← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 40

Sashe 3

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*INA* *JINJINA* *YAN* *GROUP* *DINA*
My zee
Hauwa sani
Safiya Muhammad
Hajjo
Maman ilham
Beby
Nagode da addu'arku Allah ya saka da alkhairi Ammafa ku Kara yawan comment 🤣🤣🤣

Fiddausi umar (maman intisar) yasin haryanzu Banga comment dinki ba 😔🙄.

*NOT* *EDITING* 🤗

بسم الله الرحمن الرحيم

🅿️4
📝 Farrah ita ce bata farka da ga baccin daya dauketa ba sai misalin karfe 1:35,tayi mamakin yanda tayi nisa a baccin.

Plant shues ta saka a kafarata ta nufi kicin da sauri danta dora girkin rana.

Momy ta tadda a kiching din harta dora.

"Momy ai dakin tasheni na dora"

"Karki damu Farrah na leka naga kinyi bacci,nasan akwai gajiya saboda dazu kinsha aiki".

"Tau Momynah shiyasa nake Kara kaunarki"

"Hmmmm ja'ira kawai haka kike so daman, je kiyi sallah sai kizo mu karasa aikin".

A bangaran Yasir kuwa, shi ne bai dawo gida ba sai wuraren karfe takwas na dare.saboda Yana fitowa da ga Goruba road cikin unguwar kwado ya tsaya wurin freind dinshi Jamil, saida yayi sallar isha'i kafin ya nufo Barhim.

Saboda haryanzu yanaji zuciyarashi tanayimashi zafi,abubuwa sun taru sunyimashi yawa.ga furucin da Abbah yayimashi haryanzu Yana yimashi yawo a kwakwalwarshi.

Yana karsowa gidan direct part dinshi ya wuce danya dan watsa ruwa ya rage kayan jikinshi.

_________________
Farrah ce da Momy a falo suna kallan tashar zeeword ana film din zarah nikah,na Kabir da zarah ita dai tana San wannan series din sosai saboda masoyan suna birgeta.

Ta ce "Dan Allah kiyima Yaya Yasir magana ya maidoman da key din motana,saboda kinga offer week zamu koma school".

"To zanyimashi magana insha Allah kafin ya tafi"

"To amma Momy...............

Daddadan kanshin turaren da dogon hancinta ya jiyo,shiya hanata karasa maganar dake bakinta.

Da sauri ta zabura zata ruga daki,Momy tayi saurin riketa ta zaunar da ita akan kujerar .

Sallamar ya karayi a karo na biyu Yana kokarin zama Kan kafet din da yayima falon kawanya .

Momy ta amsa sallamar tana kallan yadda duk yayi wani sanyi kamar ba Yasir din da ta sani ba jarimin maza.

"Momy barka da dare"

Muryarshi ta dawo da ita da ga Dan gajeran tunanin da ta tafi.

"Yauwa magaji yaka baro su Umman Jabir"?

"Suna lafiya sunce suna gaisheki".

"To muna amsawa"

"Ke tashi ki kawoma yayanki abincinshi,Dan naga ba sasai ya fiye San zaman dinning na".
Cewar Momy tana kallan Farrah da take ta faman wur-wurga idanu, saboda yanda take jin bugun zuciyarta na karuwa da duk dakika guda na karuwar numfashinta.

Kokarin tashi takeyi amma ta kasa,saboda irin kallan da taga Yana jifanta da shi ta kasan idonsa.

Kananun kayane a jikinta bakin wandon juens da yar karamar riga yellow colour mai gajeran hannu ,domin kuwa ana hangen kyakkyawan damtsen hannunta.ta dora black cap mai kyau gashin kanta ya fito ta kasan hular zuwa bayanta Baki mai santsi .

In Ina ta farayi alamar Bata da gaskiya.

"Ehmm in wallahi mantawa nayi in saka hijaf,nazo daukan abu ne a kiching".

Ta nufi dakinta da sauri Dan kada ya tsaidata.

Shi dai baicemata komai ba harta shige, sai kallo daya bita da shi Yana girgiza kai.

Kallanshi ya mayar ga Momy kamar mai Shirin yin kuka.

Da ido Tayimashi alamar yayi hakuri.

"Yi hakuri magaji na gane matsalarka ,idan Allah ya kaddara Farrah matarka ce to insha Allah komai zai dai

Ya ce" afuwan UMMANA"Yana hade hannuwanshi wuri daya alamar ban hakuri .

"Idan Allah ya nufa Farrah zata zama mata a gareka komai zai daidaita insha Allah".

"Amma sai kabi komai a hankali wannan takuramatan da kakeyi ba shi ne mafita ba".

