← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 40

Sashe 14

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai take yimai fada ta inda ta shiga batanan take fita ba,har suka shiga harabar gidan tana abu daya.

Shi dai Jabir bawan Allah bai ce ma ta komai ba sai hakuri da yake bata.

Tana fita ta nufi cikin gidan shi Kuma ya juya Kan motar zuwa clinic din ya dauko Abbahn nasu.

Yana isowa bakin kofar asibitin yaga iyayen nasu sun fito waje suna tattaunawa akan matsalar da doctor yayi masu baya ni agame da Yasir.

Karasawa yayi wurin su Yana gaishe da Dady tare da tambayar ya jikin Yayan shi,Dady amsawa yayi ai da sauki sosai.

"To Allah ya ba shi lafiya" cewar Jabir ya nufi cikin hosbital din Dan ganin ya jikin dan uwan nashi".

Dady Bishir ya ce "Ba damuya Yaya Allah ya shigemana gaba,insha Allah zan Kara yiwa mahaifin ta bayani gobe idan Allah ya kaimu dan duk abinda ya ce shi za'a bi".

"To Allah ya kaimu" cewar Abbah.

Cikin suka koma suna masu amsawa da Ameen.

Jabir yamay shiga yaga brother din shi a kwance ga dukkan alamu bacci yake yi dan ko bai ji ya amsa sallama ta.

A kujerar dake fuskantar gadon ya zauna Yana nazarin shi da Kuma irin kalaman da ya ji mahaifiyar su na fada kafin ya sauketa a gida.

A ranshi ya ce "Tabbas akwai wani boyayyyan al'amari a cikin wannan abin,Amma Allah ka zabama na abinda yafi alkhairi a rayuwar mu da addinin mu".

Yana cikin wannan zancen zucin su Dady suka turo kofar dakin, karasowa sukayi suna tambayar har yanzu baccin yake yi.

"Eh bai farka ba har yanzu" cewar Jabir.

"To taso mu wuce da safe sai mu dawo,Dan doctor sunce akwai masu kula da shi ba sai mun bar kowa ba".

Daga haka suka fice Dady Bishir shi kadai ya nufi Barhim Abbah da Jabir suka wuce GRA kowannen zuciyar shi da abinda take saka mai.

******************
*WASHEGARI*
Washe gari tunda asuba Momy ta kwankwasa room din Farrah ta sanar da ita ta zo su kammala kayan break da wuri zasu je asibitin.

Cikin ikon Allah zuwa karfe 8:00 am sun kammala komai Wanda za'a tafi da shi sun zuba a cikin basket. Suka nufi kimtsa jikin su Dan Dady har ya fito.

A bangaran su Ummah ma hakan take suna ta shiri dan zuwa ganin dan nasu zuciyar ta cike da sake saken rashin mutumcin da zata yiwa Farrah.

Duk kusan a tare suka iso bakin asibitin,motar su Jabir tana karasowa sai ga ta su Dady ta shigo.

Bayan sun firfito aka fara gaggaisawa da Juna,Ita dai Farrah tana like jikin Momy ta gaishe Da Abbah da Jabir ta ce "Ummah Ina kwana".

Yi tayi kamar Bata jita ba tayi gaba Autah Umar ya take mata baya.

Sosai Farrah jikinta ya Kara yin sanyi ganin irin yadda tayi mata.A hankali suma suka kara sa shiga ciki.Dan shi kanshi Jabir bai ji dadin irin yadda Umman tasu ta nuna ba dan shi harga Allah baiga laifin ta anan ba.

Suna shiga room din daidai lokacin Yasir ya fito da ga wanka kayan shi Momy ta ciromashi Wanda ta sako cikin jakar kayan su.

Toilet din ya koma bayan ya canza ya dawo bakin gadon dukan su suna yimashi ya jiki Yana amsawa cikin sanyi murya.

A hankali Farrah ta gaishe shi kauda kanshi yayi Yana yiwa Autah Umar magana.

