Sashe 37
Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wannan yammacin farisu abokin salisu yayan Bilkisu yazo gidan su,da farko kin fita tayi saida Inna ta hauta da fada kafin ta fita tana goge kolla.A zauren gidan ta riskeshi Yana ganinta yahau doka murmushi,Dan shikam ya dade Yana San Bilkisu tunda dadewa.A hankali tayi sallama bayan ya amsa ta gaisheshi.dukansu shiru sukayi na Dan wani lokaci kafin ya fara magana kamar haka "Kiyi hakuri Bilkisu idan na takura ki,zuciyata ce ta kasa daurewa akan irin son da take yimaki,Ina fatan a wannan karon zan samu karbuwa"Yana kallan yadda duk ta sauya kamar ba Bilkisun daya sani ba.
Har zuwa wannan lokacin nata tanka ba,sai ma Kara yin kasa da kanta da tayi tana wasa da karamin zoben hannunta.
Haka yayi ta zuba shi kadai,sai a karshe ta ce "na amimce,Amma ka sani ni yanzu Ina da banbanci da sauran yan'mata domin ya zama dole na fadama gaskiyar abinda ya faru da rayuwata,kada sai Bayan auren mu na fuskanci wulakanci daga gareka......"da sauri ya katseta ta hanyar cewa "Bakomai Bilkisu duk salisu yayi min bayani,insha Allah zan rikeki da amana,burina ki kasance mai hakuri da biyayyya nidai kinsan sana'ata bakai kudi ne ba ni,Amma Insha Allah mai nema Yana tare da samu".
Sosai taji dadin kalamanshi daga nan suka Kara daidaita kansu,ya sanar da ita zuwa ranar juma'a za'a manyan shi zasu zo Dan saka ranar auren su.godiya tayi mai kafin yayi mai kafin ya Miko mata wata leda,da farko kin ansa tayi saida yayi ta rokonta kafin ta amsa ta wuce cikin gida bayan tayi mai godiya shima tafiya yayi Yana Addu'ar Allah yasa ta sanadin faruwar al'amarin nan ta shiryu.
Tana shiga gidan ta nunawa Inna abinda ya kawo mata,leda daya kayan fruits ne dangin su kankana,lemo,ayaba da sauransu.dayar ledar kuwa kayan kolloliya ne dukda ba masu tsada ne ba Amma ba laifi sinyi kyau,ajewa tayi kafin ta wuce wurin kitchen Dan karasa aikin data bari.
Tinda ya shigo falon yake jin kukanta da sauri ya aje ledar zogalan Yana nufar inda take a konce.rungumota jikinsa yayi Yana cewa "A a Baby meya faru?Baki da lafiya ne?ko wani abu yake maki ciwo?duk bata bashi amsa ba sai cewa tayi "ni Ina zogalan,yunwa nake ji idan ban ci ba mutuwa zanyi"tana Kara kontar da kanta bisa kirjinshi.
Dariya takusan kufcemai Amma sai yayi murmushi Yana share mata hawaye yace "Kinga yi hakuri gashi na kawo ko"Yana tayar da ita zaune.duk abinda take yi Momy tana kallansu sai taji sun birgeta dukda ta fahimci Farrah tana Dan bashi wahala saboda yadda baya iya boye soyayyar da yake yimata a gaban kowa nunawa yake yi.
Da kanshi ya dauko tumatur da albasa ya jika kulin ya hada da mai ster ya kwada mata.sai a lokacin ya lura da Momy a wurin,sosai kunya ta rufe shi,Amma ba yadda zaiyi kinci tayi dole ya fara bata a baki ganin yadda ta birkice,Momy tashi tayi ta basu wuri ta wuce bedroom Dan jin an fara Kiran sallar magriba.
Ai zogala kaman jira take ta karasa cinyewa ta fara kokarin amai,ganin haka Yasir ya rude Yana ta faman girgizata.jin haka yasa Momy har tayi alwala ta fito da sauri Dan ganin meke faruwa.
