← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 40

Sashe 35

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daidai lokacin da Farrah ta fasa wannan Karan,yayi daidai da lokacin da Bilkisu ta farka da wani azababen Kara Wanda duka gidan saida ya amsa,innar ta ce ta fito daga dakinta ta leka dakin na Bilkisu,ganin tana ta faman fisge-fisge ga wasu sururtai tana yi marassa dadin ji,cikin sauri Inna ta karasa gareta tana riketa ganin yadda take kokarin rugawa.tana tambayar ta lafiya?meya sameta?.Amma Bilkisu ta kasa bayar da Amsa.Addu'a ta fara tofa mata, kafin ta dauko sauran magungunan ta Bata wasu ta shafa mata na shafawa kafin tadan lafa tana juya kanta.A haka Inna suka Kai har asuba ba tare da sun runtsaba da zummar zuwa da safe zata kaita *ISLAMIC DAN FODIO* *CENTER* a yimata rukiya duk a iya saninta da Bilkisu Bata da aljanu,sai dai ko daga bisani abin ya sameta.

Yasir kuwa da baisan duniyar da yake ba,ba tausayi ballantana saurare yake gudanar da aikinshi Dan akalla yaje makka sau goma Yana dawowa a tsakiyar Daren nan (🤣🤣Ina Aunty saudat kinji har garinku yaje saboda tsabar lulawa da yayi 🙈🙊).

Farrah kuwa baiwar Allah tun tana sanin me yakeyi garta fita hayyacinta tana suma tana farfadowa,a karshe tayi wata Kara tare da sakewa gaba daya jijiyoyin ta suka daina halbawa.sai a sannan ya fahimci aika aikar da yake yi,har gwamma lokacin data cije shi,da lokacin da take faman Kiran Momy,Aunty Husnah,Aunty safiyya,harda su Dady ta rinka Kira Amma baiji tausayinta ba.aiko tuni ya rude ganin bata motsi mirginawa yayi gefe daya Yana shafa fuskarta data jike sharkaf da zufa saboda wahala da ta sha.

Kayanshi ya mayar kafin ya kunna light din dakin a zuwa lokacin har an fara Kiran sallar Asubah.ruwa ya dauko masu sanyi a freadge ya zuba a tafin hannun shi Yana shafa mata a fuska,shairu yaji haka yayi ta shafa mata ruwannan kafin yaga taja wani dogon numfashi tana fisge-fisge,da sauri ya aje gorar ruwan Kan site drower kafin ya riketa, wani wahalallen kuka ta saki tana jijjuya kanta saboda azaba..sun Jima a haka kafin ya kwantar da ita bisa kirjinshi.har zuwa lokacin batayi magana ba sai ajiyar zuciya da take faman saukewa.

Suna a haka aka fara salla a masallatai,kafin ya samu a hankali ya kwantar da ita saboda yaga tayi bacci.bargo ya rufa mata jin yadda jikinta ya dau zafi sosai yaji tausayinta ya kamashi.toilet ya wuce,wanka yayi ya gyara jikin shi tare da dauro alwala,Yana fitowa ya canza kayanshi tare da fesa turare ya shimfida abin sallah Dan Yana gudun ya fita Kuma ta tashi.bayan ya idar da sallah Yana lazimi wayar shi ya dauko Yana kunnata ganin har shida saura yasa ya fara Kiran wayar Aunty Husnah tana ta ringing ba'a daga ba harta katse,Kara Kira yayi a karo na biyu kafin tayi picking.
Sallama yayi kafin ya gaisheta jin muryar shi wani iri yasa tace "Magaji lafiya meya sameka naji muryar ka ta canza ?"

"Ammh Aunty Dan Allah ki taimake ni kizo,wallahi Farrah ce ba lafiya yanzu haka zazzabi ne a jikinta,Dan Allah ki zo please"ya karasa maganar kamar zaiyi kuka ..

