← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 40

Sashe 30

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin shabiyu ta gota duk Yana zaune hakan yasa ya kashe wayar tare da kashe light din ya kunna dum light kafin ya haura Kan gadon.hularta ya janye ganin ta kusa fita yana sinsinar kanshin kanta.ido ya lunshe jin wani sihirtaccen kanshi ya ratsa kwalwar shi.

A hankali yake shafa sumar kanta har zuwa Kan fuskarta a ranshi yana cewa "Baby ki tausayamin ki tashi bazan iya kwanan zaune ba Ina kallanki kina baccinki hankali konce ba"yawo ya dingayi da hannun shi a jikinta har yayi nasarar janye Yar karamar rigar data saka,kadan ya hana ya fasa Kara saboda yadda yaga surar jikinta.tafin hannunshi ya kifa saman kirjinta jin wani taushi da sanyi daya rata tafin hannun shi yasa shi sauke wata munafikar ajiyar zuciya Yana Kara shigewa jikinta.kamar a mafalki ta ji ana lalubarta saita Dan motsa jin an Kara riketa yasa tayi saurin ware idonta tar sai akan fuskar shi,sosai taji faduwar gaba,a ranta ta ce "Wai shi wannan me yake nufi ya gama ceman Ina bin maza sannan yanzu ya zo Yana kwakube ni wallahi bazan yarda ba.shiko baisan ta farka ba sai ji yayi zata gantsara mai cizo a damtsen hannu yayi saurin janye hannunshi Yana Kara riketa,kokowa tahau yi dashi ganin zata Bata mai lokaci gashi ya Kai makura dole ta saka ya mirgina samanta gaba daya ya sakar mata nauyin shi yadda bazata iya motsawa ba.cikin karkarwa ya lalubo kunnenta da yaji Yana wani asirtaccen kanshi ya saka harshenshi Yana wasa da shi a ciki,Yana yi Yana hura mata isakar bakin shi,ai kafin kace me saiga yarinya nunfashinta na neman daukewa tana wani mimmike wa.dan dagata yayi kadan Yana Kara kaimi wurin hura mata iskar bakin shi.Ita ko baiwar Allah rukunkimeshi tayi tana juya kanta Dan ita kadai tasan abinda take ji tuni ta fice daga hankalinta tana neman taimako.da sauri ya kife fuskar shi saman kirjinta Yana mayar da numfashin da sauri da sauri kamar ya Kara zukata Bata San likocin data sanya hannunta ta kamo...........

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

~*DAGA ALKALAMIN*~ *~AUTAH~*

👏👏👏👏👏.
[3/17, 10:55 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
_(HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI*

*NOT EDITED* 🤗

🅿️43
📝A hankali ya fara daga hannunshi ya dire su akan fararen yatsun hannunta Wanda suke bisa Kan kirjinta tana kokarin Kare su.wurin daya cijeta kwanaki yake shafawa ganin ya warke Amma ya danyi duhu alamar raunin ya dishe.gani yayi tana kokarin zubewa kasa yayi saurin tarota tana dawowa jikin shi yaji nunfashinta ya dauke dif babu alamar shi.cikin sauri ya janyo towel din daya yar a kasa ya nadeta a ciki ya nufi bedroom da ita,a Kan gadon ya ajeta Yana shafa sumar kanta,saboda tsabar kidima da yayi ya manta da suma tayi surar jikinta kawai yake kallo yadda duk yake ganinta cikin Kaya ashe a zahiri ta wuce haka,santala-santalan fararen jinyoyinta yake shafawa har suwa samanta Dan tunda ya ajeta towel din ya yaye daga jikinta hakan ya bashi damar Kara kallonta sosai.bakinshi ya dora saman nata ya lalubo halshenta cikin sauran karfin daya rage a jikin shi ya fara hura mata iskar bakinshi a hankali take responding shiko Yana ansar Wanda take fitarwa.kawai sai ji yayi taja wani dogon numfashi tana Kara rukunkimeshi kamar wadda zata koma cikinshi.kokarin bude idonta tayi tana ganin shi ne ta mayar dasu ruf ta rufe su.tana kokarin tureshi daga samanta.Nauyi ya Kara sake mata yadda ta kasa tashi.ganin ba zata iya tureshi ba yasa ta hakura tana Kara lafewa a jikinshi.shigo goganka ya samu abinda yake so Dan Kara kaimi yayi wurin bata kiss mai zafi saida ya tabbatar da tayi lakas kafin ya mike waje yayi,har yakai bakin kofa ya tsaya cak ba tare daya juyo ba ya ce "raguwa kawai dake,Amma sai cika baki kike zanyi maganin rashin kunyar nan taki" Yana karasa fadi ya fice da sauri,kicibis sukayi da Aunty Husnah tana kokarin shigowa dakin.kallon banyarda da kaiba take jifanshi da shi,Dan shafa keyar shi yayi Yana mazurai.rabawa yayi zai wuce tana kallan shi tace "Ina farrah?"

