← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 40

Sashe 38

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai zuwa dare har sun konta dakin Nusaiba ita da Aunty Husnah sai little Hibbah.can wuraren karfe shabiyu saura ta kasa bacci ta tashi.wayarta ta janyo ta tura mai texs kamar haka :Dan Allah kazo mu tafi wallahi na kasa bacci.ta tura mai.ba'a dau tsawon lokaci ba taga reply din shi "ki fito mayn falo ganinan zuwa"ai tana gani ta mike cikin tsuma ta saka silifas da hijaf saman kayan baccin ta.cikin sanda ta fice daga dakin,harta fice daga dakin Aunty Husnah tana kallanta.saida taga ficewarta tayi murmushi tana Kara gyara konciyar ta.

A tsaye ta riske shi Dan haka bai tsaya wata wata ba ya sungumeta ta Suka shige part dinshi.

Tunda asuba Farrah ta nufo dakin Nusaiba,a zaune ta riski Aunty Husnah bisa abin sallah.cikin sanyi ta wuce falo ita ko batace da ita komai ba.

Bayan itama tayi sallah,cikin turo baki ta ce "Aunty yunwa nake ji"tana kallanta.

"To Farrah ai dole kiji yunwa,irin haka tana" tana dariya.

Batace komai ba saboda wata azababbiyar yunwa da taji tana tukota,ta nufi kiccin da sauri ta dafa imdomie anan cikin tukunyar ta cinye tasha ruwan sanyi kafinta koma bacci.

A ranar ma haka suka wuni bayan sun dawo daga gidan bikin.kuma a ranar aka saka auren Bilkisu da faresu nan da wata daya,Dan yace bayaso a saka da yawa,kawai duk abinda Allah ya hore akai mata.

Itama Aunty safiyya a ranar ta shigo garin,sai gidan su Jabir daya cika da Baki na nesa Dana cikin gari,itama Aunty Fatima tazo daga kaduna dangi duk an hadu ga Yan Dutsinma iyalan kawu Yakubu da sauran yan'uwa.

Sosai Aunty safiyya taji dadi ganin yadda Farrah ta kontar da hankalin ta,ga labari mai dadi da taji na cikin da take dauke da shi.hakan yasa ta sake mata da dare sukayi ta fira a dakin Nusaiba.saida lokacin konciya yayi Farrah harta konta Aunty Husnah ta tada ta saboda yawan Kira da Yasir ya dameta da shi.ba yadda ta iya haka ta nufi part dinshi tana rangaji irin na masu jin bacci.

A washe gari dubban mutane Suka sheda daurin auren Jabir da Bahijja akan sadaki mafi daraja.sosai Yan uwa aka hadu suna ta Jan Farrah ganin yadda take ta longabewa irin na masu laulayin karamin cikin.da haka dai aka yi yinin biki duk sunsha ankon leshin mai tsada.da dare aka Kai amarya gidanta dake can ckin GRA gaba da su Ummah.kafin su tafi Farrah tana ta yiwa Bahijja dariyar mugunta ganin yadda duk take a tsorace Dan haka tayi ta Kara tsorata ta,har saida Aunty Husnah ta fita da ita daga dakin ita da Matar yayan Bahijjah.kafin aka ce Ya Yasir Yana kiranta a wajen gate din gida.a mota ta same shi suka tafi gida.tana ta mitar ita wallahi duk an saka ta gaji ga yunwa tana ji.a hanya suna tafiya ta hango mai siyar da kwakwar manja,Aiko da sauri ta saka ya tsaya tace "ya Dan Allah siyaman kwakwar can gobe tunda safe ita nake son ci".

Yasir ba yadda ya iya dole ya fita kwano guda ya siyo mata,kafin suka wuce.sauran yan bikin ko sai bayan sun Jima da dawowa kafin suma Suka karaso.

*Wai fns Ina labarin* *khairiyya? 🤔to ku biyo* *ni dan jin inda take* .

