Sashe 1
A Makabarta Aka Haifeni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]
Bismillahir Rahmanirrahim, inafarawa da sunan Allah megirma da daukaka. Yanda zanfara rubutun nan lafiya Allah yabani ikon kammalashi lfy.
GARGADI..... Banyarda wani ko wata su juyamun littafi naba, ko kuma su canzamun labarina. Allah yabada ikon kiyayewa.
GODIYA.....Ina mika godiya ta ga dukkanin masoyana wadanda nasani dama wadan da bansani ba, nagode da irin kaunar da kuke mani, duk da bazan samu damar binku inyi maku godiya ba, amma nayi amfani da wannan dama ga duk wanda yakaranta yazama amatsayin sakon gaisuwa zuwa gareshi. Allah yakara dankon zumunci.
Season 1⚜5
Babban mutum ne, kuma kyakkyawan dattijo wanda akalla baze wuce shekaru 50 aduniya ba, acikin keken guragu aka turoshi wanda da alama yana fama da mutuwar shanyewar barin jiki, daga dakin gashi aka fito dashi bayan angama gasa mashi jikinshi, wanda ake masa duk bayan kwana 3.
Sarki Qaseem ne yashigo dakin wanda yakasance kanine ga dattijon dayake bisa kujera. Sannu Yaya yakarfin jikin? Kwalla ce tacika idonshi, wadda tariga da tazamar mashi sabo aduk lokacin dazeyi magana, Babban bawan dayake kusa dashi wanda yazama shine hadiminshi yasaka kyalle yayi saurin goge mashi idonshi.
Hannu Sarki Qaseem yadaga, nan take kowa yabar dakin. Zama yayi kusa dashi yadafa kafarshi, fuskarshi cike da damuwa, yace Yaya dan Allah kayi hkr, yakamata ace zuwa yanzu kayi hkr da abinda yafaru shekaru 18 dasuka wuce. Akullum semunsa manyan malamai sunyi addu,a akan damuwar datake cikin masarautar nan. Kuma kasan ba,a fidda rai da rahamar Ubangiji. Murmushi yayi tare da girgiza kai, yana kallon kaninnashi, wanda yake so sosai, kasancewar shikadai gareshi kuma Uwa daya Uba daya suke.
Sarki Qaseem shima murmushin yayi ganin Yayanshi yanayi, yace tabbas Yaya yau naji dadin ganin murmushi afuskarka, wanda rabon dakayi hakan tunkafin karasa farincikinka. Segashi yau kayimun murmushi.
Dariya ce tafito daga cikin dakin, wanda wasu manyan mata ne, zaune acikinshi. Daya daga ciki tace, ai wlh Medaki kema kinsan bazan taba barin aci mana fuska acikin gidan sarauta ba, kamar yanda kikazo kika sameni acikin gidan nan shekarata nawa kika sani muna tare da Memartaba, kuma nayi hkrn zama dashi, harkikazo kika sameni, kekanki dabakiyi biyayya ba, ai da tuni nayankar maki Ticket nabarin duniyar baki daya.
Dariya Medaki tayi tace haba Gimbiyar Babbar Gida, aini kinganni nan, tunda nataso haka Allah yayi ni, bandamu dasena zama babba ba, inde zanzama 'yar kore kuma inkarbu toni banida damuwa, zan iya yinkoma menene. Dan haka kada kidamu, koda yanzu bamune matan sarki Qaseem ba, aide kanin mijin mune. Kuma aide haryanzu muna cikin masarautar.
Gimbiyar Babbar Gida tadauki apple tasa abakinta, ta maida kallonta gurin Jakadiya, wadda take mata tausa tace, Jakadiya bamu labarin cikin gida. Jakadiya ta gyara zama tace Allah yatemakeki Babbar Gimbiya, wadda babu kamarta, ba,ayi ba, kuma baza,a tabayin kamarki acikin gidan nan ba. Allah yakara tsawon kwana. Babu wani labarin daze firgitaki acikin gida, kinriga dakinsan Gimbiya Shuwa haryanzu bata yarda dani ba. Narasa dalilinta nayin haka, ace mace duk wani hali irin na mijinta Sarki Qaseem tadaukeshi. Kodan ita tata sarautar gado ce, shiyasa bata yarda da kowa? Medaki tace haba Jakadiya atunanina babu wani abu daze baki tsoro acikin masarautar nan, kinsan ketamu ce, muma haka. Dariya tayi tace hakane, Gimbiya, karku damu asannu zakusha labari.
