← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 40

Sashe 36

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🅿️46
📝Akalla sun Kai karfe shadaya suna bacci,sai sannan Yasir ya juya da sauri ya bude idonshi Yana kallan agogo, ganin yadda lokaci ya shude ya makara shi yaushe rabon da yayi bacci mai dadi irin na yau,badan ya soba ya tashi da addu'a a bakinshi kafin ya nufi dakinta.yana shiga yaga baccinta take yi,Daman yayi tinanin Aunty Husnah sun wuce.wayar shi ya dauka ya dawo falo Yana Kiranta.bayan ta daga ya ce "Aunty ashe har kun tafi?"Yana Dan lumshe idon shi alamar har yanzu baccin bai sake shi ba.

"To ai Magaji dole muke tafiya,kuna ta ramuwar bacci mun zauna muna gadinku?kaga ni anjima kadan idan na karasa girki kazo ka amsar maku,Kuma bayan ta farka ta Kara shiga ruwan zafi,Kuma Dan Allah kana jina?"

"Eh Aunty Ina jinki" cewar Yasir da yake kokarin konciya bisa kujera.

"Dan Allah Magaji ka kyale yarinyar nan,kadan daga mata kafa Kona sati biyu ne,kaga yanzu wallahi idan ta tashi nasan zaka Sha rigima dan cewa tayi saina taho da ita bazata zauna ba kaji ko?"tana tona miyar data Dora akan gas.

Ajiyar zuciya ya sauke can kasan makoshi ya ce "Haba Aunty two weeks ai yayi yawa,ni Baku tausayin dan kanin nan naku,kunfi jinta a kaina,to ba damuwa zanga idan zan iya jurewa idan ko bana iyawa to,zan dan........"
Sai Kuma yayi shiru Yana rufe bakin shi da tafin hannu.

"A a Magaji gwamma ka karasa fadi,acan baya ma baka jin kunyata ballanta na yanzu da kake jin kanka a sama ko?to nidai da Allah na hadaka,idan Kuma kaki wallahi zan Kira Abbah na cemai Farrah bata da lafiya Amma zan kawota gidana harta warke kafin na mayar da ita,kasan cewar yarda zaiyi ko?"

Dariya ya danyi kafin ya ce "Haba uwar dakina kada miyi haka da ke,wallahi wasa nake yi saita warke kafin Dan Nima tsoranta nake ji,ita data kusa sumar da ni"Yana Kara sautin dariyar shi jin Aunty Husnah tayi saurin katse kiran.kwanciyar shi yayi anan Yana faman doka murmushi.

*KATSINAN DUKKO*

Da misalin karfe daya saura Dady, Abbah,sai kawu Yakubu da ya iso daga dutsamma Suka nufi gidan mahaifin Bahijja dan nemawa Jabir auren Yar shi.a wannan ranar su Dady sunga karamci da mutunta Baki,sosai iyayenta sukayi farinciki saboda ranar weekend ne,kanin mahaifinta shi ya anshi kayan auren inda aka saka wata biyu masu zuwa,kafin azimi kenan .a lokacin Bahijja tana gidan matar yayanta dan haka acan Jabir ya risketa suna fira,ya juna farinciki shi kwarai da gaske.
"Wai ni ya Jabir ina labarin kawata"tana kallanshi.
"Hmmm ke zan tambaya dan tun ranar da suka tafi raban da muyi waya da brother,Amma Bari na Kira shi sai ya bata wayan tinda kina son magana da ita"Yana laluben wayar shi.tana ta ringing ba'a daga ba.

Shiko Yasir a lokacin Yana ta fama da rigimar Beby dan sau lokacin ta farka tana ta yimai kuka da complen din bayanta da kafafunta ciwo suke yi,to so yake tayi wanka ya bata magani,Amma ta kiya.suna haka yaji Karan wayar.mika hannu yayi ya daukota sai yaga sunan Jabir picking yayi ya sakata a speaker Yana magana.

Tana jin muryar Yaya Jabir sai tayi lamo a jikin shi tana zubda kolla.

"Yaya ya gida"cewar Jabir da yake kallon Bahijja ganin yadda take ta faman doka murmushi.