Hakan yasa Farrah ta koma gefe a ranta tana cewa "Dan rainin hankali ni ya kamata na ji haushi saboda kwana nayi yatsuna suna yiman zafi damma nasha magani.

A wannan karon Umman su ta hada mai abinci ta fara ba shi.

Ita dai Farrah bata Kara cewa uffan ba har doctor ya shigo bayan ya Kara duba shi yayi discharging din su tare da jaddada masu a kula da ba shi magani,Kuma ya rage yawan tunani da sanya damuwa a ranshi.

Kayan su suka fara tattarawa dan tafiya gida bayan sunyi bill din komai.

Farrah ta dauki wasu kayan ta yi waje Daman ta gaji so take su tafi gida ga yunwa ta fara kwakularta.

Jabir Yana ganni ta fita shima ya dauki sauran kayan ya bi bayanta.

A jikin motar ya risketa kamar zata yi kuka Dan ya fahimci bata ji dadin abinda Ummahn su tayi mata ba.

Kusa da ita ya jingina Yana kallan fuskarta cikin kulawa ya ce "Matar tau kuma ba magana"?

Murmuy take kokarin kakalowa Amma yaki zuwa,cikin dakiya ta ce "Sorry Yaya kaina ne ya fara yiman ciwo shiyasa"

"Ayya sorry yanzu zamu tafi ai sai ki sha magani idan kin je ko".

Kai ta gyada ma shi saboda yadda take jin zuciyar ta nayi mata zafi kuka Yana iya kufemata ba tare da ta ankare ba.

Fitowar su Dady yasa Jabir barin gurin ya nufi jikin motar su.

Gani tayi Momy ta bata rai tana magana kamar tana fada.

Ita dai tana nan tana hango duk abinda ke faruwa.sai ta ga Abbah ya janyo hannun Yasir ya nufo motar su da shi.

Mamaki take yi ganin kowanne ranshi a bace,a ranta ta ce "may be bayan na fito wani abin ya faru".

Suna karasowa inda suke itama Ummahn su Jabir ta biyo su day sauri tana cewa "wallahi Alhaji bakuyiman adalci ba wato mayar da shi zaka yi wanna mai fuskar irin ta munafikai ta kasara kashe min shi ko"? Ta fada cikin fushi tana nuna Farrah da yatsarta.

Sosai Farrah ta ji faduwar gaba,cikin in Ina ta ce "Umm..mah..me..na.yi."?tana kwabe fuska kamar zata yi kuka .

Cikin fushi Abbah ya daka masu tsawa da cewar kowa ya shiga mota.

Kowa a motar da ya zo ya shige Abbah ya Saka Yasir motar su Farrah shima ya koma tasu suka dunguma zuwa Barhim.

Tofa fns Wai meke Shirin faruwa ne?

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

~DAGA ALKALAMIN~ ~AUTAH~

*PLEASE COMMENT* *AND* *SHARE* 👏 .
[3/1, 6:29 AM] Hayat: *🤦‍♂️ZAMANINMU🤦‍♂️*

_(HATTARA YAN MATA)_

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*NOT EDITING* 🤗

________________________

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*Bainar rujuli wa bainar* *shirki* *wal* *kufur,tarukussalat* .

*FASSARA*
*Tsakanin dan Adam da* *shirka da kafirci barin* *salllah* .

_______________________

*SUHANALLAH*
*WALHAMDLILAH*
*WALA'ILA HA'ILLALAH*
*WALLAHU AKBAR*

_____________________

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

🅿️21
📝Isuwar su Barhim keda wuya Farrah ta dauki wasu kayan da aka saka Burt din motar ta wuce cikin gidan ba tare da ta tsaya sauraren wani abuba tana ajewa ta nufi bedroom dinta da sauri ta saka key,ko hijaf dinta bata tsaya cirewa ba ta fada bisa gado tana kuwa ita ta rasa me yake damun zuciyar ta,Dan ta lura Ummah tana yimata wulakanci ne saboda zalimu ai da ta San yanda bana kaunar shi da ta samamin lafiya.
To ni mema zanyi da shi ?Ai ko kaddara bana fatan tasa na aure shi.mtsssss ta ja dogon tsaki tare da Kara mirginawa daga kwanciyar da take.

