← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 40

Sashe 22

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya tayi sosai kafin tace "To naji kanina ya wuce,Kuma insha Allah zanyi magana da Farrah 🤣 karka damu zata yafema,Amma fa saika daina zarginta ka ji ko"?

"Insha Allah zan yi kokarin ganin na cire wannan tinanin daga zuciya ta"

"Da yafiye maka dai,Ai ranar Friday duk zamu je katsinar saboda kasan Asabar ne bikin Diyar kawu Yakubu a Dutsinma "

"Oh my God wallahi na manta "cewar Yasir Yana dafe goshin shi.

'To ai dole ka manta Beby duk ta rudamana kai,Ai wallahi gwamma haka Allah ne yake saka mata ja'iri kawai"tana mikewa tsaye ta nufi kiching .

"Ajiyar zuciya ya sauke Yana Kara mayar da kanshi jikin fulon kujerar tare da lumshe idanunshi Yana murmushi kamar mai tinanin wani abu.

Abin tabawa ta kawo mai Yana ci suna fira dan raban da yaci abinci na kirki tun jiya da dare dan hankalin shi duk a tashe yake.

Sai da akayi Kiran sallar mangariba kafin yayi mata sallama har bakin motar shi ta rako shi suna ta fira irin ta yan'uwa dan ita kadai tasan wannan sirrin nashi saifa uwar gayya wato Farrah.

Da haka sukayi sallama akan zasu hadu a katsina idan taje wurin biki.cikin gida ta koma shi Kuma ya kama hanyar komawa gidan Aunty Safiyya.

****************

Bilkisu ce a tsunne gaban malaminta ko nace boka Dan daka ga kayan daya tanada nayin aiki baiyi kama da malaman kwarai ba.
Daga mata hannu yayi alamar dakatarwa Yana mai janyo wata kwarya daga gefen hannun hagun shi wani abu na hango a cikin kwaryar shi ba jini ba Amma ya canza kala daga ruwa zuwa wani yallow-yallow da wani abu kamar ganye a ciki sosai ya Fara tsafe tsafan shi sai ga fuskar Farrah ta bayyana data Yasir.Wata muguwar dariya ya fara mai rikitarwa hahahahahaha saida ya gaji Dan kanshi ya dakata Yana ce wa "matso kiga wannan ba su ne ki ke magana akan su ba"? cikin muryar shi mai kamar ta katon zaki.

Cikin karkarwa ta Kara matsawa jikin kwaryar tana leka kanta "eh eh sune boka gagara"tana duban kawarta khairiyya dake kusa da ita.

"To a yanzu haka maganar da nake maki jiya aka daura auren su,Kuma duk Wanda ya ce zai raba wannan auren to zai iya rasa ranshi,Amma akwai mafita guda daya mahaifiyar shi Bata San wannan auren dan haka zamuyi amfani da wannan damar Dan ganin mun sanya rikici a tsakaini su sannan zamu dawo da soyayyar da yake yimata kanki,Amma kuma akwai sharadi duk ranar da ya kusanceta to daga wannan ranar asirinki zai tonu Kuma zaki fuskanci matsala kin amince ?

Tana kokarin yin magana kawarta tayi saurin cewa "Ta amince boka,mudai burinmu ya sota kuma mu samu manyan kudade daga gare shi"cewar kawar ta ta.

Daga haka ya Basu magani da yadda zasu yi amfani da shi a cikin sati daya hankalin shi zai dawo gareta.

Makudan kudade suka ajemai takalmansu a hannu su fito daga cikin kunkurimin dajin har zuwa inda suka aje direban daya kawo su kafin suka nufi hanyar da zata sadasu da garin na katsina.

```To fns Wai me yake``` ```Shirin faruwa da``` ```rayuwar Farrah``` ?