"Lafiya Lau ya yan gidan,da fatan duk kuna lafiya?"

"Lafiya Lau,munga kun manta da mu tunda kuka tafi,ko Kira a waya bakwayi sai Sweety take tambaya ta Ina Beby shiyasa na Kira Dan su gaisa"Yana mikawa Bahijja wayar.

"Ok bata wayar"cewar Yasir Yana dorawa Farrah wayar bisa kunnenta.

Ai Farrah najin haka kawai sata fashe da kuka .

Cikin rudewa Bahijja ta fara tambayar ta "lafiya kawata meya same ki haka kike kuka"?tana kallan Jabir da shima ita yake kallo.

Yasir dauke wayar yayi Yana cewa "sorry Bahijja bata da lafiya ne,Amma anjima San kawo mata new phone zata kiraki da wayanta"

"To Yaya Allah ya bata lafiya nagode"kafin ta katse wayar.

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallan Jabir ta ce "Wai sweety ka ji bata da lafiya,kuka take yima,wallahi hankalina harya tashi kada ya rinka cutar da ita"cewar Bahijja cikin sanyin murya.

Jabir kallanta yayi ya ce "A a sweety kada kiyi wannan tinanin,nasan brother Yana santa saidai in rigimarta ce ta motsa,Dan nasan halin Beby kamar Yar goye haka take idan ta kama rigima daman shi kadai take tsoro,yanzu ko tunda sun zama daya ai sai dai yayi hakuri"Yana kashe mata ido daya.

Sinnr kanta tayi tana murmushi,da haka suka Dan taba hira ya wuce gida ita Kuma ta shiga gidan yayanta.

Yasir kuwa Yana kashe wayar ya sungumeta zuwa tiolet Dan ya fahimci bata mai time zata yi ga lokacin azahar har ya karato,Dan haka kawai ya sakata cikin bathroom kafin shima ya shiga.sosai take kokarin ya saketa Amma ya kiya saida ya tabbatar ta gasu kafin ya cireta yasaka tayi alwala ya mayar da ita bisa gado,shima ya koma tiolet din Dan Kara yin wani wankan.

Bilkisu kuwa tunda suka dawo daga Danfodio tana konce tana faman kuka da nadama,Dan da akayi mata ruqiyya aljanin kin fita yayi saboda ya ce anyi da ita Idan baiyi nasara ba kanta zai dawo,to a karshe dai dakyar aka samu ya fice.aka Basu magunguna suka dawo gida inna tana ta yimata fada.

Bayan ya fito tana konce ya dauko mata wani leshin ta saka da hijaf shima ya shiya ya jasu suka gabatar da sallah azahar.kafin ya fita Dan anso masu abinci gidan Aunty Husnah.

Ummah ce gaban Abbah bayan sun dawo daga gidan su Bahijja ta tsuguna a gaban shi tana bashi hakuri,Amma ya kyaleta.
Sai can yace "wato sai yanzu kika hakura da Magaji ya zauna da Amina,ai wallahi kin bani kunya nayi tinanin tsare shi zakiyi ya saketa,shiyasa muka sashi ya dau matar shi suka tafi tunda ke bakyasan konciyar hankalin mu ko,ni tashi ki bani wuri ,Kuma yauma minkai kudin auren Jabiru gidan su Bahijja Diyar Alhaji murtala,shima kice Baki so kiga yadda zan Bata maki rai,Banda wulakanci kiri-kiri ki nuna bakisan yarinya idan da rabo to ya zakiyi,Dan kila yanzuma idan aka ce tana da ciki kar kiyi mamaki da hukuncin Ubangiji"haka Abbah yayi ta mata fada tana bashi hakuri,har a karshe dai ya ce ya yafemata.kafin suka daidaita.

Yasir tunda ya amso abincin ya hadomata da iccecrem mai sanyi Dan yasanta akwai San zaki.a haka suka yini a wannan ranar Farrah tana ta zuba mai shagwaba san ranta,shiko bawan Allah duk yabi ya rude sai faman tarairayarta yakeyi tana Kara rudashi.Amma a zuciyarta tausayin shi take ji ganin yadda yake ta rawar kafa a kanta,Dan zuwa wannan lokacin ta daina kukan.haka suka wuni har dare Yana ta tarairayarta.salloli ma duk shi ya jasu jam"i Suka yi a gida.sai Bayan sallar isha'i Aunty Safiyya ta Kira wayar shi Dan ta kasa daurewa so take yi taji muryar Autarta ta.

