← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 40

Sashe 26

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta fara motsa hannunta jin an Kara rike ta yasa tayi saurin bude idonta,sai yanzu ta tuna da inda take saboda ta ji dadin baccin.

Hannun ta take bi da kallo har zuwa Kan hannun shi ganin wasu gashi baki masu salki da sheki konce saman fatar shi yasa ta ji ya wurin ya birgeta,Kara kura idonta tayi tana kallon kekykyawar fatar shi.A hankali ta fara kokarin zare hannunta daga cikin nashi.ganin haka da yayi yada yadan sassauta rikon da yayi mata,zare hannunta tayi tana turo bakinta,Amma a ranta tana son ta shafa wannan gashin na hannun shi,Dan ita fa gaskiya ya birgeta.

Hanyar gidan Aunty Husnah ya nufa da ita.

Jabir kuwa tunda yaga tafiyar bro din nashi,ya mayar da kalla shi ga Bahijja.ita ko cikin kunya ta dan ja gefen mayafinta tana Kare fuskarta.

Cikin dariya ya ce "lallai kina da aiki,wato ni kike jin kunya ko? To gwamma ki yakice ta tun yanzu,idan ko ba haka ba to ni zan fara cire maki ita,Dan ga dukkan alamu wannan kunyar zata iya cuta ta eheh,na dai fada maki"Yana yin gaba ta bishi a baya.A tare suka shiga falon,sallama suka yiwa su Momy akan zai mayar da ita gida kafin ya wuce gurin aiki.

Sosai Momy ta nuna farin cikin ta akan wannan hadin,tayi masu addu'a da fatan alkhairi,har tana jan Bahijja tana cewa "shi dai wannan da kike gani yana da farin jinin Yan mata,Dan haka sai kin zage damtse kin kama kayan ki,idan ko ba haka ba to *YAN MATAN* *ZAMANI* su kwace shi".

Ita dai Bahijja sai dai tayi murmushi Dan Daman can bata fiye yawan magana ba.
Da haka suka yi mata sallama ya nufi goruba road Dan ya sauke Bahijja,shi Kuma ya wuce gurin aiki.

**************

"Lallai zan tarwatsa farin cikin su,zan ruguza jin dadin su,Wai meyasa wannan lokacin yake zuya min baya?A lokuttan baya Ina ganin nafi kowa samun nasara,Amma yanzu meyasa burina yana gaf da cika sai watsu matsalar take kokarin dakatar da ni ne? why?why?"tana dafe goshinta.

Daga bayanta ta ji an dafa kafadar ta,hakan yasa ta juyo ganin khairiyya ya ce yasa ta ture hannunta gefe daya tana yimata mugun kallo.

Itama khairiyya tashi tsaye tayi tana cewa "Kinga me yayi zafi haka kike kokarin hucewa a khaina"itama tana hararar ta.

Bilkisu jiyowa tayi fuskar ta sharkaf da hawaye tana yimata kallan kin isa ,cikin kakkausar murya ta ce "kema ban yarda da ke ba,domin na fara tinanin akwai saka hannun ki a cikin wannan al'amarin,Dan haka ko ki fada man gaskiya ko na dauki mummunan mataki a kanki"tana matsota.

"Haba kawata ke kinsan bazan taba cin amanar ki ba,Kuma bazan yarda a haka baki da ni ba wurin hana cikar burin ki ba,Amma yanzu yi hakuri zauna ki sanar da ni matsalar da take faruwa dan musan yadda zamu shawo Kan lamarin"tana kokarin zaunar da ita a bakin katifar.

Hawayen fuskar ta take gogewa kafin ta mayar da dubanta ga kawar ta ta cikin rauni ta ce "na shiga cikin wani yanayi sakamakon mummunan labari daya riske ni a yanzu,Wai Yasir sun koma Abuja shida Farrah a matsayin ma'aurata ni Kuma sun barni anan da dawainiyar ciwon San da,Dan Allah ki fada min ya zanyi?wace hanya zan bi dan ganin na mallaki Yasir a rayuwa ta,domin shi ne farin cikina,Ina ji a jikina idan har na rasa shi bazan ci gaba da rayuwa ba"tana Kara rushewa da kuka tare da dora kanta bisa kafadar Khairiyya.