```Ko wane laifi Yasir ya``` ```yiwa Farrah``` ```Wanda yasa``` ```har take tsoran``` ```shi``` ?

```Shin ko Bilkisu zata``` yi ```nasarar shiga``` ```tsakanin Farrah``` ```da Yasir``` ?

*Duk wannan amsoshin* *suna ga AUTAHR ku Dan* *haka kudai ku* *biyoni Dan jin yadda* *wannan lamari zai kasan* *ce* .

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

*PLEASE COMMENT AND* *SHARE* 👏 .

*PLEASE COMMENT AND* *SHARE* 👏.

*PLEASE COMMENT AND* *SHARE* 👏.

[3/11, 12:07 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .

*ALHMDLILLAH ALA* *KULLU HALIN* 🤲

*YA ALLAH UBANGIJI* *KAYIMANA SITIRTA MU* *DA SITIRAR KA,BA* *DAN HALINMU* *BA* 🤲.

*NOT EDITED*

🅿️36
📝Zuwa da dare wajen karfe goma hannun Farrah ya kunbura suntum abinka da farar fata,ga taushin hannu gareta hakan yasa dandanan wurin yayi yayi ja sosai ga wani mugun zugi Yana yimata.ta kife kanta a Kan abin sallah tana sharbar kuka dan tunda ta idar da sallar isha'i bata tashi daga wurin ba.tana a haka Momy ta turo kofar ta shigo,sosai ta bata tausayi ganin yadda hannun yayi ga idanuwan ta duk sun kunbura saboda kuka.

"Bari na sanar da Dadyn ku,ya Kira doctor Umar ya zo dan ya duba maki hannun"cewar Momy tana ficewa daga dakin.
Ita dai kukanta ta ci gaba da sharba ba kakkautawa.

Momy a tare suka dawo da Dady da Aunty Husnah.kamata tayi tana kokarin dagata ita kuwa ta langabe a jikin Aunty Husnah tana Kara rushewa da wani saban kukan.

Dady Fada yayi ta yi,Yana kokarin Kiran nomber doctor.yana jin ya daga Bayan sun gaisa ya ce "Dan Allah doctor idan kana gari ina so ka zo zaka duba Farrah,rauni ne ta ji a hannunta".

"Ok ranka shi dade gani nan zuwa insha Allah"Yana katse kiran.

Fita yayi daga dakin ya nufi hanyar part din Yasir ranshi a bace.

Ga dukkan alamu Yasir zai sha fada 🤣🤣🤣

------------------------

"Wallahi Abbah na hakura da ita,Daman Allah ya riga ya kaddara ba rabona ce ba,Amma dan Allah ku barni mu rinka zuminci ni da ita,ku kanku ba zaku so zumincin mu ya samu rauni ba ta sanadiyyar faruwar wannan al'amarin,domin ni nasan wani baya auren matar wani"cewar Jabir da yake kasan kafet a zaune kusa da Mahaifin su.
Duk da Yana jin zafin rabuwa da Farrah,Amma dole ya danne zuciyar shi,ko domin kada zumincin su ya lalace.

Abbah nisawa yayi ya kalli dan nashi cike da jin dadin kalaman shi ya ce "Tabbas Ina alfahari da ku a matsayin yarana,Na ji dadin Yadda kayi tawakkali da hukuncin Ubangiji,Dan Ina tabbatar maka ko mu kanmu umarni ne muka cika,domin Allah ya riga ya rubuta shi ne mijinta,A lokacin shaf muka manta da shakuwar dake tsakanin ku,Amma ba komai kaima Allah ya baka mace ta gari wadda zata yima biyayya kamar yadda kayi Mana.

Sosai ya ji dadin addu'ar mahaifin na shi,da murmushi akan fuskarsa shi ya ce "Godiya nake Abbah Allah ya Kara girma da nisan kwana".

"Amen ya Allah Jabir,saboda yadda naga ka kontar da hankalinka nayima alkawarin insha Allah next week zan canza maka motor"

