← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 33

Sashe 31

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adaren ne kafin azo daukar Ayman, Sarki yatarasu duka domin ayi masu nasiha. Nasiha meratsa zuciya sarki yayi masu, bayan yagama Baffan beauty ma yayi masu. Yace Amatullahi, kiyi hakuri kinga gobe da safe zaku tafi, babu ruwanki da kowa, bakisan kowa ba se mijinki.

Kada kiyarda wasu suzo maki dawani abu, yanda baki magana, karkiyarda kibiyema kowa, kuma kimaida hankali akan karatunki, inhar kinaso kidawo kusa damu, amma idan bakiyi kokari ba, acan zakuyi tazama. Ko kinaso kuzauna acan? Kai ta girgiza yace yauwa, Allah yayi maku albarka. Kema Ayman, kindega abinda yafaru azuwanki gidan nan, damma kinci sa,a gidanki daban ne, amma duk da haka bana son kisaki jiki da mutane, dangin mijinki kirikesu da hannu 2, kowa kizauna dashi da zuciya daya, Allah zetemakeki akan makiyanki. Allah yabaku zaman lfy. Anan Waziri shima yayi masu tashi nasihar, se yan uwan Ayman da dangin Fulani dasukazo, kowa seda yayi masu nasiha.

Se kuka sukeyi, bayan angama masu Sarki Qaseem yace kuje, yanzu za,azo adaukeki. Bayan suntafi, Sarki yace Waziri kaima yanzu zamu kawo maka taka amaryar. Dariya suka saka, gaba daya. Da misalin karfe 9 aka dauki Ayman, wanda Areef shima yadauki beautynshi amota suka tafi rakasu.

Bayan kowa yatafi yarage daga amarya da ango se su Areef. Haisam yace abokina yakamata muje inrakaku. Duka Areef yakai mashi yace wlh kai dan iska ne, wlh se ince ba inda zani, Haisam yace da kyau, ai akwai wani dakin, indarabon asamu dan gidanmu kuma shikenan.

Areef yace a,a ni baruwana kaine dan iska nikam nafison dan saudiya. Haisam ya kalleshi yace wlh abokina banason tafiyar nan taku, shiyasama bazan je rakiya ba, amma zamu zo dan acan zamuyi honey moon dinmu, Areef yace bakomai nasan sanda zamu tafi ma baku tashi daga baccin gajiya ba.

Dariya Haisam yayi yace ammade ai munyi sallah ko, Areef yace tobara mutafi nasan beauty na tagaji gara muje ta huta, mike wa sukayi, Haisam ya rungume shi idanunshi har yakawo ruwa. Shima Areef seda yazubar da kwalla, sun dade ahaka, kafin suka saki juna.

Har bakin mota suka rakasu, Ayman da Beauty se kuka sukeyi,da kyar Areef yacire beauty daga jikin Ayman. Ayman tace Yaya yanzu shikenan gobe zaku tafi? Kallonta yayi zeyi magana kuka yataho mashi, kawai jan beauty yayi suka shiga mota.

Amota yayi ta lallashin beauty, da kyar tayi shiru, haka suka nufi gida shima duk bayajin dadin rabuwarsu da Haisam dan bakaramin sabo sukayi ba. Beda wani aboki se shi, dashi kadai yasaba. Har dakinta na bangaren Jakadiya Safeeya ya kaita sannan yatafi.

Kwallan data zubo mata ta goge, takalli Jakadiya Karima tace yanzu kalli yanda duniya tajuya mani baya, kamar ni da mulki na da matsayina amma kalli yanda kowa yamanta ni acikin gidan nan, biki akayi ayau amma banida damar fita inje gurin. Jakadiya Karima tace, Zakiyya kenan, idan zakiyi hakuri ki aje wata sarauta ki rungumi kaddara kiyi.

Har garama ke, zaki iya kirga kwanakin ki,nifa? Sede afitar da gawata. Saboda haka kinganni nan namaida gurin nan kamar gidana, idan harzaki rika yimani maganar wata sarautarku, ina me tabbatar maki zanbar maki dakin nan, kuma bazaki kara ganina ba, dan kinsan babu wanda zezo yazauna tare dake. Shiru Zakiyya tayi tana jinyanda Jakadiya take fada mata maganganu. Murmushin takaici tayi tace duniya kenan.