Tana jin haka a ranta ta ce "nasan a rina,wannan rawar Kan da yake yi Allah yasa bai kassara masu yarinya ba"a zahiri ko sai ta ce "to Bari ganinan zuwa yanzu zan biya na dauko wata freind dina Doctor ce sai muzo tare ta dubata ko"

Da "to"ya amsa kafin ya katse kiran ganin Farrah tana faman juyawa,daga gani kasan baccin wahala ne take yi.

Saman gadon ya haura ganin yadda take yakune fiska.A hanakli ya Kura mata manyan eyes balls din shi Yana kallan kyakkyawar fuskarta Yana Kara sanya mata albarka Dan yau sakayau yake jinshi kamar Wanda aka yiwa sabuwar hallitta ,ga wani Nishadi da yake ji na musamman da yake jin Yana ratsa illahirin bargon jikinshi.karan mota yaji alamar sun shigo Dan haka yayi suarin fita.

Kofar falon ya bude ganin su a tsaye ita da Doctor din yasa ya gaishe da su, Doctor din kadai ta amsa tana janshi Dan ita ko Aunty Husnah cikin falon ta nufa suka bita a baya.har dakin suka shiga kafin ya dawo zuwa daya daga cikin bedroom din yayi konciyar shi Yana jin wani farinciki Yana zagaya kolwar shi.da haka bacci ya dauke shi da farar jallabiya a jikin shi.

Aunty Husnah ta haura saman gadon tana aje hijaf din jikinta a Kan mirror kafin ta fara yaye bargon daya rufamata.da sauri ta mayar tana kawar da kanta dan jin yadda gabanta yayi wata faduwa.a sanyaye ta ce "na shaiga ukku ni Asma'u meye haka Magaji ya aikata?wannan rashin tausayi har Ina?tana saukowa ta nufi toilet Dan hada ruwan zafi . Doctor Hadiza ce ta matsa kusa da Farrah tana cewa "yaran *ZAMANINMU* ai rawar kansu tayi yawa shiyasa ake yawan samun matsala,Dan idan Kinga irin haka to gaddama tayi mai,Kuma kinsan karfinsu ba daya ne ba"taba jikinta tayi jin yadda yadau safi yasa taji yarinyar ta bata tausayi Dan haka ba tare da bata lokaci ba ta fara bata taimakon gaggawa.bayan Aunty Husnah ta gama hada ruwan cak Doctor ta kudindine ta cikin towel ta nufi toilet da ita,har a sannan Farrah bata San inda kanta yake ba saida taji an dauketa duk a tinaninta shi ne,Dan haka ta saka kuka tana magiyar ya kyaleta itakam yau mutuwa zata yi.saida ta jita cikin ruwan zafi kafin taji Doctor'n tana cewa "yi hakuri kin ji insha Allah zaki ji sauki"kafin tayi saurin bude idonta tana ganin sune Aiko ta Kara karfin kukanta,tana cewa "Dan Allah Aunty ki tafi dani wallahi ya bashi da Imani kashe ni zaiyi,wallahi nidai bazan zauna da shiba mugu ne,cutata yake yi"sai hawaye cur cur daga idonta.

"Me yayi maki?"cewar Aunty Husnah

Harta bude baki zatayi magana sai Kuma tayi shiru tana cije lebanta na kasa cin ta fara jin sauki.sai ajiyar zuciya take saukewa.

Sun dade Doctor Hadiza tana ta canza mata wasu ruwan kafin suka barta ta gyara jikin ta tazo tayi sallah Dan tuni karfe bakwai ta kusa.

Tana wanka tana zubar da hawaye da haka ta karasa,wani ruwan ta gani masu kayan kanshi a ciki tayi amfani da su kafin ta daura wani towel din ta fara kokarin fitowa.

Bango take bi a hankali tana runtse idonta harta samu ta fito,a lokacin Doctor Hadiza ce kadai a dakin ita Aunty Husnah tana kitchen Dan hada masu breakfast.