Khairiyya Wata munafikar harara ta bi bayan ta da shi kasancewar ta kontar da kanta a jikin ta,wani tinani ya zo mata a ranta Dan haka cikin sauri ta dagota tana goge mata hawayenta tare da kontar mata da hankali kafin ta ce "Ke matsala ta da ke kenan,yanzu saboda namiji kike zubar da hawayen ki a banza?wallahi har kin bani kunya,haba sai kace ba mace ba ya kamata kiyi amfani da wannan damar wajen ganin kin hanasu konciyar hankali,ki haddasa fitina a tsakanin su,ya zamana har sai Kinga bayan farin cikin su kafin ki rabu da su,Kinga daga nan cikin samarin ki kawai sai ki zabi daya ki aura,tunda suma da kudin su ko?tana kokarin ganin da wace fuska zata anshi wannan shawarar ta ta.

A hankali Bilkisu ta nisa tare da sauke ajiyar zuciya tana duban kawar ta ta ta ce "Wallahi shiyasa nake Kara sonki kawata,Dan ni kota-kota wannan tinanin bace min yayi sai yanzu naga dacewar hakan,hakan kawai za'ayi".tana gogen sauran hawayen da suka bushe a saman fuskar ta.

Da haka suka ci gaba da tattatuna yadda zasu tafiyar da al'amuran su.kafin sukayi sallama Khairiyya ta nufi gidan su itama zuciyar ta cike da sake-saken yadda zata tarwatsa rayuwar Bilkisu 🤔🤔Tau fa Ana wata ga wata.

----------------------------

Yasir Yana karya konar gidan Aunty Husnah ya fara Kiran wayar ta,ba tare da bata lokaci ba tayi picking .Bayan sun gaisa yake sanar mata suna gaf da shigowa gidan ta zai kawo Farrah.cikin farin ciki ta amsa tana kokarin hada masu abinci.

Bayan gate man ya bude masu gate din a wurin parking yayi masauki,shaya fara fitowa kafin ya zagayo ya bude site din da Farrah take.

A hankali ta sauko da kafarta daya,kafin ta karasa fitowa hannunta ya riko suka jera zuwa cikin falon,sadda kanta tayi tana turo bakinta a ranta tana cewa "Ina dalili mutum sai faman kwakube min hannu yake yi kaman na shi ne"

Kamar yasan tinanin da take yi ya ce "ba hannunki ne kadai nawa ba,yanzu gaba dayanki kin zama mallakima sai yadda naga dama zanyi da ke,Dan haka ki lallaba ni inba haka ba........hmmm"Yana sakin wani shu'umin murmushi,tare da kallanta ta kasan idon shi.

Da sauri ta dago kanta tana kallan shi,saboda tayi mamakin jin abinda ya ce.bata ce mai komai ba kawai ta kauda kanta suka ci gaba da tafiya.

Daidai bakin kofar falon suka tsaya,door bell ya Danna Yana sakin murmushi.

Aunty Husnah ce ta bude cikin farinciki ta ce "woooooo luck at beautiful couples,Masha Allah gaskiya kanne na kunyi kyau"tana dariya ganin yadda Farrah ta Kara hade fusu kamar hadari.

Hanya ta basu suka wuce cikin falon.zaunar da ita yayi kafin shima ya zauna kusa da ita.yana sauke ajiyar zuciya saboda yadda yake jin gajiya.

"A lallai irin wannan zuwan bazata,Ai ni jiya fishi nayi shiyasa na tahowata ganin Dady ya hana na taho da ita"cewar Aunty Husnah tana aje masu kayan abinci a Kan dan table din saman kafet.

"Hmmmm ai yanzu gamu mun zo da kanmu"cewar Yasir yana Jan table din gaban shi.

Cikin yin kasa da voice ya ce "Beby ki ciyar da ni yunwa nake ji"

Shiru tayi ganin Yadda Aunty Husnah take kallanta,sai tayi kamar bata ji ba.

