Sashe 6
A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Diyace ga malam Audu da Uwani sunkasance talakawa ne, sosai mal. Audu beda wata sana'a data wuce Caca haka Uwani muguwar masifaffiyar mata ce, dama cirani yakawosu kauyensu alakocin Nafeesa tana da shekara 15, Uwani macece mesan kudi sosai hakan yasa take dorama Nafeesa tallar gyada, duk sanda taje talla acikin tasha dakin wani saurayinta take zuwa yasiya duka yabiya bukatarshi da ita. Seda tayi ciki har so 3 suna zubarwa, kuma Uwani bata cemata komai, shikuwa mal. Audu dama babu ruwanshi dasu.
Gaba daya sun dami yan garin, ana haka wata rana mal. Audu yayi Caca aka cinyeshi beda abinda ze bada hakan yasa yaje gidan wani mutum yasato rago, yana fitowa aka kamashi, anan mutane suka haushi da duka har gidanshi, seda sukayi mashi raga raga sannan abokanan Cacarshi sukace sutashi subar gidan dasuke ciki zasu sayar sudau kudinsu.
Uwani da Nafeesa bakaramin shiga tashin hankali sukayi ba, suna zaune suka farajin hargowar mutane, Mal. Audu yana kwance ko tashi be iyayi yaji mutane sun shigo sunfara yimasu wurgi da kaya, nan take zuciyarshi ta buga ya mutu, koda mutanen suka zo gurinshi se suka samu ya mutu, anan suka fadama Uwani sukayi tafiyarsu, kuka suka saka Uwani tana fadin shikenan katafi kabarmu da tashin hankali.
Da kyar suka samu wasu daga cikin abokananshi suka yimashi wanka da sallah suka kaishi makabarta, duka basufi mutum 10 ba wadanda suka kaishi. Bayan kwana biyu da rasuwarshi Uwani tafara rashin lafiya, gashi basuda abinci bare kudin magani, haka Nafeesa tayita jinyarta, koda taje gurin saurayinta yabata kudi tasiyo mata magani korarta yayi dan alokacin ma tare da wata tagansu, haka tadawo tana ta kuka. Lokacin da akayi 7 da mutuwar mal. Audu masu siyan gida sukazo, anan suka koresu, duk inda sukaje neman temako babu me temakonsu dan babu wanda besan halin Nafeesa da uwani ba. Daga karshe suka baro garin har suka hadu da Sarki.
××××××××××
Bayan kwana 7 da rasuwar Maman Nafeesa aka daura aurenta da sarki, mutanen garin sunyi matukar mamakin aurensu, sede wasu suna cewa auren tausayi ne Sarki yayi. Duk wasu kayan aure Sarki ne yayi mata, aka gyara mata bangarenta aka hadata da bayin dazasu rika yimata hidima. Haka Sarki yasa Jakadiya takoya mata duk wasu al'adu na masarautar.
Seda Nafeesa tayi wata 1 agidan sarki Jakadiya tana gyarata sannan takaima Sarki ita, bakaramin kyau tayi ba, dan gyara akayi mata bana wasa ba, fatar jikinta kanta seda ta canza. Abubuwa da dama Jakadiya takoya mata, wanda aciki harda biyayya ga gimbiya dan tafada mata ko ita wacece kowa binta yakeyi. Haka kuma ta bata Gimbiya Suhailat agurin Nafeesa.
Aranar da Sarki ya kwana da Gimbiya Nafeesa yasameta bata da budurci ajikinta, yayi mamaki sosai, bayan sunyi sallar asuba yadawo yasameta tana kuka, zama yayi yafara tambayarta lafiya, cike da kissa tace kayi hakuri rankai dade dama nasan tunda Mama tarasu bata ida baka labarina ba, nasan dole zaka fahimci wani abu, nasan kagane banzo da budurcina ba, hakan yasamo asaline ta dalilin barayin dasuka shigo mana gida ana gobe za'a koremu daga garinmu, sune suka yimani fyde wanda shine dalilin ciwon Mamana dan Allah kayi hakuri, naso ace tunkafin adaura auren mun samu dama nayi maka bayani dako daya daga cikin bayinka kahadani dashi.
Tausayinta yakara kama Sarki yace bakomai Nafeesa, kada insake inji wannan maganar abakin kowa, kibarta tsakaninmu nayafe maki kinji, tace tonagode.