Washe gari tunda safe aka fito rakiyarsu Areef, idanunshi sunyi ja sosai, dan tunjiya yakema iyayenshi kuka, Abbanshi har cewa yayi kode afasa tafiyar ne, yace a,a Abba, nasan damun tafi komai ze wuce.

Haka suka shiga mota aka nufi air pot dasu, ko acan da kyar aka ciresu daga jikin iyayensu, suma seda sukayi hawaye, suna kallo har jirginsu yadaga, sannan suka juya zuwa gida. Acikin jirgi kam lallashin beauty Areef yayi tayi, mutane se kallonsu sukeyi, dan sunga suna kama sosai, gashi dama beauty da kyar tashiga jirgin, shiyasa tashige jikin Areef, ko ido takasa budewa. Shiyasa kukan nata yazama 2.

Suna sauka dama mota tana jiransu,daukarsu tayi suka nufi gidansu, gida ne, mekyau, yaji komai, kayansu aka shigo masu dasu. Wanka Areef yace suje suyi, rufe fuska beauty tayi tana murmushi. Cak yadauketa bema tsaya jiran yardarta ba. Haka sukayi wanka suka fito, dakanshi yashiryata aka kawo masu abinci.

Da dare ma kawo masu abinci akayi, bayan sungama yadauketa suka nufi toilet, wanka sukayi tare da alwala, sallah sukayi sannan yajawota suka nufi gado.

Washe gari da safe dakanshi yashiga kitchen yahada masu break, bayan sungama yajata zuwa daki suka koma bacci, seda azahar suka tashi, wanka sukayi sukaci abinci suka fito falo, takarda da biro yadauko yajawota suka zauna falo, yace beauty yau labari zamuyi fa.
Haka yayita rubuta mata yana bata tana rubuta mashi abinda tasani, idan ta manta ya tuna mata.

Haka suka cigaba da rayuwarsu acikin gidan gwanin ban sha,awa, akullum suna yin waya da yan gida, satinsu guda sannan suka fara fita, aranar yakaita makaranta shi kuma yawuce gurin aiki, seda yayita lallashinta kafin ta hakura, yace dasun tashi zezo yadauketa.

Rayuwar Areef da Amatullah gwanin ban sha,awa, suna matukar son junansu, akullum tare suke fita ya kaita makaranta, shikuma ya wuce aiki, se da yamma suke tashi, dayake makarantar hade take da islamiya, shiyasa sesun kai yamma, kuma Beauty tana gane karatun sosai, babu ruwanta da kowa, karatunta tasa gaba.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, suna da wata 3 dayin aure, ciki yafito ajikin beauty, bayan sunje asibiti akayi test aka gano ciki dan wata 2, bakaramin murna Areef yayi ba, haka yakira gida ya fada masu, suma sunyi murna sosai. Tunda suka koma gida yake riritata, damma cikin beda laulayi,

Haka yakira Haisam yayi mashi albishir, shima alokacin yake fada mashi Ayman ma tana dauke da ciki itama wata 2, Areef yace amma naji dadi, zamu fara cika ma su Abba gida da jikoki. Haisam yace idan muna da rai muma semu hada zumunci. Areef yace Allah ya kaimu. Amma wai yaushe zaku zo, kasanfa muna son zuwa ziyara gurin yan uwa, gurin dangin su beauty, danasu Momy. Haisam insha Allah zamu shirya muzo. Yace to Allah yakaimu

Baffan beauty ya kalli Fulani, datake kwance ajikinshi, dawowarsu daga asibiti kenan, fuskarshi dauke da murmushi, yace babu abinda zance maki Fulanita, sede godiya, tabbas ke haske ce acikin rayuwata.

Ashe inada rabon ganin yarana, aduniya. Ina rokon Allah ya saukeki lfy. Murmushi tayi tace amin. Yace ina ganin Gimbiya Suhailat zata rigaki haihuwa ko? Kai tadaga mashi, tace wlh ni kunya nakeji, yace kunyar me kuma?.

Tace haba dan Allah, yanzu kana ganin Amatu ciki gareta, Ayman ma haka, ga Aunty, yanzu kuma ace nima haka, kuma suk kusan tare zamu haihu. Dariya yayi yace kin manta dayar ai, tace wa kuma? Yace matar Waziri mana.

Tashi tayi fuskarta dauke da mamaki, tace da gske Aunty Safeeya tana da ciki? Yace da gske mana, dazu yake fadamun, nace kinga ikon Allah ko? Tace gaskiya kam, wama yayi zaton Aunty zata haihu, yanda ta dade bata taba haihuwa ba.