Addu"ar mu take bukata, saboda haryanzu akwai yarinta tattare da ita.A wannan zamanin takurawa, ko yawan tsangwama da fada ba shi ke gyara tarbiyar yara ba,musamman yanmata,addu'a da nasiha sune kadai mafita.

Ta dora da "Amma Ina tabbatarma saika cire kokwanto da take sanyaka wasi-wasi a zuciyarkadomin Ina jiyemaka wata rana da zakayi nadama,domin kuwa ita yarinya ce amma duk abinda kake nunamata Yana zaunawa a zuciyarta".

Ta Mike hadi da cewa"nidai na fadama gaskiya".

Kara sadda kanshi kasa yayi,saboda TSANANIN kunyar Momy da ta Kara kamshi .
Kara muskudawa yayi saboda wata zufa da take ketomashi,hadi da daduwar bugun zuciyarshi.

A hankali ya nisa tare da Sanya hannunshi na dama mai daure da hadaddiyar agogon silver irin na kamfanim gucci, bisa kyakkyawan bakin sajenshi Wanda yammatan wannan zamanin suke ce ma quater million Yana shafawa,a hankali ya bude bakinshi kamar Wanda bayasan yin magana.

Ya ce "Afuwan Momy wallahi zuciyata ce ta kasa nutsuwa,Amma Ina ta addu'ar Allah ya kawoman nafita"

"Amin ya Allah "cewar Momy tana kokarin shiga daji.

"Ka je ka ci abincindan kasan tunda ta shige daki bazata Kara fitowa ba".

A hankali ya Mike saboda gaba daya jijiyoyin jikinshi sun gama yin sanyi.tunani yakeyi ya akayi Momy tasan wannan sirrin nashi da shi kadai yasani sai abokinshi Jamil.

Jiyayi abincinma bazai iya cinshi ba,Daman ya Dan ci dambun shinkafa da miyar alhasa a gidan su Jamil.

Dan haka kawai ya wuce part dinshi.

Yaga har kafe Tara da Yan mintina tayi.

~DAGA~ ~ALKALAMIN~ ~AUTAH~.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*FOR* *COMMENT*
*OR* *CORRECTION* *08162385196*..
[3/1, 6:29 AM] Hayat: ________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*🤦🏽‍♀️ZAMANINMU🤦🏽‍♀️.*
_(HATTARA YAMMATA)_

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

*Wannan littafi kirkirarran labari ne, Banyishi dan cin zarafin wani ko wata ba.Nayi ne dan fadakarwa, ilimintarwa tare da nishadantarwa.idan yayi daidai da rayuwarka/ki to arashi ne.*

__*GODIYA*__
INA GODIYA GA ALLAH (S W A) DAYA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTATI,ALLAH KARA DADIN TSIRA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S A W),DA ALAYENSA DA SAHABBAN AMEEN.

__~GARGADI~__
~BANYARDA~ ~WANI~ ~KO~ ~WATA~ ~YA~ ~JUYAMAN~ ~LITTAFI~ ~BA~ ~TARE~ ~DA~ ~AMINCEWA~ ~TA~ ~BA~, ~A~ ~KIYAYE.~

*SADAUKARWA*__
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GA MAHAIFANA,
*MALAMA* *AMINA* *IDRIS*
*MALAM* *IDRIS* *BALAH* *MAI* *GORO*
ALLAH YAYIMAKA RAHAMA AMEEN.

*Ina Mika godiyata gareki* *uwar room KHADIJAH ADAM IDRIS* *(shalelen kainuwa)Allah yabar zuminci ameen.*
*God bless you my Aunty.*

*INA* *JINJINAR* *BANGIRMA*
*AUNTY* *HAUWA* *TARE* *DA* *DOCTOR* *MARYAMA* *ALLAH* *YABAR* *ZUMINCI* 💋💋

*NOT* *EDITING* 🤗

بسم الله الرحمن الرحيم

🅿️3

📝 YASIR Yana isa G R A ya tadda su JABIR a falo suna kallo a system.

Yayi sallama
Bayan sun amsa,ya zauna suka gaisheshi.

Ya ce "Ina UMMAH"?

UMAR ya amsa da tana off-site dakin ABBA.

Saman ya haura Naga yabiyo ta wani hadaddan falo komai na falon kalar brown ne da milk.

Yayi sallama dai-dai UMMAH ta fito da ga dakin ABBA.

Kaman daman jiranshi takeyi ya ta fara fada,baka sati 2 baka zo garinnan ba Kai ba mata ka aje a garin ba,Amma baka iya zama kayi aikinka.

Kamo hannunta yayi ya ce "Haba UMMANA kiyi hakuri mu gaisa Mana"

Bayan ta zauna kan daya daga cikin kujerun dake falo,kannan ya samu damar zama kasan kafet din ya tankwashe kafafunshi Yana kallanta .

