← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 40

Sashe 13

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin daukar basket din tayi zuwa bakin gadon.
Cikin sanyin murya ta ce Ummah ya jikin na shi?tana kokarin zuba tea a cikin cop.

Momy tsayawa tayi tana kallanta ba tare da ta ce komai ba .

Hakane yasa Farrah jikin ta ya Kara yin sanyi sosai itama ba tare da ta Kara cewa komai ba harta gama zubawa.

Akan dan karamin table din ta dora ta koma sit daya ta zauna tana wasa da zoben hannun ta.

Yasir kuwa duk abinda take yi Yana kallanta ta kasan eyes din shi har zuwa lokacin da ta zauna.shi kadai yasan irin zafin da yake ji a zuciyar shi.

Bude eyes din yayi a kanta sosai yake duban ta duk da hijaf ce a jikin shi amma tayi ma shi kyau.

Momy ta dube shi tana cewa "Magaji ta shi ka yi brosh sai ka sha tea din"tana kokarin tayar da shi.Dady ya kama suka karasa tayar da shi.

A hankali yake saukowa daga bisa gadon harya mike tsaye.

Momy ta kalli Farrah "ta shi ki hada ma shi ruwa yayi brosh.

Sosai ta ji gabanta ya fadi,Amma cikin dauriya ta mike zuwa tailet din dake cikin dakin.

Bayan ta fito tana cewa "Momy na hada ruwan akwai saban brosh a ciki.

Da kanshi ya karasa toilet din.

Daidai ya fito ya tarda Abban shi sun Kara so.

Sosai Ummahn shi ta rude ganin yadda dan nata ya zabge a cikin yini daya.

Da sauri ta nufi dan nata tana riko hannun shi.
"Magaji Kai ne ka rame haka?meya ke damunka ? .

Shi dai bai ce komai ba har ya zauna bakin gadon.

Umman shi Bata rai ta yi sosai dan harga Allah ta fara tunanin akwai hannun wannan yarinyar, A da tana San Farrah,Amma a yanzu gaskiya ta fara fita daga ranta saboda ta fahimci so take ta kashe mata yara har guda biyu.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

~*DAGA ALKALAMIN*~ *~AUTAH~*

*PLEASE COMMENT AND* *SHARE* 👏.
[3/1, 6:29 AM] Hayat: *🤦‍♂️ZAMANINMU🤦‍♂️*

_(HATTARA YAN MATA)_

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*Abin da Wanda ya ji ciwo* *a jikinsa zai ce* .

*Annabi tsira da amincin* *Allah* *su* *tabbata a gare shu* , *ya* *ce"ka* *sanya* *hannunka a wajen da* *yake maka ciwo a* *jikinka" ka ce,*

*(Bismillahi)* *sau* *ukku*

*Ma'ana: Da sunan Allah* .

*Sannan* *ka* *ce* :
*Auzubillahi* *wakuduratihi,min sharra* *ma* *ajidu* *wa'uhaddiru* .

( *Sau bakwai* )

*Ma'ana:Ina neman tsari* *da Allah da Kuma* *ikonsa daga* *sharrin abinda nake ji ( *na* *ciwo),Kuma* *nake* *jin tsoransa** .

-------------------------

*BAN MANTA BA MASOYA* *WANNAN* *BOOK,DUK INA GANIN* *COMMENT DIN KU DA* *IRIN ADDU'AR DA KUKE* *YIMAN TARE DA* *FATAN ALKHAIRI A* *GARE NI.TO WLH* *NIMA INA KAUNAR KU* *IRIN SOSIE DINNAN* 🥰🥰😀.

*Na baku kyautar wanna* *page saboda Ina* *jin dadin yadda kuke* *bibyar wannan* *book dan jin yadda za'a* *Kare tsakanin Yasir da* *Farrah 🤣😂 sun ce na* *gaishe* *ku* 🌹🌷🌹🌷🌹.

*_Safiya Muhammad_*
*_Mom suzan & Aisha_*
*_Saudat_*
*_Maman ilham_*
*_Salma Muhammad_*
*_Shafa'atu *Aliyu* *galadima_**
*__Maman minal_*
*_Hauwa L Idris__*
*_Khadeejat m ishaq_*
*_Hannat Ibrahim_*
*_Siyada Umar_*

*_Da sauran Wanda ban_* *__ambata ba duk_ __Ina_* *_gdy__ _Allah yabar_* **_zuminci__** 🤝🌹🌷🥀.

