← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 40

Sashe 28

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta fito wanka anan bakin gadon ta zauna ta tallafe kumatunta da dukkan hannuwanta buyi.tinani take yi a zuciyar ta Wai Bilkisu ce take kokarin aikata haka a gareta duk kokarinta na san ganin ta kyautata mata,Amma a karshe zata saka mata da haka.ita kam tayi alkawarin daga yanzu ba ruwanta da kawayen wannan ZAMANIN,gwamma tayi rayuwar ta ita kadai.Alamar tafiya taji ana nufo dakin da take,da sauri ta mike tana shiryawa.

____________________

A katsina ko Bayan tafiyar su Yasir da Farrah, suma su Jabir suntafi Dady ya Kira Abbah Yana sanar mai tafiyar su Yasir da abinda ya faru .godiya yayiwa kanin na shi tare da Addu'ar Allah yasa Basu zaman lafiya da zuri'a dayyi ba.ya amsa da amen.nima na ce Amin.

Bilkisu ce take ta faman kaiwa da komowa a tsakiyar dakinta bayan tafiyar kawar ta khairiyya.sosai ta shiga rudani ganin komai na kara cakude mata,tinawa tayi da rigimar da sukayi da sukayi da Bahijja,anan taba kanta amsa lallai ba makawa itace ta fallasa sirrinta,da wannan tinanin ta danwa wata nomber call,dukda wani bangare na zuciyarta Yana sanar da ita ta hakura da Yasir domin kuwa yayi mata nisa.Amma ta kasa yarda da hakan.

"Hello barau ana jina ko"cewar Bilkisu tana zama bisa katifar tsakar dakin.

"Eh Ina jinki Hajjaju,wani aikin ne ya taso?"
Ya amsa cikin amon muryar shi mai kama data gardawan kauye.

"Eh barau idan harka anshi aikin nan to kada ka Bari a samu matsala,Dan a wannan karon bazan yadda da hakan ba,kawai anjima mu hadu da Kai wurin da muka Saba haduwa"tana gama fada mai ta kashe wayar tana saka ta cikin hand bag ta fita daga dakin.

________________

A yinin wannan rana har zuwa dare Farrah a haka suka wuni ita da Aunty Husnah tana Kara koyamata wasu abubuwan da suka shafi yanayin zaman takewar aure.Ita dai Farrah jinta kawai take yi Dan Tasha alwashin saita rama abinda yayi mata.

_WASHE GARI_
A washe gari ne tunda yamma Yasir yake faman shirye-shirye Dan zuwa ganin abin kaunar tashi.wanka ya dauka sosai sai faman zuba kanshi yake kamar wani sabon ango.danyan boyel ne dark blue ya saka danki yamai shar,ya kara fito da samartakar shi,sai cover shueis days saka black sumar Tasha gyara gwanin sha'awa.
Yana daura agogon shi ya nufi site din Aunty safiyya.tana ganin ya shigo falon ta ce "Masha Allah son irin wannan cin gayu haka sai Ina?"tana murmushi.

Shima murmushin yayi Yana zama Kan kujera"Hmmmm Aunty gurin Beby zanje Dan zuwa jibi nake so idan ankammala gyaran gidan mu wuce"Yana dan sadda kanshi alamar kunya.

"Tau Allah ya bada zaman hakuri,sai kayi ta hakuri da Beby dan har yanzu kuruciya na damunta,zaka ga shirme kala-kala,Kai zaka dorata akan hanya"

"Tau insha Allah Aunty ngd,Bari naje saina dawo"Yana mikewa tsaye.

"Tau ka gaishe w Auntyn take"cewar Hajiya Safiyya tana wucewa dakin mai gidan nata.

Da haka ya tayar da motar shi,yayiwa gidan Aunty Husnah tsinke.

Wallahi Farrah idan baki yi sauri kin fito daga toilet din nan ba ranki zai baci,haba ke kwata-kwata kamar Baki da wayo ayita fama dake,to ki Bari har ya karaso kinanan kiga yadda zanyi da ke"tana fita daga dakin cikin jin haushi,saboda doorbell da taji ana dannawa.