Haka zamansu yacigaba da tafiya, Sarki da kyar yasamu yashawo kan Qaseem dan tunda yayi aure yake fushi dashi. Gimbiya Shuwa da Gimbiyar Baban Gida da Gimbiya medaki kwata kwata basa shiri, shiyasa babu me shiga harkar wani, Su biyu sunware Gimbiya shuwa, basa sata acikin harkarsu, sede itama Gimbiya madaki wato Nafeesa awulakance take agurin Gimbiya babba, se abinda tace takeyi, ita kuma tana kaskantar da kanta ne, kawai dan tasamu fada agurinta, dan Gimbiya Shuwa bata kulata, sbd akidarta na tsanar wanda ba dan sarauta ba.
Sarkin Fada ne, da jakadiya zaune alambu. Sarkin Fada yace waini Jakadiya haryanzu acikin matan Sarki babu me ciki ne? Yamutsa Fuska tayi tace inaji fa Sarki beda rabon samun da aduniya, bare aje ga maganar magaji, kaga ko mutuwa yayi ai sede abama Kaninshi. Sarkin Fada yace kinko san banason Qaseem ya anshi mulki kinsan yafi Sarki mugun hali, towai meze hana muyi masu kullalla. Jakadiya tayi dariya tace lallai Sarkin fada baka da dama, aini nafison ace sunbata shida kaninshi, shiyasa lokacin dayayi fushi dashi dan zeyi aure naji dadi, sede dayake akwai kauna atsakaninsu kaga basu wani dade ba, suka shirya.
Sarkin fada yace amma Jakadiya babu wata hanya dazakibi kishiga jikin Gimbiya Shuwa? Zaro ido tayi tace ni? Rufamun asiri, kana ganin sbd tsabar jinkai irin nata haryanzu bata yarda da kowa ba, sede mijinta. kai de kawai ayi sha'ani amma ina nan ina shirya masu gadar zare kaide kawai ka tsaya kayi kallo. Matso kaji wata magana. Ko kasan cewa nice nan na hana Gimbiya Zakiyya haihuwa agidannan? Sarkin Fada yace lallai Jakadiya nasara maki. Tace uhm kawai ka kalleni kabarni akwai sauran abubuwan bam mamaki atattare dani. Kaide muje zuwa, da sannu sena tarwatsa farin cikin masarautar nan, haka nake bani da kyau, banki kowa yarasa ba, tunda har Allah yasa nazo a Jakadiya.
Muje zuwa danjin sauran labarin. Nagode da kulawarku.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]
Season 25⚜30
Masarautar BUBAYERO, babbar masarauta ce mecike da tarihi, ashekaru 18 dasuka wuce Sarki HASHEEM shine Sarki amasarautar, yana da Kani wanda suke Uwa daya Uba daya, su 2 iyayensu suka haifa, kafin iyayensu surasu mahaifinsu shine Sarkin agarin.
Sakamakon hatsarin jirgi dasukayi shida mahaifiyarsu wadda ita kadai ce matarshi kuma uwar yaranshi, shine yayi sanadiyar mutuwarsu. Bayan kwana biyu da rasuwarsu .Waziri wanda shine mahaifin wazirin sarki Qaseem, shine yatara jama,a domin anada sabon sarki, ananne aka zabi Hasheem yayan Qaseem aka nadashi Sarkin masarautar Bubayero. Kuma shima Waziri yasauka daga mukaminshi yamika ma babban danshi wato Wazirin Sarki Qaseem.
Alokacin Sarki Hasheem yanada Matarshi 1 mesuna Zakiyyah, diyace ga Sarkin Yobe, kuma abokine ga mahaifin su Qaseem, shiyasa suka hadasu auren zumunci, duk da Sarki Hasheem baya sonta haka yayi biyayya ya aureta. Mahaifiyar Zakiyya takasance su 3 ne agurin mijinsu Sarkin Yobe, amma dayake macece wadda tasan kissa da iya tuggu hakan yasa tazamo yar gaban goshi agurin mijinsu, baruwanta dabin boka ko malam, tayarda da kanta.
Hakan yasa Zakiyyah tadauki duk wasu halaye nata. Kuma da wannan halinne tajawo hankalin Sarki Hasheem har yabata babban matsayi azuciyarshi. Alokacin da aka nada mijinta Sarki bakaramin dadi taji ba, sede babbar matsalar datake damunsu haryanzu basu sami haihuwa ba, ko batan wata bata tabayiba. Sede yanda takeyima Sarki yasa baya nuna damuwarshi akan haka.
