← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 40

Sashe 25

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima forget din shi yayi Yana ci gaba da chat din shi a zuciyar shi Yana Kara jin jina san Kai irin na mutanan wannan *ZAMANINI*,duk da ba abin mamaki ne ba Dan abinda yafi haka ma to zai iya gani.

Har tsawon wani Dan lokaci ba Wanda ya tankawa dan'uwan shi.

Momy tunda ta fara tako matakalar benen ta hango su kowa Yana faman Shan kamshi,a ranta ta ce akwai matsala.

Da sauri Jabir ya mike ganin ta Kara so inda suke Yana cewa "Momy barka da fitowa,da fatan na same ku lafiya?"

"Lafiya Lau Jabiru,ya su Ummah taku?"

Dan darawa yayi Dan yasan inhar ta Kira shi da wannan sunan to sai tayi ta Jan shi.
"Duk lafiya Lau muke"

"To Masha Allah,kaga Farrah ko"?

"Eh na ganta harna dubata ma,naga banga fitowar ki ba da tun dazu na wuce"

"Eh wallahi tunda Husnah ta tafi na koma ciki Dan itama Nusaiba tana islamiyya,Amma yanzu nasan sun kusa tasowa"

"Wayyo Aunty Husnah harta tafi kenan,shiyasa tun dazu na so na fito Dan musha hira da ita,Ashe dai na makara"

"Wallahi harta tafi Dan yanzu nasan sun kusa zuwa"cewar Momy tana mikewa tsaye
"Bari a kawoma ko lemu ne ka sha"

"A a Momy na koshi,wucewa zanyi kar magriba tayi min a hanya"Yana tashi daga kujera.

"To Allah ya kiyaye hanya,mun gode kaji ka gaisheman da Autah shi dai ya dade rabon shi da nan gidan"

"To Momy shi insha Allah,ai zanyi kokari na kawo shi Koda da dare ne saboda ba lokaci kusan any time yana school shiyasa"

"To nagode"cewar Momy tana kallan inda Yasir yake ganin bai tanka ba yasa Jabir na fita itama ta koma part din Dady ta barshi anan.

Yana ganin Fitar Jabir daga gidan, shima ya wuce masallaci Dan an kusa fara Kiran sallar mangariba.

***************
_Wai Ina Farrah_? 🤣

Tinda ta shige dakinta ta bayan ta sha magungunan ta bata Kara fitowa ba,domin ita yanzu banda haushin Zalimu da take ji to shima Jabir ta fara jin haushin shi,Dan meye ba zaiyi wani abu aka ba,karshe ma ki zancan yaki yimata,ai dai yasan ita kadai ba zata iya banbare wannan auren ba sai da taimakon shi,Amma ba komai tunda ta ji da sauki anjima zata anshi wayar Momy ta Kira shi dan ya samo masu mafita tun kafin abin yayi nisa.

Da wannan tinanin ta kunna tv din dakinta ta kamo sunna tv tana kallo abinta har wuraren kafe takwas na dare.

Jabir har yaje gida Yana al'ajabin abinda brother ya nuna mai,Amma ya kudirta a zuciyar shi ba zai kara zuwa ba har sai Farrah tabar gidan,Koda kuwa an tambaye shi dalili zai ce kawai ba komai.

______________
Dan Allah Bilkisu kada ki cutar da wannan yarinyar ,yanzu fisabilillahi wane lefi ta aikata maki da zakiyi kokarin rabata da mijinta kwai saboda wani buri naki na hauka?"

"Dakata" malama,tana daga hannunta alamar tsawatar wa,bance maki Ina bukatar wa'azinki ba Dan haka ki adana kayanki may be wata rana zai maki amfani,ke kinsan yadda na Dade Ina shirya plan akan zuwan wannan lokacin to wallahi kar ki sake ki shiga wannan lamarin idan ko ba haka ba to ki sani du zanyi maganin ku daga ke har ita na fada maki"tana nunata da yatsa.