Taimaka mata tayi zuwa toilet ana tayi ta amai saida ta amayar da zogalan nan tas kafin taji saukin tashin zuciyar da yake addabar ta.ji tayi jikinta yayi sanyi lakos Bata da kuzari.alwala ta dauro shiko ya fita zuwa masallaci, anan dakin Momy tayi sallah a zaune tana ta faman zubar da kollah.a bisa abin sallah ta konta.kafin kace meye wannan bacci ya dauketa ga wani zazzafan zazzabi daya sauko mata lokaci daya.
Shiru Momy tayi tana nazarinta,Dan da Alama Farrah zata yi laulayin ciki irin na Mamanta mai wahalarwa,Dan ita Aunty safiyya a lokacin har saida Alhaji Ubah ya kawota katsina aka Dan kula da ita kafin bayan taji sauki ta koma.
Bayan ya dawo tare suka shigo da doctor Umar Dan gani yayi gwamma ya Kira shi a dubata,suda Suka zo biki Kuma rashin lafiya ta samu.anan falo doctor Umar ya zauna shi Kuma ya shiga ciki Dan fito da ita.bacci ya taras tana yi sai Momy dake kuda da ita.
Sanar da ita yayi kafin ya fara tayar da ita.dakyar ta bude idonta Dan tana jin baccin sosai,hannunta ya kamo suka fito.ana doctor ya dubata Yana yimasu albishi da tana dauke da juna biyu na sati biyar da kwana hudu.Yasir tsabar farinciki baisan time din daya rungimi doctor ba .ita ko Farrah tsoro ne ya kamata ganin yadda yau kadai Amma duk ta fita hayyacinta,to Ina ga nan gaba".
Da haka dai ya rubuta masu magani kafin ya wuce.shiko kusa da ita ya dawo ganin yadda tayi shiru.rungumota yayi Yana kissing din wuyanta ya ce "Baby Naga bakiyi murna ba,ko bakison yaron da zamu haifa?".
Shiru ta mai tana kasa da kanta.ji yayi jikinshi yayi sanyi Dan haka ya tashi Yana cewa anjima ki shirya muje zaki gaishe da Ummah Dan dazu tana tambayarki,yanzu zan kawo maganin sai kiyi kokari ki sha.kafin ya fice ba tare daya Kara kallanta ba.ajiyar zuciya ta sauke tana shigewa cikin kujerar jin wani sanyi Yana ratsata a zuciyarta tana jin wani farinciki Wai ita ce zata haihu?hannunta ta dora tana shafa shafaffen cikinta da kamar ba komai a ciki.wayarta ta janyo tana Kiran nomber shi.yana gani ya kyale da kamar nazai daga ba,Amma sai yayi picking ji yayi cikin sanyin muryar ta ce "Dan Allah ka siyoman agwalima"tana Jan numfashi.
A zuciyar shi yace "yau ni dai na gode Allah"Amma a fili amsawa yayi da "to"kafin ta katse kiran tana gunguni, kasa-kasa take cewa "yanzu ni shikenan a hanaka bacci,shiko nan zaiyi ta baccin shi niko ko ohoo sai dai abar mutum da wahala"mtssss tana Jan siririn tsaki,mikewa tayi jin lokacin sallah yayi ta shige dakin Momy.
A ranar dakyar ta yarda suka nufi gidan Abbah bayan tasha magani.Ummah tana ganinsu ta hau murna ba kamar data fahimci cikin dake jikin Farrah tana ta kaffa-kaffa da ita har wuraren kafe goma lokacin Abbah ya dawo Suka je suka gaisheshi shima yaji dadin ganin su haka yayi ta saka masu albarka.Amma har suka tafi Bata ga Jabir ba.a bayan sun dawo ya wuce tsohon part din shi ita ko tayi cikin gidan tana jin jiri Yana daukar ta.a gyare tsaf riski part din Dan haka ya shige wanka.
Farrah ko abinci ta dan ci kadan sai agwalumar daya kawo mata take ta faman Sha tana sude Baki Momy duk tana kallanta sai Nusaiba da take faman yi mata dariya.
Sai wuraren goma da rabi Momy ta ce "Farrah tashi ki tafi wurin mijinki Dan kayanki suna can tun dazu nasa aka kaimaki"
Sosai ta gwalo ido tana kallan Momy.
