Sashe 8
Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sweety Ina kika shige Ina ta Kiran phone dinki bata shiga, why meya yake faruwa ne"?
"Wallahi matsala aka samu,kasan bazan kashe wayata ba har tsawon kwana hudu,ni kaina duk na damu Ina so inji muryan ka amma ba hali yanzuma wayan Baba Auwal ce na amso duk dan na kiraka".
"Cikin jin haushi ya ce "waye ya anshe wayar taki"?
Shiru ta danyi kafin ta ce "sweety ba fa anshewa aka yi ba,ta lalace ne amma da Dady ya dawo da ga tafiyan da yayi zai siyaman sabuwa".Dan ita har ga Allah a zuciyar ta ta ji ba zata iya fadamai zalimu ne ya anshe mata waya ba,saboda duk da tana San Hasan bata jin dadin yadda yake kushe mata dan uwa,dan ko ba komai Yaya Yasir jininta ne bata da yadda zata yi da shi. (Kai Farrah kodai-kodai kina........🤣🤣ehmmm bari dai inyi shiru kar Jabir ya ji ni 🤭.)
"Ok ai nayi tinanin wannan yayan naki ne ya anshe ta". Amma kina ji na?
"Eh ina jinka sweety na"
"Gobe zan zo in kawo maki sabuwa sai ki dora layin ki,dan kinsan ban jin dadi idan ban ji muryar ji ba".
Hmmm murmushi tayi sosai dan tasan halin rigimar shi."kasan ya za'ayi"?
"A a saikin fada"
"Ka bari basai kar Kawoman waya ba,saboda zan fuskanci matsala idan aka ganni da wata,idan har ba su suka saiman ba,Amma Insha Allah zan rinka aron wannan muna waya kamin su bani wata ka ji ko sweetyna,karka damu ni nasan ba mai rabamu insah Allah"ta karasa fada tana turo karamin bakinta kaman tana gaban shi.
Ajiyar zuciya yayi yana dunkule hannunshi kaman zai naushi wani abu.
"Ba matsala sweetyna na yarda da ke , saboda nasan kina so na".
Daga nan suka ci gaba da firar su irin ta masoya,har sai da ta kwantar mai da hankali kamin suka yi sallama.
Sai yanzu taga dadewar da suka yi suna wayar kusan awa biyu suka shafe.Baba Auwal ta mayar wa da wayar shi ta nufi cikin gidan,Allah ya taimake ta ba Wanda ya ganta momy tana site dinta Nusaiba ko tana makaranta.
***************
Duk cikin week dinnan haka al'amura suka yi ta tafiya.inda a bangaran Farrah duk basu yi mata dadi,sai dai godiyar Allah.
Suna zaune a Falo ita da Momy a yammacin ranar juma'a hira suke yi sosai,inda Momy take Kara yimata nasiha akan al'amuran zamani tare da bata shawarwari a gameda 'al'amuran samarin wannan zamanin.Nasihar tana shigarta sosai dan sai yanzu take gane illar da Yaya Yasir yayi kokarin yimata a shekarun baya,Wanda har zuwa wannan lokacin ba Wanda ya sa ni,Daga ita sai shi,sai Kuma Allah.
Sosai ta lula duniyar tunani,inda kunnuwan ta suka daina jin Nasihar da Momy take yimata.
Momy lura tayi kamar hankalin ta baya wurin,ta dan girgiza ta da hannu.
"Farrah tunanin me kike yi haka kinyi shiru"?
Firgigit tayi alamar bata cikin nutsuwa.
"Ah ehm Momy ina jinki"ta na Yan kame -kame alamar rashin askiya.
Momy tsayawa tayi tana kallanta ba tare da ta ce komai ba,har tatsawon wasu mintina.l
"Farrah akwai abinda yake damunki,amma tunda bakya san ki sanar da ni ba komai,Amma ki sa ni ni dai a matsayin diya kike a wajena,kuma Ina iya bakin kokari na dan ganin na nusar dake daga hatsarin dake cikin wannan zamanin".
