← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 33

Sashe 32

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Areef yace kasan Allah daga wannan haihuwar beauty tagama haihuwa. Dariya maganar tabama Haisam sede ya dake ganin halin da akeciki. Haisam yace addu,a zaka rika yimata, yace haba Haisam kalli fa yanda take shan wahala, baiwar Allah wlh da ana karbar haihuwa dana karbar mata. Amma anyi na farko anyi na karshe, banason yaran dayan dazata haifa ya isa.

Haisam yace duk wannan ma bata taso ba, kaide muyi Addu,a Allah yasauketa lfy. Areef yace amin. Amma......... sunanshi yaji ankira cikin wata irin murya da Yaya Areef,, cak ya tsaya da magana dazeyi, yajuya yana kallon inda yaji muryar tafito. Ai dasauri yanufi cikin asibitin Haisam yabi bayanshi.

Suna zuwa kusa da labour room din suka jiyo kukan jariri, da gudu Areef yanufi dakin, cikin sauri Haisam ya rikeshi, yana fadin maza basu shiga, kajira afito da ita. Areef yana hawaye yace kasakeni, wlh duk da bansan muryar beauty ba amma nasan ita ce ta kirani, kasakeni inje inga beauty na.

Da kyar su Waziri suka hanashi shiga, Momynshi ta matso tace haba Yarima kayi hakuri mana, kallifa yanda ake kallonmu. Zonan kazauna kaji, yanzu za,a fito da ita. Wani likita ne yafito fuskarshi dauke da murmushi yanufo gurin. Sarki Qaseem ya tarbeshi yace yaya jikin Amatullah?.

Likita yace Alhamdulillah tasauka lafiya, tasamu baby girl, kuma duk suna cikin koshin lafiya. Sarki yace Alhamdulillah. Likita yace yanzu za,a kaisu dakin hutu, idan kungama kusameni office, akwai wani albishir din. Godiya sukayi mashi, yawuce. Areef yariga kowa shiga dakin da suke, kotakan jaririyar be biba, gurin beautynshi yanufa.

Hannunta yakama yarike sosai yana sannu beautu na, nine ko? Murmushi tayi mashi, yace sannu bazan karaba kinji? Kamar daga sama yaji tace Yayana ga babynmu. Surin dago kai yayi yana kallonta. Itama shi take kallo, cikin farin ciki yanunta yama kasa magana, kai tadaga mashi.

Ai yama manta da mutanen dakin kawai ya rungumeta da karfi, harseda tayi dan kara. Momy tace lfiyarka Yarima? Saurin sakinta yayi yajuyo yana sosa kai yace wlh Momy beauty tayi magana.

Suma mamaki ne yakamsu, suka nufi gurinta. Murmushi tayi tace Momy. Cike da farin ciki Momy ta matsa kusa da ita tace da gaske ne, ashe? Ikon Allah, lallai Fulani zatayi farin ciki. Allah mungode maka. Sarki yace Sannu Amatullah, cike da kunya tace yauwa Abbah, yace bari muje gurin likita mudawo.

Zaune suke a office din likita, bayan yagama rubutunshi yacire glass dinshi yace albishir din dana ce maku kilama idanunku sungane maku? Sarki yace tabbas yau munga abin farin ciki, sede muyi ma Allah godiya. Likita yace haka ne, dama nafada maku, akowane lokaci maganarta zata iya budewa, sbd akwai irinsu, kasan akwai wani zakaga kurma ne, bayaji baya magana amma sakamakon wani tashin hankali bakinsu yana budewa.

To itama Allah yasota gashi ta dalilin haihuwa bakinta yabude. Kuma jikinta babu wata matsala, zuwa anjima idan tahuta zaku iya tafiya, ga magungunan dazatayi amfani dasu anan. Allah yabada lafiya. Godiya sukayi mashi suka fita.

Segurin karfe 11 na dare suka koma gida, gaba daya murna tacika gidan, Ayman jitake kamar itama tadawo gida, dan Haisam yace tazauna tunda hidima tayi masu yawa, agidan. Kowa cewa yake yarinyar tana kamada Areef, shiko bakinshi yaki rufuwa, yamaki fita daga dakin, seda Momy tayi mashi da gaske sannan yafita.

Haka akayita shirin suna, Momy tace ma, Haisam yamaido Ayman gidan ayi suna gaba daya,daga baya sesu koma. Aranar suna bakaramin taro akayi ba, diyar Beauty aka samata Khairat, dan Areef da kanshi yace babu sunan wanda zesa, shi khairat yajeso.

