← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 33

Sashe 20

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta tayi tace haba de tunyanzu sallar isha,i ma yanzu za,ayi, wai meyasa yanzu bakison zama anan sosai, musammamma da dare? Gaban Jakadiya yafadi, aranta tace nasan Fulani tana can takusa tashi ai dole inkoma kada su Yarima suganota. Dasauri tayi murmushi tace ai dole intafi inje inji inda aka tsaya amaganarsu, murmushin jindadi Gimbiya tayi tace hakane fa, Jakadiya tace nikam yanzu ai nasamu yan fira tunda de kunya tahanasu zama anan, dan yarima ma cewa yayi bayaso kusani harse Sarki yasamu lafiya yasan dayayi maku magana za,a sa rana. Gimbiya tayi dariyar jin dadi tace kibarni dasu, zamu gwada masu bamusan komai ba dakanshi zezo mana da maganar, bari hubby yadawo infada mashi, sosai Jakadiya taji dadin maganar Gimbiya, sallama tayi mata tafita.

Koda taje kowa yana zaune tare da masoyiyarshi, Areef yanata koyama beauty rubutu da karatu, kitchen ta wuce ta dauko abinci tace sannuku da aiki, Yarima yace Aunty har kindawo? Tace bari inshiga ciki inci abinci inyi wanka sukace to afito lafiya.

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya babu wanda yasan abinda yake tafiya atsakanin masoyan. Abangarensu kuwa soyayya me karfi tashiga tsakaninsu, akoda yaushe suna part din Jakadiya Safeeya, Areef yadage sosai yana koyama beauty karatu da rubutu, suna dawowa office beda gurin zama se gurinta, dayake itama tanada basira kome yakoyamata take daukeshi, ayanzu har rubutu ta iya, dan tana hada kalmomi.

Ganin haka yasa hankalin Jakadiya yafara tashi, samunta tayi tafada mata kome Yarima ya tambayeta kada tabashi amsa, idan ba haka ba, duk ranar da yasan labarinta bazata kara ganinshi ba kuma zesa akoresu, kada kisake kice mashi A MAKABARTA AKA HAIFEKI, kawai kifada mashi abinda nafada mai, kinji ko? Ta daga kai, da wannan hankalin Jakadiya Safeeya yadan kwanta, kuma akaci sa,a shima be cika yimata tambayoyi ba.

Abangaren Gimbiya Zakiyya kuwa ta kwace ma Medaki Sarkin fada, dan duk dare agurinta yake kwana, wani irin sonshi takeyi, har bataso yayi nisa, sosai Medaki tashiga damuwa sede tunda Jakadiya Karima tayi mata bayanin komai, shima Sarkin Fada yace mata yayi hakane dan kawai yarama irin cin mutuncin datayi masu ne, kuma kudinta yakeci sosai, kuma yana kawoma su Medaki, hakan yasa hankalinta ya kwanta idan yasamu lokaci kuma yana zuwa gurinta.

Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya Waziri akullum yana kara sakama Sarkin fada ido, dan sunyi waya da malam yace mashi yayi kokari yagama hada duk wata sheda daza,a fara tuhumar Sarkin fada yana nan zuwa tunda jikin Sarki yafara sauki, yanaso akawo karshen matsalar gidan.

Gimbiya Suhailat ce tafito tana neman Ayman, ganin bata ganta ba, wata baiwa tace sunfita bagaren Jakadiya Safeeya. Murmushi tayi tace yaude bari inje da kaina inga wata wainar ake toyawa, kuma in nuna masu nasan abinda suke boyemun, ai gara azo ayi bikin nan kowama yahuta. Allah nagode maka da zaka cikamana burinmu, bari indawo in bama Yaya albishir medadi, itama nasan zataji dadi ace Ayman dinta zatayi aure. Fita tayi wasu bayi suna take mata baya, suka nufi bangaren Jakadiya Safeeya.

Zaune suke afalo, Areef da beauty suna zaune bisa doguwar kujera, sungama karatu, yana bata biscuit abaki, suna ta firar su gwanin ban sha,awa, Haisam da Ayman suma suna zaune kasa yana bata ice cream tana ta zuba mashi shagwaba.