Yace aishi Allah babu ruwanshi, yana yin abunshi aduk sanda yaso,babu ruwanshi da tsufanka ko yarintarka. Fatanmu Allah yasa mugama da duniya lfy. Tace amin. Amma de ba gida su Yarima zasu dawo ba idan zata haihu ko? Dariya yayi yace wai naga duk kinbi kin damu, ina ruwanki dasu?.

Kinsande muna da inda zamu ajesu ko? Kuma zamu sami masu kula dasu, dan haka ki kwantar da hankalinki. Shiru tayi bata ce komai ba. Jawota yayi yace dazu Yarima yake fadamun zasu je ziyarar yan uwa. Murmushi tayi tace kagani ko,

Nibanje ba, ga jikarsu nan har zataje, yace karki damu kema zakije, Allah yasaukeki lafiya. Tace Amin.

Zaman Haisam da Ayman, zama ne na so da kauna, yana kula da ita sosai, itama haka, kuma tana daraja yan uwanshi. Acikin satin ne, yagama shirya masu visa suka daga zuwa saudiya domin zumunci.

Bakaramin dadi su Areef sukaji ba, da ziyarar dasuka kaimasu, kuma agidansu suka sauka, ko abinci basa tsaywa girkawa, sede sufita suci awaje, dagacan suwuce gurin shakatawa. Dayake Beauty suna hutu.

Sun zagaya gurare dayawa, sannan suka shirya dukansu suka nufi misra, yan uwansu bakaramin dadi sukaji ba. Kwanansu 3 sannan suka wuce garinsu Fulani, suma sun tarbesu sosai, sun sha gata, kwanan su 3 acan ma, sannan suka dawo gida.

Kwana 2 su Haisam suka kara sukace zasu wuce, har kuka sukayi dasuka rakasu, da kyar Areef yacire beauty daga jikin Ayman, haka jirginsu yadaga suka dawo gida yana lallashi.

Bayan wasu watanni Gimbiya Suhailat ta haifi diya mace, ansha hidima sosai, sede su Areef basu jeba, dan beauty tana Exams. Yarinya taci sunan mahaifiyarsu Sarki Qaseem Fatima, ana kiranta da NOOR.

Bayan wata 2 da haihuwarta Fulani ma tahaihu yan biyu, mace da namiji,gaba daya gidan seda kowa yasan anyi haihuwar yan 2, Sarki Qaseem bakaramin dadi yaji ba, ganin Yayanshi yana samun haihuwa yanzu. Alokacin beauty tagama Exams dinta, shima yadauki hutun shekara.

Hakan yasa suka nufo gida, bakaramin farin ciki mutanen gidan sukayi ba, apart dinsu da aka gina masu anan suka sauka, wata dattijuwa aka kawo ma beauty wadda zata rika temaka mata, ana cemata Ladingo.

Ranar suna akasama namijin sunan Mahaifinsu Sarki, macen Kuma sunan Mahaifiyar Fulani. Ana kiransu da AMEER DA AMEERA. Anyi shagali sosai, su beauty da Ayman da Jakadiya Safeeya sunata fama da tsohon ciki.

Bayan suna da sati daya Ayman da Jakadiya Safeeya suka haihu, Ayman ta haifi Namiji itama Jakadiya Namiji. Beauty kuwa kuka tasaka dataji ance Ayman ta haihu. Areef yatambayeta lafiya awayarta ta rubuta mashi ita fa tsoro takeji, dariya yayi uajawota yace ki kwantar da hankalinki, babu wata wahala kinji ko? Kai tadaga mashi tana murmushi.

Adaren itama ta tashi da nakuda, dama beauty ga tsoro, gaba daya taki sakin jikinta se kuka takeyi, tun Ladingo tana kokari harta gaji, Areef kuwa kamar shine yake nakudar, kallonshi Ladingo tayi tace agaskiya Yarima ina ganin sede fa akaita asibiti, idan bahaka ba, za, iya rasa abinda ke cikinta.

Cikin rudewa yace to kihada kayan bara infada ma su Momy. Cikin lokaci kankani aka nufi asibiti da ita, hankalin kowa yatashi ganin yanda beauty tafita hayyacinta. Suna zuwa aka nufi labour room da ita. Kowa yakasa zama, Areef kuwa kuka yasaka, Haisam ne yajashi suka fita waje yana lallashinshi.
Chapter 31 · 0% Book details