Tana budewa Yasir ta gani a tsaye Yana murmushin shi mai tsada.

"Wayyooooo kanina kaga wani mayen kyau da kayi ko🤔?lallai idan kuka haihu zamuga damsels girls"tana matsawa alamar ya wuce.

Shidai baice komai ba illa wucewa da yayi Yana Kara jin wani farinciki a kalbin shi.

Waige-waige ya farayi,Dan ganin ta inda zumar tashi zata fito,Amma shiru.daga bayan shi yaji Aunty ta ce"to wallahi sai dai ka jira,dan tun dazu ta shige toilet taki fitowa".

Dan Bata rai yayi Yana kallanta yace "Tom ni Bari na fito da ita"da sauri ya nufi hanyar dakin.duk Kiran da Aunty Husnah ke yimashi bai tsayaba.

Yana shiga dakin kanshi tsaye ya tura kofar toilet din.

Daidai ta fito daga Bathroom tana kokarin daura towel,a hankali yayi sadaf-sadaf sai ji tayi an fige towel din daga hannunta.cikin tsoro ta jiyo da tsinkewar zuciya bakinta na kakkarwa ta fara kokarin Kare kirjinta da su kadai ya tsurawa mayun idanun shi Yana jin jinin jikin shi Yana neman tsayawa.

A hankali ya fara matsota tana yin baya har saida ta ji ta jingina da jikin mirron wurim,kafin ta fara kokarin tsugunnawa.da sauri ya tarota Yana jefar da towel din hannun shi.gaba daya ta fado cikin faffadan kirjin shi,wani yarrrrrrrr yaji lokacin da nashanunta suka sauka akan kirjin shi ajiyar zuciya ya sauke Yana Kara matseta, A hankali ya lalubi kunneta wata makirar iska ya fara huramata mai kamar da yanayin fito.da sauri yaji ta Kara rike shi gam tana juya kanta bisa kirjinshi ga wata matsitsiya da take shi,ji yayi kamar tana yimai tafiyar tsutsa Dan haka da sauri ya rabata da jikin shi steal Yana rike da ita,gani yayi gaba daya ta birkice tana lumshe idonta,kirjinta yake kallo Wanda suka gama tafiya dw sauran imaninshi.A hanakli ya fara daga hannunshi ya dire su akan..............

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

👏👏👏👏👏👏
[3/17, 10:55 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .

*NOT EDITED* 🤗

🅿️44
📝Washe garin ranar ya kama juma'a ne Yasir da wani farinciki Wanda bazai iya misaltashi ba ya tashi,sosai yake jin wata sabuwar annashuwa tana lullube illahirin jikinshi.da haka ya shirya ya nufi CBN wurin aikin shi dukda ya Dan so ya makara.

Farrah tunda Aunty Husnah ta tayar da ita da asuba bata Kara samun damar Kara runtsawa ba da sunan bacci,domin irin tsoro da fargabar da suka makaye zuciyar ta,duk yinin ranar cikin sanyin jiki take yinshi,sai wasu magunguna da Aunty take faman duramata wasu idan taji da zaki ta shanye wasu ko saboda baurin su sai dai ta saka mata kuka.yanzuma Bayan an sauko masallaci tana cikin kujera a konce tinani duk yayi mata yawa ga shi tana tsammanin yanzu luctures sun kankama school ta rasa wa zata tinkara da batun komawa makaranta.hannu biyu ta saka tayi tagumi tv take kallo Amma a badini tinani ne take yi.

Aunty Husnah da yanzu ta shigo falon da babban tray a hannunta tsayawa tayi tana kallanta ganin yadda tayi nisa a duniyar tunani.tary'n ta aje akan table din wurin kafin ta zauna kusa da ita,a hankali ta dafa kafadarta . firgigit tayi tana mazurai kamar marar gaskiya.

