← Book details A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 33

Sashe 16

A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda muka fara tambayarta bata bamu amsa ba, sede kuma tanajin abinda muke fada, shine daga karshe tajawo ni muka taho nan. Ajiyar zuciya Jakadiya tayi jin bayanin da Areef yayi mata. Murmushi tayi tace Allah sarki sannunku nagode sosai, inbadanku ba kila data halaka, mantawa nayi ban kulle kofar ba, kuma nasan nitafito nema dan banyi mata sallama ba dazantafi.

Shirun dakaji tayi ai bata iya magana, tunda aka haifeta ahaka take, sede tanajin duk abinda aka fada. Tausayinta ne yakamasu, jikinsu duk yayi sanyi bakamar Haisam. Areef yadaga baki zeyi magana kenan tafito, baki yasaki yana kallonta, gani yake kamar ba ita bace, tasaka riga doguwa me siririn hannu tayi mata kyau sosai, kalarta Ja ce, gashi bata daura dankwali ba, fuskarta tasha kwalliya kamar meshirin zuwa gasar kyau, hannunta rike da comb, tana zuwa tafada jikin jakadiya ta mika mata comb din.

Murmushi tayi tace Uhm Yar Baba sarkin kwalliya yanzu seda kika kara wata kwalliyar? Kwantawa tayi jikinta takamo hannunta tadorashi akan wuyanta, jakadiya tace kai naji jikinki dazafi, ko ruwan dakika shiga ne, ze sakar maki Zazzabi?.

Kai tadaga mata, tana lumshe ido, Haisam yace Aunty ai dama yakamata abata magani tasha, kada yarufeta. Jawo hannunta takarayi tana mata nuni data sharce mata gashinta, fara Sharce mata tayi tana fadin kuma gashi babu magani agidan nan, sede inje gurin Gimbiya kozan samu.

Haisam yace a,a bari kawai idan muka fita semu siyo mata, kallon Areef yayi yace kai kuma mr. Watching seka tashi mutafi musiyo magani, shiru yayi mashi yana kallon yanda tarufe ido tana bacci, ga gashinta daya gama tafiya dashi. Dan bakinta yasha red janbaki, tayi mashi kyau sosai. Dukan dayaji akafadarshi ne yamaido dashi tunanin dayakeyi.

Hararar Haisam yayi, gwalo yayi mashi yana murmushi. Areef yace Aunty amma bansanki da diya ba ina kika samota? Tace tare muka dawo da ita daga Darazo, acan gidan Malam take, diyar Dan uwanmu ce. Zekara magana Haisam yace katashi muje musamo mata magani bata lafiya, idan mundawo seka idasa tambayar taka. Tashi yayi yana sosa kai yana murmushi yace Aunty semun dawo.

Kallonshi tayi tace dan Allah banason inji wannan maganar agurin kowa, koda kuwa Gimbiya ce, ko Sarki, kuje kudawo zakuji dalilina nafadar haka. Suka ce to, fita sukayi Areef yanayi yana waige, bugewar dayayi da kofa ce tasashi saurin dafe goshin shi. Dariya Haisam yasa hada rike ciki, suna fita Areef yakai mashi duka yana kara dafe goshin shi. Haisam ya tsagaita dariyarshi yana fadin sannu abokina ai bansan kaji zafi ba. Areef yace kacigaba lokacinka ne dariya ma yanzu kafara yimani inde akan beauty ne. Haisam yazaro ido yace akwai wata a kasa kenan? Areef yayi murmushi yace a,a sede asama dan iska. Dariya suka saka kafin suka nufi hanyar parking space.

Cak sarkin fada yatsaya ganin abinda beyi tsammani ba, adede lokacin dayake fitowa daga part din Medaki, daka ganshi kasan baya cikin nutsuwarshi. Wani irin kallo Waziri yake binshi dashi, cikin tsarguwa Sarkin fada ya matso yana washe baki yace rankaidade barka da fitowa, nima yanzu nafito zani fada shine Jakadiya Karima take shedamun Gimbiya Medaki tana nemana. Toyanzu nashiga ko minti 3 ma banyi ba, tambayta tayi shine kaga nafito. Muje fadar ai can kayi ko? .

