← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 33

Sashe 21

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama su Gimbiya Suhailat suka shiga falon Jakadiya Safeeya, adede lokacin da Beauty tana karbar biscuit ahannun Areef shi kuma yana ta mata wasa da hankali, se dariya sukeyi, hannu tasa zata karba, cikin rashi sa,a tafada jikinshi. Kwanciya tayi saman cinyarshi tana ta dariya shima haka.

Cak Gimbiya ta tsaya da sauran Sallamar data fara, tsayawa tayi tana kallonsu cike da mamaki, da takaici, sam bata kula dasu Ayman ba, sede kawai taji dariya agefenta, saurin kallon gurin tayi, ai jitayi kamar tazube dan takaici, Haisam ne, yake kokarin saka ma, Ayman sweet abaki, sunata dariya abinsu.

Kamar daga sama sukaji wata irin tsawa, wadda tasa beauty saurin kankame Areef, tayi,wani Uban ashar Gimbiya tasaki, wanda ita kanta batasan ta iyashi ba. Gaba dayansu hankalinsu atashe suka juyo suna kallonta, cike da kaduwa Haisam da Ayman suka sauko kasa, shikam Areef sam abun be daga mashi hankali ba, kara rungume Beauty yayi saboda kukan datasa mashi, sam bata taba jin wata aba wai ita tsawa ba, tunda take, hakan yasa tayi mugun tsorata.

Gimbiya cike da bacin rai tace kai dan Ubanka bazaka saketa ba, kabani hankalinka? Jakadiya ce tayi saurin fitowa daga dakin fulani, dan dama tayi bacci ta tsaya gyara mata dakinne kafin tafita, tana cikin gyara taji wannan hayaniya.

Alokacin data fito saura kadan tazube saboda kaduwa, cak ta tsaya bakin kofa tana zaro ido tare da kallon Gimbiya. Areef yakama beauty suka sauka kasa, dan shima alokacin da Gimbiya tamashi wannan zagin bakaramin kaduwa yayi ba, dan tunda yake betaba jin irin zagin abakin momynshi ba, ko fada bata taba yimashi ba.

Wani irin murmushin takaici Gimbiya tayi, ta kalli Jakadiya, rai abace tace sannu munafukar Allah, mayaudariya, maha inciya, ashe dama abinda kike kullawa kenan? Kinaso ki batama yarona tarbiyya tunda ke baki dashi? Wato duk ginin da nakeyi kece kike rushe shi? Kinje kinsamo wata matalauciyar yarinya kin hadata da Yarima, ita kuma diyata kin hadata da abokinshi.

Ashe dama duk zaman damukeyi zaman munafurci ne ? Wai meyasa duk wanda be fito daga gidan sarauta ba, zaka sameshi maci amana ne? Lallai zamanki yazo karshe agidan nan, bazan kara amincewa da banzan halinki ba. Kai kuma Haisam kake kowa? Inaso kasani Ayman Yarima zata aura, garama ka tattara soyayyarka kayi waje da ita, ko kuma kaima kaje kasamu diyar dan siyasa ka aura, danmu bama auratayya da yan siyasa, domin Sarauta gado ce, kuma ajininmu take, kufa?.

Mulki ne, da lokacinku yacika ko kunaso ko bakwa so, dole kusauka kubama wanda yaci, dan haka kada inkara ganinka agidan nan, bare kuma tare da Yarima ko Ayman. Ke kuma kisaurari hukuncinki, matsawa tayi ta ture beauty wadda tundazu take kuka.

Hannu Areef yasa yariketa sosai shima hawayene suke zuba a idonshi, da kyar yace Momy dan Allah kiyi hakuri wlh beauty itace rayuwata, idan kika rabani da ita mutuwa zanyi, ture ta tayi takama hannunshi dana Ayman wadda itama kukan takeyi, Haisam ne kawai medauriya acikinsu, amma har jakadiya kuka takeyi.

Jansu tarikayi kamar yara har suka fita daga falon, dasauri Jakadiya ta matsa takamo beauty ta dagata zasu shiga daki, kuka kawai, takeyi harda sheshsheka, tana tashi takoma tazube kasa sumemmiya.