"Ba komai momy,Ina jin dadin zama da ke,dan ko Aunty bata yiman irin nasihar da kike yiman,nagode Allah ya saka da alkhairi.kuma insha Allah idan Ina da matsala zan sanar maki,duk da yanzu akwai abinda yake damuna amma na barwa zuciya ta"ta karasa fada tana mai rungume Momy ta kwantar da kanta bisa kafadar ta.
"Ba komai Farrah ki ci gaba da addu'a komai zai daidai ta insha Allah".
Sunyi shiru na dan tsawon wani lokaci,sai Farrah da take ta sauke ajiyar zuciya.
Sai daga bisani ta kalli Momy tana ce wa"Dan Allah idan ya zo yau ki amsoman key din mota ta,saboda wannan Monday din hutun mu yake karewa".
"Tau karki damu insha Allah zan amso maki".
"Tau Allah yarda,bari na je na kwanta Ina jin gajiya"ta na mikewa tsaye.
"Kada kiyi bacci yanzu,kinga yammaci ne ba'a son baccin yammaci".
Ta amsa da "To" tana shigewa bedroom dinta.
* * ** *** ** ****
Cikin ikon Allah Yasir a wannan ranar ya shigo katsin,sai karfe 8:00 daidai Baba mai gadi ya budema shi gate ya danno hancin motar sa.yana mai cike da farin ciki,Yana fitowa site din Momy ya nufa.Fitowar ta kenan daga kiching hannunta rike da cup tana juya coppe da sporn ,Tana kallan shi ta wuciyar idanun ta ta yi fiska da sauri ta shige bedroom dinta ta sanya key da sauri dan tasan ba wuya ya biyota.Tana sauke ajiyar zuciya ta ce"Dan kwawa duk weekend sai ya zo,duk kudin salaryn shi anan suke karewa dan rashi aikin yi irin na shi.
Haushi ya ji ya kama shi,juyawa yayi cike da jarumta ya koma part din shi.Wayar Momy ya Kira tana daga wa bayan sun gaisa ya ce"Momy yunwa nake ji,Dan Allah kiba Beby abinci ta Kawoman"
"Tau gatanan,Kuma ka bata key din motar ta da ka amsa".
"Tau Momy zan bata"
Dakin Farrah ta nufa,tana murda kofan ta ji shi a rufe.knocking ta yi.
"Farrah ta ce "waye"
"Ni ce bude kofar Farrah meye kika rufe kofa"?
A hankali ta bude duk da ta ji muryar Momy,Amma a tsorace take.
Tana budewa Momy ta ce"ki zo yanzu za ki kaima yayan ki abincin sa Yana part din shi,daga nan zai baki key din ki".
Ita dai sororo ta yi,saboda yadda ta ji kirjin ta ya amsa.ta rasa abinyi ta ce "Momy ganinan zuwa".
Momy juyawa tayi ta koma kiching din dan shirya abincin a babbabn faranti.ita kuwa farrah tunani take yi ta je ko Kuma ta ki zuwa,har ga Allah tana so ta amso key dinta Kuma Bata iya yiwa Momy gardama.
_*To* *readers ku bata*_ *_shawara, shinya zata yi_* *?* *_Ta je ko kuwa_* 🤣🤣😜😜
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
~DAGA~ ~ALKALAMIN~ ~AUTAH~ .
*PLEASE* *COMMENT* *AND* *SHARE* 👏.
[3/1, 6:29 AM] Hayat: ________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA_ _YANMATA_ )
*NA*
*RUKAYYA* *IDRIS* *BALAH*
*(AUTAH)*
Wannan littafin kirkirarran labari ne Banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba.Nayi ne Dan fadakar wa, ilimantarwa,tare da nishadantar wa,idan yayi daidai da rayuwar ka/ki to arashi ne.
```GODIYA```
INA GODIYA GA ALLAH UBANGIJI (S W T) DA YA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTAFI,ALLAH KARA DADIN TSIRA GA SHUGABAN MU ANNABI MUHAMMAD (S A W) TARE DA ALAYEN SA DA SAHABBAN SA AMEN.
