← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 40

Sashe 29

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Husnah ta fito mata da akwatinan kayanta.da sauran tarkacen ta na bukata sai wani akwati da ban da ta zuba kayan kanshi da wasu kayan sirri dukda kowanne da takadda a jiki na yadda zata yi amfani da su.
Driver ya kaisu cikin Burt din motar Yasir kafin Aunty Husnah ta sallami mai makeup ta tafi.har zuwa wannan lokacin suna a yadda suke sai faman matsitsiya takeyi Dan kafafunta har sun fara sagewa.a hankali naga Yana yimata rada a cikin kunne banji me take fada mata ba naga sai ta Kara shigewa jikin shi,shi Kuma Yana murmushi.

Aunty ce tayi gyaran murya ganin abin nasu bamai karewa ba ne,da sauri ya dago Yana dariya "to miss love ku mije ko,inba anan zaku kwana ba?"tana yin gaba.

Yana shafa Dan siririn sajen shi da dayan hannun ya ce "yo Aunty idan muka kwana nan ba kuba wallahi ko makotanku sai mun hanasu bacci ballantana ku"Yana kunshe dariya,hannunta yaja suka bi bayanta.

"Ohhh ni Asam'u jikar Hashim,yanzu Magaji saboda tsabar baka data ido ni kake fadawa haka?to wallahi kabi min kanwa a hankali na dai fadama,baiwar Allah shiyasa duk yau ta kasa sukuni duk a tsorace take"tana kamo hannun Farrah daidai sun karaso bakin motar.site din da zata zauna ya bude mata,a maimakon ta shiga sai ta rirrike Aunty Husnah tana fashewa da wani sabon kukan.tausayin Yar kanwarta ta ji ya kamata rarrashin ta ta farayi tana bata hakuri da haka har tabar kukan sai ajiyar zuciya take saukewa.Yasir duk Yana kallansu,sosai yaji tausayin kanshi ya kamashi Wai Baby saboda an hadata da shi take wannan kukan.yana ganin Aunty ta sakata gaban motar shima ya bude mazaunin driver ya zauna da addu'a a bakinshi.rufewa tayi tana yimasu Allah kiyaye hanya,itako Farrah bata iya amsawa ba saboda kukan dake cin zuciyar ta.da haka ya tayar da motar suka haura titi ba tare daya Kara kallon inda take ba.hanyar gidan Babanta taga ya nufa Dan haka ta danji sanyi a ranta Daman tana so taga Mamanta.

Har gaf da bakin kofar falon kafin yayi parking.shiya fara budewa ya zagayo kafin ya budemata,hannunta ya riko a hankali ta ziro kafafunta tana biye da shi suka nufi cikin falon.da sallama ya bude kofar suka shiga.Aunty ce kadai a falon tana kallon labarai Suka shigo.

"A a Magaji ai da kun wuce kawai dare Yana Kara kusantowa,Amma ka biyemata kuka taho nan"

Zama yayi itako da gudu ta fada Kan Aunty safiyya tana saka wani sabon kukan.dafe kanshi yayi a ranshi yana cewa "yauni na bani da wannan yarinyar,nasan haka zata yi ta min Dan ta hanani samun farinciki.

Dan tureta Aunty safiyya tayi tana cewa "ke ni bansan sakalci dagani kada ki gajiyar da ni,Kuma ki yiman shiru ko na tshi na baki guri"tana kallan yadda duk ta lafe a jikinta.

Ita dai shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya,sai can da taji duk sinyi shiru ta ce Aunty kema yanzu bakya sona ko,duk kun tsaneni"tana lumshe idonta daya jike da ruwan hawaye.

"Inji waye ya ce mun tsane ki,ba tsanar ki mukayi ba Baby gatane mike San yimaki Wanda ko Bayan ranmu nasan zaki ji dadin hakan"tana gyara mata mayafin kanta.

Yasir fita yayi Dan jin ta fara yimata nasiha mai ratsa jiki da jini,Dan haka ya koma mota yana jiran fitowar su.