Abakin kofar falon Areef ya toge, duk yanda Gimbiya taso tajashi kasawa tayi, hannunshi ya fisge alokacin dayaji Jakadiya tasa wani irin kuka tana fadin munshiga 3 Yar Baba dan Allah kitashi, dasauri yakoma falon, Gimbiya tabishi tana fadin kadawo nace maka ko. Yana zuwa yaga beautynshi kwance akasa babu alamun rai atare da ita, wata irin kara shima yasaki tare da dafe kanshi yazube kasa asume.

Urs.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]

Season 90⚜95

Da gudu Gimbiya da Haisam sukayi kansu, tana zuwa takama Areef hankali tashe tafara jijjigashi tana kuka, Jakadiya Safeeya ma beauty tarika jijjigawa tana kuka. Haisam ne yayi kokarin fita waje yakira wasu bayi maza, suka dawo tare.

Su suka dauki Areef shi kuma yadauki beauty suka fita, Jakadiya, Gimbiya da Ayman suna binsu abaya, cikin mota yasakasu, Jakadiya tashiga tare da Ayman ya kulle kofar ko kallon Gimbiya beyi ba yaja motar suka barta nan tsaye dan babu halin tabisu, tunda Sarki Qaseem besani ba.

Komawa tayi part dinta tana kuka, kara tunano kalaman Areef tayi,,,, Momy wlh kika rabani da beauty nima mutuwa zanyi. Hannutasa tarufe duka kunnuwanta tana fadin bazaka mutu ba Yarima, kaine farin cikina, dan Allah kar kamun haka. Saman kujera tafada tana kuka bayinta se hakuri suke bata.

Waziri ne, tare da wasu manyan bayi maza suna binshi abaya, hanyar lambu suka nufa dan yafi zaton suna can, koda sukaje basu same su ba, tunawa yayi da Medaki, hakan yasa suka nufi can.

Alokacin Sarkin Fada da Medaki suna cikin daki, ita ko Jakadiya Karima tana zaune falo tana kallo ta tasa farfesun kaji tanaci. Wata baiwa ce tashigo falon, ai dasauri Jakadiya tace Uban wa yabaki izinin shigowa? Bana hanaku idan muna gidan nan kushigo ba?.

Dukawa tayi tace Allah yabaki hakuri, dama Waziri ne, ya tambayeni ko keda Sarkin fada kuna ciki, shine nace masa kuna nan, shine yace amaku magana. Cikin Jakadiya ne yayi wani kara, nan take zufa tafara keto mata, batasan lokacin data saki cinyar kazar datake hannunta ba.

Cike da tashin hankali tace ubanwa yace kifada masa muna ciki? Innalillahi wainnailaihirraji,un. Munshiga 3 kada de ace asirinmu ne yake shirin tonuwa? Tashi kiba mutane guri munafuka. Hanyar dakin Medaki tanufa, har tuntube takeyi, tana zuwa tafara bubbuga masu,alokacin sunyi nisa cikin harka, dade sukaji bugun yayi yawa, shine Sarkin Fada yayi saurin zira babbar rigarshi, ko wando besa ba, haka yaje yabude.

Ai yana fitowa Jakadiya tajawoshi tana fadin munshi 3 gasu Waziri can abakin kofa suna jiranmu. Zaro ido yayi yana fadin waya fada masu muna nan? Tace kaide kawuce muje, bawannan bane agabanmu, yanda zamu kare kanmu bakamar ma kai, danni wlh tawa mesauki ce, tunda ni macece kuma kowa yasan inada hakkin shiga duk inda nakeso amasarautar nan.

Sarkin fada yace kiwa Allah kije kice ke kadai ce, bakisan inda nayi ba, nasan zasu kyaleki. Zaro ido tayi tare da dafe kirji tana fadin Jar Uban nan, ai wlh baka isa ba, ai gara ma kai, kome akayi maka kasha dadi, nifa? Menasha, kun hadani da naman kaza da kallo kunshige daki, ai wlh inde nafita kaima seka fita.