Wata doguwar riga ta ciro mata mai taushi da hijaf ta saka abin busar da Kai ta sanya mata gashinta ya bushe,kasancewar ba kitso a kanta.da haka ta dorata bisa abin sallah tana janta "gaskiya kedai Farrah raguwa ce,da haka zamu zo amsar haihuwar kina langwabewa?"ita dai batace komai ba,ta fara sallar ta a zaune.

Bayan ta idar Aunty Husnah ta kawo mata kayan Kari kasancewar akwai komai na bukata a gidan shiayasa tayi saurin karasawa,a lokacin karfe tara har tayi.

Doctor Hadiza ganin Bata ga Yasir ba yasa tayi tinanin ko ya fita Dan haka ta ba Baba mai gadi takadda da kudi ya amso masu magani dukda da Dan nisa.

Kafin a kawo maganin ta hada mata tea mai kauri da Arish sai farfesun kayan ciki da yaji tarugu da kayan kanshi.kadan ta ci tana ta faman zubar da hawaye.
"Aunty Husnah ta ce "yarinya gwamma ki zage ki ci Dan anjima da dare ma Yana iya karawa"tana dariya.

Aiki Farrah tana jin haka ta Kara rudewa tana ta karkarwa da hawaye."Dan Allah aunty ki tafi dani wallahi tsoranshi nake ji,bazan iya ba mutuwa zanyi".tana Kara volume din kukanta.

Saida Doctor Hadiza tayi ta kontar mata bata hakuri tana kontar mata da hankali kafin ta Dan ji ta samu nutsuwa,Dan Doctor Hadiza ta ce zata fadamai kada ya Kara.

Bayan an kawo maganin suka Bata tasha,kafin suka Kara gyara gadon ta konta bacci.

Doctor Hadiza tafiya tayi bayan Aunty Husnah ta anshi nomber account dinta,Dan sallamar ta tana ta yimata godiya.

Bayan Aunty Husnah ta dawo falon ta fara neman inda Yasir ya konta.can daki na biyun karshe ta ganshi Yana ta sharar baccin shi hankali konce.kyaleshi tayi ta wuce gidanta da zummar idan ya tashi ta kirashi waya tayimai bayanin yadda zai Bata maganin,sai yaje da kanshi ya anso masu abincin rana.bayan ta tare mai nafef taji Karan wayarta dubawa tayi ganin nomber Aunty safiyya yasa tayi saurin dagawa tana gaisheta.

"Amm Husnah Dan Allah kice ki duba kanwar ki kiga ko lafiya,Dan wallahi tunda jiya da suka bar nan hankalina ya kasa konciya".

Murmushi Aunty Husnah tayi kafin ta ce "Aunty ki kontar da hankalin ki yanzu haka daga can nake tunda safe ya kirani sai naje da wata kawata ta dubata, insha Allah ba matsala,komai ya daidaita".

Ajiyar zuciya ta sauke tana ji a ranta Farrah an girma yanzu kila ta Kara hankali da wayo kafin ta ce"to Husnah na gode Allah ya Basu zaman lafi ki rinkayimata nasiha da nunamata yadda rayuwa take,Dan Wallahi Ina tausayin Baby duk randa Magaji zai Kara aure zata gane kuranta".

"A a Aunty insha Allah ma bazai Kara ba saboda Yana santa,itama Kuma zata yimai biyayya insha Allah"tana dariya danjin yadda Auntyn tasu tace.

"To Allah yasa ta gyara"cewar Aunty safiyya.

Aunty Husnah ta amsa da "Amin ya Allah"kafin sukayi sallama ta katse call din.daidai mai nafef din ya iso gate din gidanta,sallamar shi tayi kafin ta nufi cikin gidan tana murmushi Dan tadan drama Bata kareba idan Farrah ta farka taga sun taho,to shikam ya bani wuni zaiyi faman rarrashinta.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

👏👏👏👏.
[3/20, 6:32 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*Masu taya Farrah jaje* *duk tana jinku tace tana* *godiya,iya wuya* *ana tare 🤝🥰 Amma fa* *Wai saita rama* 😂🤣🤣

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .

*NOT EDITED* 🤗
Chapter 35 · 0% Book details