Sosai tayi mata nasiha kafin ta dauko wata jaka da Kaya a ciki ta kamo hannunta suka fito.a gaban motar ta ajiyeta tana doramata jakar akan jinyarta kafin ta rufe tana yimasu addu'a,da sauri ta juya jin wani kuka Yana kokarin kufcemata saboda sai yanzu take jin maraicin rabuwa da tilon diyarta ta,dukda ta Jima Bata gabanta,Amma taji ba dadi sai dai ba yadda zatayi wannan shi ne gatan da zasu yimata.

Cikin sanyi yake Jan motar kasancewar har an fara Kiran sallar magriba a masallacin unguwar.saida yahau babban titi kafin ya Kara gudun motar Yana hamdala da hailala ga Allah (s w a)daya nufeshi da ganin ranar auren shi.tun kafin su shiga cikin unguwar bacci ya dauketa saboda irin kukan da Tasha duk ta goge kolloliyar da aka yimata.yana zuwa bakin gate din ya Danna horn Wanda aka samomai a matsayin gate man shi ne ya leko ganin mai gidanne yasa da sauri ya bude yana yimai barka da zuwa.amsawa yayi kafin ya wuce ciki.
Har yayi parking bata farka ba Dan haka daya fito zagayowa yayi ta inda take jakar ya cire daga Kan cinyarta danak ya dauketa a hannunwan shi da kafa ya rufe motar kafin ya nufi hanyar cikin gidan.A hankali ya tura tare da yin addu'ar shiga gidan.itako Bata bude idonta ba Amma ta farka tun sadda taji ya dauketa .kyaleshi tayi Dan Farrah akwaita da San jiki kamar mage 🤣.

Darect cikin bedroom dinta ya nufa da ita.shimfideta yayi Yana cire mata mayafin da nadin dankwalin da akayimata.waje ya koma duk ya shigo da kayan da suka zo da su kafin yayi arwalla,bayan ya fito ya fara tayar da ita a hankali,Amma farrah da yake bata jin nasiha shiru tayi ta kyale shi.gajiya yayi kwai ya fita zuwa masallaci.tana jin ya fita ta mike tana turo Dan karamin bakinta,rigar ta cire da sarkar ta fitar da takalmin daga ita sai pant da bra sai ondy haka ta nufi toilet,towel ta daura suma inners ta aje su a toilet din wanka ta Kara yi ta dauro alwala.tana fitowa dakin ta rufe kafinta daga akwatin kayanta shiryawa tayi cikin atamfa ta tayar da salla.tana nan har lokacin isha'i yayi ta gabatar.kafin ta fesa turare tayi konciyar ta Dan Bata jin yunwa sosai saboda ciye-ciyen da tayi.

Shiko daga masallaci wani restaurant ya nifa take away yayi masu da wasu lafiyayyun dakwalen kaji hadi da lemuka kafin ya nufo gidan.

Yana aje motar kayan ya dauka ya nufi hanyar falon.wani sanyin kanshi yaji ya ratsashi,Wai yau shi ne da Baby a gida daya karkashin inuwa daya a matsayin ma'aurata,sosai yaji wani sanyi a ranshi dukda a wani bangaren Yana jin fargaba Dan baisan ya zasu Kare da Yar rigimar tashi ba.whooooo freinds gaskiya gidan ya hadu tun daga waje wasu mayun flawors ne masu Dan Karan kyau gate din kanshi abin kallo ne,babban falo ne Wanda yaji manyan kujeru papules color komai na falon papules ne idan ka cire plasma da freadge harta labulayen kalar su ne.sai bedrooms kusan guda biyar sai wurin dinning area da site din kitchen kusa da wurin,kowanne bedroom akwai kayan purnitures masu kyau da tsada,Amma kowani daki kalar su daban kitchen din kanshi yayi masifar haduwa.

Dakin ya wuce Yana murdawa yaji shi a rufe Dan haka ya dauko spare key ya bude,can kuryar gadon ya hangota ta kanannade guri daya.light ya kunna sannnan ya aje kayan hannun shi.

A hankali ya haura gadon,danak ya mikar da ita,Bata San da shigowar mutum ba sai ji tayi an tayar da ita zaune.da sauri ta wartsake tana neman fasa ihu,hannun shi ya saka ya rufe mata bakin lura da yayi da hakan.