"Gaskiya Bilkisu ban taba sanin Ke dakikiya ce ba sai yau,a tinanina ko wani kikaga zai cutar da Farrah sai inda karfin ki ya Kare,Ashe ita Farrah bata sani ba tana tare da makiyiyar ta.lallai Bahaushe yayi gaskiya da ya ce "Ashe makashinka yana nan tare da Kai"idan ko hakane to ki sani wallahi saina tona asirin ki,muguwa mai mayar da alkhairi ya zama sharri,Kuma ki jira kiga karshen ki insha Allah sai kinyi dana sani tunda kin biyewa sharrin *ZAMANI* kina sharholiyar ki,idan anyi magana sai ku ce ai *ZAMANIN* ne ya zo da haka,ni nasan duk da *ZAMANINMU* ne ya zo da haka to wallahi harda San zuciyar ku,ke da su khairiyya idan har baku tuba kun koma ga Allah ba to zakuga yadda Allah zaiyi da ku,munafikan banza". Yarinyar tana gama fada mata ta juya cikin takun ta nabirgewa bigewa tabar Bilkisu tana bin bayanta da kallo.ko Ni dai Banga fuskarta ba 🤣😜.

Sosai Bilkisu take cizon yatsa a fili ta furta "Duk zan yi maganin ku ta hanyar nuna maku true colors dina,munafikai ku kuna tutiyar iyayen ku suna da kudi ko?to ku saurari abinda zai biyo baya"tana hararar gurin tamkar har yanzu yarinyar ce a tsaye.kafin itama ta juya zuwa gurin inda tabar saurayin nata a cikin motar Yana jiran ta.

```Kai fns🤔 ```wannan``` al'amarin na``` ```Bilkisu naga sai karuwa``` ```yake``` ```yi``` .

```Wai wacece wannan``` ```yarinyar da``` ```take kokarin``` ```tonawa``` ```Bilkisu asiri``` ?

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

[3/17, 10:55 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM* .

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .

*NOT EDITED* 🤗

🅿️39
📝Wuraren karfe tara na daren wannan lokacin farrah ra nufi dakin Momy,da sallama ta shiga.Momy ganin ita ce yasa ta mike daga kishingiden da tayi tana cewa "Kara so Mana"
Shigowa tayi tana zama kasan kafet din tsakar dakin.
"Momy dan Allah wayar ki nake so ki aro min zan Kira Aunty"

Momy kallanta tayi tana nazarin abinda taji ta fada,sannan ta nuna mata inda wayar take saman site drower.tana dauka ta fito waje,can ta nufa bayan gidan wurin wasu shuke-shuke na filawowi masu kyau wurin sai kanshi ruwa ke tashi,kamar lokacin damina.wata Yar bishiya ta samu ta jingina da gurin tana neman Nomber Jabir.

Tayi ta faman bincike contact din bata ga nomber ba,harta fitar da rai tana sakawa a ranta bari ta Kira Aunty Husnah dan taji sun je gida lafiya kwatsam sai taga wata nomber an saka Son,da sauri ta danna call saboda tafi tunanin ita ce.tana fara ringing aka yi picking,tana yin sallama bata jira ya amsaba cikin raunin murya ta fara cewa "Yaya Jabir Kuma dazu shi ne kayi tafiyarka baka jira munyi magana ba,to nidai wallahi na gaji tunda ba zaka tambaye ni ya zamuyi ba,shi yasa na Kira ka don mu samu mafita,kadan Kai nake so,Kai ne muradin zuciyata,Dan Allah kayi wani abu akai a farke auren nan".
Shiru ta ji bai tanka ta ba.ta ce "Yaya Jabir ko baka jina ne?kayi shiru ehe?"tana kokarin tsugunnawa a gurin saboda yadda ta ji kafafunta sun Kara yin sanyi.a wannan karon ma bai ko tanka ba.kawai saita fashe da kuka,kuka take yi ba kakkautawa.
Shiko Yana saurarenta dukda Yana jin sautin kukan har cikin kokon ranshi,Amma bazai iya yin magana ba.
Ziro kafafuwan shi yayi kasa daga konciyar da yake ya nufi kofar fita daga part din nashi.yana shiga cikin gidan ya konkosa dakin Momy Yana raba wayar da kunnen shi,gani yayi bata katse kiran ba Kuma har zuwa lokacin kukan take yi.kashe wayar yayi bayan Momy ta ba shi izinin shiga.sallama yayi Yana cewa "Momy naga Kiran ki ne a wayana"