Ya ce" afuwan UMMANA"Yana hade hannuwanshi wuri daya alamar ban hakuri .

Shafa kanshi tayi ta ce"Allah ya albarkaci rayuwarka da sauran yan'uwanka.

Ameen UMMAN MU Allah ya karamaku nisan kwana.

Amen Amma kasan me zakayi dan kaga farincikina .

Tau UMMAH kuyi hakuri adan karaman lokaci insha Allah komai zai daidata.

Tau Allah yarda ka jira ABBANKU ya fito ku gaisa .

Dai dai ta fita da ga falon ya amsa da "To".

Jima kadan ABBAH ya fito ya gaisheshi cikin girmamawa.

Ya amsa cikin sakin fuska.

Ya Kara da ce wa duk naji irin maganar da kukayi da UMMANKU,karka damu MAGAJI na gano matsalarka Amma Insha Allahu komai ya zo karshe.tashi ka tafi ni zan fita cikin gari.

Haka ya tashi sororo kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki.

Yayima su UMMAH da kannanshi jabir da umar sallama ya nufi BARHIM.

______________

__ASALINSU_

Asalin iyayensu haifaffun garin DUTSIMMA ne daya da cikin local government din jahar KATSINA STATE. Sunan mahaifinsu Alhaji UMAR HASHIM UMAR.

A wannan lokacin Alhaji UMAR HASHIM UMAR duka iyayenshi sun rasu Yana zaunene a hannun Kanan mahaifinshi wato Alhaji YUSUF UMAR matar shi ta rike Alhaji UMAR HASHIM UMAR,Anan yayi dukkanin karatunshi tunda ga matsayin primary School aka kaishi bording school BINDAWA. Bayan ya gama Alhaji YUSUF HASHIM ya hadashi da Yan uwanshi guda biyu ya kaisu B U K KANO anan kowanne ya kammala digreen shi na farko.bayan sun dawo gida kowanne aka bashi kasuwancinshi a hannu shi Alhaji UMAR HASHIM UMAR aka budemashi shago a cikin centeral market cikin garin katsinan dukko shida Dan Alhaji YUSUF din ya kamamasu gida a katsina a cikin unguwar kofar dirbi sukaci gaba da harkokin kasuwancinsu.

Daman shi Alhaji UMAR HASHIM UMAR shi kadai iyayenshi suka haifa a wannan lokacin.

Cikin ikon Allah business dinsu ya bunkasa musamman shi Alhaji UMAR HASHIM UMAR saboda an hadamashi da dukiyar da iyayenshi suka barmashi bayan sun rasu.

A bangare daya Kuma Yana soyayya da masoyiyarshi wato HINDATU itama haifafiyar garin DUTSIMMA ce babanta Yana koyarwa a G. D .S.S DUTSIMMA .

_BAYAN_ _SHEKARA_ _DAYA_

Saida Alhaji umar ya tabbatar sun mayar da hankalinsu akan business dinsu kafin ya fara yimasu maganar aure.inda Alhaji UMAR HASHIM UMAR ya gabatar da HINDATU shi Kuma Dan uwanshi Abdullahi ya yadu da wata nutsasiyar yarinya HAUWA'U a anan unguwar filin samji.

Cikin ikon Allah ba'a dauki lokaci ba akayi aurensu inda aka siyanmasu gidaje anan cikin KASTINA .

_BAYAN_ _AURANSU_ _DA_ _SHEKARA_ _26__

A lokacin Alhaji UMAR HASHIM UMAR ya Kara zama babban mutum Yana da yara guda 3 USMAN, BISHIR, sai auta SAFIYYA.

Daga su haihuwa ta tsayamasu.

Hajiya HINDATU ta Kara zama babbar mace tana rayuwa da yaranta guda uku cikin jindadi da annashuwa.

Alhaji ABDULLAHI shima Yana zaune da matar shi HAUWA'U lafiya da yaransu biyar IBRAHIM shi ne babba sai mai bimasa YUSUF wato sunan mahifin Alhaji ABDULLAHI kenan.sai UBAIDULLAH,FATIMA da karamarsu BILKISU.

A lokacin USMAN Yana da shekara 25, BISHIR nada 22,sau autarsu SAFIYYA tana da 18 years.

Inda USMAN yake Aji karshe A B U ZARIYA Yana karanta LAWYER saboda ya ce gwmma ya sauya course saboda Babanshi BUSINESS ADMINISTRATION ya karanta.

Shiko BISHIR Yana aji 2 inda shi ya gaji mahaifinshi yake karantar business administration.

Itakuwa Autah little
SAFIYYA a wannan lokacin tana S S THREE bording school din AJIWA local government
Chapter 3 · 0% Book details