfara Baba, kaga kamar yanda akayi mana bayanin akan 'Yar Baba, bazata iya rabuwa da kai ba, shine nace meze hana idan har kanajin zaka iya zama dasu, kayi hkr da waccan sana'ar taka kadawo nan cikin gari kaida iyalanka nikuma namaka alkawarin gurin zama harma da aikinyi aduk inda kake so.

Amma Baba kaduba kagani mekace? Gyara zama yayi yace agskiya Malam, nikaina banajin zan iya hkr da rashin 'Yar Baba akusa dani, nayi sabo da ita sosai wanda basauki bane ace za'a rabamu, kuma kamar yanda nayi alkawari zankula dasu nayarda zanbar aikina da muhallina indawo nan mucigaba dazama.

Malam yace gaskiya naji dadi, kuma insha Allahu zaka samu aiki me kyau, duk da acan ma aikin lada kakeyi nan ma wani aikin ladan ne, tunda temakon bayin Allah zakayi. Zamucigaba dazama dasu anan kuma gobe zamuje asibiti mukai ita wannan mata domin a aunata asan wace irin kalar hauka gareta, idan maganin asibiti ne, se adorata akan magani, idan kuma na hausa ne, semudawo acigaba dayi mata addu'a.

Jakadiya tace Yaya, dayake kanwarsu ce itace auta, tunda mijinta yamutu bata kara aure ba kuma bata taba haihuwa ba, shine Malam yasama mata aiki agidan Sarki, ta dalilinshi Gimbiya Shuwa tabata Jakadiya dan tace ta aminta da ita. Kallonta yayi yace inajinki meyafaru? Saddar da kanta kasa tayi tacigaba da magana.

Dama wata alfarma ce nakeso zannema agurina kaida Baba, amma dan Allah kada kucemun a'a. Wlh tun da muka dauko bayin Allan nan naji 'Yar Baba tashiga raina, musamman dazu datake kwance akan cinyata senake mata kallo kamar 'Ya ta dana haifa da cikina, duk da Allah be bani haihuwa ba, amma ayau naji inada sha'awar samun diya tabbas da za'a bani 'Yar Baba zanfi kowa farin ciki da hakan, kuma zantafi da ita can gidan Sarki mucigaba dazama da ita, amma Yaya mekace?.

Shiru yayi yana kallon kanwar tashi, yana ganin lokacin datake goge kwalla afakayce dan tasan yahanata kuka akan rashin haihuwa. Tausayinta yakamashi, kallon Baba yayi yace Baba mekace game da maganarta? Baba yace ai Malam kai muke saurare duk abinda kayanke dede ne, nide fatana kada akawo wani abun dazeyi sanadiyar nisantani da kuma mahaifiyar wannan yarinya daga 'Yar Baba. Allah yasani nidanake cikin hankalina zanshiga damuwa sosai, bare kuma ita wadda ta haifeta.

Malam yace shikenan gobe idan mundawo daga asibiti mukaji bayanin likita nikuma zan fada maku abinda nayanke, amma Baba dan Allah kada kacemun a'a aduk abinda zan zartar, kuma kaima insha Allahu babu abinda ze rabaku da Yar ka, duk inda taje kaima zakaje. Bayan kowa yatashi Malam ya kwanta yana kara tuno yanda wannan aljanin yafada mashi yanda suka tsinci wannan mata, rufe idonshi yayi yakara tuno lokacin da Sarki yake fada mashi halinda Fulani take ciki alokacin dasuka nemeta suka rasa. Ajiyar zuciya yayi yatashi cike da tunani aranshi yana addu'ar Allah yasa tunaninshi yazamo gaskiya, amma koma menene yace zeyi istahara da dare.

Wai lafiya Yarima naganka cikin farin ciki haka? Murmushi yayi yace wlh momy yau Baffa yayi murmushi, kuma yasha maganin damuka karbo mashi agurin Malam na Darazo, Tashi zaune tayi cike da annashuwa tace lallai ga dukkan alamu kunzo mashi dawani bayani me dadi ko? Nan yafada mata abinda Malam yace, hamdala tayi tace ai insha Allahu Allah zebayyana Fulani da ita da abinda akema bakin ciki agidan nan, kasanni tausayin Baba nakeyi, shiyasa banason haduwa dashi sede nayi mashi aike.
Chapter 4 · 0% Book details