"Ni kuma"?a a ba ni ce ba sai dai ko Farrah Dan ta anshi wayana tun dazu zata Kira Mamanta".

"Ok" kawai ya ce Yana fita daga dakin,Dan yasan inda zai risketa derect can ya nufa.

Saboda yanayin gurin ba wadataccen haske shiyasa baya hangota sosai har saida ya karasa gaf da ita,kafin ya ganta a tsugunne ta saka kanta tsakanin cinyoyin ta a hankali ya tsuguna gabanta Yana kallan yadda take faman sheshsheka.ji yayi tausayin kanshi ya kama shi wato saboda an hadata da shi shiyasa ta kasa samun nutsuwa,sai ya fara zargin kanshi,shin Anya yayi mata adalci kuwa?ya fiye san kanshi da yawa,Amma ba yadda zaiyi zuciyar shi ce ta kasa jure hakuri da rashinta,ji tayi kamar numfashin mutum a kanta,tsoro ta ji ya fara kamata dan haka ta dago kanta da sauri.
Idonta ya sarke da nashi suka kurawa juna ido ba tare da sun san me suke yi ba,ita ta fara kawar da kanta tana yunkurin tashi tsaye ya ruko hannunta cikin nashi Yana mikar da ita.Bata hana shi ba ya fara tafiya tana biye da shi a baya kamar jela har zuwa dakinta.A bakin gado ya ajeta Yana goge mata hawayen da suke silalowa bisa fuskarta.a wannan karon ma bata hana shi na,domin yadda take jin zuciyar ta tana tafarfasa tasan dole tana bukatar a rarrashe ta.

Cikin raunin voice ya na duban fuskarta ya ce "kiyi hakuri Beby ni ne bakya so ko?,saboda an hadani da ke kike zubar da kolla ko?banyi mamaki ba saboda ni na jawa kaina,Amma ki sani bazan iya rayuwa babu ke ba,Dan haka ki saka a ranka auren mu Babu yaji ballentana rabuwa,har sai idan mutuwa ce ra rabamu"Yana kaiwa nan ya saki hannunta ya fice daga dakin Yana jin wani abu Yana Kara tasowa daga kasan zuciyar shi.

Ita ko baiwar Allah ba sautin kuka sai hawaye da suke silalowa cur-cur daga koyar idonta.

Anan ta kife tana hawaye har bacci ya dauketa da.

Tinda ya koma part din shi yake kaiwa da dawowa a tsakiyar falon na shi,Yana neman mafita Dan yasan idan har Abbah ya Fahimci Beby bata so to tabbas zai iya raba su,shiko idan aka yi haka to an saka shi cikin wani hali Wanda zai iya sanadin rusa rayuwar shi.da wannan tinanin ya kunna kira'ar kur'ani tare da Shirin konciya a lokacin har karfe 10:30 ta yi.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

👏👏👏👏
[3/17, 10:55 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI*

*_Rabbana_*
*_Atina_*
*_fidduniyya_*
*_Hasanatan_*
*_wafil akhirati_ _hasanatan_*
*_Wakinna azabannar_* .

______________

*NOT EDITED* 🤗

🅿️41
📝Gudu yake sosai dan tunda suka taho basu tsaya a ko Ina ba,Farrah ko baccinta take ta yi hankali konce ita ce bata farka ba sai suna gaf da shiga garin Abuja.
Chapter 25 · 0% Book details