~*Aaishe* *ku~*

*NOT EDITING* 🤗

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

🅿️17
📝Su Dady duk tsawon lokacin nan suna wurin a zaune basu matsa ko Ina ba.

Cikin ikon Allah Yasir karfe 10:25 pm dai-dai lokacin ya fara kokarin motsa hannun shi a hankali,Hakan yasa nursing din da take kokarin shigowa dakin dan Kara dubashi tayi saurin karasowa tana cewa "Sannu ka farka,bari na Kira iyayen ka daman suna ta jiran farkawar ka"ta fita da sauri.

Momy tana ganin tahowar nursing din ta tareta cikin sauri tana tambayar ta ya jikin dannasu.Dady ma ya taso suna hada baki wurin tambayar ta.

"Kuna ji? Ku kwantar da hankalin ku ya farka yanzu,Amma yana bukatar hutu sannan kada ayima shi hayaniya a Kan shi,Yanzu zamu Kara duba shi Idan ruwan ya Kare muna sa ran zuwa gobe insha Allah zamu yi discharge din shi".tana juyawa zuwa dakin,suka bi bayanta a zukatan su suna masu tasbihi ga Allah daya tashi kafadun yaron nasu.

Daidai sun shiga Yana kokarin tashi zaune,cikin sauri suka taimaka mai ya zauna filo aka sanya ma shi a baya ya jingina da jikin bangon suna yi mai sannu.

Shi dai bai ko uffan bai ce ba,Amma Yana jin me suke fada.

Nursing din ce ta Kara shigowa tare da doctor.Cikin kulawa suka Kara duba shi tare da gyara ma shi Karin ruwan ,wata allurar ya Kara yima shi a cikin ruwan da aka jona mai,sannan ya mikowa Dady wata takarda daya rubuta magungunan da ake bukata.

"Ga shi Alhaji ku samo wadannan magungunan yanzu za'a ba shi kafin muga zuwa anjima".

Cikin sanyin jiki Dady yasa hannun shi ya amsa Yana cewa "Wallahi doctor saboda rudewa da muka yi kaga ko walet din da waya ban dauko ba,Amma bari na je yanzu insha Allah zan daw".

"To ba matsala Alhaji muna jiran ku " cewar doctor Yana kokarin futa da ga room din nursing din tana biye da shi a baya.

Dady ya mayar da duban shi wurin da Momy take zaune ta yi tagumi ba tare da ta ce komai ba ya ce "Bari na je ki kula da shi Yanzu zan dawo insha Allah,idan na dauko wayar dai a sanar da su Yaya ko"?

"To Alhaji Allah ya kiyaye,ka ce ma Farrah ta hado ma shi kayan tea saboda idan ya sun cire Karin ruwan a ba shi ko ya ji dan karfin jikin shi,Dan Ina tinanin bata San mun fito ba".

"Tau ba matsala Allah dai ya ba shi lafiya"cewar Alhaji Yana fita daga dakin.

Yana fita Momy ta matsa kusa da gadon ganin yadda ya Kara rufe idanun shi kamar mai bacci.A hankali ta ke Kiran sunan shi "Magaji! Magaji! Magaji!".

Sai a sannan ya bude idanun shi kadan saboda dishi-dishi da yake gani .

Ruko dayan hannun shi ta yi Wanda ba kanula a jiki tana mai yima shi kallan tausa yi ganin yadda lokaci daya fuskar shi ta fada tayi wani fayau alamar Yana jin jiki.

"Sannu Magaji Allah dai ya baka lafiya".

Shi dai bai ce komai ba sai idanu da ya tsura ma ta Yana kallan ta.

**************

Dady yana isowa Barhim Baba Auwal ya bude mai gate ya shigo Yana tambayar shi ya mai jikin,ya amsa "Da sauki Baba".

"To Allah ya ba shi lafiya"cewar Baba Auwal.

Ya amsa da "Amin ya Allah" yana yin parking ko marfin motar bai tsaya rufewa ba ya nufi cikin gidan da sauri

Darect dakin Farrah ya nufa ya fara kwankwasa wa.

