← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 40

Sashe 12

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momy ko bayan tafiyar mai gidan nata,sosai ta lula duniyar tinani Dan ita a nata bangaran tafison a hada Jabir da Farrah, saboda tafi sabawa da shi Kuma zata fi samun kulawa da nasuwa sabanin Yasir da Basu Shan inuwa daya.Da wannan tinanin ta mike dan Kara gyara dakin mai gidan nata.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

*PLEASE COMMENT AND* *SHARE* 👏.
[3/1, 6:29 AM] Hayat: *🤦‍♂️ZAMANINMU🤦‍♂️*

_(HATTARA YAN MATA)_

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*NOT EDITING* 🤗

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

( *Innalillahi wa'inna* *ilaihirraju'un Allahumma* *ajirni* *fi* *musibati wa'akirni kairan* *minha* ).

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

🅿️16
📝Duk wainar da ake toyawa a wannan lokacin Farrah bata sa ni ba har zuwa dare har zuwa dare bata fito ba Kuma ba Wanda ya bi ta kanta.

Shima gogan naka Yasir tunda ya dawo daga masallaci bai Kara fitowa ba har zuwa dare.sosai naga fuskar shi ta dan fada eyes balls din shi sun Kara fitowa waje a cikin yini daya duk ya fara susucewa,Damuwar shi daya kada su Dady su bada Farrah ga Jabir ko saurayin da suka ji tana waya da shi,Idan kuwa haka ta kasance shikam kila ajalin shi ne ya taho.A bangare daya na zuciyar shi tana umartar shi daya fito ya sanar da Farrah hakikanin abinda ke cikin zuciyar,kada ya bari garin kallan ruwa kwado yayimashi kafa.

Da karfi ya daki dan karamin tebur din dake gaban shi gaba daya ya tarwatse kayan da ke Kai suka yi dai-dai a tsakar daki.Dandanan hannun ya fara zubar da jini sakamakon yayyankewa da yayi.Zirga-zirga ya fara yi a tsakar dakin Yana cewa "Ina imporsible bazan iya ba,daga lokacin dana furta ma ta zata Kara raina ni,gaskiya bazan iya ba idan ko har ban sameta ba dole na bar kasar nan gaba daya".

Sosai Yasir ya rude kuka take yi kaman Wanda akayi ma mutuwa a karshe jiri ya dauke shi anan ya zube saman kafet din a sume.

Jabir ne gaban Ummah Yana ta damunta akan maganar Farrah,Duk yabi ya isheta.
Cikin jin haushi ta ce "Wai Dan Allah Jabir meyasa kake so ka mayar da ni abokiyar wasanka,Baka zuwa ka samu iyayen ka sai ni da ka raina ko? To ka baceman da gani tun kafin Raina ya baci".

Cikin sanyin jiki ya mike Yana cewa" Allah ya huci zuciyar ki"ya fita a cikin zuciyar shi Yana mamakin wannan sauyi.

_________________

Misalin karfe 8:30 na dare Momy tana zubawa Dady abinci jefi-jefi suna dan taba hira.Bayan ya kammala ya Kai duban ta gare shi ya ce "Wai ni Ina Magaji"?

"Wallahi tun dazu ban Kara ganin ya shigo ba,Amma bari na leko inga ko lafiya nasan halin shi da zuciya"ta karasa fada tana mike wa ta nufi site din Yasir.
Dady ba tare da ya ce ma ta komai ba ya mayar da hankalin shi Kan jaridar da yake dubawa.

Tana shiga ta taras baya falo saita karasa bed room din shi tana sallama shiru ta ji ba a amsa ba hakan yasa tayi tinanin ko Yana toilet.
Tana bude cotean din ta hango shi yashe saman kafet,Da sauri ta karasa tana Kiran sunan shi "Magaji! Magaji? Lafiya meya sameka?tana bubbuga shi amma shiru bai motsa ba,hannun shi ta daga taga baya ko alamar motsi.da sauri ta koma part din su tana kwalawa Alhaji kira,tasowa yayi Yana cewa "Lafiya Hajiya?meya faru?.