Yaron Ayman shima Haisam be tsaya saka sunan kowa ba,yasa mashi Fahat. Waziri kuwa sunan Baffan beauty yasaka ma yaronshi wato Hasheem, ana kiranshi da Karami. Bakaramin dadi Baffan beauty yaji ba da irin karar da waziri yamashi ba. Sarki Qaseem shine yasayi komai na jariri harda ragunan suna.

Gaba daya masu laifin gidan aka fiddo haka aka raba masu aiki, kowa danashi, Zakiyya abangaren masu abinci aka kaita, tanayi tana kuka, ahaka suka gama, aka sallamesu kowa aka bata nata.

Bayan kwana biyu mahaifiyar Zakiyyah ta kawo mata ziyara, sunsha kuka sosai, ayanayin data ganta, kallonta tayi tace Zakiyyah kinga irin abinda nake fada maki ko? Yanzu ina sarautarki da mulkinki gashi nan kinkare a gidan kurkutu, acikin talakawa marasa galihu. Cikin kuka tace wlh Umma nayi dana sanin shiga wannan bakar rayuwar dana shiga, kuma insha Allahu na dauki darasi. Umman tace bakomai ai kin kusa fita kema kidawo gida. Allah yayi maki sauyi da miji nagari. Ta dade kafin ta tafi, takawo mata abubuwa dayawa. Zakiyyah se kuka takeyi.

Seda suka sami wata 2 kafin sukayi shirin tafiya, visa Sarki yasa akayima Ladingo yace sutafi da ita seta rika temaka mata. Haka beauty tacigaba dazuwa makaranta tare suke tafiya da Ladingo, idan zasu shiga aji seta barmata Khairat. Yanzu karatun yana mata sauki sosai, dan har larabci tanaji tana maidawa.

After 2 years. Beauty ce tafito hannunta rike da takardu tana ta farin ciki tanufo gurin Areef da khairat dasuke tsaye jikin mota suna jiranta. Khairat tayi wayo sosai, sede haryanzu ba,ayi mata kanwa ko kani ba. Tana zuwa tafada jikinshi tana murna. Kara rungumeta yayi yace congratulation my beauty na. Allah yanufa yau kingama karatunki.

Khairat tace Dady nima kadaukeni, dariya suka saka yace yi hakuri yau ranar Mimie ce, janta yayi suka shiga mota suka nufi gida. Party sosai suka shirya aranar, dan beauty hada qur'ani tasauke, gashi aharkar boko yanzu sede takoyama wani.

Bayan kwana 2 suka fara shirye shiryen komawa gida dama tuni yagama hada komai na aje aikinshi. Bayan suje sunyi tsaraba washe gari suka dira a nigeria. Kowa yayi farin ciki da dawowarsu. Haisam kamar ze zuba ruwa akasa dan farin ciki. Beauty ta kalli Ayman wadda cikinta har yafito kadan tana dariya tace Aunty yanaga haka?

Hararta tayi tace kema zakiyi ne ai, haka suka nufi gida. Babbar tarba, kowa yana cikin farin ciki.

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya acikin masarautar, Areef yakoma aikinshi, suna zuwa cikin wanciyar hakali shida Haisam.

Iyalen Baban darazo sunajin dadin zaman gidan sarautar, babu abinda basa samu ta ko ina.

Ayanzu cikin masarautar karatu akeyi sosai, dan Malam ya aiko da malaman dasuke koya masu karatu, gaba daya bayin dasuke gidan, harma da masu laifi, ana fidda masu ranar karatu. Sosai suke jin dadin abinda ake masu, gaba daya canji yasamu agarin Gombe, duk wanda ya aikata wani laifi, ana yanke mashi hukunci dede dashi.

Bayn shekara 2 beauty takara haihuwar da namiji, ana kiranshi da Faisal, Ayman ma yaranta biyu, mace da namiji, macen sunanta Labiba.

Ayau ne Zakiyya tafito daga kurkutu, rungume suke da juna ita da Jakadiya Karima, kuka kawai sukeyi. Zakiyyah tace Allah yada fuskokinmu, da ace ba,a gidan nan kike ba, dazanyi maki alkawarin kawo maki ziyara.