Jakadiya kam tana dakin Fulani tagama yimata wanka tana sa mata kaya, tayi kyau sosai, hutun datake samu kyanta yafito har kiba tayi. Jakadiya tace insha Allhu komai zezo karshe da malam yazo kema kije gurin mijinki koze samu sauki.

Wazirine da Sarki Qaseem suka fito zasuje bangaren sarki Hasheem, dede gurin part din. gimbiya Zakiyya zasu wuce, sega Jakadiya da Sarkin Fada sunfito daga gidan, Sarkin Fada se gyara wando yakeyi, suna fitowa suka kwashe da dariya, hannu yamika mata suka kashe, yace kai wlh yau nasha roman Gimbiya, sosai, kinsan tundazu naso infito ta hanani, ashede haka Sarki yakejin dadinshi. Jakadiya tace ba dole sunemeka ba, tunda kana dauke masu nauyin abinda musakin mijinsu yakasa ba, ai wlh..........

Maganar ce ta makale sakamakon idanu data hada dasu Waziri. Hannu tasa ta tabo sarkin fada dayake shirin yin magana. Wata irin zabura yayi alokacin da idanunshi sukaga abinda take nuna mashi, wani irin kallo Sarki da Waziri suke binsu dashi,,,, kuttt suka hadiyi wani miyau me daci, ga wata irin zufa datake fito masu.

Shinko su waziri sunji firarsu? Kubiyoni anext page danjin abinda yafaru.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]

Season 85 ⚜90

Idan ran Sarki Qaseem yayi dubu to yabaci dajin irin kalaman Sarkin fada da Jakadiya Karima, Waziri ne, yajuya ya kalli Sarki Qaseem, shi kanshi ya tsorata da ganin yanayinshi. Cikin sauri yataboshi, yana kallonshi yayi mashi alamu da ido.

Juyawa yayi murmushi dauke afuskarshi yakalli su Sarkin fada yace dama gurin memartaba zamuje kuma segashi munhadu, ko kuma daga can kuke? Dasauri Sarkin fada yace wlh kuwa shinema mukashiga gurin Gimbiya muyi mata albishir naganin halin da Sarki yake ciki.

Gaskiya munji dadi sosai, jikinshi yayi kyau, yanzun nan nashiga ko kinti 2 banyi ba, shine ma muka fito da Jakadiya. Amma ai kuma yanzu kukazo nan, ko kun dade tsaye anan? Waziri yayi murmushi yace ai ko second 2 bamuyi anan ba, kuka ganmu, bari mukarasa. Wata irin ajiyar zuciya suka saki, har suna hada baki gurin fadin to adubashi, Jakadiya Karima tajuya tanama Sarki Qaseem kirari, hannu yadaga mata tare da kakalo murmushi sannan suka wuce.

Sarkin Fada yace wai! Allah yasomu damun kama kanmu ashema basujimu ba, Jakadiya tace kaide bari, nidama nasan dakyar idan sunjimu, dan Sarki Qaseem mutum ne wanda beson jin abinda bedameshi ba. Sarkin Fada yace haka ne, shima ai Wazirin na Allah ne, babu ruwanshi dajin gulma, akwai addini, muje gurin Medaki itama inkwashi rabona. Jakadiya tace to amma gaskiya yau nima inaso muje dakina.

Wani kallo yayi mata, sannan yace haba Jakadiya da girmanki kike fadin haka, ai kibarma Gimbiyoyin Sarki, ke kam yanzu ai kinwuce wannan matsayin. Hade rai tayi tace amma ai duk tsufa na ban kaika ba ko? Dariya yayi yace haka ne, amma kinmanta namiji baya tsufa? Kawai kibar wannan maganar muje inyi abinda zefishsheni.

Wani guri kafin akai part din Sarki Hasheem suka samu suka zauna, idanuwan Sarki Qaseem har rufewa sukeyi sbd bacin rai, da kyar ya iya daga baki yace, dan Allah Waziri kace abinda naji ba gsky bane, nabama mutanen gidan nan amana musamman wadannan 2, acikinsu Yaya yafison Jakadiya Karima, nima haka, dan Allah Waziri. Wani irin tausayinsu ne yakama Waziri, ganin idanun Sarki Qaseem sunyi ja yasashi matsawa kusa dashi tare da dafashi yace.