*Fns ku fara maraici tun* *yanzu 🤣 sauran* *two pages insha Allah* *book din ya Kare* .😂🤪.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*

👏👏👏👏.
[3/20, 6:32 AM] Hayat: 🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*THIS IS SECOND TO THE* *LAST PAGE* 😂😜🤣

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .

*NOT EDITED* 🤗

🅿️49
📝A washe garin biki ranar lahadi ne sauran baki suka fara komawa gidajen su musamman na nesa.sai Yan tsirari Suka yi saura.Aunty Fatima ta wuce kaduna,sai Aunty safiyya itama a ranar ta juya Zuwa Abuja,inda Yan Dutsinma suma duk a ranar suka tafi.ya rage daga Aunty Husnah sai su Farrah kadai .

Khairiyya ce a wani babban Hotel dake cikin garin Abuja,durkushe take gaban wani Alhaji mai tukeken ciki kamar Wanda zai haihu.tun tana fitar da sautin kukan ta a hankali har yakai tanayi da karfi.cikin jin haushi Alhajin nan ya nufo kanta kamar zai duketa nunata yayi da yatsa Yana cewa "na ce kizo ki tattare kayanki kibar sakin nan,Amma kinzo kin isheni da kukan banza,ada da kina biyoni baki taba tinanin wannan ranar zata iya zuwa ba ko?to kinyi kuskere khairi duk Wanda ya biyewa wannan *ZAMANIN* namu to tabbasa zaiga sharrin *ZAMANINMU* na bibiyar shi gwargwadon abinda mutum ya aikata,a yanzu alfarma daya zan iya yimaki zan tura maki one millions a account dinki Dan ki rinka siyan magani da su".

Nan take ta Kara rushewa da matsanancin kuka,cikin Kumar zuciya da tarin nadama ta bude bakinta dakyar muryarta take fita saboda tsabar tashin hankali ta fara magana "ka cuceni!ka yaudare ni,yanzu shikenan ka kasheman rayuwa!sai Allah ya saka man"tana mikewa ta nufi inda trolyn kayanta take.

Sosai Alhaji lawi ya fashe da dariya cikin karaji ya ce "wallahi karya kike yi khairi ke kika cuci kanki,domin kin biyewa San zuciyar ki da kwadayin abin hannuna,Kinga ko dole kiyi kuka da kanki ni kaina wannan cutar gogamin akayi a sanadin bin matan banza, Kinga ko Danna gogawa irinku masu kwadayi da tsallake maganar iyayensu ai ba laifi ne ba,Dan haka ki gaggauta fita daga dakin nan ga wata yarinya ta nan zata zo yanzu,Amma duk lokacin da kike da bukatar taimako to ki nemeni zan taimaka maki,nagode da shayar da ni da kikayi"Yana juyawa zuwa toilet din cikin dakin.

Da haka khairiyya taja akwatin kayanta ta fita tana sharar kollah.(khairiyya tun Bayan ta raka Farrah gurin boka gagara ta hadu da Alhaji lawi inda ya dauketa Suka tafi Abuja suna sheke ayar su,inda tayiwa mamarta karyar ta koma makaranta da zama,to shi ne a Yan kwanakin nan ta fara rashin lafiya zuwansu asibiti Bayan Yan gwaje-gwaje doctor ya tabbatar masu da tana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV,to wannan shi ne yayi sanadin rabuwarta da Alhaji lawi yanzu dai ta nufi katsina Dan komawa gidan iyayenta domin kuwa ta hadu da sharrin *ZAMANINMU* mai koyar da darasin rayuwar zaman duniya)Allah ya Kara tsare mu yasa muyi kyakkyawan karshe.

A haka da wannan safiyar ta wuce tasha inda tana shiga motar ta ciga Suka kama hanyar katsina,har zuwa wannan lokacin kuka take yi,har Yan cikin motar suka gaji suna tambayar ta ko lafiya Bata basu amsa ba Kuma bata daina kukan ba.da haka dai suka ci gaba da tafiya.