Suna karasa firfitowa Dady ya ce wa "Jabir kama Dan uwanka ka kaishi part din shi ya huta kafin mu gama tattaunawa"Yana nufar kofar da zata sada su da babban falon gidan duk suka bishi.

A hankali su Yasir suke takawa ba Wanda ya yiwa dan uwanshi magana har suka karasa cikin falon nashi.

Anan bisa kujera Jabir ya kwanta Yana jin gajiya tare da shi,ga shi yau an hanashi zuwa wurin aiki.

Yasir kuwa bedroom ya wuce cire kayan jikin shi ya daura towel a kugunshi ya fada tailet Dan Kara yin wanka.

Su Dady a babban falon suka zauna,inda har yanzu Ummah bata Kara cewa komai ba dan har yanzu haushin su take ji.

Gyaran murya Abbah yayi tare da fara ba kanin nashi hakuri akan abinda matar shi ta nuna,sannan ya Kara jaddada ma su bai yarda ta amshe Magaji daga nan gidan ba.Tunda ba ita ta kwoshi ba shi ya kawo kanshi.Kuma da kike maganar Za'a kashe maki yaro oh da bakiyi wannan tinanin ba sai yanzu ko,to wallahi zan mugun sabamaki,the last one ko ki so Farrah,ko ki Kira ya rage naki idan Allah yasa zata zama matar daya daga cikin yaran ki to mu Umarnin ubangiji kawai zamu cika .Dan haka ya rage naki cuta kuka Allah ne ya nufeshi da yinta.yana kaiwanan ya dubi Kanan nashi ya ce " ni na gama magana idan kana da abinda zaka ce bismillah,idan babu mu zamu wuce dan inaga sai naje Abujar da kaina wurin mahaifinta insha Allah.

"Bakomai Yaya duk abinda ka ce shi zamuyi,Amma inaga tare ya kamata muje Dan inaganin zaifi".

"To ba matsala karka damu insha Allah komai zai wuce"cewar Abbah Yana kokarin mikewa.

Kusan a tare suka fito Dan Ummah ko sallama bata yimasu ba ta shigewar ta mota.

Da haka suka rabu Abbah ya Kira wayar Jabir,Jim kadan sai ga shi ya fito sukayi sallama da kanin na shi ya fara tuka su suka dauki hanyar GRA.

-----------------------
Farrah ko batasan sun Jabir sun tafi ba.da kyar ta fito ta nufi kiching hannun ta dafe saman goshinta saboda tsabar yunwa da take ji,Dan lokacin har karfe goma da rabi tayi bata yi break ba.

Kular da suka dawo da ita ta buda yanda ta aje sauran arish din da waina haka ta tadda shi.plate ta dauko ta zuba tare da hada tea ta koma dakinta.

Yasir tunda ya kwanta yake aikin sake-sake a zuciyar shi har bacci yayi gaba da shi ba tare da ya sani ba.

Sosai Dady ya damu da wulakanci da Matar yayan nashi tayi mai,danma Momy na tausar shi tana Kara ba shi hakuri tunda ba dan uwan shi ya nuna hakan ba kawai ya kyaleta kanta tayiwa.

Karfe 11:30 Farrah ta nufi kiching dan dora masu girkin rana.A ciki ta taras da Momy ta kama suka ci gaba jefi jefi suna Dan taba hira.

A hankali Momy ta yi mata wanann tambayar "Wai ni Farrah a tsakanin Magaji da Jabir wanne kika fi so a cikin su kike jin idan aka aura maki shi zaki iya zama da "?

Sosai ta ji faduwar gaba dan batayi tinanin abinda zata tambayeta ba kenan .
Chapter 14 · 0% Book details