"Cikin tsoro da sarkewar murya ta ce "Alhaji Ma..ga.ji.. tana nuna mai part din cikin azama yayi gaba tana biye da shi a baya.Yana zuwa Dady yaga Magaji yashe a kasa baya ko motsi,sosai ya shi ma ya rikice Amma da yake namiji ne dole ya dauko dauriya ya yafawa ranshi.

"Hajiya bari na janyo mota sai inyiwa Baba Auwal magana ya taimaka Mana mu sanya shi a mota gwamma muje asibiti" fita yayi jimawa kadan suka shigo da Baba Auwal mai gadi.cikin ikon Allah sukayi nasarar sanya shi a cikin mota Momy tana kokarin shiga Dady ya kalleta "Ina hijaf dinki"?

Sai a sannan ta tuna da ko hijaf bata dauko ba,ciki ta koma da sauri ta dauko suka ja motar da sauri suka nufi Alheri cleanik .

Cikin ikon Allah tafiyar minti 10 ta kaisu asibitin,da sauri likitocin suka fara ba shi taimakon gaggawa.

A wurin gaban dakin aka dakatar da su Momy,nan suka zauna suna addu"ar Allah ya bashi lafiya.

Jimawa kadan daya daga cikin likitocin da suke duba shi ta fito,Da sauri suka tareta suna tambayar ya jikin nashi.

"Ku kwantar da hankalin ku Alhamdlillah munyi nasarar ceto ranshi,Amma yanzu munyi mai allurar bacci dan haka Yana bukatar hutu sai nan da two hours zai farka, sakamakon shork din daya same shi".

"Tau Allah ya taimaka ke mu ya tashi" cewar Dady.Dan sai a sannan ya tina da ko wayar da zai Kira yayan shi dan ya sanar mai ya manta bai dauko ba.

*_To fns koya za'a Kare_ _ga* *dai Yasir a gadon_* *_asibiti_* ?

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

*PLEASE COMMENT AND* *SHARE* 👏.
[3/1, 6:29 AM] Hayat: *🤦‍♂️ZAMANINMU🤦‍♂️*

_(HATTARA YAN MATA)_

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*NOT EDITING* 🤗

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*GODIYYA TA TABBATA* *GA* *ALLAH* *MADAUKAKIM SARKI* *MAI KOWA MAI* *KOMAI,ALLAH KA BAMU* *IKON RUBUTA* *ABINDA MUTANE ZASU* *AMFANA* 🤲.

*ALLAH* *UBANGIJI KAYIMANA* *KYAKKYAWAN KARSHE* *ALFARMAR* *ANNABI MUHAMMAD* ( *S* *A* *W* ).

🅿️18
📝Suna cikin tafiya Dady ya dauko wayar shi daya aje a gefen shi tun shigowar shi motar.

Kokarin danna callii din nomber yayan shi yake yi sai ya ga Kiran shi ya shigo.

A hankali yake rage gudun motar tare da yin picking call din ya saka ta a handfree yana mai yiwa yayan nashi sallama.

Bayan ya amsa ya ke ce mai "kanina Ina ka aje wayar ka Ina ta Kira baka dauka ba"?.cewar Abbah

"Wallahi yaya bana kusa da wayar dan yanzu nake Shirin Kiran ka sai naga naka Kiran ya shigo"

"Ok ba matsala ya iyali? Da fatan duk kuna lafiya ko"?.

"Da sauki dai Yaya wallahi daman Magaji ne muka ganshi ya fadi a cikin dakin shi to shi ne muka kawo shi asibiti,Amma ka kwantar da hankalin ka ya farka tun dazu.Sun ce da sun cire ma shi Karin ruwan zuwa gobe zasu yi discharge din mu insha Allah".

Ajiyar zuciya Abba ya sauke Yana ce wa "Subahanallahi Yanzu haka kuna asibitin ne ko kuwa"?