------------------------

A washe garin litinin Farrah dakyar ta yarda suka tafi Dan da farko cewa tayi ita dai ba zata koma ba ya barta anan,saboda laulayin cikin ya matsa mata sosai komai taci saita amayar da shi.akan dole ta bishi Dan yadda Dady ya bude mata wuta da fada.tun akan hanya take bacci har suka kusa shiga Abuja kafin ta farka,Aiko tana tashi ta saka rigimar saidai ya kaita gidan Aunty Safiyya,Yasir ba yadda ya iya ganin yadda duk ta galabaita yasa ya wuce.sai kwatsam Aunty safiyya ta gansu batayi mamaki ba ganin yadda Diyarta ta duk ta mugun galabaita.anan ya barta shi Kuma ta nufi gidan su.
Itama Aunty Husnah daga Barhim darect Aubja ta wuce gidan mijinta.

A bangaren khairiyya kuwa bayan taje gida Mamanta ta tsareta saida ta sanar da ita abinda ke faruwa,anan take ta yanke jiki ta fadi sai daukanta akayi ba rai.hakan yasa Bayan rasuwar ta dawo gidan yayanta dan Hausawa nacewa "hannunka baya rubewa ka yanke shi ka Yar"Dan haka yau da dadi gobe ba dadi da haka take hakuri,a karshe dai ta roki Alhaji lawi da ta taimaka ya aureta,ba tare da bata lokaci ba ya amince Dan shi Daman Yana San Khairiyya ba tare da bata lokaci ba ya biya komai cikin sati biyu yayanta yayi wakilci aka daura auren su inda ya kaita Abuja cikin iyalinshi ,haka uwar gidan da yaranta suke faman gana mata wahala danma saukinta daya shi Alhajin Yana santa Kuma Yana kokarin kyautata mata,ga gida har gida Kuma ga kayan alatu Amma haka khairiyya take rayuwa cikin zillimin cutar da suke dauke da ita har uwar gidan.shiyasa ta kafa mata Karan tsana tana ganin su suka gogawa mijinta cuta.(Kaico khairiyya har kin bani tausayi 😭).

Bayan sati biyu aka daura auren Bilkisu da farisu akan sadaki naira dubu ashirin,inda Bayan yinin biki aka kaita gidanta dake unguwar filin samji,Dan madaidaicin gidane mai dauke da kananun dakuna guda biyu sai toilet a gefe da Kan karamin kitchen,ba laifi yayanta salisu sinyi kokari Dan ba laife aka yimata na kudi suka amsa sai ya hada da abinda yake hannunshi aka yimata kayan daki irin namu na talakkawa.ganin inda aka kaita yasa jikin Bilkisu karayin sanyi tabbas sai yanzu ta Kara tabbatar da cewa duniya bata da tabbas duk Wanda ya biyewa rudin *ZAMANI* to tabbas sharrin *ZAMANINMU* zaiyi ta bibiyarsa.da haka dai ta anshi bakunci mai gidanta wafo farisu inda tayi Dana sani a wannan Daren yafi cikin kondo,Dan sai yanzu ta gane mahimmancin rike mutunci,Amma ita gashi ta zubar da nata a titi yanzu shikenan Bata da wata sauran daraja kenan a idonshi?haka dai tun tana jin nauyin shi harta sake ganin yadda ko a fuska bai nuna mata ba, ballanta ya goranta mata.

*BAYAN SATI BIYU*

tunda Farrah ta koma gidan Aunty Safiyya take shan fama,cikin ikon Allah yanzu da sauki,shiko Yasir duk lokacin da yaje ganinta sai yayi ta faman yimata Allah annabi tazo su tafi shifa ya gaji da rashinta Amma sai ta kiya,kusan ko yaushe Rai bace yake tafiya.dan haka wani zuwa da yayi ya sanarwa da Aunty Husnah abinda ke faruwa,sosai tayi ta fada kan cewar ya hada kayan lefen aje akai mata idan taga ankai ai dole ta dawo.haka kuwa akayi shida Aunty Husnah Suka je wani katon shago Suka hadi lefe na gani na fada inda aka yi akwatina guda shabiyu da sauran tarkacen,haka Aunty Husnah ta Kara yimata tsarabar kayan gyara.
Chapter 38 · 0% Book details