Sashe 21
Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbah da yake tsaye jikin kofa Yana jin duk abinda take fada ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce cikin bed room dinshi ya barta tana cigaba da kunfar Baki.
*~~DAGA~* *~ALKALAMIN~~* *~AUTAH~*
*PLEASE COMMENT AND* *SHARE* 👏.
[3/4, 11:58 PM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN MATA_ )
*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
____________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ
*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*
*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*
*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .
_______________
*NOT EDITED* 🤗
🅿️29
📝Cikin ikon Allah yana Kiran wayar yaji ta shiga,Bayan ya daga ba tare daya saurari gaisuwar da yake yimasa ba ya fara cewa "please Doctor ka taimaka Mana kar yarinyar mutane ta rasa ranta,Dan Allah kayi sauri ka zo " Yana goge zufar take tsatstsafowa daga goshin shi dukda sanyin A/C da yake kadawa dan gaskiya lamarin ya fara ba shi tsoro.
"Ok ranka dade ganinan zuwa insha Allah nan da 10 minutes zan karaso".
Katse wayar yayi Yana kaiwa da komowa a tsakiyar falon.Inda Momy ke rungume da Farrah a Kan cinyarta.
Suna a haka sukaga ji karar bude gate da sauri Dady yayi hanyar waje dan ganin ko Doctor Umar din ne ya karaso.
Daidai ya fito harabar gidan yaga Motar tana kokarin shigowa dan haka ya tsaya har yayi parking Yana fitowa ya nufeshi Yana "Dan Allah ka taimaka Mana wallahi kanwata ita kadai ta haifa idan ta rasata muma zamu iya rasa kanwar mu"
"Karka damu insha Allah zata rayu addu'ar mu take bukata"daidai sun karaso falon.
Cikin kwarewa Doctor Umar ya fito da kayan aikin shi ya fara Bata taimakon gaggawa.
Yana hada allura ya ce a miko mai ruwa a hannun shi yasa Yana shafa mata a fuska Amma shiru kake ji dukda Yana da tabbacin bata mutu ba doguwar sumace tayi saboda jijiyar hannunta tana motsawa.
Yadau tsawon 2 minutes Yana shafa mata ruwan Kanan taja wani dogon numfashi tana fisge-fisge .
Da sauri Momy ta Kara rike ta sosai tana Kiran sunan ta tana jin maganar Momy saita fashe da kuka.
"Kara riketa sosai karta fisge "cewar Doctor Umar Yana Kara hada allura a siringi.
Cikin dabara ya samu ya cikaramata allurar Yana zare siringin ta karasa zubewa a jikin Momy kamar wadda ta mutu.
"Allurar bacci ce insha Allah idan ta farka ba matsala, akwai abinda ya tsorata ta ne shiyasa tayi doguwar suma ya rubuta wasu magungunan a karamar takadda tare da mikawa Dady Yana hade kayanshi wuri guda.
Sai a sannan Dady ya nisa dan tunda suka shigo bai Kara cewa komai ba.
"To Doctor kana ganin ba matsala dai ko"
"Eh insha Allah munasa ran ba matsala dan sai nan da 2 hours zata farka,Amma a fara bata abinci kafin a bata magunguna".
"To Doctor mun gode ba damuwa insha Allah,zamuyi magana da Kai daga baya"cewar Dady suna fitowa daga cikin gidan.kowa motar shi ya hau
Motar Doctor na gaba ta Dady na biye suna fitowa shi Doctor yabi titin mani dan komawa gidan shi,Shi Kuma Dady ya nufi titin kwado Dan zuwa *FARIDA CEMIST* siyan magunguna.
Suna fita Momy ta Kara gyara mata kwanciyar ta tare da sanya mata filon kujera a kanta,Ta zauna tana nazarin wannan al'amari.
**************
A Abuja kuwa ta bangaran Yasir Yana kammala cin abincin ya wuce part din shi dan kimtsa jikin shi,Saboda duk ji yake Yana yimashi ciwo.