Bugun kofar falo ne, ya sasu saurin kallon gurin alokacin Medaki tayi saurin fitowa da daurin gaba ajikinta, kanta ko dan kwali babu, tana fadin wai meke faruwa haka? Shigowar Waziri ce tasata yinshiru, idanu 2 suka hada dashi, hakan yasa yayi saurin kauda kanshi, ai dasauri takoma daki, kallon Sarkin Fada yayi wanda ko rawani babu akanshi, dagashi se babbar riga,, jikinshi kam ko wando babu.

Hannu Sarkin Fada yadora akanshi yana fadin shikenan yau kuma ahaka tazo mani. Waziri cike da bacin rai yasa fadawa sukamashi, Jakadiya Karima tace ai dama kullum ina fada maku kune bakwaji, yau ga irin ta nan, nikam baruwana, Allah yakara, hanyar waje tanufa tana shirin fita. Wani kallo da Waziri yayi mata yasa dole taja burki tana raba idanu.

Wazirin yace ku kamosu dukan su akaisu kurkutu zuwa gobe, kuma inaso kusaka kwakkwaran tsaro agidan nan, yanzu zan fadama sauran masu tsaro, kada abari kowa yafita daga gidan nan koda kuwa matar Sarki ce, koma waye dole akirani kafin yashigo ko yafita. Haka aka tasa keyarsu zuwa kurkutu. Medaki kuwa tana daki tarasa inda zata sa ranta.

Suna zuwa asibiti aka karbesu akayi emergency dasu, kowa aka fara bashi temakon gaggawa, cikin lokaci kankani Areef ya farfado, sede beauty ko alamun motsi batayi, hakan yasa likita yace akai Yarima dakin hutu, nan suka cigaba da duba Beauty.

Tunda Areef ya farfado yafara kiran beauty, kuka yasakama Haisam da Jakadiya Safeeya, se lallashin shi sukeyi, Areef yace wlh idan wani abu yasami beauty na, nima Momy zata rasani. Haisam yace kadena fadin haka Areef insha Allahu zata warke. Karar wayar Haisam ce ta katsesu, Areef yace idan Momy ce kace mata ban farfado ba dan Allah.

Yana dagawa tace Haisam yaya jikin Yariman? Wani irin haushi yaji, wato ita ta danta ma kawai takeyi. Ahankali yace Momy Areef yana cikin wani yanayi, addu,a kawai zakitayashi. Cike da tashin hankali tace ina likitan banishi, yace suna can akanshi suna bashi temako.

Dan Allah Haisam kace ma likita yayi duk yanda zeyi kada dana yarasa ranshi, ko wani abun yasameshi dan Allah. To kawai yace mata, yakashe wayar. Runtse ido Haisam yayi yana karajin haushin kalaman Momy, Areef yace hankalinta yatashi ko?.

Kai kawai yadaga mashi, yace ina ganin matsalar mu zatazo cikin sauki, sbd Momy tana sonka sosai, dan haka dole muhada mata plan. Murmushi Areef yayi yace haka ne, abokina nagode, yanzu muje inga jikin beauty na. Jakadiya Safeeya tace a,a Yarima ka kwanta jikinka babu kwari, likitoci suna kanta suna nema mata sauki. Komawa yayi yakwanta zuciyarshi tana zafi.

Sarki Qaseem ne, afalonshi hankalinshi tashe da abinda Waziri yafada mashi sungani apart din Medaki, haka yazauna yadafe kanshi da hannu 2, jin haryanzu shiru bega Gimbiya Suhailat tafito ba, yasa yatashi yanufi dakinta, kwance yasameta tana ta kuka, cikin sauri yakarasa gurinta tare da kamota ya rungume.

Kara rungumeshi tayi tasaki wani sabon kuka, shafa bayanta yafarayi yana fadin meyafaru kike kuka haka? Kanta tadago, tana share hawaye tace shikenan munshiga 3 Hubby, zamu rasa danmu guda 1 da Allah yabamu. Cike da tashin hankali Sarki yace bangane mikike nufi ba, meyasamu Areef din ? Ko hadari yayi? Kai tashiga girgiza mashi, tace yana can asibiti likitoci ma sunkasa samo kanshi. Sarki yace dan Allah kitashi kifadamun abinda yafaru, wlh zuciyata gab take da bugawa, bakisan irin tashin hankalin daya sameni ba, kifadamun abinda yafaru tunkafin nima kirasani.
Chapter 21 · 0% Book details