"Shiiiiiiiii tashi muyi salla sai ki koma baccin kin ji?"Yana Kara tayar da ita.

"Ehmm ehmm ni bana sallah fa"tana sunne Kai.

Murmushi yayi jin abinda ta ce ya ce "eh naji tashi hakanan miyi"bai Bari ta Kara magana ba ya sungumeta zuwa tiolet din.a tare sukayi alwalar ya kamo hannunta hijaf ya Mika mata wadda ya gani akan gadon,abin sallah kuwa a shimfide ya ganshi alamar anan tayi sallah.
Shiya jasu suka gabatar da sallah raka'a biyu ta Mika godiyar su ga Allah.bayan sun idar dafa kanta yayi Yana kwararo addu'o'i kafin ya fara yimata tambayoyi a game da addini,Amma Farrah tayi kememe ta kyaleshi bawai Dan Bata sani ba Dan Farrah tun tana ss one tayi saukar alkur'ani mai girma.akan dole ya kyaleta.kayan daya kawo ya bata umarnin ta juye su cikin plate,tana zinburo baki ta nufi kitchen din shiko kaman wani soko haka yabi bayanta da kallo yadda take juya kugunta sai yaga kamar tana sane take yi,Amma yayi alkawarin yau sai ya saka tayi hankali yadda zata rinka respect dinshi.
Tana dawowa ta juye ko wanne a cikin plate din.kayan fruit din ta dauka ta sake komawa saida ta wanke su kafin ta yanko su a saman plate ta kawo gaban shi ta aje.har zata juya ya ruko hannunta tana juyowa bata sani ba gaba daya ta fado saman shi.kunnenta ya lalubo Yana radamata "ko ki tsaya muci abincin nan ko yanzu nayi maki dura Kuma kinsan zan iya ko?"Yana daga mata gira.

Tsam ta tsaya suka fara ci saboda Bata so a samu matsala,Allah Allah take su gama ya fita daga dakin ta saka ke a jiki.

Suna gamawa ta kuskure bakinta,dukda bata ci na kirki ba,turare ta Kara fesawa tana kokarin hawa gado wayanshi tayi Kara,dagawa tayi taji Yana cewa to Aunty gata nan.Miko mata yayi ta amsa.a kunne ta Kara sai taji muryar Aunty Husnah tana cewa "Farrah a cikin jakar nan akwai turare yana nan a wata gold din kolba kiyi amfani da shi zaki ji kanshin jikin ki kinji ko?"

Gyada kanta tayi kafin ta amsa da" to"ta Mika mai wayar.
Dariya yayi Yana cewa" tou Aunty mungode Allah ya saka da alkhairi".Yana kallan farrah da take kiciniyar bude troly.

"To Amin saida safe" ta kashe wayar

Wuceta yayi ya nufi toilet,tana ganin turaren ta budeshi shafawa tayi a lungu da sako na jikinta.kafin ta mayar ta saka wasu riga da wando na bacci masu santsi ta hayewarta gado ta konta bayan ta Kara iskar fanka.

Ya dade Yana wanke jikin shi kafin ya fito,ganinta yayi idonta a rufe a tunanin shi harta fara bacci,Amma sai yaji tana cewa "Dan Allah ya idan ka fita ka rufeman kofar"tana Kara gyara konciyar ta.

Dan Jim yayi kafin yace "to ba damuwa"yaci gaba da Shirin shi.itako tayi tinanin da gaske fita zaiyi kamar yadda ya ansa,Dan haka taci gaba da baccinta hankali konce.a kalla ya kwashe kusan two hours Yana shiryawa kafin ya idar a lokacin kusan karfe shadaya na dare.wayan shi ya dauka ya koma bakin gadon Yana duba wasu sakonni.

Lemu ya dauko a cup wani abu Naga ya tsiyaya a ciki bayan ya zuba lemun kafin a hankali ya fara kurba Yana lumshe ido har ya shanye shi tas ya aje cup din.
Chapter 29 · 0% Book details