Memartaba wane irin matsayi kabani azuciyar ka? Kallonshi Sarki yayi yace aduk gidan nan kaine mutumi nafarko damuka fara aminta da kai, kawuce kowane irin matasayi agurinmu har ka kai matsayin dan uwa agurinmu. Bari kaji aduk fadin duniyar nan kai kadai muke iya fadama sirrinmu, shiyasa bama jayayya da duk wata shawara dazaka kawo mana.

Kawai kafadi abinda ke ranka namaka alkawarin komenene zankarbe shi, nasan bazaka taba fada mana abinda ze cutar damu ba. Gyaran murya Waziri yayi, fuskarshi cike da annurin kalaman dayaji daga bakin Sarki Qaseem, ahankali yafara fada mashi duk irin abubuwan daya fara gani agurin Sarkin fada, har firar dasukayi seda yafada mashi, daga karshe yace zakayi mamakin idan nafada maka Gimbiya Fulani tana cikin gidan nan tsawon watanni 3?.

Seda Sarki yakusa kwarewa saboda firgita, kai waziri yadaga alamun da gaske yake, sannan yacigaba, akwai abubuwa da yawa wanda bakusansu ba, daga ni se Malam, se Jakadiya Safeeya kadai muka sansu, amma inaso abari se gobe idan Malam yazo zeyi maku bayanin komai, sede abinda nakeso kasani bawai munboye Fulani da wata manufa tamu bane, a,a wannan umarnin Malam ne.

Kuma alokacin da muka kawota gidan nan, babu wanda yasan itace, dan tun lokacin data bace tsawon shekaru 18, har zuwa yanzu tana cikin yanayi na hauka, kuma wahala data sha ne yasa muka kasa ganeta, acikin yan kwana kin nan dayake tana samun kulawa agurin Jakadiya Safeeya, dan agurinta take zaune, tofa alokacin ne, tafara dawowa kamanninta, sbd tana samun tsafta, shine Jakadiya ta ganeta.

Bayan tafada ma Malam, yace kada tafada ma kowa, kuma yakirani yafada mun, nima yace kada infada ma kowa, dan wadan da suka aikata mata wannan laifin suna cikin masarautar mu, dole semunbi asannu zamu iya ganosu.

Ajiya mukayi waya dashi yace mun zezo gobe domin yanaso yakawo karshen halin da masarautar mu take ciki. Babban abin farin ciki tahaifi cikin dake jikinta, Allah ya azurta ta dasamun diya mace, aranar data bar gidan nan kamar yanda su Malam suka sami labari daga gurin wadan da suka tsinceta, to aranar ta haihu, kaga yanzu Yarinyar tana da shekara 18 da watanni.

Babban abinda yasa nataboka alokacin damu kaji abinda su Sarkin fada suke fada shine, kasan idan baka iya kama barawo ba, to shine zekama ka. Nadade dasanin halin da Sarkin fada yake ciki shida matar Sarki Medaki, suna aikata kazamar harka, kusan kullum agurinta yake kwana, nasamu wannan bayanin ne daga gurin daya daga cikin bayin dana sa ya kular mun da duk wani motsi na waziri.

Dan haka ayanzu base gobe ba, inaso kabani dama nasa akama Sarkin Fada da Jakadiya akullesu har zuwa gobe, idan Malam yazo se afito dasu, nasan idan aka maimaita masu laifin dasukayi, zasu tona duk abinda sukayi. Hawayen dake idanun Sarki Qaseem yagoge, saboda bakaramin kaduwa yayi dajin labarin Waziri ba.

Da ace beji abinda suka fada dazu ba, kuma ace ba waziri bane yafada mashi dabaze taba yarda da abinda aka fada ba, kallon Waziri yayi yace ayanzu bani da sauran bakin magana, da kai da Malam nabaku damar ku aiwatar da duk wani abu da yayi dede da hukuncin masarautar nan, sede abu daya nakeso, inaso akawo ma Yaya Fulaninshi yagani, kila ta silar haka yasamu sauki, banaso afadi wani abu harse yasamu sauki, dan yaji duk irin abinda mahintan makusantanmu suka aikata. Waziri yace godiya nake, bara inje insa akama su, kafin wani tunanin yashige su sugudu. Sarki Qaseem yace shikenan bara inshiga gurin Yaya kada yaji shiru.
Chapter 20 · 0% Book details