Shi ne bai fito ba sai wuraren karfe 8 na dare part din Aunty ya Kara komawa dan amsa Kiran da Mijin Auntyn tashi yake mai Wanda yake addu'ar nan gaba ya zama sirikin shi In Allah ya yarda.
A main falo ya taddasu dan haka da sallama ya karasa ciki tare da durkusawa saman kafet din kafafun shi a tonkwashe Yana Kara sadda kanshi kasa alamar akwai nutsuwa tattare da shi.
Bayan ya Kara gaishe su ya yi shiru Dan jin me Sirikin na shi zan ce.
Cikin dattijanta ka Alhaji Ubah yayi gyaran murya tare da fara yimashi nasiha mai ratsa jiki,Har Yasa Yasir ya fara zargin ko wani ya Mutu a cikin familyn nasu,Amma kafin ya karasa tunanin yaji Alhaji Yana cewa "Kayi hakuri Magaji mun yanke wani hukunci ba tare da shawarar ka ba,Dan ni harga Allah Kai nafi ji ba Farrah ba,Dan namiji ba'ayimai auren dole,Amma da farko ina fara baka hakuri a jiya aka dauramaka aure da Farrah.
Cikin razana Yasir ya dago kanshi yana kallan Alhaji ubah,Fuskar shi ba yabo ba fallasa dan bazaka iya tantance yanayin da yake ciki ba.
"To Amma dan Allah karka dauka munyi haka ne dan mu takurama sai dan Kai na gida ne munsan ba zaka bamu kunya ba"cewar Alhaji Ubah yana duban Yasir cikin tsanaki.
Sai a sannan Aunty sis tayi magana "Kayi shiru Magaji ko hadin baiyimaka ba"?
"Am ehm ba komai wallahi Allah ya tabbatar Mana da alkhairinsa"Yana Kara sadda kanshi kasa.
"To to.. ba komai Magaji sauran bayani Kuma kaji daga wurin iyayenka,tashi kaje Allah yayi maku albarka"
"Mikewa yayi jikin shi duk yayi sanyi Yana amsawa da "Amin".
Har yakai ga bakin kofar part dinshi Yana tinani a ranshi Anya kuwa anyima shi adalci dukda Yana San Farrah , yana da burin ya rayu da ita har karshen rayuwar shi Amma akwai matsala dan shi yasan tunda akayi haka to akwai abinda ake rufemai,Daman tun fil'azal bai yarda da yarinyar ba yanda yaga daga baya duk ta canza dabi'unta ta koyi rashin kunya da fitsara .
A fili ya firta "Kai gaskiya da sake wallahi bazai yiwu ba"yayi kwafa da hannun shi Yana karasa shiga falon nashi da yaji kayan alatu.
*_Taufa ana wata ga_ _wata me kake nufi_ _Yasir_* ?🤣😂🤣🤣😂
✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*
🤦 ZAMANINMU🤦
(HATTARA YAN MATA)
*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
__________________________

*HAPPY JUMA'AT* *KAREEM TO ALL MUSLIM* *UMMATI* 🌹🌹🌹
*ALLAH YA SADAMU DA* *ALKHAIRAN* *WANNAN* *RANA,SHARRIN DAKE* *CIKI ALLAH KAREMU* 🤲.
🅿️31
📝Yasir ajiye wayar yayi ranshi duk Yana jin ba dadi Wai meyasa Umman su tafiye yawan fada?kwata-kwata ba halayyar su daya da Momy ba,Ya kamata ace ta tambaye shi abinda ya faru Amma taki ba shi dama ballantana yayi mata bayani.A fili ya firta "zanje insha Allah,Ya Allah ka fitar da ni daga wannan chakwakiyar"Yana mai Kara gudun motar shi dan ganin magariba ta fara kasasowa.
Yana karasawa suka gaisa da mai gadin gidan daman sun saba da juna.A falo ya risketa tana yima Hibba kwalliya .