"Akwai maman su Nusaiba tare da shi,Amma ni yanzu gida na je dauko kayan da za'a bukata dan yanzu haka mun kusa karasa wa clinic din nida Farrah".

"To ba damuwa bari nasa Jabir ya kawo mu nida Umman su yanzu".

"A a. Yaya ai da kun bari tunda naga kaman dare ya yi sosai,da sai mu barwa safiya".

"Karka damu kanina nasan zaka ba Magaji kulawa fiye da yadda mu zamu ba shi, saboda Umman su kar ta ga ba'a yi ma ta adalci ba ko"?

"To Allah dai ya ba shi lafiya,ba komai Yaya sai kun Kara so" cewar Dady yana katse wayar dai_dai lokacin da suka yi sallama. Yana mayar da hankalin shi bisa titi.

"A hankali Farrah da ke sit din baya ta sauke wata boyayyar ajiyar zuciya a hankali tana lunshe idanun ta tare da jingina bayan ta jikin kujerar a hankali ta ji jikin ta yayi sanyi ta fara yunani a ranta may be ko abinda tayi mai ne ya saka shi a damuwa dan tasan shi da bakar zuciya
Wani bangaran na zuciyata ta ji ya bata amsa da "ke meye laifin ki a cikin wannan lamarin ?Ai ke ya kamata ki yi fushi da shi saboda ya dade Yana musguna ma ki da salan wulakancin shi".

Amma duk da haka sai ta ji babu dadi a ranta dan ko ba komai Yaya Yasir dan uwanta ne na jini Akwai alaka ta yan'uwan taka a tsakanin su.tana cikin wanna tinanin ta ji motar ta tsaya alamun su iso kenan.

Cikin sanyin ta ta bude kofar motar ta fita dai-dai lokacin har Dady ya bude burt.

Tana daukar basket din suka nufi cikin hosbital din tsayawa tayi a Bayan shi saboda door din kamar irin ta bank ne ba'a wucewa mutum biyu har sai tayi charging din mutum kafin wa wuce ciki.

Suna shiga darect make word suka wuce a dai-dai lokacin doctor shima yake kokarin komawa dan ganin an siyo magungunan.

A bakin kofar suka hadu anan Dady yake ba shi hakuri akan bata time da suka yi .

"A bakomai Alhaji kuyi sauri yanzu ku amso zamu Kara duba shi"cewar doctor suna karasa shiga dakin dukan su.

Ita dai Farrah tana biye da su kamar jela🤣 sai rabe-rabe take yi kamar wadda take jin tsoron wani ya kama ta.

Yasir ba bacci yake ba Amma idon shi a rufe yake,Koda ya ji maganar su Dady baisa ya bude su ba.

Daidai sun Karaso jikin gadon Momy ta mike tana cewa "Har kun karaso"?

"Eh mun samu karasowa" daidai yana zama akan kujerar da ke kusa da gadon.

Hannun shi ya ruko yana Kiran sunan shi Magaji,Magaji!.

A hankali yake bude idanun shi har yayi nasarar bude su gaba daya akan Dady.

"Sannu Magaji ya kake jin jikin naka"? Yana mai taba wuyan shi jin ba zafi .

"Akwai abinda yake yima ka ciwo "?

Hannun shi na dama ya da ga ya dora bisa goshin shi, alamar nan yake yi ma shi ciwo.

"Tau sannu kaga ga doctor dinnan ya dawo,bari ya cire maka Karin ruwan sai kayi burosh a baka abinci ko"?

A daidai nan doctor ya iso wurin,Karin ruwan ya cire ma shi,tare da cewa ga magungunan ku ba shi ko ruwan tea ne ya sha sai mu ba shi druks din.

"Ok ba matsala doctor mu hado mai abinci ke Farrah yi sauri hado mai yanzu".

Sai a sannan gaba dayan su suka juya zuwa wurin da suka ga Dady yakai duban shi.

A raku be suka ganta wuri guda kaman mai Shirin rugawa,sai a sannan suka ankare da ita a wurin.
Chapter 12 · 0% Book details