Shima kyaleta yayi yaci gaba da magana shi da Aunty.

Sai can Aunty Husnah ta galla mata harara "ta ce wallahi Farrah yau so kike na fara bata maki rai anan gidan"

"Ehm to menayi Kuma,ni kullin nace mai laifi,komai zanyi banyi daidai ba"tana sunburo baki alamar shagwaba.

"Ban sani ba"cewar Aunty Husnah tana mikewa tsaye "Kuma ki bari na dawo na tadda baki zuba ma shi abincin ba".tana wucewa dakin ta.

A hankali ta fara zuba mai abincin tana gunguni kasa-kasa.da haka ta gama tana turamai gaban shi ta mike da sauri ta nufi cikin daki,Dan tasan Yana iya cewa sai ta bashi a baki.

Girgiza kanshi yayi Yana murmushi,Dan yasan abinda takewa gudu.da haka yaci gaba da cin abincin shi.

Saida ya kammala kafin Aunty Husnah ta fito,har wajen Motar ta rako shi suna Kara tattatunawa.

"Yanzu dai kasan dole kayimana alart ko, saboda saina Kara gyara yarinya ta kafin ka dauketa,Dan naga alamar idonka a bude yake,Dan haka nake so Muje gurin *AISHA ALIYU* *GARKUWA* ta gyara Mana ita tsaf yadda zaka rinka yimana kuka"tana kunshe dariyar da take neman kufce mata.

Murmushi yayi Yana cewa "Ai kyaleni da ita,wallahi ko zata gane kuranta,Dan kinsan cewa tayi ni raggo ne tau so nakeyi tsakanin nida ita a gane waye raggo?".

"Karfa kasa in hanaka ita,Dan nasan wannan tazurancin naka saika fanshe shi,to wallahi zan iya hada maka bom ya tashi da Kai"tana yimai dariya,ganin yadda danda nan ya marairaice fuska Yana bata hakuri.

"Na tuba Aunty da wasa nake yi,bazan yimata komai ba".

"Tau yanzu dai ka sallame mu kafin a gama gyaran gidan".

"Ba matsala ki turoman nomber account,zuwa anjima idan na zauna saina turo maki ko?".

"Tau mun gode Allah ya kara arziki,Kuma Dan Allah idan ka tafi karka isheni da zarya Dan so nake yi yarinyar ta taji gyara ciki da waje".

"A beg My Aunty 🙏Yana hade hannuwan shi guri guda"

Dariya ya bata sosai ganin yadda yake rudewa yanzu duk ya daina wannan Shan kanshin nan,lallai Farrah tayi dace,idan harta kontar da hankalinta to zata ji dadi a gurin Magaji.

Da haka ya shiga motar shi,yayi mata sallama tare da cewar gobe da yamma zai dawo,saboda yana da ayyuka a office.itama Aunty Husnah ta nufi cikin gida.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

👏👏👏👏👏.
[3/17, 10:55 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

_____________________________

*AREWA WRITER' ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN KAI* .

*NOT EDITED* 🤗

🅿️40
📝 Murmushi yayi Dan jin wata dubara ta fado mai a ran shi.ya kudirta a zuciyar shi a gobe litinin da safe kafin ya tafi zai aiwatar da wannan plan din,Dan Yana jin karfin gyuywar insha Allah zaiyi nasara.da haka bacci ya dauke shi Yana Allah Allah safiya tayi.

A washe gari ne itama Farrah ta shirya nata plan din Wanda take ganin idan har tayi haka to zata iyayin nasarar rabuwa da wannan likakken auren, kodan ta auri zabin ranta.

Karfe takwas ya fito cikin Shirin shi sai tashin kanshi yake yi,jakar wasu kayan shi ya saka cikin bort sai wayoyin shi da ya zuba cikin ajjihun rigar shadda.cikin gidan ya nufa Yana Addu'ar Allah yasa a yau yayi wenner dan gaskiya hakurin shi ya fara kasawa,gwamma a ba shi matar shi tun kafin wata matsalar ta taso.
Chapter 26 · 0% Book details