Jakadiya itace babbar baiwa datakema Sarki Hasheem hidima tunkafin yazama sarki, ita kadai yabama amana aduka bayin gidan, hakanne yasa lokacin dayahau kujerar mulki yanadata Jakadiyarshi, ko Matarshi batasan wasu sirrinkanshi ba kamar yanda Jakadiya tasani, shiyasa kwata kwata basa shiri.
Bayan kaninshi yagama karatunshi akasar misrah yadawo gida, alokacin Sarki yasa aka gyara mashi part dinshi anan cikin gidan, kuma alokacin yazo mashi da maganar matar dayakeso ya aura, Yayanshi bakaramin dadi yaji ba, dan yana son kanin nashi kamar yanda shima yakesonshi. Daya tambayeshi wacece yace mashi diyar Sarkin Misra ce, atare sukayi karatu.
Babu bata lokaci yasa waziri yashirya masu tafi sukaje neman auranta, koda sukaje sunsami tarba me kyau, kuma anan take aka bama Qaseem auran Gimbiya Suhailat, Bayan sundawo aka fara shirin biki.
Sati 1 akasa yanazuwa akaje akadaura aurensu, suka taho Gombe, sede Sarki Hasheem yace base anbasu bayi ba suna da isassun bayi, haka aka kawo amarya akasata part dinta. Tunda suka hadu da Gimbiya Zakiyya taji ta tsaneta, hakan yasa bata sakan mata fuska, kowa yanaji da kanshi, ita Zakiyyah tana ganin ita diyar Sarki ce, kuma matar Sarki, hakan yasa mulkin yayi mata yawa. Ita kuma Suhailat tana ganin masarautarsu tafi tasu Zakiyyah.
Bayan kwana 2 Sarki yasa Jakadiya tadebi bayi masu yawa takaima Gimbiya Suhailat tazabi wanda takeso, bayan tazaba Jakadiya tace tazabi amintattar baiwa acikinsu, wani kallo tamata tace aini bana zabar amintattiyar baiwa alokaci guda, dan haka ki kama gabanki idan ina bukatar hakan basekin fadamun ba. Jakadiya taji zafin maganar haka tajuya tawuce ranta abace, sede dayake ta iya duniyanci bata nuna mata afuska ba. Tsaki Gimbya taja, dan ita duk wanda befito daga gidan sarauta ba gani take beda wani matsayi, shiyasa ra'ayinsu da mijinta yazo daya, dan shima sarauta tashiga jikinshi dayawa yana bata muhimmanci.
Sarki Hasheem yakasance mutum ne mesaukin kai sosai, sede shima yana daraja sarautarsu sosai, kuma baya son kai acikin masarautarshi, duk wanda ya aikata laifi ana yanke mashi hukunci dede dashi.
Dalilin aurenshi da matarshi ta 2 kuwa yasamo asaline, wata rana yafita rangadi shida Waziri da Kaninshi da fadawa, sunzo wajen gari nesa da cikin gari, se suka hadu dawasu bayin Allah agefen hanya uwa da diyarta, yarinyar bazata wuce shekaru 17 ba, tana zaune kusa da uwar tana ta kuka. Tsayawa sarki yasa akayi yasa aka kirawosu, sede yarinyarce kawai tazo dan matar tana cikin halin rashin lafiya bazata iya tashi ba. Tanazuwa tafadi kasa, Waziri yatambayeta meyasa suke zaune anan haka?.
Tana kuka bata basu amsa ba, Qaseem ya daka mata tsawa yace waike ba magana ake makiba kin tsaida mutane, Kallonshi Sarki yayi dan yasan abinda kaninnashi ya tsana kenan, murmushi yayi yamaida kallonshi kan yarinyar. Ihun matar dasukajine yasa babu shiri Sarki da Waziri da sauran fadawa suka sauka daga dokinsu suka nufi gurinta, yarinyar tarigasu zuwa gurinta.
Jinine yake fita daga hancinta da bakinta, haka tarike hannun yarta hawaye suna fita daga idonta, akusa da ita Sarki ya tsugunna, fuskarshi cike da damuwa, yayi bakin cikin dabasu fito da mota ba, kallon Waziri yayi yace yazamuyi da ita, yakamata akaita asibiti. Hannun matar yaji takamo babbar rigarshi, dasauri fadawa suka matso dansu cire, amma yadakatar dasu. Kara dukawa yayi yace baiwar Allah kibari mukaiki asibiti kina zubar da jini.