*GARGADI*
BAN YARDA BA KUMA BAN AMINCE BA WANI KO WATA YA JUYAMAN LABARI TA KOWACE CIGA BA TARE DA AMINCE WA TA BA A KIYAYE.
*SADAUKARWA*
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GA MAHAIFI NA, ALLAH UBANGIJI YAYIMA RAHAMA YASA MUTUWA HUTU CE A GAREKA DA SAURAN AL'UMMAR MUSULMI AMEN.
*NOT* *EDITING* 🤗
BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM
🅿️12
📝Bayan rabuwar su derect Barhim ya koma,tunda ya je yana part din shi dan yayi ma kanshi alkawarin bazai Kara shiga site din ba sai idan zai koma Abuja abinci ma ya rinka zuwa restaurant ya siyo .
Momy bayan sun karayin waya da Ummahn su Jabir ta ce tayi hakuri ba sai ta maido Farrah ba saboda ta fadama Abban su matsalar da ke faruwa akan haka suka bar maganar,Dakin Farrah ta nufa dan ganin lafiyar ta dan tasan halin ta Sarai tana iya ta zama da yunwa.Tana tura kofar dakin ta hango ta a Kan prayer mat ta kudundu ne cikin hijaf kanta a tsakanin cinyoyin ta,cikin sauri Momy ta karasa wurin dago kanta tayi tana ce wa "Farrah me yake San ya same ki ne eyeh? Ok tau idan na fahimce ki abida ya faru ne yasa kike so ki saka Kan ki a cikin damuwa ko?taso mu je"ta mikar da ita tsaye suka nufi wurin danning,tea ta fara hada mata mai kauri ta sha kafin ta zuba mata jolop din makaroni da ya ji danyun kayan miya da kifi.sosai ta ci saboda daman yunwa na addabar ta kawai bacin ran da zalimu ya saka ta shi ya hanata ci.
***************
Jabir ne na hango a gaeding din bayan gidan su da alama waya ce yake yi cikin sanyin voice dinshi yake cewa "Dan Allah aunty ki taimake ni wallahi Ina santa da yawa bazan iya hakura Ina kallo wani ya aure ta ba".
A dayan bangaran na ji ta ce"ka bari Dady ya dawo za'a san abinda za'a yi insha Allah, karka damu ka ji dan kanina"
"Hmm to ba matsala Aunty nagode Allah ya tabbatar Mana da alkhairin sa".
"Amen kanina nagode,sai mun Kara magana"cewar Aunty Husna.sallama suka yi ya katse wayar Yana jin karfin gyuwa a zuciyar shi.
------------------------
A washe garin ranar lahadi misalin karfe 2:00 am na rana jirgin su Dady ya sauka a filin jirgin usman na gwaggo airport katsina.ita Momy Daman tasan da zuwan shi dan haka ta hau shirye shirye dan tarbar mai gidan nata.wayar Yasir ta Kira tana fadama shi ya je ya dauko Dadyn su a Airport sun kusa karaso wa.A lokacin Yana kwance a bedroom din shi abin duniya duk ya dame shi,Hakan yasa ya mike Dan Shirin zuwa dauko Dadyn.
A bangaran Farrah ko tana karasa cin abincin bedroom dinta ta koma saboda ta tuno da wata yar karamar wayar ta da ta dade a aje dan harta manta da ita,wani layin waya naga ta ciro daga cikin yar jikar post dinta ta bude ta saka kunnanta tayi taga da dan sauran caji a ciki.Dan haka cikin sauri ta saka nomber Hasan ko plashing ne tayi,cikin sa'a kuwa ta ji tayi ringing alamar Kiran ya shiga.Yana dagawa" ta ce sweety ka Kira ni ce ".
"Tau bari na kira" cewar Hasan.
Tana katsewa call din shi ya biyo baya,Cikin azama yayi picking tare da karawa a kunnan ta.A tare suka sauke a jiyar zuciya,Da sauri ya ce "wallahi sweety na kusa biyo ki gidan ku koma mai zai faru sai dai ya faru dan wallahi na gaji da wannan boye-boyen da kike yiman,kamar ba da gaske kike sona ba?.