Aunty Husnah bata ce da ita komai ba illah wata kula data bude kaza ce guda a dafe da romonta sai tashin kanshi take yi.a karamin plate ta juye ta dora mata akan cinyoyin ta cikin tubune fuska ta ce "yi sauri ki cinye Ina jiranki "

Marairai fuska ta farayi,tana kwabe baki cikin zubda kolla ta dubi Auntynta ta tace "please Aunty wallahi cikina zai fashe,kiyi hakuri na koshi"tana hade hannuwanta alamar ban hakuri 🙏

Shiru tayi ta kyaleta tana ci gaba da Danna wayarta.
Itama Farrah shiru tayi tana goge kolla,Dan tunda taji tayi shiru to ba zata kulata na,sai kawai ta wanke hannunta ta fara cin kazar.

"Banda kashin zaki ci,ki cireshi tsokar kawai ake bukatar kici"haka taji muryar Auntyn Husnah tana fada mata.

Itama shiru tayi Bata Kara cewa komai ba har saida ta cinye tsokar tas ta shanye roman,duk da ta koshi turawa kawai take yi Dan ba yadda zata yi.

Gani tayi ta yanko mata kayan fruits ciki da wani Dan madaidaicin plate ta Kara Miko mata.da sauri ta zaro idonta tana kallan Auntyn tata.ita ko da ido tayi mata inkiya da cinye ki bani plate din.shiyasa cikin sanyi farrah ta ansa.A hankali take tura kayan fruits din har ta kusan shanyewa,da taji kamar zata yi amai sai kawai ta fashe da kuka.Aunty Husnah sororo tayi tana kallanta,wato ita dai abin kuka baya yimata wahala.tashi tayi ta Bata wuri,ruwan wanka ta Kara hadamata da turarika masu kanshin sanyi a ciki.

Hannunta tazo ta kama ta nufi toilet din da ita.har ciki ta kaita tana cewa mayar da hankali kiyi wanka Ina jiranki.ta fice ta barta anan a tsaye.

Ta Jima a wurin kafin ta cire Yar rigar dake jikinta ta shiga cikin bathroom din ta fara cuda jikinta da ruwan masu kanshin dadi,har wani lumshe ido take yi.

Lokacin data fito har an idar da sallar la"asar Dan haka ta dauro alwala ta gabatar da tata.tana zaune aunty ta Kara dawowa da wata matashiyar budurwa na biye da ita a bayanta."taso Farrah idan kin idar"cewar Aunty Husnah tana ba budurwar umarnin ta jirata.dakyar Farrah ta yarda aka fara yimata kwalliyar Dan cewa tayi Bata so.karfe biyar da rabi sun gama shiryata cikin doguwar rigar material mai danbanzan kyau da kyalli.mayafi aka sakamata da set na yari da banglos masu tsada dukda ba kunshi sai kanta da aka gyara mata,Amma kar kuso kuga kyan data zuba sai tashin kanshin humra da colakcer take yi irin na Yan maiduguri.tayi Shar abinta dukda bata yin fara'a tayi kicin-kicin da fuska ita a dole fishi take yi.

Falo suka nufo da ita,dakyar take tafiya saboda tsinin takalmin data saka.

Shiko Yasir tun dazu yazo,Yana zaune Yana kallan ta hanyar da zasu bilo saiko yaji alamin tahowar su ta wurin bedroom din,da sauri ya tashi da murmushi a saman fuskar shi.A hankali suke tahowa da mayafin aka rufe kanta har zuwa fuskarta dukda shara-shara yake ana iya hango fuskarta.suna karasowa gabanshi Suka tsaya Aunty Husnah ta ce "to nidai na huta gata na damka maka ita,Dan haka yanzu aiki ya rage naka sai kasan yadda zakayi da rigimar ta"tana dariya.

Cikin fargaba ya Kara matsota har suna jin numfashin juna ya saka hannuwan shi ya rungumota.kusan a tattare suka sauke wata ajiyar zuciya mai zafi.Farrah matsitsiya ta farayi tana son kwace jikinta Amma sai ya Kara matseta tsam Yana shinshinar kanshin jikinta.
Chapter 28 · 0% Book details