Cikin baccin da ya fara alamar daukar ta ta ji kamar ana bugun kofa.

A hankali ta mike da addu'a a bakinta ta nufi jikin kofar a ranta tana tinanin kila Momy ce.

Turus ta yi lokacin da ta bude kofar ta ga Dady a tsaye.

"Dady ina yini?

Ba tare da ya bi ta Kan gaisuwar da take yimai ba ya fara cewa "kiyi sauri yanzu ki hada kayan tea zamu je asibiti yayan ku ne baya da lafiya,ki hamzar ta bana so mu bata lokaci saboda sai na je za'a ba shi magunguna" ya juya zuwa off-site ba tare da ya Kira amsar ta ba.

Gaban ta ta ji ya bada wani sautin *rassssss!!!!-rasssss* !!!!! da karfi har sai da ta dafe saitin zuciyarta da hannu.

A hankali ta koma dakin,plant shues dinta ta sako a hankali ta nufi hanyar kiching kamar wadda bata san tafiyar.

Cikin sanyi ta fara kokarin hada abubuwan da ake bukata da sauri ta fere arish ta fada kwai ta kada shi da magi ta yanka albasa zuwa wannan lokacin ruwan tea din da ta dora ya dahu ta juye shi a plas tare da fara soya wainar da arish din da ta hada.

Cikin ikon Allah a cikin five minutes ta gama hada komai a muhallin shi wani basket ta dauko duk ta zuzu ba kulas din ta nufi falo da shi.

A zaune ta tadda Dady yana jiranta.

Tana ajewa a Kan dinning ta yi saurin zuwa ta dauko dogon hijaf din ta ta saka tare da daukar basket din tabi bayan Dady da tuni ya nufi wurin motar shi.

Burt ya bude ta aje abincin bayan ya rufe ya shiga mazaunin drever ita Kuma tayiwa kanta masauki a sit din baya.Ya tashi motar da gudu Baba Auwal ya bude ma su gate suka nufi hanyar Alheri cleanic.

*To fns wasa farin girki* 🤣🤣 *yanzuma fa za'a* *hadu ga Yasir ga Farrah* *koya zata kasan* *ce* ?

*Ku biyo AUTAHR AREWA* *WRITERS dan* *jin yadda zata kasan* *ce* 😂😂

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

~*DAGA ALKALAMIN*~ *~AUTAH~*

*PLEASE COMMENT AND* *SHARE* 👏 .
[3/1, 6:29 AM] Hayat: *🤦‍♂️ZAMANINMU🤦‍♂️*

_(HATTARA YAN MATA)_

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*NOT EDITED* 🤗
___________________

*_Alhamdlillah ala kullu_* *_halin 🤲 Ya_ ~_Allah* *ka_~* *_wadata_* *_mu_* *_da_* _*lafiya,wadatar*_ _***zuciya,nutsuwa,kwanciyar_*** *hankali tare da arziki* *mai amfani* *duniya da lahira* .

*Ya Allah 🤲 ka karemu* *daga* *shagala,wauta,gafala,kunyatar* *bashi,rinjayar* *mazaje,kumcin zuciya da* *aikata aikin dana* *sani Alfarmar annabi* *Muhammad (S A W* ).

__________________

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

🅿️20
📝Jabir daidai sun kawo wurin round din kwado a lokacin karfe 10:55 tayi sai jefi jefi motoci ke giftawa suma ba na haya ne ba irin na masu kudi ne .

Kiran sunan shi tayi "Jabir"

"Na'am Ummah"Yana kokarin rage gudun motar dan jin me zata ce.

"Kana ji na wallahi da Kai da Magaji ku kiyayi wannan yarinyar dan na fara fahimtar makira ce duk wannan rawar kafar da kuke a kanta shiyasa take neman rainaku,kamar ku karamar yarinya ta rinka juyaku to wallahi ku kiyaye ni daga ku har ita idan ba haka ba kunsan hali na (Daman Ummahn su Jabir akwai ta da fada dukda tana da fara'a ga San jama'a,Amma bata daukar raini wannan dalilin yasa yaranta suke shakkarta fiye da mahaifin su ALHAJI Usman).
Chapter 13 · 0% Book details