Zaune take cikin wasu kodaddun kaya, acikin wata bukka ta kara, wadda take daga gefen wata tsohuwar MAKABARTA. Wani tsohon kwanone ahannunta,abinci ne, aciki wanda gaba dayanshi bewuce rabin kwanonba. Kyakkyawar matashiyace wadda bazata wuce shekaru 18 aduniya ba. Akusa da ita wata dattijuwa ce, wadda itama bazata wuce shekaru 38 aduniya ba, da kaganta zakasan tana cikin yanayi na hauka, gaba daya kamanninta sun bata. Jawota diyarta tayi tana mata magana irin ta kurame, tana mata nuni da kwano alamun taci abinci.
Dariya Uwar tayi cikin halin hauka tace a,a Babyta yau bazanci abinci ba, kece zaki faraci, dariya yarinyar tayi mata, dan taji abinda tafada, sede kawai maidawa ne bata iyayi (KOMEYE DALILI🤔 OHO🤷🏻♀ MUJE ZUWA). Matsawa Wadda naji ankira da Baby tayi kusa da Mamanta tasa hannu tafara bata abincin, itama hannu tasa tana bata abinci. Kwalla ne, suka zubo ma baby tayi saurin gogewa.
Wani Kyakkyawan Matashi ne, me kama da Larabawan Shuwa, baze wuce shekaru 25 aduniya ba, da Sallama yashiga dakin kyakkyawar matar, wacce take kishingide abisa kafet din dakin. Murmushi tayi tace, Yarima Arif sannu dazuwa. Kwanciya yayi kusa da ita yace yauwa Momy na, sannu da hutawa. Kallon bayin cikin dakin tayi, lokaci guda suka fita, Madarar shanu tamiko mashi, ya amsa yana murmushi, yace Momy naje gurin Abba ance yana dakin ganawa da baki, kuma inason magana dashi. Kanshi tashafa tace to ai sekayi hkr kajira yagama ko, wace irin magana kakeson yidashi? Momy dama akan rashin lafiyar Baffa ne,tunda nadawo naga yakamata ace anfitar dashi waje ko za,a dace. Murmushi tayi tace Arif bakasan komai akan ciwon Yaya ba, Abbanka yana kokari sosai amma koma menene idan yafito zamu gana dashi. Kwallan idonta tagoge.
Kubiyoni domin jin labarin masarautar.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ...🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
[email protected]
Season 5⚜10
Zaune suke adakin memartaba sarki Qaseem, Areef yadora kanshi asaman kafar Abbanshi, Gimbiya Shuwa Momyn Areef tana kusa da Sarki tana gyara mashi Inibi tana mika mashi. Sarki yashafi kan Areef yace Yarima inajinka wace magana kakeson kafadamun?
Tashi zaune Areef yayi yadauki inibi yasa abakinshi yace Abba dama akan maganar Baffa ne, naga yanda nabarshi haka nadawo nasameshi, shine nace meze hana afitar dashi waje koza,a dace. Murmushi Sarki yayi yace wlh Yarima nafika son inga Yaya yawarke, kozamu samu damar yin bincike akan babbar matsalar datayi sanadiyar shigarshi wannan halin. To amma Abba baka ganin fitar dashi ze iya temakawa gurin samuwar lfyrshi tunda acan sunfimu kayan aiki?
Hakane Yarima, amma babu yanda banyi da Yaya akan yabari afitar dashi ba, yakiya gashi ba magana yakeyi ba, sede yana jin duk abinda muke fada, yana ganin kamar gara abarshi yayi tazama haka, wanda kuma hakan bashine mafita ba, dole se mutum yana da lfy yake iya komai arayuwarshi, ni babban damuwata wadancan munafukan matan nashi, danni wlh haryanzu banyarda dasu ba. Gimbiya tace hakane Me martaba, sede kasan bamuda wata hujjar dazata nuna mana sune sanadiyar faruwar komai agidan nan, kamarde yanda kace acigaba da addu,a hakan zamuyi, fatanmu de Allah yasa Fulani da abinda ke cikinta koma menene, yasa suna raye, kuma cikin koshin lafiya.