"Wooo alhamdlillah 🤲 ala kullu halin,Amma gaskiya na ji dadi Abban mu nagode Allah ya saka da alkhairi".

"Amen ya Allah"cewar Abbah Yana kokarin kunna tv.

"Ai dole kake canza mai motor,saboda an san shi ne mai hakuri"

Dukan su a tare suka Juya dan jin muryar Ummah a bakin kofar shigowa falon.

Ci gaba tayi da cewa "ita figaggiyar yarinyar da kuka dauki son duniya kuka Dora mata Ai ita bata San naku yaran,domin kuwa da tana San su,to da ta so Wanda kuka aura mata.yarinya karama sai wani lallabata ake yi,to wallahi inhar ni na haifi yarannan to sai Magaji ya saki wannan yarinyar tinda har ta iya nuna bata kaunar yarana to Nima bana kaunar ta daga ita har wannan munafikar uwar ta ta"sosai tahau ruwan masifa ba kakkautawa.
Shi dai Abbah ko kallonta baiyi ba,a karshe ya ce "Jabir jeka na sallame ka Allah ya albarka ce ku da sauran yaran musulmi"

Sai a sannan Jabir ya motsa dan duk fadan da Umman su take yi Kan shi kawai ya sadda Yana sauraren ta.Mikewa yayi Yana yiwa Abban su godiya ya fice daga part din Yana jin zuciyar shi ba dadi Dan kwata-kwata Jabir baya San hayaniya Dan shi ma'abocin raha ne Amma baya da fada ko kadan.
Da wannan tinanin ya shige part din su Yana Kara kokarin danne zuciyar shi.

Ummah kuwa saida ta gaji dan kanta kafin ta yi shiru da bakinta,Dan ganin Wanda take yin fadan domin ya tanka ko kallo bata isheshi ba Dan haka taja kafafunta fuuuuuuu ta nufi dakin ta tana huci kamar zakanya 🤣🙊.

************
A gidan su Farrah kuwa baiwar Allah kafin karasowar doctor ji tayi kamar hannunta zai fita saboda azabar zafi,har wata zufa take ketowa daga goshinta kamar wadda maciji ya ciza.

A tattare suka shigo da Dady sai Doctor na biye a bayan shi,sai Kuma Yasir da aka tattago shi Yana faman cira ido. Yana karasa shigowa ya hangota rungume jikin Aunty Husnah tana faman jijjuya kanta dan kukan yanzu ba hawaye saboda har sun kafe sai dai kukan zuci.
Wurin ta ya karasa da sauri Yana kokarin kamata tare da cewa "Subahallah Beby meya same ki haka?Daman baki da lafiya ne?ko wani ya taba min ke"?duk a lokaci daya ya jero mata wannan gustion din.

Ita kuwa Farrah abin tausayi tana jin muryar shi ta Kara kankame Aunty Husnah idonta ta Kara rufewa gam Dan yanzu ita ta tsani ganin shi,Dan gani take yi kamar cizon ta zai Kara yi.

Aunty Husnah cikin jin haushi ta ce "malam tashi ka bamu waje idan mun gama ka zo kayi jinyar ta"tana Kara kauda kanta site guda.
Jiki ba kwari ya koma gefe guda ya tsaya, doctor ya fara duba hannun ganin yadda ya kunbura,Kuma ga dukkan alamu idan aka Bari ya kwana to zai yi ruwa dan haka ya dauko box din kayan aiki wata fata da yaga ta Dan tashi ga dukkan alamu rufe wurin zata yi kawai ya yanketa tare da rubuta magunguna da allurai ya ce a siyo su yanzu yayi mata,kafin zuwa da safe kunbirin zai saki.
Dady ya amsa takardar Yana mikawa Yasir da duk kunyar da fargaba sun rufe shi,Dan ya fahimci yadda Dady ya dau abin da zafi to zai iya yanke ko wane hukunci.
Chapter 22 · 0% Book details