A takaice ya Bata amsa "tana ciki"
Yayi saurin ficewa daga gidan gabaki daya.ciki ta karasa hangota tayi ta lafe cikin bed tana juya kanta.karasawa tayi tana Kiran sunanta,Farrah!Farrah!!
A hankali ta juya tana bude idonta da suka sauya color.
"Ehhm Aunty bacci nake ji"tana Kara rufe idonta.

Aunty Husnah tsayawa tayi tana karemata kallo ganin yadda take mayar da numfashi da sauri da saur.a zuciyarta tace "wannan yaran Yan duniya ne,wato ni zasu nunawa *ZAMANI* ,shi daga bari in fito da ita yayi luf Yana lalube yar mutane,to da sake tunda naga tun jiya ya turo kudin gwamma na gyarata ya dauki kayanshi su tafi tun kafin Dady yaji labari yayi ta yimin fada"gani tayi ta Kara juyawa tana dafe barin kanta da hannunta.hakan yasa ta kyaleta sai tayi tinanin kila kanta yake ciwo.

Tana fita Farrah ta bude idonta tabi bayanta da kallo,tana addu'ar Allah yasa karta Kara shigowa Dan wata muguwar kasala taji ta rufeta.kawai juyawa ta karayi tana jan blanket ta Kara rufe jikinta.

Yasir kuwa tunda ya shiga mota ya kasa tayar da ita,Dan shi kadai yasan abinda yake ji Yana yimasa yawo a jikinsa.kwantar da kansa yayi bisa sitiyarin motar Yana Jan numfashi sosai jikinshi yake kakkarwa, addu'a yayi ta karantowa dakyar ya Mika hannunshi Yana kunna karatun kur'ani kafin yaji jikinshi yadan fara sassauta wa.A hankali ya tayar da motar ya samu ya fita daga gidan.

_________________
Jabir bawan Allah soyayya tayi karfi shida Bahijja,Dan har iyayenshi sun shiga cikin maganar yanzu hankalinshi konce Bahijja na kula da shi yadda ya kamata,a dayan bangaren Kuma tana zuwa makarantar ta.

Momy taki hakura da batun Yasir ya saki farrah,Dan randa ta samu labarin an bashi ita sun tafi Abuja ranar tayi ruwan masifa ba adadi Dan sai Jabir yayi ta bata Baki kafin tadan sauko.shiko Abbah fita yayi daga gidan ya kyaleta tana ta kumfar Baki ita kadai.

Yanzu Bilkisu hankalinta ya Kara tashi,domin Bata da nutsuwa tsoratata akeyi sosai tun bayan sun dawo daga gurin boka gagara inda ya sanar da su sai dai suje wani gurin Amma shi bazai iya raba wannan ma'auratan ba,domin kaunace da Allah ya dasa a zukatan masoyan Wanda ba mai iya rabasu sai Allah.tun a sannnan jikinta yayi sanyi to tun daga ranar data konta sai ayi ta tsorata ta tana faman firgita.sosai innarta ta shiga damuwa ganin halin da yarinyar ta take ciki hakan yasa ta nufi wani isalamic CEMIST tayi masu bayanin abinda ke faruwa,magunguna suka Bata ta biya kudin tare da yimata bayanin yadda za'ayi amfani da su.ta dawo gida tana Bata magungunan.