Sarki yace amin. Kallon Areef yayi yace Yarima yanzu angama karatu gashi zaka fara aiki kaga dole ace kaima kashigo sahun manya ko? Kwantar da kanshi yayi saman cinyar Gimbiya ya lumshe idonshi, shiru yayi bece komai ba. Gimbiya tace Yarima yanaji kayi shiru kode boye mana surikar tamu kakeyi? Murmushi yayi sosai wanda har seda dimple dinshi ya lotsa duka 2, yace Momy kubar maganar nan, niharyanzu banga macen danakeso ba. Sarki yace aiko Yarima yakamata ace kafara nemanta, dan kasan bazamu barka kazauna haka ba, atsarin masarautar nan kasan baza,a barka kazauna haka ba, damma de Yaya beda lafiya, ai da tunkafin kadawo anduba maka acikin 'ya'yan sauran masarautun ansama maka mata.
Dariya Areef yayi yace haba Abba niko aure zanyi ai banason yar gidan sarauta, nafison insamu mace wadda bata tashi acikin sarauta ba, kuma nibanason mace wadda zatazo tarika rainamun iyaye, kawaide akaramun lokaci ahankali zansamo wata wadda ra,ayina yayi dede da ita.
Harararshi Gimbiya da Sarki sukayi atare, Sarki yace uhm Yarima idanma mafarki kakeyi to kadena, acikin masarautar nan babu yanda za,ayi kashigo mana da bare, dole se yar sarauta, kana ganin yanda Momynka dani kaina muka fito daga gidan sarauta, jininmu gaba da baya cike yake da sarauta, kai kuma yanzu sekafara zuwa mana da wani batu. Ka godema Allah Yaya beda lfy, da kila seyafini daukar zafi akan wannan magana taka.
Duk da shima matar daya aura ta 2 data 3 basu fito daga cikin gidan sarauta ba, amma kowa yayi mashi uzuri, matarshi ta 2, agidan nan kowa yasan yanda akayi ya aureta, haka ma ta 3 dole ce tasashi ya aureta, sekuma babban rabon daya shiga tsakaninsu, bayan wannan babu abinda zesa Yaya ya auri wata mata wadda ba,a gidan sarauta ta taso ba.
Gimbiya tace Allah yahuci ranka Me martaba, banason ranka yana baci akan wannan maganar, abinda bamu taba yima Yarima agidannan ba, Fada shine yau da bakinka kake mashi, kaima kasan Yarima mebin duk wani umarninmu ne, ai base anbata mashi rai ba, sekasashi shiga damuwa, wanda kuma betaso acikinta ba, karka manta mungina rayuwarmu abisa soyayya dan Allah kada kabari zafin zuciya yacanza maka zuciyarka. Sarki yakamo Areef wanda idonshi har yayi ja dan bacin rai.
Kwantar dashi yayi saman kafarshi yana shafa kanshi yace ba ina nufin bata maka rai bane, kaji, kawai ina maka tuni da ra,ayin masarautarmu ne, banaso kasa wannan aranka haryadameka. Hawayene suka zubo daga idon Areef, cike da damuwa Gimbiya tamatso kusa dashi tace kagani ko, kalli abinda kajawo mashi, yaushe rabon da Yarima yayi kuka agidan nan? Inajin tun yana yaro, jawoshi tayi tamaidashi saman kafarta tace Ya isa haka Yarima na, kasan Abbanka yana sonka baya son bacin ranka yishiru hakanan.Sarki yace ya isa haka maganar tawuce kaji, amma kaima kaje kayi tunani.
Lumshe ido Areef yayi, aranshi yana fadin akwai babban aiki agabana, kuma gaskiya yanda ra,ayina yake bazan taba canzashi ba, bana bukatar yar sarauta, duk da haryanzu bansamu wadda nakeso ba, amma zantajira seranan dana samu sannan, nasan suna sona, dole zasu barni na auri ra,ayina. Amma dole nacirema su Momy wannan ra,ayin nasu.
Anesa da masarautar Sarki Qaseem, wani dankaramin gidane, me kyau, duk da karami ne, amma anyi mashi gini mekyan fasali. wani tsoho ne, fari, yafito daga cikin gidan, daka ganshi zaka gane ba asalin bahaushe bane, yafi kama da irin larabawan dasuka baro garinsu sukazo nigeria har zama yakamasu anan, zama yayi bisa wata kujera dake kofar gidanshi ya kunna redio yana kokarin kamo tasha.