Da ido Waziri ya kafeshi, bece mashi komai ba, kifce kifce yafarayi yana fadin ai semu wuce ko? Murmushi Waziri yayi ya girgiza kai yace muje, haka suka nufi fada cikin Sarkin fada duk ya duru ruwa, se addu,a yake Allah yasa Waziri be harbo jirginshi ba.

Baban Fulani ne zaune akofar gidanshi tare da Baba suna ta fira, dan zaman dayayi bakaramin sabo sukayi ba, Baba yace gaskiya ina tausaya maka halin daka shiga, tabbas ka hadu da jarabawa, sede kuma hakurin dakayi gashi nan Allah yabarka da lafiyarka, kuma dama anason me hkr aduk lokacin da wata jarabawa tasameshi. Baban Fulani yace hakane, nima ada nayi niyar komawa kasata, sede ganin irin karamcin da mutanen nan sukayi mani da kuma rashin sanin Rayhana tana raye ko mace, wannan dalilin shine babban abinda yahanani tafiya, amma insha Allahu nasan za,a ganta tunda de anfada mana tana raye. Baba yace ai Allah baya bacci, koma a ina take wata rana zata dawo.

Koda su Areef suka koma jikin Yar Baba yarikice, Zazzabi ya saukar mata sosai, dan bata tabayin zazzabi mezafinshi ba, se kuka takeyi dama kuma gata raguwa, kwance take ajikin Jakadiya Safeeya suka shigo bakinsu dauke da sallama, dasauri Areef yazauna kusa da Jakadiya yana fadin Aunty bade jikin bane?.

Tace wlh kuwa, tunda kuka fita ta kwanta shikenan zazzabi yarufeta, Haisam yace Aunty kawai kutashi mutafi asibiti, zaro ido tayi tace A,a kawai ku kawo maganin inbata nasan zata samu sauki, kaga abincinma taki ci. Zata kara magana kenan taji motsi adakin Maman Yar Baba, saurin tashi tayi ta kwantar da ita bisa kujera tace inazuwa bari inshiga bandaki, Yarima kabata abinci kila taci seku bata maganin nasan zata samu bacci, bari infito.

Abakin kofa tasameta, dama tasan lokacin cin abincinta yayi jira take Yar Baba ta kyaleta taje ta tadata tabata abinci tasha maganinta, saurin kama hannunta tayi tasama kofar key suka koma ciki, bandaki tajata seda ta wanke mata baki tayi fitsari, sannan suka dawo tazauna dan tabata abinci.

Abincin yadauka ya matsa kusa da ita, hannu yasa yadagota, tana tashi ta lafe ajikinshi, zama yayi akan kujerar, hakan yasa takara shigewa jikinshi. Dariya Haisam yayi yazauna yana fadin wlh Beautyn Areef keda mage bansan wanda yafi wani son jiki ba, Areef yace kaga malam kabarta taci abinci tunda ba,a jikinka ta kwanta ba. Haisam yace ato adebi ahankali dan wlh kosannu bazan cemaka ba idan kacemun,,,,,,, gira yadaga mashi yana murmushi yace ai kagane?.

Areef yace kaide kasani dan iska kawai, kamata yayi ya rungumeta ahankali yace kinajina ko beauty? Kai tadaga mashi tana turo baki, murmushi yayi yace yauwa idan bakiso inkira mutane sukamaki to kici abinci inbaki magani zaki warke, ai dajin haka tabude baki. Dariya Haisam yayi yace anya beauty bata tsoron mutane kuwa? Wannan shine karo na biyu danaga tana tsoro idan ance mutane. Areef yace haka ne, nima nalura da haka, kuma inaso Aunty tafito tadan bani labarinta, dan ban gamsu da bayaninta nadazu ba, yarinyar nan tafi kama da diyan larabawa.

Haisam yace shiyasa naga kuna dan kama , harararshi yayi yace ta ina? Haisam yace wlh ba batun wasa ba, dazu data kulle idonta na kalleta naga kundanyi kama, musamman tagurin idanunku da bakinku. Areef yace kaji dashi, nibanga wata kama ba, kyaleshi yayi yadauki cokali yafara bata abinci.