**************

Tun kafin ya karasa jikin gate din yake faman danne horn har ya karaso ,da gudu mai gadin ya bude mai gate din Yana yimai barka da dawowa.bai tsaya bashi amsaba saboda burinshi ya ganshi a toilet ya sakarma kanshi ruwa ko yaji saukin abinda yake yimai yawo a bargon jikinshi da jijiyar shi.ko parking din kirki bai yiba ya balle marfin motar ya fito wayar shi kadai ya dauko amma sauran kayan a cikin motar ya barsu.

Turus yayi ganin Aunty safiyya da mai gidanta sun tsaya suna kallanshi.a sanyaye ya karasa Yana Kara yin kasa da kanshi.

"Wai son lafiya kake wannan uban horn kamar mai Shirin tashi sama?"cewar Aunty safiyya tana Kara kallan yadda yanayin shi ya canza.

Gefen fuskarshi yadan shafa kafin yace "kaina ne yake ciwo shi ne nakeso nayi sauri Dan nasha magani".Yana kokarin juyawa.

Basuce da shi komai ba,shiko ganin haka yasa da sassarafa ya karasa part din shi Yana sauke ajiyar zuciya.

Juyawa sukayi zuwa falonsu a lokacin har an fara kiraye-kitayen sallar magriba a masallatan cikin unguwar,Dan haka Alhaji Ubah yayi arwallah ya nufi masallaci.
Itako Aunty safiyya dakinta ta wuce da waya a hannunta tana kokarin Kiran nomber Aunty Husnah.tana jin ta fara ringing ta Kara a kunnenta,itako Aunty Husnah a lokacin tana fama da Farrah ta tashi tayi salla abin ya gagara yarinya ta nade a Kan gado tana ta faman birgima kamar wadda aka yiwa duka.

"Assalamu Alaikum Aunty Ina yini"cewar Aunty Husnah da take yaye blanket din da Farrah ta rufe jikinta da shi.

"Amin wa'alaikas salam kina jina ko?a gobe ba sai jibi ba nake soki ba Magaji matarshi su tafi gidansu,idan ba so kike yaron mutane ya rasa ranshi ba,Banda shirmen ki kina babba amma sai ki rinka biye shirmen Beby,tau wallahi zuwa gobe da yamma ki bashi matarshi idan ba hakaba zan sanar da Yaya kinji na fadamaki"

"Aunty wallahi ba laifina ne ba,shi ya kawota kafin Adan share masu gidan shiyasa,Amma kiyi hakuri insha Allah gobe zai tafi da ita"cewar Aunty Husnah muryar ta cikin sanyi,Dan ita kanta ya Bata tausayi,Amma tasan ko sun tafi Farrah gwarashi zatayi saidai inta karfi zai anshi hakkinshi.

Ji tayi ta kashe wayar ba tare da tace komai ba.

Duk maganar da sukeyi Farrah tana jinsu,Bata tantanceba sai ji tayi Aunty Husnah ta zuba mata dundun a bayanta tana cewa "ni gashi nan kina so ki jamin tashin hankali ko?duk kokarin da nakeyi a kanki bakya gani sai kinsa Dady yaimin fada,tashi ni Kona kirashi yanzu yazo ya tafi dake idan ma cinyeki zaiyi ni ba ruwana,da haka har kin saba zama da shi".

Farrah tana jin haka da sauri ta mike tana mitstsike idanuwa, cikin sanyin muryarta tace "Dan Allah Aunty kiyi hakuri karki bari ya tafi dani,wallahi tsoranshi nake ji"tana kwabe Baki alamar shagwaba.
Chapter 30 · 0% Book details