← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 40

Sashe 23

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sanyin jiki ya saka hannuwan shi biyu ya amsa ba tare da ya ce komai ba ya fice Dan baya bukatar Karin bayani.part din shi ya koma walet din kudin shi ya dauko da wayoyin shi ya zuba a cikin aljihu sai key daya riko.cikin sauri ya shiga Motar shi da gudu ya nufi gate Yana faman Danna horn tun kafin ya karaso gurin Baba Auwalu ya bude yana mamakin wannan sauri na uban gidan na shi,domin kuwa da ga gani ba lafiya a cikin gidan.su Dady da Doctor Falo suka dawo Dan jiran dawowar shi.inda ita kuwa Farrah kamar mai nakuda haka ta koma abin tausayi.

Suna cikin wannan halin ya shigo da ledoji a hannun shi,karba yayi doctor ya fara hada Allurar Yana cewa "Gaskiya Alhaji na kasa gano ko meye ya cijeta,domin kuwa wannan ba cizon zuma ne ba Dan wurin ya fashe ne shiyasa".

"Ai doctor ba zaka iya gano ko meye ba,Dan wannan cizon mutum ne ya kunbira mata hannu haka"

"Mutum dai"?

"Kwarai kuwa,ga garjejen katon daya cijeta nan a gaban ka"Yana nuna Yasir da yake jin kamar ya tashi ya ruga saboda kunyar da yaji ta rufe shi,Dan shi harga Allah kawai ji yayi Yana marmarin ya cijeta shiyasa,Amma baiyi tinanin lamarin zai kawo har haka ba.

Doctor murmushi kawai yayi Yana girgiza kai,ya nufi dakin Farrah suna binshi a baya.

Tana jin Aunty Husnah ta ce ta tashi ayi mata allaura,Ai ko ta Kara rudewa tana rike ta,Dan a rayuwar ta ta tsani allura gwamma ta sha magani da ayi mata allura.

Doctor yayi ta faman ta tsaya abin ya gagara Dan Aunty bata iya riketa fisgewa take yi.

Cikin kosawa Dady ya ce "ke saketa ku fito falo dukan ku,Magaji ya riketa tinda nema take yi ta Bata Mana lokaci"Yana ficewa daga dakin suma duk fita suka yi aka barsu da Doctor sai Magaji da yayi shiru kanshi a kasa baya da alamar motsawa .ganin haka da doctor yayi yasa ya matsa kusa da ita Dan har sha daya takusa yi.zai riketa kenan Yasir yayi wata Zabura yana cewa ke "tashi na ce maki"
Zaune ta tashi tana girgiza kanta alamar bata so.

A hankali ya durkusa a gabanta Yana kokarin saka idanuwan shi cikin nata,Amma taki bashi damar yin haka ta hanyar Kara rufe idanuwan ta.hannuwanta ya hade guri daya ya cukukuyeta ya saka ta a faffadan kirjin shi,kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya.
A saitin kunnenta ya rada mata "wallahi dakin kuskura kika yi wani motsi anan zan Kara maki wani sabon cizon tunda kin rainani".

Baiwar Allah lamo tayi a jikin shi tana kokarin mayar da kukan da yake kokarin fitowa.A haka ya jaye Hijaf din jikinta gefe daya ya Dan daga rigar jikinta ta gefen da za'ayi allurar Yana cewa "Doctor yimata a haka"

Doctor da yayi shagara Yana kallan ikon Allah,sai a sannan ya samu damar matsawa ya fara cira mata siringin a hankali.

Tun tana daurewa harta kasa saboda zafin da taji Yana shigar ta, Ai tana jin ya gama saka siringin duka ta zabura zata mike da sauri Yasir ya Kara riketa yadda ba zata iya kwacewa ba.Ba yadda zata yi Dan haka kawai itama ta rike shi gam tana zubar da kolla har ya gama ya zare siringin tana a haka.

Sun Jima a haka har doctor ya fita bata sake shi ba,Dan ji tayi wani bacci Yana kokarin daukar ta.saida yaji motsi alamar tafiya kamar za'a shigo dakin kafin ya dauketa ya mayar da ita bisa gado Yana kokarin cire mata Hijaf.
Da sauri ta rike cikin sanyin muryarta ta ce "ka kyale ni hakanan bana so,Kuma ka sani saika sake ni na auri Wanda nake so tunda Kai ka tsane ni"tana mai juya mai baya.

Murmushi yayi Dukda ya ji ciwon maganar ta,Amma yayi mata uziri Dan auren su mutu ka raba ne Babu zancen saki.
Har ya bude Baki zai yi magana kawai sai ya juya ya fita. tana jin fitar shi ta Kara gyara konciyar ta tana addu'ar Allah ya saka mata.

A falon ya riske su doctor Yana nuna masu yadda za'a Bata maganin idan ta farka.wucewa yayi ya nufi part din shi Yana jin zuciyar shi na yima shi suya.

A wannan ranar duk a haka suka konta ransu ba dadi,Dan shi Yasir haushin Farrah yake ji wato danta gama raina shi,shi take cewa ya saketa,hmmmm Beby kenan ai ki fara Shirin zama da ni,domin kuwa ni ne kaddarar ki.

Ita kuwa Bayan fitar shi bacci mai nauyi ne ya dauketa sakamakon allurar da aka yi mata,ga kuka da ta sha.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

👏👏👏👏.
[3/11, 12:07 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .

*NOT EDITED* 🤗

*WASHE GARI*
Tun gab da asuba ta farka jin jinkinta alamar zazzabi ga kanta Yana faman Sara mata,wanka ta shiga tare da dauro Arwalla ta kabbara sallah tana Kai kukanta wurin zaljalali akan ya zaba mata abin da yafi alkhairi a rayuwar ta.saida ta ji an tayar da sallah kafin ta yi tata,bayan ta idar dakyar ta rarrafa zuwa Kan gadonta ta konta tana jin zafin zazzabin Yana karuwa.

Sai karfe Tara Momy ta shiga dakinta bayan ta kammala break,Dan ta tayar da ita.Gani tayi tana bacci,a hankali ta fara tayar da ita.
Dakyar ta bude idanunta saboda nauyin da kanta yayi."Momy kaina ciwo yake yi"tana dafe barin goshinta da hannu.

Jin jikinta tayi yayi zafi,"Subahanallahi Farrah zazzabin ne?tashi kiyi break sai kisha magunguna"kamata tayi ta kaita toilet ita Kuma ta nufi kiching.
Bayan ta fito bakin gadon ta zauna ta buga uban tagumi tana tinanin meke Shirin faruwa da rayuwar ta ne?ta kasa gane inda matsalar take.
Momy ce ta turo kofar dakin da tire a hunnunta ajewa tayi Kan kafet tana yimata sannu,tea ta hada mata mai kauri ta Mika mata bayan ta dan Sha ta ballo magungunan kamar yadda ta gani a rubuce ta Mika mata.tana Sha ta fara kokarin yin amai,Amma Allah ya taimake ta Bata yiba,Dan haka Momy ta Kara gyara mata filo ta konta.bargo ta rufeta da shi tana tattare kayan ta fita da su.ita ko rufe idanunta tayi tana jin haushin Ya Yasir,Dan tasan yau Aunty Husnah zata wuce Abuja shikenan ya ja mata Dan tasan Dady ba zai Bari a tafi da ita ba.

~~~~~~~~~~
"Gaskiya boka gagara ni bazan yarda ba ace na baka kudi amma aiki yaki ci,Dan wannnan shi ne burin da take raina naga ya rabu da ita hankalin shi ya dawo gare ni".

Cikin amon muryar shi marar dadin saurare ya ce "A wannan karon zamuyi nasara a kansu,Amma hanyar da zamu bi ita ce :yanzu haka tana konce Bata da lafiya zamuyi amfani da wannan damar ta hanyar tura ALJANI ya Kara rikita rashin lafiyar daganan sai a sanya tsanar shi a zuciyar ta ta birki ce mai har sai ya saketa,Dan shi Yana da yawan yin addu'o'i shiyasa yake neman gagarar mu,Amma ki kontar da hankalinki".

"Yauwa boka yanzu muka ji magana"cewar khairiyya da take gefenta.

Kudi suka Kara masu yawa suka ajemai suka bar wurin cikin farinciki.

**************
Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un shi ne kalmar da ta fito daga bakin shi lokacin da ya farka daga baccin da ya dauke shi tun bayan ya dawo daga sallar Asuba.
Sosai ya ji gaban shi ya fadi tinawa da yayi da mafarkin da yayi na ganin Farrah a cikin wani mawuyacin hali,Yana ta kokarin taimakon ta Amma sai yaga wata yarinya ta shiga tsakanin su.
Saukowa yayi ya shiga Wonka Yana gamawa ya dora arwallah tare da shiyawa,duk cikin sauri yake Shirin Dan burin shi ya je yaga ya lafiyar Beby take.

Part din ya shiga da sallama dauke a bakin shi.Su Momy suka amsa bayan ya zauna Yana gaishe su yake tambayar jikin Farrah,amsa mai tayi da sauki Dan ita Aunty Husnah sama-sama ta amsa saboda ta ji haushi ga shi nan ya jawowa yarinya cuta ba gaira daga cizon soyayyay ita ya zamar mata na wahala.
Ganin yadda suka yi biris da shi yasa ya nufi dakin ba tare da ya Kara ce masu komai ba...A rufe ya riketa Dan haka ya zauna kusa da ita Yana Dora hannun shi saman goshinta jin ba zafi sosai sai zufar da take yi.karfin fanka ya Kara mata,Yana janye bargon da aka rufeta.sosai ya ji tausayinta ya zarga zuciyar shi da bargon jikin shi.Dan karamin bakinta yake kallo ganin yadda take motsashi gwanin sha'awa.jiyayi gaban shi ya Kara faduwa Dan haka ya fara karanto addu'o'i Yana tofa mata cikin kwarewa da sanin haruffan larabci. A kalla ya dau tsawon 20 minutes kafin ya fita daga dakin bai tsaya a falon ba kawai ya wuce part din shi.

Wata muguwar dariya ya fara saida gaba dayan dajin ya amsa saboda karfin muryar shi,tsagaitawa yayi Yana wasu irin surutai masu kama da yare "Ai ko ya tabowa kansa tunda har ya konaka,sai na kaskantar da shi,idan ko har hakan Bata samu ba to sai dai ka koma jikin Bilkisu Dan tun farko na fada mata"Yana kaiwa nan ya kara kwashewa da wata mahaukaciyar dariya kafin naga a karo na biyu.

Kasancewar ranar lahadi ne ba aiki Dan haka yasa Jabir shiyawa cikin wata shadda kalar sky blue dinkin zamani,yayi kyau sosai bai saka hula ba sai kanshi da ya gyara.karfe hudu na yamma ya nufi Barhim dan ya gaisa da Farrah Dan ya Kira Momy take cemai ai Bata jin dadi.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

👏👏👏👏👏👏.
[3/11, 12:07 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .

*NOT EDITED* 🤗
Chapter 23 · 0% Book details