Amma yanda zanbar gidan nan bana fatan inkara dawowa. Kiyafemun abinda namaki nima nayafe maki. Jakadiya tace nayafe maki. Allah yabaki miji nagari kema kiyi aurenki. Da kyar suka rabu sunata kuka. Sallama tayima sauran mutanen gurin tafito.

Mahaifyarta ce, tazo daukarta, haka suka nufi fada kallo daya zakama Zakiyya kasan tafita hayyacinta, gaba daya tayi baki ta rame. Azaune suka iske iyalan masarautar, kowa fuskarshi cike da annuri.

Kallonta sukeyi cike da tausayi. Zama tayi bayan sungama gaisawa, ta kalli Baffan beauty, suna hada ido ykara daure fuska ya dauke idonshi daga kanta. Wasu hawayene suka zubo mata, ahankali tace

Nasan banida bakin dazan rokeka gafara, amma duk da haka bazan yi kasa aguiwa ba, dan girman Allah kaya femun abubuwan dana yimak. Hakika naga rayuwa, kuma hakan kadan ya isheni darasi. Banaso in mutu da hakkinka kayafemun.

Kuka ne yaci karfinta. Shiru yayi kamar bazeyi magana ba, can yace bakomai nidama nadade da yafe maki. Allah ya shiryeki. Matsawa tayi kusa da Fulani, takamo hannunta, tana kuka tace Fulani dan .... saurin rufe mata baki tayi tana girgiza kai, hawaye suna fita daga idonta tace nayafe maki. Allah ya yafe mana baki daya.

Haka tayita rokon mutanen falon tana kuka, har seda tasa wasu kuka. Tashi sukayi auka masu sallama, har bakin mota aka rakasu, amma banda Sarki Qaseem, Waziri da Baffan beauty. Seda suka tafi sannan suka dawo.

Bayan kwana biyu da komawar Zakiyyah gida tadan murmure, mahaifinta yakira Ummanta da ita suna zuwa, ya kalleta yace, zakiyya ina tayaki murnar fitowa daga gidan yari. Basena kara tunatar dake rayuwa ba. Nasan azaman da kikayi kin kin koyi darussa da dama. To Alhamdulillahi dama arayuwa ana son idan mutum yayi kuskure yayi kokarin gyarawa.

Shiyasa Allah da kanshi ya saukar da hukuncin daza,ayi ma masu laifi, domin yazama darasi agaresu. Mutane dayawa ta dalilin wannan hukuncin suke shiryuwa. Naji dadi sosai danaga kin koyi darasi.

Abunda yasa nakiraki dama kinsan nace dakin fito zan aurar dake,somin zamanki agidan nan babu abinda ze amfana maki, se tarin bakin ciki. Dan haka nazaba maki miji, amma idan beyi maki ba, kinada ikon canza wani ba dole zanyi maki ba.

Goge hawayen idonta tayi tace, babu wani zabi dazakamun inki binshi, nayarda da duk wanda kazabamun. Murmushi yayi yace naji dadi, kuma bakowa bane se Wazirina. Shikadai ne, nasan zerikemun ke da amana kobayan rai na. Sede kinsan matanshi 3, sekiyi hakuri da abokanan zamanki. Wannan asabar din za.a daura auren akaiki dakinki. Allah yayi maki albarka.

Tashi tayi tana hawaye tanufi dakinta. Zama tayi tabuga tagumi, tana fadin kaicona dana kasa yin hakuri agidana, Allah yamun ni,ima amma na butulce mashi. Yanzu gashinan zan shiga cikin matan da suka haifeni inyi kishi dasu. Allah kabani ikon cin wannan jarabawa daka jarabceni da ita.

Kwance take ajikinshi sunata fira, Areef yace beauty na, yakamata fa ace akamar yanzu kinada yaran 3. Murmushi tayi tace a,a 2 ma sun isa, kaidama kace daga daya bazan kara ba. Dariya yayi yace nima bansan yanda akai kika karaba my beauty.

Kallonshi tayi tace habibina yakamata ka canzamun suna haka nan, kanaji rannan Khairat tacemun beauty ko, dana tambayeta ce tace wai Auntynsu ce itama take cemata beauty, data tambayeta meyasa tace mata haka setace ai tana da kyau ne, shine yan ajinsu suke cemata beauty, ahine Fahad yaketa kuka wai meyasa zasu rika cemata haka shine zerika fada mata haka ai.
Chapter 32 · 0% Book details