"A lallai kanina sai yau nake ganinka,duk ka biye ni nayi tinanin har yanzu kana katsina?
"Hmmm Aunty ai kinsan bazanki zuwa ba idan ina garin,yau kwana na ukku da dawowa duk abubuwa sun kara cunkusheman na rasa ya zanyi da rayuwa ta"Yana Kara lunshe eyes din shi kamar mai Shirin yin bacci.
"To mai yake faruwa kanina ?yiman bayani dan muji inda matsalar take".
"Aunty Beby"......sai Kuma yayi shiru Yana firzar da iskar bakin shi.
"Ehe Ina jinka Mana"
Shiru yayi harna wasu dakika kafin ya nisa a hankali Yana ci gaba da cewa "Aunty Wai aure aka dauramin da Beby ga Ummah ta kirani tana ta yiman fada,na rasa yadda zanyi duk sun Kara sakani a cikin damuwa".
"Hmmmm Yasir kenan na fahimceka nayi tinanin zakayi farinciki da faruwar hakan,Amma sai naga akasin haka saboda wani shirmen tinaninka Wanda baka da hujja dan Ina da tabbacin baka da sheda akan hakan,kana abu kaman wani yaro eye?to wallahi ka nutsu kasan me ya kamata kayi duk yadda kake tunanin Farrah ba haka take ba,Kuma Bari kaji wallahi idan ka bari su Abbah suka fahimci abinda kake boyewa tsaf suke warware auren su ba Jabir na fadama dan haka ka farka daga wannan shirmen mafarkin da kake yi"ta Kara she maganar tana Kara hade Fuska daidai ta karasa shirya Hibba.
Itako yarinyar da gudu ta karasa gurin Yasir tana magana cikin gwarancinta .
Daukar ta yayi Yana cillata tana kyalkyala dariya .
Sosai Aunty Husnah take kallan shi duk yabi ya saka kanshi a damuwa a zuciyar ta ta ce"Ai sai nan gaba zaka fara gano kuskuran daka aikatawa Farrah daga ranar data fara gwaraka kamar kwallon mangwaro,duk da kana kanina hakan bazai hana na zigata ta rama abinda kayimata ba".
Sai a sannan ya dire Farrah suna kyalkyala dariya cikin farinci,Dan gaskiya Yana san yarinyar she is beautiful har yana addu'ar Allah yasa Beby ta haifamai kyakkyawa kamar Hibba saboda kamar su daya da Beby (kaji su malan Yasir harda zakewa irin haka🤣🤪).
Gyara zaman shi yayi Yana Kara fuskantar Antyn tashi Dan Hibba ta ruga dakin su.
"Wallahi Aunty na rasa meya kamata nayi ga Beby duk ta rainani yanzu bata ganin girmana ta daina respect dina"
"To ai dole ta rainaka tunda ka riga ka zubar da girmanka tun fil'azal a wurinta Kai a naka tinanin a lokacin ai karama ce kana dauka bata da wayo ko?to ai ga shi Yanzu ta kasa mantawa kaga wa gari ya waya ?Inaga kawai kayi hakuri ka lallabata kuyi zaman lafiya shi ne mafita kawai"
Dan danan ya hade ranshi Yana cewa "Dan Allah Aunty ki daina taso da abinda ya wuce ai ita kanta ya kamata tayiman uziri ta manta da abinda ya wuce"Yana sosa keyar shi.
"Hahaha wallahi kanina kai dan rainin wayo ne wato sai yanzu ka tina da haka ko?wallahi kabi ni a hankali idan ba haka ba na fadawa su Dady abinda kayi har yasa Farrah take tsoranka"ta karashe maganar cikin dariya.
"Double sorry my Aunty 🙉 Yana kama kunnuwan shi alamar ban hakuri"Dan yasan halinta tsaf take korawa Dady bayani ta Kara sanya shi a cikin wata chakwakiyar.
Sosai ya bata dariya ganin yadda lokaci kalilan daga tayar da maganar duk yabi ya rude.