Cikin kunya ya daga ga Farrah duk ta kanainaye shi yadda bazai iya tashi daga gurin ba.dole ya amsa anan bayan sun gaisa take cemai ankai kudin auren Jabir, addu'a yayi masu da fatan alkhairi,sannan yace ga Beby zasu gaisa.
"A a Magaji kyaleta ni Daman kaina Kira a gaisa da naga baka shigo ka gaishe mu ba"cewar Aunty safiyya cikin jin kunya.

Cewa yayi "zan shigo gobe insha Allah"

Sauri Farrah tayi ta anshe wayar tana dariya ta ce "Aunty yanzu duk kun tsane ni,ni ko tun dazu nake cewa yakiraman ke mu gaisa"ta karasa fada tana turo bakinta.

"Ba haka neba Baby so nake yi ki nutsu kiyi hankali tukunna sai na rinka kiranki"cewar Aunty safiyya,dukda taji dadin jin yadda Diyarta ta hakura ta zauna.

"To Aunty yanzuma ai nayi hankali tunda ya jiman rauni ban fadamaku ba ko"cikin yanayin sakalci.

Da sauri Aunty safiyya ta katse wayar tana girgiza kanta a fili ta furta "Baby har haryanzu da sauranki.

Shiko Yasir amshe wayar yayi Yana saka bakin shi cikin nata yayi niyyar sai yayi fornishing dinta tinda Bata jin magana shi zata kunyata,ya kasa zuwa gidan.tayi ta faman ta kwace Amma ta kasa saida ya gaji dan kanshi kafin ya zare bakinshi daga cikin nata Yana mayar da numfashi.
Kwanciya tayi a jikin shi tana jin yadda jijiyoyin jikinta suka saki.lumshe ido tayi tana jin wani yarrrrrrrr a cikin jikinta.sun Dade a haka kafin yace "ni ki kagani duk kin tumurmushe ni,Amma sai kice Ina cutar ki"Yana leken fuskarta.

A hankali ta mirgina gefe tana Kara kudindine jikinta guri guda jin wani sanyi na ratsa ta.

A haka suka Kai har lokacin konciya sai kayan fruits daya yanko masu a tray suka sha.da zasu yi bacci sosai ta tsorata tana ta raba eyes lura da yayi da hakan yasa ya fara lallabata da cewar ba abinda zai yi mata.kafin ta yarda suka konta,Amma dukda haka ya kwakumeta cikin jikinshi ya hanata sukuni.ita ko baiwar Allah sai fargaba take yi Dan ita yanzu harga Allah tsoro yake bata.shiya fara yin bacci, saida ta tabbatar yayi nisa a baccin kafin taji hankalin ta yadan konta itama tayi bacci.

*Asuba ta gari Farrah* *matar* *Yasir* 🤣😂

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

👏👏👏👏.
[3/20, 6:32 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI*

*NOT EDITED* 🤗

🅿️48
📝Tinda ya shiga gidan ya fahimci akwai canji musamman a fuskar mahaifiyar tasu,yadda ta tarbeshi cikin sakin fuska sai tambayar shi take yi Ina Farrah,sai ya ce "tana gidan Momy Amma anjima zuwa da dare zan kawota ta gaisheki.taji dadin hakan sosai,anan ta gabatar mai da abinci cikin farinciki ya ci ganin Ummahn tasu ta huce daga fishin data dauka.yana cikin cin abincin Jabir Suka shigo shida little Umar.anan Suka ci gaba da hira Jabir Yana ta tsokanar shi ganin yadda yai bul gwanin kyau abinshi.kafin yayi masu sallama da zummar zuwa dare zasu dawo tare da Farrah.akan hanya ya siyamata zogala da kuli dakakke ya tafi da su.
Chapter 36 · 0% Book details