"Ko Baki ji Mena fada ba" cewar Momy tana mikewa "Dan Nima wurin mai gidana zan wuce,Nusaiba ko tuni ta wuce dakin Farrah na da Wanda yanzu ya zama mallakinta.
Tana kallo har Momy ta fita kafin itama cikin sanyin jiki ta wuce dakin mai gidan nata tana faman gunguni da mita.
Bata ganshi a Falo ba Dan haka derect ta wuce dakin shi.a wata yar kujera ta ganshi Yana duba system din shi.a hankali ta karasa Yana kallonta ta nufi toilet wanka tayi ta saka kayan bacci ta fesa turaren oud mai kanshi da humra irin ta Yan maiduguri.gadon ta haye tayi konciyar ta tana shakar kanshin jikinta.a hankali ta rinka jin yanayin ta Yana sauyawa,wasu igiyoyo suna yimata yawo a cikin jikinta.kafin kace me tuni ta rude ita kanta tayi mamakin kanta,meyake neman samunta ne? Sosai yanayinta ya sauya ta fara mirginawa.jin motsinta ya sakashi juyowa Yana kallon yadda take birgima.rufe system din yayi Yana rage hasken dakin kafin ya haura inda take.dagota yayi Yana kallan yadda take zillewa."Baby meya same ki ne?ai tana jin muryar shi da irin rungumar da yayi mata ta Kara kankame shi bata Bari ya Kara magana ba tayi saurin saka bakin ta cikin nashi.hakan da yaji ya gane matsalar ta,aiki Daman mai neman kuka aka jefe shi da kashin awaki ai sai yi.yaji dadi sosai Dan Daman tunanin tunkarar ta yake yi.da haka da haka dai nikam nayi nan 🏃🏃🏃.
******************
Washe gari haka Farrah ta wuni a part din Momy daga tace wannan take so sai tace wancan take so,haka akayi ta fama da ita ko gidan yinin biki Basu jeba kasancewar sai da dare Aunty Husnah ta iso daga Abuja.ganin Farrah da tayi a haka yasa tayi ta yimata dariya tana janta itako sai kuka take yi tana jin haushi har zuwa lokacin da Yasir ya dawo daga amso mata dinkinta daga gidan su Bahijja.fita ya karayi bayan sun gaisa da Aunty Husnah.
Cikin gimtse dariyarta ta kalli Farrah cikin salon zolaya ta ce "ooooh ni Farrah ashe kice zaki haifa mai yaran,keda kika ce saidai ya nemo wadda zata haifa mai badai keba,to ya'akayi ciki ya fito haka"tana Kara sautin dariyar ta.
Farrah kuka kawai ta saka tana sharbewa,Momy girgiza kanta tayi tana murmushi.
Ita ko Aunty Husnah cikin rarrashin Yar kanwarta ta ta dafa kafadarta tana cewa "Kinga yi hakuri kinji Yar kanwarta,yanzu abinda za'ayi anjima idan ya dawo zan anshi kudi a hada maki kayan gyara kafin ku koma Dan wannan mijin naki zafin Kaine da shi"
"Ni ba wannan nake so ba,kayan lefena nake so ya hadaman idan ko ba hakaba to bazan koma ba,sai dai ya tafi shi kadai"cewar farrah tana goge hawayen fuskar ta.
Sosai Aunty Husnah take dariya gaskiya Farrah rigimar ki tayi yawa,wato da kuna cin amarci Baki tina da baimaki lefe ba sai yanzu da ciki ya samu,to zamu saka yayi maki Dan na Fahimci cikin ne baki so ko?to insha Allah sai kin haife Mana kayanmu,tunda Baki so a karu da ke sai dai kici ki konta ko?"tana gimtse dariyarta Dan ganin tana neman Kara saka mata wani kukan.
Bayan ya dawo Aunty Husnah tayi mai bayanin abinda Yar rigimar tashi ta ce.murmushi yayi ya ce "to Aunty za'ayi komai,Amma sai an karasa bikin su Jabir tukkunna".
A wannan matsayar Suka bar zancen.