Hankalinshi gaba daya yana gurin kallon yanda take cin abincinta, shikanshi abun burgewa ne, tana jikinshi ahaka tagama cin abincin, shiko Haisam kallonsu kawai yakeyi, yafiddo waya yana daukarsu vedio, sun bala,in burgeshi, gani yake kamar atare aka halicce su. Magani ya ballo sede da kyar tasha, shima seda yayi mata wayo, tana gamasha ta koma jikinshi ta kwanta, kallonta yayi yace bacci zakiyi? Kai tadaga mashi, tare da lumshe ido, ko minti 5 ba,ayi ba. Bacci yadauketa. Areef yace beauty bakida matsala, yarinya cekace jaririya acikin minti 5 harkinyi bacci.

Bayan tagama bata abinci tabata magungunanta, sannan tajata zuwa bandaki, wanka tayi mata, bayan sunfito tagoge mata jiki, ta dauko wata doguwar riga tasa mata, kwantar da ita tayi bisa gado. Idanu ta kura mata ganin yanda dan kwanakin dasukayi tasake sosai, kara kallonta tayi, gabanta taji yana bugawa dasauri, matsawa tayi kusa da ita dan takara tabbatar da abinda tagani. Tabbas wannan matar zargin malam yazama gaskiya, wasu hawayen farin ciki ne, suka rika fito mata, zama tayi takama hannunta tana fadin ita ce, wlh itace, dama nasan malam baze taba fadin abu yazama ba haka ba, aiko ayau Sarki zeji labari medadi.

Waya tadauko takira Malam, bayan sungaisa, yace Safeeya yanajiki cikin farin ciki haka? Wlh malam tunaninka yazama gsky, dama kace kana tunanin wannan matar kamar Gimbiya Fulani, wlh, itace, nadade dafara tunanin haka tun akan diyarta, kamarsu da ita nake gani afuskarta, sede bakowane ze gane hakan ba, amma nide wlh yanda nasan Fulani kamarta bazata iya bacemun ba.

Hamdala Malam yayi yace nadade da tunnin haka, sede kinsan irin wannan al,amarin ba,a saurin yanke mashi hukunci, dole muyi ma Allah godiya, kuma zansa ayi sadaka, sede akwai abu daya danakeso daga gareki, wannan maganar daga ni seke se Waziri mukasanta, shima yanzu zankirashi infada mashi zarginmu yazama gaskiya, ammafa dole muyi shiru da bakinmu, kinsan idan har baka iya kama barawo ba, toshi seya kamaka, acikin gidan sarautar nan, akwai munafukai dayawa, idan bamubi asannu ba, bazamu iya kamasu ba.

Dan haka nasan haryanzu babu wanda yasan dazamansu agurinki, inaso kicigaba da rike sirrinmu, har ranar da Allah zebama Gimbiya lfy, bincikenmu zefi tafiya dede. Shiru tayi can kuma tace amma malam akwai mutum 2 dasuka san Yar Baba tana gurina, Yarima da abokinshi, yanzu haka suna gidan nan,,,,,,,,, kwashe duk abinda yafaru tayi tafada mashi, malam yace babu damuwa inaso kibarshi ayanda kika fada masu, sede kada kibari suga Gimbiya tunda dama kince bata fitowa falo,sallama yayi mata yace zekira Waziri.

Falo tafita ta iske su zaune, murmushi tayi tace kuyi hakuri nabarku dajira. Areef yace bakomai, hartayi bacci ma, Jakadiya tace kwantar da ita muje nima fita zanyi nasan gimbiya tana jirana, Areef yace a,a muje inkaita daki ahaka ai seta fado. Daukarta yayi kamar baby ya nufi dakin jakadiya, saman gado yadorata, juyi tayi takara rungumoshi, harseda yafada mata. Wani yarrr yaji ajikinshi, murmushi yayi yacire hannunta yajawo pillow yasa mata, nan take tarungumeshi, tsayawa yayi yana kallonta, dukawa yayi ya sumbaci goshinta, tare da fadin Allah kasa Momy da Abba sukarbi zabina. Juyawa yayi yafita.

Bayan malam yakira Waziri sundade suna magana, bakaramin dadi Waziri yajiba dayaji bayanin malam, haka suka dade suna tattaunawa, daga karshe Waziri yace akwai wani sirri dana fara ganowa agidan nan amma inaso inkara tabbatar dashi kafin infada maka. Malam yace Allah yayi mana jagora, insha Allah komai yakusa zuwa karshe, zan aiko da maganin me martaba. Godiya Waziri yayi mashi sukayi sallama.
Chapter 16 · 0% Book details